Bayan mujaheeda ta dawo daga rakiyarsu. Kujera ta zauna ta dauki kullin magungunan tana Kara kallonsa, a hankali ta numfasa , ita kanta ta na mamakin irin hankalin daya shigeta tun bayan aurenta, domin dai tuni zuciyarta ta shiga gaya Mata duk abinda Haj murjanatu ta fada akan maganin nan ba gaskiya ba ne, ta dan gyara zamanta tana Kara nazarin al’amarin shin har yaushe mahaifiyarta ta Fara damuwa da lamarin Taufiq balle harta Samo masa maganin tsari?
Nan da nan zuciyarta ta aminta da cewa lalle wannan magungunan na wani abin ne daban Wanda yake da alaka da son zuciyar mahaifiyarta amma ba maganin tsari bane domin idan shine babu yadda zaayi ta bata umarnin Kada ta nuna masa.
Zahiri ta yarda da mahaifiyarta amma bata yarda da ita ba akan lamarin Taufiq.don haka zuciyarta bata aminta da tayi amfani da maganin ba ahankali ta Mike ta nufi wajen zuba Shara ta juye maganin aciki.
Ta dawo tayi zamanta tana son Taufiq fiye da Tunanin me túnani don haka bata son duk wani abu da zai yi Mata ba don ra’ayinsa ko sonsa ba, duk da bata San maganin menene ba to tasan bazai wuce don Taufiq yayi wani abu ba ne Wanda bai yi niyyar yi ba, ita Kuma bata bukatar hakan.haka mujaheeda ta Karasa sauran ranar cike da tunanin halayen mahaifiyarta Wanda da zata iya canja Mata da tuni ta canja domin ita ayanzu jinta take kamar Wata sabuwar halitta.
Haka zalika tun dawowarta gidan mijinta take kokarin yi masa biyayya tare da kulle duk wata hanya da zasu iya Samun sabani.kuma taga amfanin abinda take yi domin dai sosai Taufiq ke nuna Mata so da kauna tare da gudun bacin ranta.
*****
Tabangaren muhseena kuwa ta yi kokarin boye damuwarta ta Kuma daure duk wayar da take da Kabir bata yi masa magana ko tambayar sa dalilin ràshin zuwa gidansu da Kuma ràshin gaya Mata ya zo garin ba. Illa iyaka ta dage da adduar Allah yasa Kabir rabonta ne idan Kuma ba rabonta bane to Allah yasa Mata juriya da danganar rashinta..ita kanta Hajara da mallam Umar cikin damuwa suke fargabarsu Kuma ta dadu Akan ta da, agame da auren Kabir da muhseena.sai dai basa nuna ma muhseena damuwarsu saboda basa son ta Kara damuwa.Ayayinda Ande Dije ta cigaba da kuntata musu da lafuzanta da ayyukanta, hatta tsakar gida Hajara bata son ta fita saboda kalaman da take jifanta dasu.
Shiko Kabir bai saduda ba duk wani Wanda yake Jin zai iya gayama mahaifinsa ya ji, ya nemi taimakonsa amma Mallam Hamza yaki saurarensu.
Domin bayan Alh Musa Kabir ya tura aminan mahaifinsa , ya tura sarkin wanzamai amma duk mallam Hamza yaki saurarensu karshe ma kiransa yayi ya tabbatar masa da cewa idan har ya Kara turo masa mutane Kan maganar muhseena sai yayi matukar bata masa rai…
Hakan ya Kara jefa Kabir cikin mawuyacin hali.
Haj Salma kuwa shawarar yaje ya Sami muhseena suyi magana ta bashi, tace yaje ya fahimtar da ita halinda ya ke ciki idan harta fahimce Shi zata San bai ci amanarta ba, domin dai duk yadda yake tunanin zafin lamarin ya wuce nan.
A dole Kabir ya dauki shawarar Haj Salma tunda baiga wata mafita ba gaba.
Ranar wata jumaa ya dauki hanyar Durmi.Tun isar sa Durmi mahaifiyarsa Hafsatu ta nemi ta sare domin ganin irin ramar da yayi matukar rama gaba daya idanunsa duk sun fada kallo daya zakayi masa Ka gamsu da cewa Yana cikin wani irin mawuyacin hali.Abinda Kuma ta Kara fuskanta ya karasa Mata tashin hankali da damuwa shine Kabir baya cin abinci domin tunda yazo aka Kai masa abinci babu abinda ya Bude ya ci.yana kwance asaman gadon dakinsa ya na cikin matukar damuwa Hafsatu ta yi sallama ta shigo amma bai ji shigowarta ba har sai da yaji karar bude kwanuka sannan ya dubi wajen.
Hafsatu ke bude kwanukan abincin da aka kawo masa, babu abinda ya ci aciki a hankali ta koma bakin gadon ta zauna tana kallonsa fuskarta cike da damuwa ta Kira sunansa ” Kabir.”
Ya amsa Yana kokarin tashi ya zauna, ta jinjina Kai tace ‘ me yasa baka ci abinci ba’. Yace asanyaye ‘ saboda babu wani abu da yake yi min dadi abaki tsawon wannan lokacin bana iya cin abinci ya tsurga min asalima ni babu abinda yake yi min dadi abaki amatsayin abinci.”
Tace ” yanzu saboda wannan yarinyar ne kake son Ka kashe kanka Kabir bayan kasan Kaine sanyin idaniyata Kaine abin alfaharina, yanzu soyayya zaka fifita fiye da rayuwarka.”
Ya girgiza Kai yace ” mama wannan abu ne da ni Kaina bani da iko da Shi , don da ina da iko da tun ranar da kuka ce na rabu da muhseena da tuni na cire soyayyar ta a raina amma ya zanyi bani da iko, kullum Sonta Kara daduwa yake yi azuciyata ba raguwa ba asalima na rasa ta yadda Zan gaya Mata cewa bazan aureta ba” Hafsatu tace ‘ Amma sanin kanka ne da ace akwai yuwuwar mu barka Ka aureta to da munyi haka, Amma ta yaya kake ganin zamu amince da ita bayan bata da asali baa San ubanta ba kaima kasan bazai yuwu ba.”
Yace ” to yanzu gaya min mama ta yaya Zan sanar da ita wannan maganar me nauyi bayan na riga nayi alkawarin aurenta nama iyayenta alkawari ” tace ” su waye iyayen nata da zaka ji nauyin gaya musu Ka fasa aurenta bayan ga dalilinka nan, alabasshi idan Ka gaya musu dalilin sun karyata to sai su gaya maka gaskiya “. Numfasa yayi kawai ya kasa magana.
Hafsatu ta cigaba da maganganunta da Sam babu abu daya da yake dauka domin yare daya kawai kunnansa zai iya fahimta shine “kaje Ka auri muhseena.”
“Ka tashi Ka ci abinci idan ba haka ba Zan bata maka rai sosai”.cewarta cikin fada.yace “Zan ci” tayi masa kallon tsaf tace “Ka tashi Ka ci yanzun nan”. Baisan damuwa hakan yasa ya sakko ya bude kwanon abincin ya Fara ci, saida ta tabbatar ya ci sannan ta tashi tabar dakin zuciyarta cike da damuwa da tausayin danta.
Sai bayan sallar isshai sannan Kabir yayima gidansu muhseena tsinke.tunda yaron da ya shigo kiranta yace ta zo inji Kabir taji gabanta na matukar faduwa,ita kuwa Ande Dije Jin wani bakinciki tayi ya cika zuciyarta domin duk a tunaninta wannan dadewar da yayi be zo ba ta dauka ko ya daina zuwa ne maganar ta watse. Hakan yasa harta fito ta fita Ande Dije harara take balla Mata.
Jingine jikin bangon zauren gidan ta tadda Kabir cikin doguwar koriyar riga Kansa ya daura hula.
Saida ta shimfida tabarmar hannunta sannan Kabir ya zauna Yana yi Mata wani irin kallo me cike da kauna da tausayi.
Itama ta zauna a gefen tabarmar tana Kallonsa tana ganin irin ramar da yayi a hankali tace ” kayi ciwo ne?” Ya dubeta yace ” me kika gani?” Ta gyada Kai tace ” Rama na gani da Kuma alamar ràshin nutsuwa da damuwa a tare da Kai” .ya yi kokarin daidaita tunaninsa da nutsuwarsa yace ” Bana jindadi ne , shine dalilin daukar lokacina ban zo ba” ta nisa hakika babu ko shakka akwai abinda Kabir yake boye Mata. Tace ” to damuwa da ràshin nutsuwar fa na menene”. Ta tambaya da murya me cike da damuwa, yace ” ke ce dai ke ganin damuwar da ràshin nutsuwar”.
Tayi shuru na dan wani lokaci sannan tace “Kabir” ya amsa Yana kallonta tace ” don Allah me kake boye min? Meye damuwar? Me yasa Kuma kake boye min bayan kasan sanin nawa shine Samun kwanciyar hankalina da nutsuwata” Kabir yayi saurin yin kasa da kansa adalilin idanunsa da yaji sun Fara Tara kwalla.
Muhseena ta cigaba da magana da murya me cike da ban tausayi da rauni. ” Kada Ka damu da koma menene kawai Ka gaya min domin idan tashin hankali ne na Saba idan damuwa ce tunda na tsuru a duniya nake cikinta babu wani abu sabo atare da ni, don haka Kada Ka damu Ka gaya min koma menene” nan ma Kabir ya kasa magana illama dagowa da yayi ya zuba Mata raunannun idanunsa da yake kokarin maida kwallar cikinsu.
Tayi wani bushasshen murmushi tace ” kadaina kallona domin ganin idonka cikin nawa zai iya cire min jarumta, Ka sani ayanzu dai babu wata magana da nake son ji wacce zata wanke min damuwa sama da gaskiya daga bakinka.”
Duk shuru sukayi ganin Kabir baida niyyar yin magana yasa ta hadiye dukkan fargabarta ta tsaida idanunta akansa sannan tace ” iyayenka sun hana Ka aure ni ko” Jin maganar yayi a matukar bazata hakan yasa ya daburce gaba daya ya Kuma rasa amsar da zai bata.
Ta cigaba da cewa ” dalilin da yasa kenan kazo garin baka zo gidan mu ba,haka zalika shine dalilin da Ka rage Kirana a waya ko? Kamar yadda ya Zama dalilin damuwarka da ramarka gami da ràshin nutsuwar Ka, Bana son Ka boye min komai domin cigaba da boye min Shi zaisa na Kara fadawa cikin masifar cigaba da sa rai akan abinda bazan taba samu ba.”
Ta Kara zuba masa Ido tace ” kace wani abu mana kayi min magana na hadaka da girman Allah Ka sanar da ni Gaskiya domin ni ina son agaya min gaskiya komai dacinta fiye da ayi min karya don Samun kwanciyar hankali na.”
Kabir yasa gefen hsnnunsa ya share hawayen da ya fara gangaro masa, hakan ya Kara tayar da hankalin muhseena nan da nan itama ta sami kanta da zubar da hawaye tun kafin ya bata amsa ta riga ta Sami amsar tambayarta.
Gaba dayansu kuka suka dinga yi kabir kamar ba namiji ba.sun dauki tsawon lokaci suna kuka babu me lallashin wani.
Saida sukayi suka gaji sannan Kabir ya Fara magana me cike da tausayi da neman mafita yace ” muhseena duk duniya ke ce mace ta farko data mallaki zuciyata ta mallaki soyayyata ina yi Miki son da ni Kaina bansan girma da iyakarsa ba, ina tausayinki ina kwadayin yin rayuwa ta har abada da ke, Bana Jin Kuma daga kanki Zan Kara son wata arayuwa,”
Ya numfasa sannan ya cigaba da cewa ” duk abinda kika fada gaskiya ne muhseena mahaifana sun ki yarda da auren mu tun ranar farko da na Fara zuwa musu da maganar suka taka min burki naki gaya Miki ne adilin ina tunanin Zan iya shawo Kan matsalar da Kaina amma zuwa yanzu duk da ban cire rai ba na gane lamarin akwai rikitarwa da ràshin sanin tabbas.”
Duk da muhseena tayi zaton Jin haka daga gareshi to fa bai hanata Jin wani mummunan sauyi da matukar tashin hankali ba atare da ita gaba daya ji tayi komai ya tsaya Mata cak kamar wacce bata da laka ajikinta.
Ya cigaba da cewa ” Ranar da kika ce nazo ban neme ki ba ranar kawuna na dakko na kawo domin ya ba mahaifana baki amma shima sunki sauraronsa, burinsu kawai shine na fita harkar ki na nemi wata.”
Cikin rawar murya tace” Mecece hujjarsu na raba mu?” Saida ya jinjina abinda zai fada sannan yace ” Hujjarsu itace wai baki da asali…..?” Tayi saurin daga masa hannu tace “Shikenan daman nayi zaton hakan Basu da lefi suna da gaskiya” ya dubeta sosai yace ” kina nufin hujjarsu gaskiya ce” ta gyada Kai tace ” Bani da amsar tambayarka domin nima kullum amsar nake nema ma Kaina har yanzu Kuma ban samu ba, sai dai tabbas lokacin Samun amsar tawa yayi.”
Kabir ya numfasa yace ” To yanzu baki da wata shawara da zaki iya bani, domin bana Jin Zan iya jurewa na karbi umarnin mahaifana” ta girgiza Kai tace ” babu wata shawara da ta wuce Ka Zama jarumi Ka amshi umarnin iyayenka Kada Ka bijire musu Kabi su a hankali idan Kai Allah ya rubuta min a allon kaddara ta to babu tsumi babu dabara sai Ka aure ni komai runtsi saboda haka mu fauwalama Allah komai shine zaiyi mana maganin matsalar mu.”
Ya runtse Ido ya bude yace “ina ma mahaifana zasu gane tsantsar nagartarki nutsuwa da kamalarki hakika da da kansu zasu kore Miki wancan zaton su rokeki ki aureni da kansu, har yanzu birni da kauye banga wacce ta kaiki ba , nasan muhimmanci muhseena ina Kuma sonki matukar so.”
Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo daga kwarmin idanunta ta kasa magana domin ita kadai tasan masifar da ruhinta yake ciki.
Ta dauka zata Zama jaruma amma ji take kamar ta kusa kasawa.
Kabir yace ” Don Allah muhseena ki Goya min baya”
Tayi masa wani bushasshen kallo tace ” goyon bayana aika samu abinda ya rage maka shine goyon bayan iyayenka Wanda shine babban abin bukata.”
Yayi shuru domin dai yasan abinda kamar wuya amma baya son ya gayá Mata domin irin masifar tashin hankalin da yake gani a kwayar idonta ya girmama don dai muhseena jaruma ce kawai amma irin wannan damuwar data Kada ita.
Ko da suka cigaba da tattaunawa Kabir ya Lura gaba daya muhseena bata cikin hayyacinta hakan yasa yaga ya kamata ya barta ta samu Hutu da natsuwa.
“Zan tafi saboda na barki ki numfasa ga Kaya nan ki shiga dasu”. Ta kasa cewa uffan haka ta bishi da kallo harya tashi shima ya Dade atsaye Yana kallon ta zuciyarsa ta Kara tsinkewa a daddafe ya fice daga zauren gidan.
Muhseena ta yi kasa da kanta domin wasu sabbin hawaye da suka cigaba da yi Mata ambaliya asaman kuncinta. Akalla Kabir yakai minti goma da tafiya kafin muhseena ta iya tashi ta zubama katin katin din ledojin dake aje idanu kafin ta iya dauka suna da matukar nauyi shin meye aciki haka?
Ledojin na rinjayarta ta shiga gidan. Abin mamaki har yanzu Ande Dije tana zaune inda ta barta.bata ko kalli inda take ba tazo zata wuce. Ande ta saki tsaki tana hararar kayan hannunta tace ” wannan yaro ana cutar da Shi,komai nasa akanki yake karewa bayan kunfi kowa sanin cewa ba zai aureki ba amma kun dage dole sai kunci haramun .” Ita dai muhseena ta wuce bata ko Jin me take cewa domin masifar da take ciki yafi wannan.
Ande tace ” Allah ya kaimu ranar biya zamu ga yadda zaayi “. Zuwa lokacin muhseena harta shige daki.
Da sauri Hajara ta dago tana dubanta yadda ta aje kayan da karfi ya tabbatar Mata ba lafiya.
Tana aje kayan ta wuce ta fada Kan katifarta ta cigaba da wani sabon Kuka me matukar daga hankali.
Nan da nan Hajara ta tashi cikin tsuma da fargaba gami da tashin hankali ta nufota tana tambayarta ” meya faru muhseena”.