Duka ƙarfinta take sakar ma Naheela amma ina, jikin Naheela ya rikiɗe ya koma fari tas kamar farin takarda, dai-dai lokacin sarki Zawatunduma ya diro dab, ƙasa ta tsage wani haske ya ɓullo mai matuƙar kaifi shaaaaaaa ko ina na wurin ya ƙara haske banda cikin garin Zawatu.
Cikin garin Zawatu kuwa duk wani aljani da ya mallaki gida a cikin gari ya ruguje, duk sun fito waje kowa yana tunanin yadda zata kasance da da shi, idan dai har ta tabbata Naheela ta mutu sun san basu da zaman lafiya har abada.
Ɓangaren Naheel kuwa wani mahaukacin zafi Yake ji a zuciyarshi da ilahirin jikinshi kamar ana zuba mishi ruwan zafi, da sauri ya miƙe tsaye tare da buɗe tafukan hannunshi guda biyu ya ware su “A ci ba a sayar ba, kwai ya fi doki, waya isa ya ja da mu, har wani ya isa ya kawo mana hari a garin Zawatu kuma a zauna lafiya ” ya faɗa, sannan ya juyar da Hannayenshi da ƙarfi ya ƙara juyar da su, sannan ya miƙe babban farcenshi tare da faɗin “Baharadi!”, nan take kukan wani Tsuntsu ya karaɗe daƙin, da alama shi ne Baharadi.
“Kana ji kana gani ka bari Banoto ya zo Zawatu, maza da gaggawa ka dira garin Mubanuwa ka hargitsa su, ka janyo musu hasara” ya faɗa.
Nan take tsuntsun nan ya tashi sama.
“Barhana ” ya faɗa yana ɗaga farcenshi sama, sai ga wata ƙatuwar tsuntsuwa girmanta ya ɗara na doki.
“Kai ni ga Gimbiya Naheela, mu je kina fitar da jin bakinki” ya faɗa, tare da yin ƙasa da hannunshi.
Cak ya ji yayi sama, ya hau kan Barhana, wani ƙarfe ya fitar daga farcenshi, ya ɗaga shi dai-dai saitin Rufin ɗakinshi, nan take ɗakin ya buɗe, tsuntsuwar ta tashi sama bakinta buɗe.
Jini ya dinga zuba daga bakinta, nan take aka fara ambaliyar jini a garin Zawatu, ran ɗan sarki ya ɓaci dole kowa ya san da ɓacin ran Naheel. Dan Naheel mugun aljani ne.
*****
“Naheela!, Naheela!, Naheelaaaaaa! ” Sarki Zawatunduma ya faɗa da ƙarfin tsiya.
Sarki duk ya rikice ya rasa ta ina zai fara, da ƙarfin tsiya ya fara magana “ na rantse da Allah sarki mai sama, wanda yayi ni yayi kowa da kowa garin sai garin Mubanuwa sai ya zama labari babu mahaluƙin da ya isa ya rayuwa ko kuma ya zauna in dai garin Mubanuwa ne, garin Mubanuwa sai ya zama guba ga duk wanda ya tunkari garin, rayuwa duk wani ɗan Mubanuwa fansar rayuwarki Naheela”.
Hannayenshi guda biyu ya ɗaga sama da ƙarfin gaske, ya ce “Sukam kayi ɓarin manyan duwatsu cikin garin Mubanuwa “.
*****
Babbo duk ya zare saboda duk inda ya tafi sai ya riƙa ganin ana rubuta NAWA ƁANGAREN a bango. Tafiya yake yi hanyar da dawowa daga kasuwa ya ɗaga kanshi ya kalli wani doki fari ƙal da shi, da wani rubutu a kai da ya gagara karantawa, ci gaba da tafiya yayi yana tunkaro dokin.
NAWA ƁANGAREN ya ga an rubuta jikin dokin da sauri ya kawar da kanshi, yana faɗin “innalillahi wa’inna ilaihir raju’un”, kallon inda dokin yake amma da mamakinshi dokin yayi tafiyarshi, juyawa yayi sai ya hangi dokin na gudu kamar zai tashi Sama, juyar da kanshi yayi.
“Da alama na fara zarewa ” ya faɗa, sannan ya ci gaba.
“Mairo Kin cika taurin kai wallahi, miye amfanin rashin ba ƙaramin Sadauki nono” Mamma ta faɗa tana girgiza Sadauki dake faman kuka.
“Abin cikin kwai, ya fi kwai dadi, me zai hana ku bashi madarar Shanu ” Mairo ta faɗa.
Mamma ta riƙe haɓa, tana faɗin “Abin mamaki! Kare da tallan tsire, in bada abun ki ina aka taɓa ba yaro madarar shanu bayan yana da abincinshi, a rashin uwa ne ake yin ta ɗaki.”
Mairo da ta turo ɗan kwali gaban kanta ta ce “to ni dai bazan bada ba, ya je yayi uwar ɗakin.”
Mamma ta ce “ ba komai ɗan kuka mai ja ma uwarshi zagi, yanzu in ba dan Bobbo ko an ce ki min rashin kunya ai ba za ki yi min ba.” tana gama maganar ta bar ɗakin tare da Sadauki.
Dai-dai lokacin Bobbo ya shigo cikin gidan, turus ya tsaya yana kallon Mamma.
“Yauwa Alhamdulillahi, faɗuwa ta zo daidau da zama tunda gaka ka zo ai sai ka ji da ɗan ka ni bani da abun ba shi.” ta faɗa.
Matsowa yayi kusa da Mamma ya ce “me ke faruwa ne?”
“Karɓi abunka sannan muyi magana.” ta faɗa tana miƙa mishi Sadauki da ke shan hannu.
Karɓar Sadauki yayi, yana kallon Mamma da tambaya a idonshi.
“Ga shi nan ka cire riga ka bashi nononka tunda uwarshi ta hana shi abinci, tun safe yake kuka, kai da ka ja mishi sai ka bashi ya ja naka” Mamma ta faɗa.
“Hhhhmm, Mamma kenan, ai namiji baya shayarwa ” ya faɗa.
Mere tayi ta ce “ ina na sani ko yau kanka za a fara.”
Murmushi yayi wanda ya fi kuka ciwo ya ce “ ba damuwa Mamma bari in je wurin shanu in tatso mishi madara ya sha.”
Mamma ta ce “to yayi kawo shi in riƙe maka.”
“Ba damuwa ai ni janyo mishi komai bari in je da shi sai in ba shi ya sha na gode ” ya faɗa yana juyawa da yaron.
*****
Ɓangaren da suke kiwo ya zagaya ya shiga ciki, Saman wani dakali ya ɗora yaron, sannan ya ɗauki wani kofi da suke tatsar madara da shi ya tatso madarar, sannan ya dawo ya ɗauki yaron.
Zama yayi tare da ɗora yaron kan cinyarshi ya ce “yi haƙuri mai sunan Manya, komai zai wuce, na san ban maka adalci ba da har na janyo aka maka horo da yunwa, amma wata rana sai ya zama labari insha Allah.”
Madarar ya dinga bashi yana sha, sosai tausayi ya kama shi, yadda yaron ke shan nono zai tabbatar maka da yunwa yake ji, kanshi ya ɗan sha, sannan ya manna shi a ƙirjinshi ya ce “kai ma kamar sauran yarana kake, ina fatan yanayin halittata kar ta cutar da ku, kar ku samu nakasu kamar ni.”