A gaggauce Ande Dije tayi kanta tana Kiran sunanta gami da jijjigata.
Dai dai lokacin mallam Umar yayi sallama ya shigo, ganin Hajara kwance akasa ko motsi batayi yasa cikin gigita ya karaso kanta, ayayinda Ande Dije take fadin ” Alhamdulillah gara da Ka dawo ummaru'” Yana taba Hajara yana tambayar Ande Dije ” meya sameta? Meya faru da ita “,
“Hakan nan naga ta yanke jiki ta Fadi, gashi nan ko numfashi naga batayi.”
Mallam umar ya Kara gigicewa , da sauri ya tashi yaje ya debo ruwa ya shiga watsa Mata Yana watsa Mata Yana Kiran sunanta.
Cikin sa’a Hajara taja dogon numfashi gami da kokarin Bude idanunta kadan ta kafe idonta Akan mijinta.
Mallam Umar ya numfasa yace ” sannu Hajara sannu” ta gyada Kai alamar yauwa tana kokarin tashi Amma duk yadda taso data motsa hannunta na hagu ta kasa.
“Yunkuro ki tashi” cewar mallam Umar, ta girgiza Kai tace ” hannuna kamar baa jikina yake ba baya motsawa”. Ande Dije ta dubeta sosai tace ” kamar yaya baya motsawa.”
Mallam Umar yasa hannu Yana Jan hannun Amma tamkar ba ajikinta yake ba yace ” kina Jin tabi ahannun” ta girgiza Kai tace “aah bana Jin komai.”
Hankalin Mallam Umar ya Kara tashi , da Kansa yasa hannu ya daga Hajara ya wuce da ita daki ya kwantar da ita Kan katifa, ya koma ya zauna Yana Jan hannunta Yana mikar dashi.
Ita Kam Ande Dije awaje ta noke bata bi su dakin ba.
Wani matsanancin ciwon Kai ke fisgar ta idanunta har hawaye suke yi saboda azaba.
Mallam Umar ya dubeta yace ” Bari naje na Kira mallam kasim ya taimaka min ya dubaki.”
Ya tashi da sauri ya fita , Kai tsaye gidan mallam kasim ya wuce, mallam kasim shine mutumin da yake taimakon jamaar kauyen idan Basu da lafiya domin yayi karatun asibiti shine Kuma yake tsaye domin ganin an Sami asibiti a kauyen hakan yasa da Kansa ya Bude Dan karamin asibitin da yakan duba marasa lafiya Wanda Kuma ciwon yafi karfinshi yakan Basu shawarar su wuce babban asibiti a jigawa.
Mallam Umar ya tadda mallam kasim Yana da marasa lafiyan da yake Kan dubasu bazai iya barinsu ya biyo Shi gida ba.
Hakan yasa ya bashi shawarar yaje ya taho da Hajara zuwa asibiti.
Komawarsa gidan Shi da Kansa ya gyara Hajara Ande Dije tana gani Amma ko dakin bata shiga ba ballefa ta taimaka masa wajen shiryata.
Sai da ya fita daker ya Samo mashin din da aka dauki Hajara zuwa asibiti.
Sosai Hajara ke cikin zafin ciwo nan da nan harta rame, bakinta ya bushe, kwata kwata jikinta babu dadi.
Sai da likita kasim ya Gama duba marasa lafiyan da suka cika gabansa , sannan ya dawo Kan Hajara.
Gwajin farko ya tabbatar masa da cewa jinin Hajara yayi mummunar hawa Wanda shiya Haddasa Mata ciwon Kai da Kuma ràshin aikin hannunta.
Ya dubi mallam Umar sosai yace ” Amma mallam Umar meke faruwa da me dakinka da ta Sami hawan jini, domin dai KO yanzu jininta ya hau sosai Kuma wannan faduwar da tayi Allah ne ya rufa asiri Amma da akwai yuwuwar ta Sami mutuwar barin jiki gaba daya.”
Mallam Umar ya numfasa cike da damuwa yace ” to yanzu likita hannun da baya aiki ya zaayi dashi, sannan wane irin taimako zaka bata akan ciwon hawan jinin.”
Likita kasim yace ” hannu akwai sa ran zai dawo dai dai zai cigaba da aiki, Zan rubuta magungunan da zatayi amfani dasu “. Ya Kara kallonsa yace ” Amma abu mafi muhimmanci shine kusan damuwarta da abinda yake sata damuwar domin yaki da hakan domin kuwa duk maganin da zata sha idan bata Sami kwanciyar hankali ba babu amfanin da zaiyi Mata ajiki.”
Mallam Umar ya nisa , damuwar Hajara Kam Baisan ta yadda zai magance ta ba, hawan jini Kuma Shi Kansa ya San ya cancanta Hajara ta samu don ma macece me juriya da dakewa, Amma kalubalen rayuwar da ta shiga da Wanda take ciki idan ma ciwon zuciya ne to ya ci ace ta samu.
Likita kasim ya Gama rubutu ya Mika masa takarda yace ” ayi kokari asayi maganin Tasha bayan mako daya ta dawo, insha’Allah hannun zai dawo aiki, zakuma ta Sami saukin ciwon kan, sannan ta rage damuwa”, yace ” insha’Allah nagode.”
Daganan suka bar asibitin.har suka Kai gida mallam Umar cikin tunani yake, shin Allah ba zai kamashi ba da kasa kulawa da Hajara da yayi ? Babu wani farinciki data taba samu tunda ta aureshi tsawon wadannan shekarun Hajara tana rayuwa ne kawai saboda Allah bai yanke numfashinta a doron kasa ba.amma babu wani dadin rayuwa da take ji.
Sun koma gida suka tadda muhseena ta dawo Wanda tunda ta dawo daga tallan ta tambayi Ande Dije inda mahaifiyarta taje ta gaya Mata komai, tun lokacin ta koma bakin Kofa ta zauna tana kuka Wanda Sam Ande Dije bata bi ta kanta ba,
Tare da muhseena Mallam Umar yabar Hajara ya fice domin ya Nemo kudin da zai sayo Mata magani, domin dai kwata kwata abinda ke aljihunsa bai wuce dari biyar ba.
Kemis din saida magunguna Wanda duk kauyen Durmi Shi kadaine, Mallam Umar yaje me kemis din ya lissafa maganin na nera dubu shida da Dari biyu shima din akwai guda daya da baa Samu ba.
Mallam Umar yayi shuru ya rasa inda zaisa Kansa tunaninsa daya shine ina zaije ya samo kudin.
Asanyaye ya dubi me kyamis din yace ” Hassan da zaka taimaka min Ka Bani magungunan nan, insha’Allah bazan Maka wasa da kudi ba Ina samu Zan kawo maka , me dakina ce bata da lafiya tana Kuma bukatar maganin nan da gaggawa, ni Kuma Bani da kudin.”
Hassan ya dubeshi yace ” gaskiya mallam Umar na rufe bada bashi, saboda nema ake a karya ni, sakamakon wannan matsatsi da talauci da kunci da ake ciki mutane na cikin masifa ga ràshin lafiya hakan yasa kowa sai dai yazo ya ci bashi Kuma basa iya biya , to kaga idan na cigaba da bada bashi bazan Kai labari ba.”
Mallam Umar ya Matso sosai wajen Kantar yace ” nasan haka Hassan,Amma Ka sani bazan taba yi maka wasa da kudi ba da zaran na Samu Zan kawo maka, nasan kana kokari kana Kuma rufama mutane da yawa asiri don haka nima don Allah Ka taimaka min yau Ka rufa min wannan asirin don Allah.”
Hassan yayi dan Jim sannan yace ” gaskiya Mallam Umar don dai Ka cika min Ido ne, Kuma nima idan na hanaka nasan bazan taba Samun nutsuwa ba shiyasa kawai Zan baka.”
Cikin fara’a yace ” Amma nagode Allah ya saka maka da alheri , Allah yasa kafi haka”.
Yace ” Amin, amma don Allah Kada ayi wasa da zaran kasamu Ka kawo min” yace ” insha’Allah Kada kadamu Na gode.”
Daganan ya hada masa magungunan ya bashi ya amsa ya tafi.
Mujaheeda ta na kusa da mahaifiyarta tana mammatsa Mata hannun,gami da kokarin goge hawayenta.
Tace ” Inna duk arayuwata Bani da wani buri illa na jiyar da ke dadi na Kuma Zama me share hawayenki, tunda na taso ban taba ganinki cikin farinciki ba, Inna na so ace nayi karatun boko domin nasan tanan ne Zan iya cika burina” a hankali Hajara tace ” Kada ki damu ,ki sani duk yadda kika so da ki sanyani farinciki idan Allah bai so ba babu yadda zaayi hakan ya kasance, Shi yasa na dau kaddara ta nasama raina kila bani da rabon farinciki a duniya ne don haka nake adduar kullum Allah ya jiyar da ni farincikin lahira” .
“Amin ya Allah ubangiji Allah ya Sanya farinciki atare dake ya Kuma yi Miki tukuici da aljanna Firdausi abisa hakurin da kikayi da halin da ta saki a duniya”. Cewar Mallam Umar Yana kokarin shigowa dakin.
Kusa da katifar ya tsuguna Yana yi Mata sannu gami da fito da ledar maganin yace ” muhseena jeki ki debo ruwa ta samu tasha maganin.”
Da sauri ta Mike ta nufi wajen randar ruwan dake bayan kofa ta debo ruwan ta dawo da kamshi ya bare maganin ya bata Tasha.
Sannan ya cigaban da kallonta bayan ya maidata ta kwanta , a hankali ys kira sunanta
“Hajara” ta amsa cikin muryar da ciwo ya Fara galabaitarwa.
Mallam Umar yace ” bazan zargeki ba ba Kuma Zan Miki fada ba don damuwa tasa ciwon hawan jini yakama ki, domin baki da laifi” a gaggauce muhseena ta dubeshi sannan ta dubeta tace ” hawan jini?” Ya gyada Kai yace ” ciwon da ke damun mahaifiyarki kenan, Shi yasa nake son na roketa tayi hakuri ta cirema kanta damuwa domin duk abinda ke faruwa idan da sabo ya kamata ace kin Saba wata rana sai labari”.
Idanu kawai Hajara ta maida ta rufe , ta yaya zata daina damuwa bayan kullum Ande Dije Saita dawo Mata da hannun agogo baya, sannan ta yaya zata raba kanta da damuwa bayan gudan jinin. Yarta ta Kai munzalin aure Amma babu Wanda ke son ya aureta , babu Mai son ya hada zuria da ita.
Muhseena ta goge hawayenta tace ” don Allah Inna ki rufa min asiri ki daina damuwar komai kisa aranki duk abinda Allah yayi da bawansa dai dai ne.”
Hajara batayi magana ba har mallam Umar ya Gama yi Mata nasihohi ya tashi ya fita.
Kai tsaye labulen dakin Ande Dije ya daga ya shiga gami da sallama ta amsa masa tana zaune bakin gado , Kan yar tabarmar dake shimfida atsakar dakin ya zauna gami da aje Kansa a kasa.
Ande Dije ta dube Shi tace ” lafiya kazo Ka sani agaba kamar Mai daukar karatu wani abunne.”
Yadan muskuta ya gyara zamansa yace Ande nazo muyi wata magana neaiuhimmanci.”
Tace “toh ina jinka ya akayi”. Mallam Umar yace ” munje asibiti likita ya tabbatar mana da cewa Hajara tana da hawan jini.”
Ta aje idonta akansa tace ” to me Zan Mata don tana da hawan jini ko an gaya maka INA bada maganin hawan jini ne, tunda ita ba zata taba Zama lafiya a rayuwarta ba sai ta jefa mutane cikin masifa.”
Cike da son shawo kanta yace ” kusan ke ce kike da maganin hawan jinin nata, domin idan kika daure kika daina hantararta kika daina gsggaya Mata magana kika daina tsanarta tare da daukarta a matsayin ya to nayi Imani ba zaa Kara Samun hawan jini ajikinta ba.”
Ta saki tsaki tace ” in dai Saina dauketa a matsayin ya ne zata warke to taje tayi ta ciwonta tunda ita bata aje komai ba sai fitina.”
Yace ” don Allah don son Annabi ki sassauta ma Hajara da muhseena agidan nan.”
Cikin fusata ta nuna masa hanyar kofa tace,” tashi Ka fita shanyayyen Hajara ” zaiyi magana ta Kara dakatar dashi tace ” Kada Ka ce min komai tashi Ka fita kawai.”
A sanyaya mallam Umar ya tashi ya fita zuciyarsa na kuna shin yaya zaiyi? Ta ina zai shawo Kan matsalar tunda yasan Ande Dije ba zata taba bashi hadin Kai ba.