Skip to content
Part 26 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Hafsatu ta aje gauruwar ajiyar zuciya sannan ta lalubi kujera ta koma ta zauna tana cigaba da kallonsa, cikin shakewar murya tace, “Na dai gaya maka ba zaka iya aurenta ba saboda ba zamu yarda da ita a matsayin surukar mu ba, Kada ma Ka bari ko da wasa mallam yaji shi da yafi kowa burin Ka auro ya agidan dattako.”

Cikin matsananciyar damuwa Kabir yace ” mana idan ko dattako ake nema ina ganin idan aka Sami gidan Mallam Umar to an wuce wajen, haka zalika idan natsuwa da cancanta ake nema shima idan aka Sami muhseena an je matakin karshe.”

Ta girgiza kai tace ” hmmm babu abinda Ka sani a wañnan bangaren sai abinda idonka ya gani kawai Wanda Kuma yaudara ce kawai, babu wani dattako awannan gidan kamar yadda babu wani kamun Kai da nutsuwa da zaa samu awajen wannan yarinyar.”

Kan Kabir yayi nauyi zuciyarsa ta shiga tafasa Sam Sam bai son yadda ake aibata muhseena, ya Kara kallonta cikin Jan Ido yace ” aah mama babu yaudara acikin Kamala da nutsuwar muhseena na yarda da dabi’un ta sune Kuma suka ingizani wajen kaunarta adalilin hakan har na fara sha’awar yin aure.”

Hafsatu ta shiga girgiza Kai tana cewa ” kabar wannan maganar domin kuwa abinda kake so ba zai taba yuwuwa ba, don haka kayi gaggawar cire wannan maganar aranka, kaje Ka Samo wata yar gidan mutunci gasu nan da yawa.”

Ya runtse Ido ya bude Jin abin yake tamkar Yana mafarki domin bai taba tsammanin zai Sami matsala da iyayensa wajen auren muhseena ba.

Ya gyada Kai yace cikin murya Mai cike da ban tausayi ” na rantse Miki ina son muhseena so na hakika bansan yadda zanyi da Kaina ba matukar na rasata domin rashinta tamkar Rasa wani bangare ne na jikina.”

Hafsatu ta saki salati da karfi tana tafa hannayenta ” ni ko na shiga uku yaushe kayi zurfi a soyayyar yarinyar nan haka bayan ba zaka taba samunta ba domin dai matukar mune zamu fada aji to Baka Isa Ka auri wannan yarinyar ba.”

Cikin kaguwa Kabir yace ” wai mama Mai tayi da baza’a iya aurenta ba , meye laifinta?”. Tayi masa kallon tsaf tace ” bata da wani laifi , laifin mahaifiyarta shine ya shafeta” Kabir yace”

Aiko Allah baya kama bawa da laifin wani bawa face abinda bawan ya aikata da Kansa don haka babu dalilin da zaa hukunta muhseena da laifin mahaifiyarta” ya daga hannayensa biyu alamar roko yace” don haka don Allah mama na rokeki ki Goya min baya na auri muhseena”. Ta girgiza Kai tace ,” bazan iya Goya maka baya baya Ka aureta ba domin Ka godema Allah da ya kasance ni Ka Fara gayama wannan maganar ba mahaifinka ba domin da kasha mamaki.”

Kabir yayi ajiyar zuciya yace ” don Allah mama Mai mahaifiyar muhseena tayi da har zaiyi sanadiyyar da zaa hanani auren muhseena.”

Hafsatu tace ” nace kabar wannan maganar, kadai sa aranka babu aure tsakaninka da ita har abada.”

Kabir ya dafe Kansa da hannu biyu Yana fitar da wata boyayyiyar ajiyar zuciya baya Jin tunda yazo duniya ya taba riskar Kansa cikin tsananin tashin hankali da damuwa irin na yau , daker ya iya yunkurawa ya tashi Yana gauraye hanya ya fita daga dakin ba tare da ya Kara cewa komai ba. Hafsatu ta bi bayansa da kallo cike da tashin hankali bata taba tsammanin zata taba Jin wannan maganar daga bakin danta Wanda ta dora dukkan fata akansa, burinta da yawa ya cika ta hanyar dan’uwanta Alh Musa Wanda ya daukar Mata Kabir ya inganta rayuwarsa ta hanyar bashi ilimi da tarbiyya da Uwa uba aikin yi Wanda yaja ya Sami arziki shima tunda ya wuce da bukatun Shi da nasu duk abinda take so da ga ita har mahaifinsa mallam Hamza wanzami to fa zaiyi musu, to ta yaya bayan danta nagartacce ne zasu bari ya auri yar da bata da asali, ai idan ma sukayi haka lalle sun ci amanar dansu.

Ta zuba tagumi tana addu’ar Allah kada yasa wannan lamarin ya zama damuwa a tare dasu.

Shigar Kabir dakinsa ya fada kan gado ya kwanta rigingine gami da runtse idanunsa, hakanan yaji wasu siraaran hawaye suna fita daga idonsa.zarihi bazai iya rabuwa da muhseena ba Amma, zaiyi yaki har sai ya aureta , domin idan yace bazai aureta ba bai San inda muhseena zatasa kanta ba Kuma zafi da radadin da yake ji ayanzu baya son ko kadan Muhseena ta ji irinsa domin shi kadai yasan abinda yake ji ayanzu.

Domin har wani zazzabi yaji Yana neman ya kama Shi,baisan Yana son muhseena ba sai yau domin yadda yake Jin tamkar zaa cire masa rai.

******
Akalla yau Mujaheeda ta sami wajen kwanaki shida agidansu.taji sauki sosai, Amma duk yadda Taufiq ya so Mujaheeda ta dawo gidansa abin ya fassakara domin Haj Murjanatu ta hana wannan damar domin ta hana Mujaheeda komawa gidan mijinta ta Kuma ki yarda iyayensa su zo ayi magana kamar yadda taki sauraren Alh Mustapha labaran Akan komai.

Burinta daya Mujaheeda ta yarda ta amince mata a raba aurenta da Taufiq, amma har yanzu bata bata wannan damar ba sannan taji yin maganar da ita kawai ta gaya mata bata son tayi mata maganar Taufiq ta gaya mata ta bata dama harta sakko daga fushin data keyi tukuna. Hakan ne yaja ma Haj Murjanatu tsaikon aiwatar da abinda take so domin duk abinda Mujaheeda take so ta kuma ambata shi take yi.

Duk irin kiran wayar ta da Taufiq yake yi taki dagawa, sakonnin da yake turowa kuwa kullum ko dubasu batayi , domin tayi matukar daukar zafi dashi.

Tabangaren Alh jibrin kuwa burinsa ya cika ya hada fitina atsakanin Taufiq da Mujaheeda. Bata zuwa office hakan yasa ya koma shike aiwatar da komai kamar da shi da murtala suka cigaba daga inda suka tsaya tare da adduar Allah yasa sanadiyyar barin mujaheeda office din kenan Wanda hakanne zai Zama sanadiyyar Kara mallakar duk abinda ya rasa. Tun komawar mujaheeda gidà kusan kullum sai Alh jibrin yaje ya dubata agida.

Hakan yasa Mujaheeda ke kara Jin zafin Taufiq da har yake tsammanin wani abu zai iya shiga tsakaninta da mutumin data dauka tamkar babban yayanta, a shekaru kuwa tamkar mahaifinta domin tasan ya haifeta, Kai Taufiq ya zalunceta, ya ci amanar kauna da soyayyar da take masa.

Bayan har kasa ta nade bazata taba son wani mutum irin yadda take sonsa ba, domin tana sonsa fiye da komai arayuwarta Shi ne kadai mutumin da take jinsa har cikin bargon jikinta. Amma ta yaya zaace Taufiq bai yarda da ita ba yana zarginta anya Taufiq yana sonta kuwa? Tambayar da takema kanta kenan kullum.

Gaba daya Taufiq ya shiga damuwa ya rasa inda zai bulloma al’amarin, yaje wajen mahaifinsa yafi a kirga domin ya shiga cikin maganar amma ya ki.

Yauma Yana tsugune gabansa cikin damuwa, Haj saratu na gefen kujera a zaune yau dai itama cikin fushi take don haka ko maganar da take yi yanzu cikin fusata take.

“Wai meye kaifin Wanda yayi kuskure yasan yayi sannan ya bada hakuri, don me ba zaa yafe masa ba, Kuma duk Wanda ya turo wadannan hotunan shine babban shaidani Kuma Taufiq Yana dukkan damar dazai yi fushi, kuskurensa daya daya yanke hukunci cikin fushi wanda shine ya zama damuwa yanzu, amma don me zaa zauna ana gara yaro ana dora masa laifi.”

Alh Yusuf lamido ya tsareta da ido yace ” to wa zaa daurama lefin bayan shi saratu Kada kiso kanki fa, idan Shi Yana da tunani tun lokacin da aka turo hotunan zai gamsu da cewa duk Wanda ya turo rabuwarsu kawai yake so Shi da matarsa amma kishin banza da zato da zargi na wofi yasa ganin farko Ka aminta da mutumin da baka sani ba Ka Kuma zargi wacce Ka sani asalima abokiyar rayuwarka, to yanzu me kake so nayi?”

Haj saratu ta gyada Kai tace ” nasan haka ,Amma dai ai yakamata shima a amshi uzurinsa Kuma a dawo masa da matarsa.”

Taufiq ya amshe” bukatata kenan, Abba kasa Baki tunda daga mujaheeda har mahaifiyarta sunki saurarata shima Àlh da yake saurarata sunki saurarensa, akalla dai na fahimci nayi kuskure saboda haka ai yakamata ayi min Uzuri.”

Alh Yusuf lamido ya dubeshi sosai yace” kana tunanin banyi maganar bane nayi magana da Alh Mustapha labaran amma ya nuna Shi Kansa bazai iya tankwara Haj murjanatu ba don haka sai mu Jira har sai mujaheeda ta sakko tunda tana sonka zata nemeka amma mu bata lokaci bayan ta warke daga jinyar jikinta da Kuma jinyar abinda kayi Mata kila zata iya nemanka.”

Yayi kasa da Kansa Yana Jin shigar wata sabuwar damuwar.

Haj saratu tace ” yanzu ita Haj murjanatu babu wanda ya isa da ita Kenan abinda taga dama Shi zatayi a rayuwa, gaskiya idan ko hakane Akwai matsala, ace hatta mijinta bai isa da ita ba Kuma ahaka take son yarta itama ta dinga yin irin rayuwarta.”

Alh Yusuf lamido yace ” Shi yasa idan kasan halin mutum sai kaci maganin zama dashi , yakamata Shi ya toshe duk wata hanya da zaa iya samun damuwa tunda yasan halinsu, Kuma Allah ya kaddara auren nan to sai Shi yayi kokarin kawo gyara.”

Haj saratu ta tabe baki tace ” Ka Kara Kiran Àlh Mustapha gaskiya kuyi magana, shima fa Taufiq ba daga sheka ya fito ba shima Yana da uwar da take son ganin farincikinsa, idan Kai kana goyon bayan mujaheeda to ni goyon bayan dana nake.”

Ya dubeta yace ” kina ganin Bana goyon bayan Taufiq ne, to mujaheeda amanace agaremu ya Zama dole Kuma mu rike amana babu yadda zaayi mu wofintar da ita bayan tana da gaskiya.”

Haj saratu tace ” ummm ba zaka gane ba, yanzu dai Ka Kira Alh Mustapha Ka Kara masa magana.”

Ba tare da musu ba Alh Yusuf lamido ya fito da wayarsa ya Kira Alh Mustapha labaran bugu daya ya dauka. bayan sun gama gaisawa ne Alh Yusuf lamido yace , ” Alh Kan maganar yaran nan ne, yanzu haka zamu zauna amatsayin mu na manya ba zamu kawo karshen wannan matsalar ba, yakamata zuwa yanzu ace mujaheeda ta dawo dakin mijinta.”

Alh Mustapha labaran cike da damuwa yace “Nafi kowa son hakan, amma na rasa tunanin Haj akan hakan ko maganar taki yarda muyi balle ta saurareni, ita kanta mujaheeda ta tabbatar min ba zatayi magana ba har sai ta sauka da ga fushinta Wanda hakan yayi dai dai domin yanke hukunci cikin fushi shike kawo dana sani kamar yadda ya kawoma Taufiq ,”

Alh Yusuf lamido yace ” to yanzu meye abin yi Alh” ya nisa yace “hakuri za muyi mu Jira har zuwa lokacin da mujaheeda zata sakko, sai ayi koma meye, Kada Ku damu wannan auren in sha Allah babu abinda zai kashe Shi duk zasu gama fushin ne su sauka don nasan Mujaheeda tana son mijinta so na hakika ba kuma zata iya rabuwa dashi ba.”

Taufiq ya jidadin maganar Àlh Mustapha amma anya yanzu Mujaheeda tana yi masa son da take masa da?

Alh Yusuf lamido ya gyada kai yace ” shikenan Alh Allah yayi mana jagora” ya amsa da Ameen sannan sukayi sallama.
Ya dawo da kallonsa ga Haj saratu da Taufiq yace ” na kirashi kun Kuma ji abinda yace ko to duk sai mu cigaba da Jira.”

Haj saratu ta saki tsaki tace ” Kai Allah ya wadaran aure gidan karanta kai Kuma jarabawarka kenan, to Allah ya baka ikon cinye jarabawar” tana gama fadin haka ta tashi cike da takaici ta bar falon .
Yayinda Taufiq ya Kara Mike Kafa cike da damuwa.

Hakan yasa Alh Yusuf lamido ya cigaba da yi masa nasha musamman akan zamantakewar aure wanda hakuri da juriya da sadaukarwa sune ginshikinsa.

<< Nima Matarsa Ce 25Nima Matarsa Ce 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
1
Free daily stories remaining!
×