Washe gari Kabir haka ya tashi cikin matsananciyar damuwa, hatta karyawa ya kasa yi.
Hafsatu tana lura da irin yanayin da Kabir din yake ciki amma bata ce masa komai ba.
Ya kasa Samun karfin guiwar yin komai haka zalika tunanin yadda zai shawo Kan lamarin kawai yake yi. Soyayyar muhseena ta riga tayi matukar zurfi acikin zuciyarsa, Kuma ma ta yaya zai iya kallon muhseena da iyayenta ya iya gaya musu bazai iya auren ta ba.
Hakika Yana cikin matukar rudani Yana bukatar sanin gaskiyar lamarin.
Ko da Kabir yaje wajen muhseena ya kasa sakin jiki ko fuska kallo daya zakayi masa kasan akwai damuwa a tattare dashi. Muhseena ta gane hakan jikinta Kuma yayi sanyi zuciyarta cike da adduar Allah yasa ba maganar aurensu bane ta haifar da damuwa ga Kabir, don haka ta kafe Shi da Ido gami da yi masa tambayar ” lafiya kuwa, Naga gaba daya Ka canja idonka na bayyana damuwa da tashin hankali.”
Yayi saurin kallonta Yana kokarin boye abinda ke cikin idanunsa,yayi Dan murmushi sannan yace ” to hasashenki bai yi ba, domin dai ni babu wata damuwa dake damuna, balle tashin hankali”. Ta Kara masa kallon tsaf tace ” to menene matsalar?”
Ya gyada Kai Yana yi Mata wani kallo Mai cike da kauna , yace “tun jiya cikin dare wani irin zazzabi ya rufeni da ciwon Kai Mai tsanani.”
Nan da nan Muhseena ta gigice tana kallonsa cike da kulawa tace ” Amma shine Ka fito Ka taho cikin sanyin nan , haba Kabir”
Yace ” Shi yasa tun farko naki gaya Miki don nasan sai kinyi irin wannan maganar da kikayi.”
Ta numfasa tace “Amma akalla ko dai yayane ai yakamata Ka tsaya Ka Kula da lafiyarka, domin tafi komai muhimmanci agareni.”
Yace Yana kokarin rike kunnuwansa biyu da hannayensa, yace ” Na tuba ayafe min sarauniyata”. Yadda yayi shine ya bata dariya gaba daya suka fashe da dariya , tace ” to kasha magani?” Yace ” eh nasha Shi yasa na Sami karfin zuwa wajenki, saboda gobe lahadi nake son komawa Kano, don na so na zauna har litinin amma har an Fara Kirana na dawo gobe saboda akwai kayan da zaa sauke ma kamfani ranar litinin Kuma dole nine Zan karbi kayan.”
Ta gyada Kai tace ” babu komai Allah ya tsare maka hanya Allah Kuma yasa kaji sauki sosai zuwa goben.”
Yace ” Amin.” Zuciyar muhseena tana cike da son ta tambaye Shi ko yayi magana da iyayensa amma kunya da fargaba ya hanata. Sosai Kabir ya karanci fuskarsa muhseena don haka ya dan gyara zamansa akan tabarma yace ” zazzabin da nayi ya hanani yin magana da Baba , saboda Bai dawo gida da wuri ba , har na kwanta,”
Ta numfasa fargabarta ta lafa, ta dube shi tace ” babu komai Allah yayi mana jagora, ya Kuma Baka lafiya “. Yace ” Amin” ya Kara kallonta yace ” Kada ki damu zamuyi magana in sha Allah yau kafin gobe na tafi “. Tace ” Kabi ahankali babu damuwa” yadan lumshe idonsa Yana Jin zafin yadda yake yima muhseena karya amma baida wani zabi da ya wuce hakan.
Anan yayi sallar magriba da issha’i sai dai yaje masallaci ya dawo ta Kara fitowa su cigaba da hira. Har mallam Umar ya dawo bayan sallar issha’i. Sun gaisa sosai cike da girmamawa. Sannan mallam Umar ya Kira Shi gefe daya, tsugunawa yayi agabansa Yana sauraronsa . Mallam Umar yace ” Kabir naso muyi magana tuntuni amma jiya muhseena ta gaya min da kanka kayi maganar zaka turo magabatanka Wanda na jidadin hakan , Ka turo su muyi magana domin dai daga Kai har muhseena babu Wanda bai Kai munzalin da zaiyi aure ba”. Kabir ya jinjina Kai yace ” hakane Baba.”
Mallam Umar ya cigaba da cewa ” muhseena tayi kyakkyawan zabi domin Kai din da daya ne tamkar da dubu Bani da haufin zaka jiyar da yata dadin data rasa jinsa a duniya domin Kabir babu abinda Ka sani acikin irin rayuwar da muhseena tayi na ràshin jindadi ina gaya maka wannan ne domin a yanzu an Kai matakin da zaka sani, da ma wasu abubuwan da dole zaka sani kafin aurenku don baka cancanci a boye maka komai ba a game da muhseena”. Kan Kabir ya kàra yin nauyi zuciyarsa ta Kara sarewa, ya cigaba da yi ma Kansa tambayar menene yake neman tarwatsa mafarkinsa agame da muhseena.
“Ina adduar Allah Kada ya kawo duk wani sanadi da zai Zama silar kawo tangarda a cikin aurenku, Kuma wannan lokacin shine lokacin da ya kamata Ka bayyana ma duniya irinn son da kakema muhseena Amma hakan baya nufin ina son kayi fito na fito da kowa akan wannan lamarin”, maganganun mallam Umar suna son su zo daya da maganar mahaifiyarsa da baisan inda suka dosa ba.
“Shikenan maganar Kabir, Allah ya taimaka”. Kabir yace cikin sarkewar murya ” nagode Baba in sha Allah komai zai tafi yadda Muke so, gobe Zan koma Amma kafin na koma zanyi magana da mahaifina” yace ” to ba laifi Allah ya bada iko”. Daganan ya dago Shi Kuma mallam Umar ya ratsa zai shige gida da sauri Kabir ya fito da kudi ya dunkula masa ahannu, mallam Umar ya girgiza Kai yace ” aah kada muyi haka da Kai bazan Karba ba hidimar tayi yawa Kabir” ” da ne fa yayima babansa kyauta ta yaya zakace ba zaka Karba ba”. Bashi da sauran abin cewa daga maganar da Kabir yayi dole ya amshi kudin yace ” Allah yayi maka albarka, ya Kara tsarewa”, yace ” Amin sai da safe” ya shige gida Yana fadin ” Allah ya tashenu lafiya.”
Jugum Kabir yayi komai na duniyar ya tsaya masa , baida wani karfin guiwar da zai cigaba da tsayuwa agaban muhseena don haka sallama kawai yayi da ita bayan itama ya bata kudi masu yawa, tadan raka shi sannan ta tsaya tana kallon bayansa harya bacema ganinta duk da jefi jefi Yana waigowa Yana ganin duhunta harya wuce . Muhseena ta saki ajiyar zuciya cikin damuwar da ayanzu bata San dalilinta ba ta juya ta nade tabarmar ta shiga gida.
Tana shiga ta tadda Hajara da mallam Umar suna wata magana da bata San ta meye ba ce, amma shigarta dakin duk suka yi shuru suka shiga kame kamen Wata maganar da ban, duk da ta Kara Jin babu dadi amma bata nuna musu ba tabarma kawai ta aje ta dauki buta ta fice alamar Zata bandaki ne.
Amma tayi haka ne saboda ta Basu damar cigaba da maganar tasu wacce tasan basa son taji duk da ta riga ta sani cewa maganarta suke yi.
Tana shiga bandaki ta jingina jikin bango ta aje butar . Hakanan ta ji hawaye na kwarara a kwarmin idonta.
Me yasa mahaifiyarta ba zata gaya Mata gaskiyar lamarin rayuwarta ba, shin ko dai duk abinda mutane ke fada akanta gaskiya ne? Domin idan ba gaskiya ba ne babu yadda zaayi su dinga shakku da fargaba Akan maganar aurenta da kabir.ta Jima acikin bandakin tana kuka kafin ta share hawayenta ta fito.
Nan ma tana shiga dakin mallam Umar ya shiga kame kame Yana fadin ” ina yi ma innarki bayanin yadda mukayi da Kabir ne,” Kai kawai ta gyada ba tare da tace uffan ba ta shiga kakkabe yar karamar sabuwar katifarta da aka sayo Mata a cikin irin kudin da Kabir yake bata.bayan ta Gama ne ta miko na Hajara kudi cikin raunananniyar murya tace ” gashi Kabir ya Bani”. Hajara na karba bata saurari irin addua da takema Kabir ba tayi kwanciyar ta zuciyarta da numfashinta suna yi Mata nauyi.ido kawai ta rufe ba don wai zatayi bacci ba sai don ta ji dadin cigaba da tunanin data Saba yi arayuwarta.
*****
Tabangaren Kabir shima yadda yaga rana haka ya ga dare, damuwarsa tafi ta jiya, nan da nan har ya rame yayi dan wuya.washegari duk inda yabi Hafsatu na binsa da kallo domin ta Lura kwarai da ramar da yayi hakanne yasa ta Fara fargabar Kada fa ace Kabir yayi nisa a son yarinyar nan ne yadda zai iya shiga matsala bayan rabuwarsu.
Cikin sallama Kabir ya shiga dakin mahaifinsa mallam Hamza wanzami. Yana zaune Kan buzunsa da alama Bai dade da shigowa gidan ba. Ya dago ya dube Shi yace “Kabiru Ka shigo ” ya amsa yana kokarin Zama ” eh Baba Dama Kai nake jiran shigowarka kafin na tafi”. Yace ” aah wai tafiyar dai tana nan ne yau din”, ya gyada Kai yace ” eh Baba, saboda sunki min uzirin gobe shima kawu Musa Yana ta Kira gara na tafi yau din kawai” yace ” to ai shikenan Allah ya tsare hanya.”
Kabir yace ” Amin, na Riga na biya kudin shinkafa buhu daya dasu man gyada da manja su taliya kusan dai komai anjima mado zai kawo daga shagonsu”. Mallam Hamza wanzami yace ” Masha Allah Allah ya saka da alheri ya Kara budi na alheri yasa kafi haka”. Yace ” Amin Amin”
Malllm Hamza ya Dan tsare Shi da Ido sannan yace ” Kabiru Naga kamar kana cikin damuwa ne Kuma fuskarka ta fada kamar Baka da lafiya.”
Kabir ya dan muskuta Yana dubsn mahaifinsa yace ” a zahiri Baba damuwa gare ni ” ya tattaro hankalinsa Kan sa yace ” damuwa Kuma wace irin damuwa Kabiru” yace ” na Sami matar aure ne?” . Mallam Hamza yace” kash kajika da wata magana don Ka Sami matar aure sai hakan ya Zama damuwa, bayan kasan bamu da burin da ya wuce mu ji irin wannan furucin Alhamdulillah Kabiru ai gara kayi auren domin shine cikar kamalarka”. Kabir ya numfasa yace ” akwai damuwa kamar yadda na fada domin yarinyar da nake son na aura mama ta ce bazan aureta ba na bar maganar Kai kanka Kada na gaya maka domin ba zaka yarda ba”. Ananne mallam Hamza ya tattaro hankalinsa ya Kara maidawa ga Kabir yace ” bazan yarda ba? To wacece yarinyar yar gidan waye Aina Kuma take?”
Sannu ahankali Kabir ya sanar dashi komai akan muhseena.
Malllam Hamza yayi dif komai ya tsaya masa ya dubi Kabir sosai yace ” yar gidan mallam Umar, aah ina Kabiru kabar wannan maganar , akwai Mata da yawa babu Kuma inda zaka nemi aure ace ba zaa Baka ba don Baka da wani aibu, Amma wannan yarinyar tana da aibun da bazan taba yarda ta Zama surukata ba.”
Kan Kabir ya Sara ya Kara daburcewa yace ” Baba menene aibunta , Allah ya sani ina Sonta ia kadai zuciyata ta ke so Bana Jin Zan iya rabuwa da ita komai girman aibunta”.
Ya watsa masa harara yace ” Kai bana son shashanci ba zaka iya rabuwa da ita ba komai girman aibunta? Kasan abinda kake fada kuwa?”. Kabir yace ” to menene aibunta? Me tayi da baza’a iya aurenta ba?”.
Cikin fusata da daga murya yace ” To shegiya ce bata da uba, babu Kuma Wanda baisan hakan ba a kauyen nan, sai irinku da baku rayu a kauyen ba.”
Cikin matsananciyar daburcewa Kabir ya ce” shegiya?” ” Kwarai da gaske babu wai, don haka kowa so yake yayi aure cikin kyakkyawar zuria ba irin wannan ba Ka aureta kace me? Waye ubsnta kafi kowa sanin dole sai mace ta haifo da me irin halin gidan ubsnta ta yaya zaka aureta a haka?”. Kabir yace cikin rawar murya ” Baba ayi bincike ” ya watsa masa harara yace ” Ayi bincike don me? Bayan komai agaban mu akayi, watan wannan yarinyar takwas da haihuwa mallam Umar ya auri uwarta ba yarsa ba ce “. Tikisa Kabir yayi kasa da Kansa zuciyarsa na suya dai dai lokacin Hafsatu ta shigo dakin .
Mallam Hamza ya dubeta yace “kinji shirmen da danki ya zo dashi KO” ta dubi Kabir yanayinsa kadai ya tabbatar Mata da cewa maganar da ta ce yabarta Kada yayi ne yazo yayita.
Tace ” Au wai sai da yayi maka wannan maganar Bai barta ba kamar yadda nayi masa umarni”. Mallam Hamza yayi tsaki yace ” Bai yarda ba , Kuma ko yanzu banga alamar zai yarda ba domin har wani cewa yake yi wai ayi bincike,abinda ya faru Akan idon mu babu Wanda baisan shegiya bace agarin nan ba, don haka bazan taba hada jini dasu ba.”
Hafsatu daga tsaye ta cigaba da fada ” Naga alamar kasa ma kanka damuwa dubi yadda Ka rame daga jiya kawai, to kayi gaggawar rufama kanka asiri Kayi hakuri da abinda kasan ba zaka taba samu ba.”
A kausashe mallam Hamza wanzami yace ” ko zaka iya auren shegiya?” Da sauri ya dago yace ” Na rantse Zan iya aurenta matukar muhseena ce domin bata da laifi ba zabinta bane ta kasance awannan matsayin itama ba haka ta so ba, don Allah ku barni na aureta.”
Gaba daya suka saki tsaki lokaci daya, mallam Hamza yace ” to bazaka aureta ba” Hafsatu tace
“Ko da ko Ku kadai aka bari jiran duniya, babu aure a tsakaninku.”
Kawai ji yayi hawaye Yana fita masa masu matukar zafi sai kace mace. Ya kasa Kara yin wata magana saboda yadda zuciyarsa ke radidi,. Ko kadan Bai ji haushin muhseena ba bai kuma tsaneta ba don ance shegiya ce,asalima tausayi da kaunarta sune suka Kara mamaye zuciyarsa . Son da baiyi Mata da ba ma yanzu Shi yake mata.
Har suka cigaba da maganganunsu masu kama da sukar mashi aransa bai tanka ba. Daga bisani ya tashi Yana gauraye hanya yayi musu sallama ya fice ba tare daya saurari komai ba.
Haka Kabir ya tattara ya koma Kano cikin tashin hankali da damuwa mara musaltuwa. Zazzabi Mai zafi ya rufeshi har komawarsa Kano babu wani abu daya daya faranta ransa, tausayin muhseena ya Hana Shi sakat ga Sonta tamkar ana Kara turawa cikin zuciyarsa, shin ta ina zai Fara , bazai taba iya gayama muhseena bazai aure ta ba, sannan bazai iya ketare umarnin mahaifansa ba don haka ya Zama dole duk yadda zaayi yayi domin ganin ya shawo Kan mahaifansa sun amince da aurensa da muhseena. Amma ya zaiyi yadda mahaifansa suka nuna abune mawuyaci ace sun yarda Amma ya Zama dole yayi tunanin mafita domin magana ce ta rayuwarsa da muhseena ba Kuma zai taba yin wasa da ita ba.