Skip to content
Part 29 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Isar Haj murjanatu gidan Haj Nana Kai tsaye ta shige cikin gidan.

Zaune a katon falonta ta isketa da alama zuwanta take jira.haj murjanatu ta fada Kan kujera tana runtse idanunta, Haj Nana ta taso da sauri ta dawo kujerar da take zaune tana yi Mata kallo me cike da alamar tambaya ta dafa kafadarta tace ” Haj wai lafiya kuwa?” Ta bude idanunta da suka rine suka koma jajir ta dora akan Haj Nana gami da numfasawa sannan tace “Haj ina cikin damuwa.”

Ta gyada Kai a kagauce tace ” na sani, yanzu damuwar ce kawai nake son na ji menene?” Ta huro iska daga bakinta tace “Ina da damuwar data wuce na wannan sakaran yaron ne Taufiq.”

Haj Nana tace ” Dama nayi zaton damuwarsa ce, me Kuma yayi ya saki mujaheeda ne?” Ta saki tsaki tace ” ni dama zai sakenta ai saina fi kowa farinciki , nema kawai yake ya zamar min karfen kafa, gaba daya kamar ya asirce min ya bata ganin laifinsa akan komai.”

Haj Nana tace ” aah kada dai ki ce min duk abinda ya faru mujaheeda ta manta.” Ta gyada Kai ” ba zata manta ba tunda ta dora ma kanta jarabar sonsa, shi yasa nake tunanin Kada ya kassara min ya domin dai nayi Imani bazai canja halinsa ba akan zamantakewar sa da mujaheeda hakan yasa nasan mujaheeda ba zata taba fita da ga damuwa da tashin hankali ba kin Kuma fi kowa sanin babu abinda na tsana sama da damuwarta.”

Haj Nana tace ” nasani shiyasa tun farko na so ki hanata aurensa komai tsiya amma tunda Muka je wajen malami daya ya tabbatar sai anyi auren shikenan kika saduda, babu fa abinda zaki hada da talaka kiga dai dai, yanzu katsmaimai menene ke faruwa.”

Haj murjanatu tace cike da damuwa” duk zaman nan nata agida na dauka ta hakura da Taufiq ne musamman data ce min Sam bata son na dinga Mata maganarsa, ashe wai yarinya nan Jira take ta huce daga fushin da tayi kawai dazun nan muna karyawa tace min wai zata koma dakinta, na rantse Miki Haj ji nayi kamar an buga min guduma a kahon zuci.”

Haj Nana tace tana kebe baki ” Haj kema fa tun farko kinsan sakacinkine tunda kin riga kin fahimci taurin Kai da son nuna isa da iko sune taken Taufiq ai kamata yayi tuni abi ta kansa a murkushe Shi, tunda dai ba zaki hana mujaheeda sonsa ba balle ki iya rabasu Kuma ma ta yaya kike son ki gogama yarki bakin fenti ki bata mata tarihinta ta hanyar maida ita karamar bazawa, ai maimakon hakan kamata yayi a kamashi a daure ya bi ba wai ki kashe mata aure ba tunda kika riga kika bari akayi to fa bai kamata akashe ba.”

Haj murjanatu ta gyara zamanta tana kallon Haj Nana sosai tace “hakane kuma fa, shi yasa nazo wajenki neman shawara ya za’ayi domin dai raina ya fara raya min na bi hanyar da ba na son bi.”

Haj Nana tace ” hmmm wannan dai hanyar da bakya son bi din itace ya dace kibi” ta Kara muskutawa tana cigaba da cewa ” mafi yawanci mazan yanzu sune suke sa Kabi hanyar da bata kamata ba saboda bakin halinsu da mugunta da kokarin maida mace baiwa gami da kuntatawar da suke yi mana, shine dalilin da yasa idon mu yake rufewa Muke fadawa hanyar da mu kanmu mun San ba dai dai bace amma ya za muyi? Hakurin ne da wahala.”

Haj murjanatu tace ” hakane gaskiya ne” Haj Nana tace ” Shi yasa kika ga na gwammace na zauna na rayu ba aure tunda maigidàna ya rasu ke shaida ce ban Kara marmarin aure ba domin babu komai acikinsa face hawan jini da ciwon zuciya, Shi yasa nake mamakin Matan da mijinsu ya rasu idan Naga suna rubibin Kara aure na kance su Kam me suka tsinta a aurensu na baya da har suke marmarin Kara yin wani.”

Haj murjanatu ta saki ajiyar zuciya tace” hmmm aure Kam akwai jarabawa da yawa acikinsa, haka zalika duk wata fitina da mace ke fadawa na kauce hanya duk namiji ne sila yarinya da tsohuwa duk babu wacce ta tsallake siradin wulakanci da cin amanar namiji, yanzu dai ko ni aya ce irin cin amanar da Alh yayi min har na koma ga Allah bazan taba mantawa ba da cin mutunci hakan yasa nayi masa abinda nayi amma har yanzu ban huce ba duk iya shekarun nan zuciyata kamar ta fashe nake ji Kuma duk mallakar da nayi masa ban taba Samun sauki da natsuwa ba, hakan yasa akullum nake tunanin yadda zan katange yata daga masifa irinta da namiji sai gashi kuma ta jajibo Wanda zuciyata bata taba Samun nutsuwa da Shi ba.”

Ta kara numfasawa ta cigaba da cewa ” ke shaida ce akan irin son da nakema yata da irin kulawar da na bàta babu abinda ta rasa arayuwa kudi da matsayi duk baya ta basu to ta yaya duk Zan gama wannan fafutukar sannan na bari wani can da ya ganta daga sama ya zo ya wulakanta min ya bayan yasan irin lalurar dake tattare da ita bai tayani Kula da lafiyarta bane Zan barshi ya Kara nakasa min ita ina bazai yuwu ba ba’a haife Shi ba.”

Haj Nana tace tana Kara kafe idonta akan Haj murjanatu” To idan ko hakane sai dai abiyo masa ta bayan gida, domin dai kinsan Maza da kafiya da tsayawa akan kalma daya don wannan bazai taba tankwaruwa ba Kuma Kota koma haka zaa cigaba da yi babu abinda zai daina tunda ya riga ya amsa sunansa namijin bahaushe.”

Haj murjanatu tace ” Nima tunanin da nayi Kenan , kawai mu je wajen Mallam me guru ayi ta ta kare” (subhanallah duk Wanda damuwa zata same Shi Bai maida lamarinsa ga Allah ba ya zabi ya je wajen wanin ubangiji domin biyan bukata wannan asara ta tabbata agareshi domin yayi hannun riga da Allah da manzonsa Yana kuma cikin bata mabayyaniya matukar Kuma ya mutu akan haka to bashi da makoma face wutar jahannama abadan da’iman, ta yaya Kan duniya da iya dadewarka acikinta kayi shekara dari itama idan hakan ya riskeka kana cikin fitina ne domin awannan lokacin Baka Jindadin komai a duniya amma Ka zabi duniya akan lahirarka wacce itace madauwamiya , ance da digon wutar jahannama zai diga a duniya kamar kofar allura to da duk duniya da abinda ke cikinta sun kone kurmus to kayi tunani balle ace Kai zaa dauka ajefa acikin wannan wutar wa’iyazubillah Allah Ka barmu da imaninmu Ka rabamu da shirka).

Haj Nana tace ” fakat wannan Shi kadaine mafita sai ki shirya kisa rana muje.”

Ta gyada Kai tace ” eh, zan bari Naga komawar ta ta idan harta dage da son yin hakan bayan ta koma Zan kiraki sai kizo muje”.

Haj Nana tayi dariya tace ” magana ta kare, don Allah hajiya ki saki ranki kiyi walwalarki Taufiq din banza dama aike ce kika daga masa kafa,” Haj murjanatu ta saki tsaki tace ” shashasha talakan banza ni dana wani me kudi ne yake wannan iko da isar dana daga masa kafa domin ya isa yayi ne, amma Kai kana talaka kana fama da ràshin kudi amma Kuma Ka dinga wulakanta wacce ko gwanjonka akayi Saita saye Ka”. Haj Nana ta fashe da dariya harda kyakyatawa tace ” Kai Haj baki da dama, bari naje na Samo Miki abinda zakisa a makoshinki” ta Mike tana dariya ta wuce Haj murjanatu tace ” ina masu aikin naki naji gidan tsit” tace ” sun tafi ganin gida” Haj murjanatu tace ” ke dai bakya Jin magana na rabaki da dakko Yan aiki daga kauye kin ki, Basu da kirki kina nan zasu nemi su kasheki” dariya ta Kara Sawa tace ” sabo Haj,na riga na Saba dasu” ta tabe Baki tace ” hmmm ke kika Sani.”

Ta dade agidan Haj Nana sai da ta Gama ciye ciyenta da shaye shayenta sannan ta Kama hanyar gida cike da daukar shawarar aminiyarta.

*****

Karfe shida na yamma mujaheeda tayi sallama dakin mahaifiyarta. Tana zaune a gefen gado tana waya, mujaheeda ta Sami gefen gadon itama ta zauna tana kallonta harta Gama wayar.

Ta juyo tana kallonta tace ” yaya dai?”, Mujaheeda tayi sanyi da muryarta sosai tace “mummy Kan maganar dazu ne na fahimci ranki ya baci Wanda ba manufata ba Kenan, ina son na koma dakin mijinta ne kawai domin ina sonsa Kuma bazan iya rayuwa babu Shi ba.”

Ta yi shuru tana kallonta Haj murjanatu tace “uhum cigaba ina jinki”

Ta langabar da Kai gefe tace ” mummy bana son Kiji haushi ko ki damu, nasan kina Sona hakanne Kuma yasa bakya son ganina cikin damuwa, na Sani Yaya Taufiq ya bata min rai na Kuma ji matukar zafi akan hukuncin da ya yanke min ba tare da nuna yarda agareni ba, amma mummy yayi nadama duk da bana saurarensa kullum Saiya turo min sakon ban hakuri da rikon na dawo, akalla yanzu na gane ya San ina da amfani acikin rayuwarsa Kuma mummy ta yaya za’a raba aurena da Taufiq bayan Shi kadaine nake son na rayu da Shi har a gidan aljanna.”

Ta nisa ta cigaba da cewa ” don Allah mummy ki so Taufiq ko yaya ne Shi kadai ne zai bani kwanciyar hankali.”

Haj murjanatu ta dan yi murmushi tace ” Babu komai mujaheeda duk abinda kike so Shi nake so idan komawarki gidansa Shi zai Baki kwanciyar hankali to ina miki fatan alheri” ta kwanto ajikinta cike da shagwaba tace” mummy nagode sosai, dazu bayan fitarki munyi waya da shi mun daidaita yace zai zo bayan sallar magriba mu tafi” wani irin bakinciki ya kama Haj murjanatu haushin Taufiq ya kara kamata ji yadda mujaheeda ta zubar da kimarta ta bashi dama yazo ya dauketa sai kace kayan wanki ba zata bari ta koma cikin daraja da kima ba.

Bazata bari ta kirashi da kanta ba ya zo ta cimasa mutunci ta kafa masa sharadai ba, yanzu shikenan ya ci bulus haka zai zo ya dauketa babu daraja.

“Kinji ko mummy” Kai kawai ta gyada cike da takaici tace ” Naji Allah ya kaimu” tace “Amin” cike da farinciki ta tashi ta fita. Haj murjanatu ta ja tsaki ta buga hannunta akan gado tace ” zaka gane kurenka Taufiq zanyi maganinka zakayi nadamar yin wasa da rayuwar ya ta.”

<< Nima Matarsa Ce 28Nima Matarsa Ce 30 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×