Da ƙarfin tsiya NAHEELA ta cira sama ta saki fuka-fukanta, sai da tayi sama sosai, sannan ta walƙata gangar jikinta na kallon ƙasa, sannan ta buɗe baƙin wani baƙin hayaƙi ya dinga fita yayin da Idonta ke fitar da wuta mai matuƙar zafi, “Zamzila! ” ta kira sunan ƙaramar macijiyarta.
Wutar da Naheela ke fitarwa Sarki Banoto take tunkara, da sauri ya sauke hannunshi ƙasa ya ɗaga ƙafarshi sama, ya fara juyi da hannunshi kamar yadda fanke ke, ‘wul wul wul’ ya dinga juyawa wani haske na fita.
Da gudun bala’i Zamzila ya nufo Sarki Banoto, yayin da Naheela ta ƙara ware ido wani haske ys haske Zamzila, take ya ƙara jin wani ƙarfi ya ƙara gudu, sarki Banoto yayi saurin juyawa ya fara mulmula cikin ƙasa ƙura na tashi, Zamzila kuma bai fasa bin ƙasa.
Wata kibiya ce ta nufi Zamzila ba tare da an ankara ba ta cake Zamzila, nan take gimbiya Naheela ta diro daga sama, dib! Kake ji ƙarar saukar ta, wanda haka ya ba duwatsu damar ɗagawa. Da sauri sarki Banoto ya tunkaro Naheela da a lokacin ba abunda take gani sai rayuwa macijin tsafinta.
Shuuuuuu! Mashi ya nufi Naheela zai cake ta, da sauri ta duƙe ya bi ta Saman kanta ya wuce, wani mashin sarkin Banoto ya sako mata ta ƙare duƙewa, haka ya ci gaba da aiko mata mashi tana kauce musu har ta samu ta isa gaban Zamzila da yake fitar jini a jikinsa, da ƙarfi ta miƙe hannunta zuwa saitin jikin Zamzila ta fara fitar da wata wuta mai matuƙar haske.
“Zamzila! “ta ambaci sunanshi da ƙarfi tana buɗe baki, wasu duwatsu suka riƙa fita a bakinta har gudu sha ɗaya, suna sakin wata danja fari da ja, daidai lokacin Sarki Banoto yayi saitin wani dogon mashi, cak! Wannan mashin ya cake gefen cikin Naheela.
*****
Zumbur Sarki Zawatunduma ya miƙe tsaye daga kan kujerar da yake yana faɗin “ina gimbiyata tafi ƙarfin azzalumi.”
“Me ya faru yallaɓai” Wani bafade ya faɗa.
Ba tare da ya amsa shi ba ya fito waje.
Hannunshi ya naɗe wuri ɗaya ya buɗe su da ƙarfi sai ga wani ƙaton tsuntsu gabanshi.
“Bilbil ka kai ni inda gimbiya take ” sarki Zawatunduma ya faɗa.
Tsuntsun da sarkin teku ya kira da Bilbil ya kwanta sarki ya hau kanshi, nan take ya cira sama da ƙarfi.
*****
“BOBBO!” ya ji ana ta fama kwaɗa mishi kira, juyawa yayi yana kallon mai kiranshi har ta ƙaraso gabanshi tana mishi murmushi.
Fuskarta bata wani bayyana da kai ba domin kuwa dishi-dishi yake ganinta.
“Wacece ke?” ya tambaya .
“Taka ɓangaren!” ta bashi amsa
“Ɓangarena? ” ya sake tambaya
“Eh kai ne Nawa ɓangaren?” ta amsa.
Ido ya ƙura mata yana son ganin Fuskarta amma ina duhu ya lulluɓe ta fuskarta ba a iya gane wacece.
“Wace ce ke? ” ya sake tambaya
“Ɓangarenka ce ni ” ta amsa.
“Na ce miki wace ce ke! ” yayi maganar da ƙarfi.
Da mamakinshi sai yarinyar ta juya ta fara tafiya ba tare da ta amsa mishi ba.
“Ya za ta ce min ita ce ɓangarena, NAWA ƁANGAREN kamar ya?” ya faɗa yana Bin ta da kallo.
Tafiyarta take yi ba tare da ta juyo ba har ta sha kwana.
Firgigit ya farka daga barci da yake yi wanda ya so ganin wacece wannan yarinyar a mafarkinshi.
Mamma ce ta hankaɗa labubulan ɗakin “Bobbonmu ka fito daga wannan ɗakin haka ka zo ka ci abinci ya fara yin sanyi ” ta faɗa.
“Na Ƙoshi Mamma” ya amsa mata yana goge zufar da yayi da manunin farcenshi.
“Ban gane ka Ƙoshi ba, dallah can ta so maza wallahi kar in saɓa maka ” ta faɗa cikin ɗaya murya.
“Mamma wallahi kaina ciwo yake min bazan iya cin komai ba” ya faɗa yana lumshe ido.
Riƙe haɓa mamma tayi ta ce “ to bari na turo Indo ta kawo maka fura da jiƙo ka sha na san kan zai rage “.
Gaɗa kai yayi yana mayar da kan ya jingina da bango a hankali ya ce “NAWA ƁANGAREN” sai kuma ya dafe kai yana jin kamar zai faɗo ƙasa tsabar ciwo.
Ba a yi minti uku ba wata yarinya ta shigo da ƙwarya hannunta da Alama ita ce Indo ta ce “Babbonmu wai Mamma ta ce a kawo maka “hannun kawai ya iya ɗaga mata alamar ta tafi.
Abun ka da ɗa da mahaifi sai ta matso kusa da shi ta ce “Bobbo baka lafiya ne?” girgiza kai yayi ya ce “a’a barci na tashi bai ishe ni ba “.
“To ka sha furar zaka daina jin barci” ta faɗa tana jawo ƙwaryar furar gabanshi.
“Bana so na sha Aisha ” ya faɗa yana shafa kanta.
“Bari in sha maka kada Mammanka ta maka faɗa” ta faɗa tana buɗe furar.
Jawo ta yayi ya rungume yana jin tausayinta, zai iya tuna ranar da Umman Aisha ta bar mai ita tana cikin zane ko kwana 20 bata yi a duniya ba ga shi yanzu har tayi shekara 8 duniya.
A hankali ya ce “Mamma ba za ta min faɗa ba, ki je kiyi wasa “.
Ɗagowa tayi tana gaɗa kai, sannan ta tashi ta bar ɗakin.
Mamma da kanta ta shigo ta bashi jiƙon da ta dafa mishi, sannan ya sha fura ya kwanta dan yanzu sanyi yake ji sosai, mamma ta ce “Allah ya yaye maka wannan rayuwa ta wahala ina dalili”.
“Ameen ya rabbi ” ya faɗa.