Da sauri Hajara ta nufi inda muhseena take gaba daya ta rungumeta itama kukan take mai karfi, ” ki kwantar da hankalinki” ta girgiza Kai tace ” babu kwanciyar hankali atare da ni matukar baku gaya min gaskiyar lamarin ba, haba Inna yaya kuke son nayi da rayuwata na rantse Miki daurewa kawai nake yi amma na kusa gazawa zuciyata ta kusa kasa daukar wannan masifar, Inna Kuji tausayina Ku fiddani daga cikin wannan kangin.”
Mallam Umar yace ” ki natsu muhseena bana son ko kadan maganganun Ande su Sanya Miki shakku acikin zuciyarki” ta waigo ta dube Shi cikin zubar hawaye tace ” Baba don Allah mu daina yaudarar junanmu kinsan gaskiya kawai ku gaya min ko na Sami kwanciyar hankali, zuciyata nayi min zafi tana min kuna Ku taimaka min.”
Hajara ta dubi mallam cikin hawaye tace ” kayi hakuri mallam nasan kayi min dukkan halacci Kuma duk duniya muhseena bata da wani uban da ya wuce Ka, babu Kuma Wanda zata kalla amatsayin uba bayan Kai, don haka ayau ina son Ka sauke min nauyin alkawarin dake Kaina saboda na gaya ma muhseena ainihin gaskiyar da take son ji domin Samun kwanciyar hankalinta da nawa.”
Damuwa ta Kara baibaye fuskar mallam Umar yace ” kina ganin gaya Mata shine zaisa kwanciyar hankali gareta ( ya girgiza Kai) Sam ba zai kawo kwanciyar hankali ba sai dai ya Kara cabe lamarin ya Kara Mata matsananciyar damuwa da tashin hankali, Kuma ma meye amfanin gaya Mata abinda babu Shi meye amfanin gaya Mata barnar da babu yadda zaayi a gyara don haka ban amince ba ban goyi bayan ki gaya Mata komai ba, idan Kuma kika gaya Mata to ba da yawuna ba kin Kuma take umarni na.”
Muhseena ta Kara rushewa da kuka ya Matso ya dafa tsakiyar kanta yace” ke ya ta ce halak malak babu Wanda zai canja hakan Kuma amatsayina na mahaifinki na umarceii da ki bar wannan maganar ki Kuma tsaida ruwan idanunki ki fauwalama Allah komai.”
Yana Gama fadin haka ya juya cikin matukar damuwa da tashin hankali mara musaltuwa ya fice daga dakin ganin Ande Dije atsakar gidan da alamun duk tana Jin abinda suke fada Kai yasa kawai zai fice daga gidan cikin daga murya tace ” Ai Kai Ka dakkoma kanka bala’i ta yaya zaka kwace abinda ba Naka ba ta ina yarinyar nan ta Zama taka to Kada Allah yasa Ku Gaya Mata gaskiya tunda ta dage dole sai taji daga bakinku zata gasgata ” haushi ya Kara cika masa ciki ficewa kawai yayi ba tare da yace uffan ba.
Ta saki tsaki tace ” naji karfin hali wai barawo da sallama, to Kada Allah yasa Ka gaya Mata Kai ba ubanta bane hakan bashi zai hana duniya ta cigaba da gaya Mata abinda bakwa so agaya Matan ba.
Haka Hajara ta cigaba da lallaba muhseena tare da kwantar Mata da hankali duk da ta tabbatar da cewa ta riga ta kai bango domin bata taba bijirewa irin na yau ba.duk wata Kalma da ke fita daga bakin Hajara kunan zuciya sukesa muhseena daga bisani kwanciya kawai tayi Akan katifa ta runtse idanunta sosai bata bukatar Jin komai da ya wuce abarta ta cigaba da jinyar zuciyarta da take ji kamar zata fashe.
Dole tasa Hajara ta tashi ta fita domin ta fahimci muhseena bata bukatar ta Sam Sam.
Tana fita tsakar gidan ta Kara tsunduma cikin tsananin damuwa domin ganin irin kallon da Ande Dije keyi Mata , kujera yar tsuguno ta janyo ta zauna ta ba Ande Dije baya tana kokarin maida hawayenta tare da adduar Allah yasa Kada Ande tayi Mata magana don bata bukatar ta Kara Mata damuwa akan wacce take ciki, Amma addu’ar ta bata karbu ba domin kuwa cikin kausasshiyar murya Ande Dije tace ” ba zaki taba rabuwa da bakinciki da ràshin sukuni ba matukar baki gaya ma muhseena ainihin gaskiyar ba domin kin cutar da ita kin zalunceta ko wannan boye Matan da kikayi ya isa ya Zama masifa atare da ke” Hajara tace ” don Allah kiyi hakuri kibar wannan maganar haka” ” naki na bari gaskiya ce bakya so Kuma dole Saina fada Miki , me kike tunani yasa kika ki gaya Mata bayan tuni duniya ta sanar da ita, ko kina tsoron tsana da kiyayyar da zata nuna Miki ne matukar kika gaya Mata ko ita wacece.”
“Babu wani abu da zatayi ko Wanda ta riga tayi da zai sani na tsaneta komai muni da girman abin uwata itace jarumata Zan Kuma yi Mata dukkan Uzuri, Kuma ko da me duniya zata cigaba da fada akaina matukar banji daga bakin mahaifana ba bazan taba yarda ba ko gasgatawa” muryar muhseena ce ta daki dodon kunnan Ande dije.
A gaggauce Hajara ta juya tana kallon inda sautin maganar ya fito.
Muhseena ce tsaye akofar daki tana yima Ande Dije wani irin kallo me cike da tsana.
Ande Dije ta yi tsaki tace ” umm kanku ake ji” muhseena tace ” Shi yasa tunda kanmu ake ji to ki kyalemu Muji da Kan namu ki daina kokarin shiga abinda babu ruwanki aciki”. Cikin fusata tace ” Kada ki sake kiyi min ràshin kunyar da kika gada kika Saba ” zatayi magana kenan Hajara ta taso da sauri ta kama hannunta suka koma daki tana cewa Kada kiyi magana.
Haka muhseena ta kasance cikin tashin hankali har zuwa bayan isshai da Kabir ya kirata gare Shi ne kawai ta Sami nutsuwa duk da taki yarda ya gane tana cikin damuwa.
Amma fa shima ta bangarensa sosai muhseena take tsinto sakon damuwa acikin muryarsa.wanda ta kasa daurewa sai da tayi masa tambayar ” meke damunka” ya jinjina tambayar ta ta ahankali yace ” me kika gani” tace ” hakanan nake Jin kamar kana cikin damuwa ” ya ce ” aah babu wata damuwa kawai yau na gaji ne da aiki gaba daya jikina duk ya saki.”
Ta numfasa tace ” Amma Ka Sami damar yin magana da magabatanka kuwa agame da maganar auren mu.”
Gabansa yayi mummunar faduwa ya dafe Kansa daya Sara masa.ahankali ya tattaro yawun bakinsa ya hadiye sannan yace ” muhimmiyar magana ce da bai kamata ayita a waya ba shiyasa na bari harna Kara dawowa sannan muyi maganar”. Ya numfasa tace ‘ to Allah ya dawo da Kai lafiya” ya amsa da Amin.
Hira suka cigaba da yi wacce gaba dayansu hirar bata musu dadi domin kowa cikin muguwar damuwa yake, hakan yasa su kayi sallama.komai dai sabo ya dawo ma muhseena domin ji take tamkar yau ce ranar da aka fara jifanta da Kalmar shegiya sosai take da bukatar Jin komai daga iyayenta, haka ta kwana cikin damuwa.Tun daga wannan ranar Kuma muhseena ta rasa walwalarta, hatta magana bata iya yi da kowa agidan gaba daya ta koma shuru, sai dai kallo daya zaka yi Mata Ka tabbatar da tana cikin matsanancin hali na damuwa.wanda hakan itama Hajara yasa ta Kara fadawa cikin tashin hankali domin idan akwai abinda ta tsana to bai wuce ràshin kwanciyar yarta ba, gaba daya ta rasa yadda zata bulloma al’amarin.
Shima can Kabir damuwarsa ta kasa boyuwa gaba daya nema yake ya fita hayyacinsa.
Hakan yasa Alh Musa a dole ya yarda da bukatarsa na zuwa Durmi domin tattaunawa da malllam Hamza wanzami agame da maganarsa da muhseena.
Tare da Kabir din suka tafi Durmi a Wata safiyar ranar alhamis,Kabir dinne ke Jan motar har Durmi.
Sosai mallam Hamza wanzami da Hafsatu suka jidadin zuwan Alh Musa.
Sai da su Ka ci suka koshi amma banda Kabir Wanda ko ruwa bai sha ba sannan Àlh Musa ya dubi mallam Hamza wanzami yace “Mallam wajenka nazo” mallam Hamza ya dube Shi sannan ya dubi Kabir yace ” Allah yasa ba maganar yaron nan bace ta shirme”. Alh Musa ya nisa yace ” itace mallam, Ka dubi yadda yaron nan ya rame ya lalace, ni Kaina da nace Bana cikin maganar domin tabbas in dai da gaske ne yarinyar nan bata da uba to nima ban goyi bayan ya aure ta ba, don haka yasa nazo domin na ji shin bincike ne ya tabbatar da hakan ko kuwa shaci fadan mutane ne Wanda in dai haka ne to auren Kabir da ita baida wata illa.”
Mallam Hamza ya gyada Kai yace ” Alh , wannan maganar ba shaci fade bane abu ne daya faru agaban mu babu abinda bamu sani ba agame da hakan babu karya wannan yarinyar shegiya ce bata da uba cikinta Kuma babu bala’i da kalubalen da bai haifar ba ga uwarta.”
Kabir ya dago yace ” Zan iya aurenta ahaka komai ràshin asalinta Zan iya aurenta?” ” Da Allah rufa min baki shashasha da bai San ciwon Kansa ba, idan Kai zaka iya aurenta to mu ba zamu iya Zama surukanta ba kaga Ka fita Ido na na maida na rufe.”
Alh Musa yace ” To idan ko hakane gaskiya nima ban goyi bayan ya aureta ba saboda son ina masa kwadayin Samun zuria ta gari”
Hafsatu ta shigo fahimtar maganar da akeyi ne yasa tayi ma Kabir kallon tsaf tace ” ai dama nasha jinin jikina cewar ba zaka hakura da yarinyar nan cikin dadin rai ba tunda na fahimci kamar Baka San ciwon kanka ba, don inda kasan ciwon kanka ba zaka so hada zuria da yarinyar da kowa ke gudu ba tunda Muke a kauyen nan ba’a taba Samun yarinyar da ta fita zakka ta yi abin kunyar da uwarta tayi ba, akanta aka fara yin cikin shege da haifar dan shege a kauyen nan, kowa na neman tsari dasu sai Kai ne zaka ce kaji Ka gani to baka isa ba.”
Ga mamakinsu hawaye ne kawai ke fita a idanun Kabir gaba daya ya Kara gigicewa.” Don Allah Ku duba lamarin nan ina son muhseena duk wañnan abin da kuke fada ba ita ta aikata ba” mallam Hamza yace ” Ah aiko ita ta aikata ba zaka gani ba tunda soyayyar ta ta rufe idanunka.”
Alh Musa ya dube Shi cike da tausayawa yace”kayi hakuri Kabir in sha Allah zaka Sami wacce ta fita” ya dube Shi Ido na tsiyayar hawaye yace ” babu wacce Zan samu wacce ta fita, ko Kai Ka ganta sau daya zaka gamsu da hankali da tarbiyyar ta Zaka Kuma yarda da ni idan nace maka babu wata kamarta.”
Hafsatu ta yi tsaki tace ” Bana son Ka jama kanka damuwar da zaka zo kana wahala domin dai ba zaka aureta ba” mallam Hamza yace ” babu Kai babu da ita,idan ma har zuwanka zai Zama damuwa to mun yafe kayi zamanka ma dinga yin waya” ya juya ya dubi Alh Musa yace ” Alh abar maganar nan Kada ma akara tayar da ita ” ya jinjina Kai yace ” shikenan Allah yasa hakan shine yafi Zama alheri.”
Haka dai suka Kara kamo hanya zuwa Kano ba tare da Kabir yaje sun gaisa da muhseena ba. Cikin matukar tashin hankalin da ya fi na kullum Kabir yake tuki ganin baya cikin hayyacinsa yasa Alh Musa ya karbi tukin haka zalika har suka kai Kano Kabir baice uffan ba duk da nasihohi da kwanta da hankalin da Alh Musa yake masa.
Muhseena ba ta da labarin zuwan Kabir Durmi , har sai washegari data hadu da abokinsa bayan ta taso makarantar islamiya bayan sun gaisa yake ce Mata nasan dai mutumin duk saurin da yake jiya ya zo kun gaisa ko?
Ta dube Shi cike da neman Karin bayani tace “wake nan?” Yace “Kabir mana.” Gabanta ya Fadi sosai ta dube Shi tace ” yazo garin ne?'” yace ” lalle na yarda Yana sauri tunda har kema ya kasa zuwa Ku gaisa, nima gilminsa na gani a mota shine na kirashi awaya yace min sauri yake.”
Duk surutan da yake yi muhseena bata jinsa riga ta fada wata duniyar, hakan yasa yayi Mata sallama ya tafi.
Jikin bango ta samu ta jingina saboda jiri da ta ji Yana neman ya kwasheta.da sauri kirjinta yake bugawa, babu yadda zaayi ta yarda da cewa sauri ne yasa Kabir kasa zuwa wajenta .Wanda idan ma hakane me zaisa bazai iya gaya Mata yazo garin ba ko dazu sunyi waya amma bai gaya Mata ba.
“Shin me hakan yake nufi? Ta tambayi kanta cikin tashin hankali. Zuciyarta ta bata amsa da cewa tabbas akwai matsala wacce Kabir be son ya gayá Mata.
Hakika maganar aurensu tana cikin jifa’i. Ta dafe kanta da ya Sara Kada fa fargabanta ta tabbata.
A hankali bakinta yake furta “Allah kasa hasashena ba gaskiya bane Allah Kada kasa na rasa Kabir Shi kadaine ya rage min a matsayin farincikina.
Gaba daya idanunta sun Fara rufewa daker take daga kafarta zuwa gida sai dai duk Wanda ya dubeta zai gamsu da cewa tana cikin matsanancin tashin hankali.