Mahaifin Bobbo (wato Mal. Jaɓɓo) ne ya shigo riƙe da wata jaka a hannunshi. Mamaki ne ya dabaibaye shi lokacin da ya ga gidan shi cike da mutane, da sauri Mamma ta aje dakan furar da take yi ta tarbe shi cikin far’a tana faɗin “Maraba da Ƴan tafiya”, “yauwa sannunki da ƙoƙari “yayi maganar cikin sakin fuska, idan ka ga mahaifin Bobbo zaka ga tsantsar kamar da suke yi da Ibrahim Bobbo kamar a tsaga kara. Ɗaki ya shiga, yayin da Mamma ta shigo mishi da jakarshi ciki.
“Ya na ga gidan ya cika da mutane lafiya dai ko?” Mal. Jaɓɓo ya jefi Mamma da zancen lokacin da take shirin fita.
Juyowa tayi ta ce “Mairo ce ta haihu”.
“To, to Madalla, me aka samu? ” ya tambaya.
“Ɗa namiji Ibrahim” ta amsa mishi.
Mal. Jaɓɓo yayi murmushi ya ce “miskilin ɗana kenan. To Allah ya raya shi, halin mahaifinshi ya bi shi.”
“A’a wallahi, wa yake burin hali irin na Bobbo, yaro sai taurin kai yadda ka san ɗan tauri.” Mamma ta faɗa.
“In banda ke da abunki minene aibun Ibrahim, haka kawai kin sa min yaro gaba ” ya faɗa.
Mamma ta ce “ai kai baka taɓa ganin baƙin Bobbo, kullum yabon shi kake yi, bari in kawo maka ruwa ni kam.”
Bata jira mai zai ce ba ta fita tana jinini.
*****
“Yau ce ranar da za a yi ɓarin ruwan bala’i biyu, na fi so mu ƙarar da rijiyar bala’i biyu kowa ya hutu, wallahi sai na ɗau fansar ran Barhim da aka ɗauke, Rai akan rai ” Sarki Banoto yayi maganar da ƙarfi dai-dai lokacin da yake jawo ruwa daga rijiyar bala’i biyu.
“ku yi ma garin Zawatu dirar mikiya, ku hanasu zama lafiya” ya faɗa yana kallon ruwan.
*****
Firgigit Naheela ta tashi tare da furta “ina, ƙaryar duk wani ɗan Mubanuwa da garin baki ɗaya, ba mai wannan ƙarfin ikon ” ta kai ƙarshen maganar wata mahaukaciyar wuƙa mai kaifin gaske ta fito daga tsakan goshinta.
Wani irin haske ne ke fita daga idonta zuwa ga wuƙar, yayin da take magana “binaf da gaggawa nake so kiyi ambaliyar ruwan bala’i biyu a garin Mubanuwa”.
Wuƙar (binaf) dake shillo gaban Naheela ce ta cira sama, shuuuuu ta dinga bin bango. Tana fita ta rikiɗa ta zama macijiya mai kai uku, nan take ta ɓace ɓat sai garin Mubanuwa, ruwan da ke cikin ƙwaryar da Sarki Banoto ya ɗiba ta yi ɓari da su, yayinda ta fara hura ruwan da ke malala ƙasa (wato ruwan bala’i biyu) nan take ruwan suke gauraye garin Mubanuwa da kewaye.
Cikin mintuna da basu wuce talatin ba Wuta ta kama ko ina na garin ya fara ci da wuta bal-bal-bal.
Sarki Banoto yayi wata irin ƙara ya cira sama, sannan ya ɓace ɓat. Cikin garin Zawatu ya dira.
Tun kafin ya shigo cikin garin an sanar da Naheela zuwan shi saboda haka ta shirya kai mishi hari.
*****
Bobbo bai dawo gida ba sai bayan isha’i. Mal. Jaɓɓo da sauran ƴan gidan duk suna zaune suna cin tuwo.
Yaran dake zaune kan ɗayar tabarmar suka tashi da gudu suka rungume Bobbo “sannu da zuwa Bobbonmu” kansu ya shafa da ɗaɗɗaya yana amsa musu, sannan ya nufi su Mamma.
“Ina wuni Abba ” BOBBO ya faɗa, “lafiya lau Bobbon Abba ya kake ina fatan komai lafiya”, “Alhamdulillahi “ya faɗa, Sannan ya kalli Mamma ya ce “ina wuni Mamma”.
“Lafiya lau Bobbonmu “ta faɗa.
Sai da ya gama gaisawa da kowa sannan ya tashi zai wuce, Mal. Jaɓɓo ya ce “ga wannan ka sha da safe, kasha da rana, da daddare ma kasha” ya faɗa yana Miƙa mishi wani galam, karɓa yayi ba tare da yayi gardama ba.
“Mahaifiyarka ta faɗa min abunda ya faru, kayi haƙuri na san ba abu bane mai sauƙi gare ka, Allah zai yaye maka, wannan maganin ni na Haɗa shi da kaina ka sha dan Allah kar kayi wasa da shi “.
“In sha Allah” Bobbo ya faɗa yana tashi tsaye.
“Allah ya maka albarka ” Mal. Jaɓɓo ya faɗa.
“Ameen” ya amsa tare da wuce ya nufi ɗakin Mairo.
Kwance ya same ta tana ba jaririn nono, tana jin ya shigo ta rufe idonta. Duƙawa yayi kaɗan ya sumbaci jaririn, tare sha mishi kanshi. Sannan ya cire rigar jikinshi ya rataye a ƙofa, ya dawo ya kwanta ƙasa yana tunanin rayuwa irin wadda yake yi.