Duk tambayar da Hajara take Mata, muhseena bata tanka Mata ba sai kuka Mai tsanani da take Kara tsinkewa da shi.
Hakan ya Kara matukar tayar da hankalin Hajara, ta zauna akusa da ita gami da janyota jikinta tana lallashi tana cigaba da tambayar ta abinda ke faruwa. Amma saida muhseena ta ci kuka harta ba uku lada sannan ta dubi mahaifiyarta cikin jan idon da har ya Fara kumbura saboda kuka sannan tace ” yau Kabir ya zo min da tambayar da na Dade ina yi muku irinta baku bani amsa ba, tambayar da ta rusa komai da ke tsakaninmu”. Gaban Hajara ya Fadi ta zuba Mata Ido tace ” ki natsu muhseena kiyi min bayanin abinda ke faruwa, ya kukayi da Kabir din.”
Muhseena ta ja doguwar ajiyar zuciya tace ” Kabir ya kufce min domin mahaifansa sun tabbatar masa da cewa ba zasu taba bari ya auri shegiya mara uba ba.”
Hajara ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya tayi kasa da kanta numfashinta ya Fara Mata wahalar fita.
Muhseena takara kafeta da jajayen idanunta da suke cigaba da fitar da zafafan hawaye ta cigaba da cewa ” Tun tasowata Inna ake nuna min tsana da kyara duk duniya daga soyayyar ki Saita Baba na Samu sai soyayyar Kabir” ta muskuta tace ” Bani da kawa Bani da aminiya Bani da masoyi saboda kowa na gudun hada rayuwa da ni, Inna menene lefina?”
Ta Kara hadiye wani zazzafan yawu tace, ” idan har zan rayu da irin wannan tarin kalubalen akaina ta yaya kuke ganin bazan iya jurar Jin asalina daga gareku ba, bayan nafi kowa sanin sanin ko ni wacece zai wanke min abubuwa da dama dake tattare acikin zuciyata kamar yadda zai sa na Sami nutsuwa da kwanciyar hankali.”
Dai dai lokacin mallam Umar yayi sallama ya shigo dakin , kallo daya yayi musu ya tabbatar akwai matsala don haka ya Matso kusa da muhseena Yana kallonta cike da kauna da kulawa yace ” muhseena lafiya? Menene ke faruwa?”
Hajara ce ta bashi amsar tambayarsa ” Abinda Muke ta tunani daga mahaifan Kabir ne ya tabbata ” yayi Mata kallon tsaf yace ” kamar yaya?” Tace ” to mahaifansa sun ce Basu yarda ya aureta ba adalilin bakin fentin da akayi mata.”
Mallam Umar ya dauke wuta damuwa da tashin hankali suka bayyana karara a fuskarsa.ya kasa cewa uffan har muhseena ta tashi tazo gabansa ta tsuguna guiwa biyu tace cikin rawar murya me cike da tashin hankali tace ” don Allah Baba na rokeka Ku sanar da ni gaskiyar lamarin nan ko na Sami hujjar kafawa aduk lokacin da aka zo min da tambaya irin wacce Kabir ya zo min da ita.”
Mallam Umar yayi Jim na dan wani lokaci sannan yace ” kiyi hakuri ki Bani kwana biyu in sha Allah zaki Sami duk abinda kike so, ayanzu dai ina bukatar haduwa da mahaifin Kabir domin mu tattauna bayan nan duk amsar tambayoyinki zaki samu “. Tace ” to shikenan ” daganan ta tashi ta dau buta ta fita zuwa bandaki.
Tana fita Mallam Umar ya dawo kusa da matarsa Yana kallonta kamar me neman mafita awajenta. Hajara ta dube Shi tace ” kaga irin ranar da akullum nake Jin tsoron zuwanta ko, na gaya maka rike muhseena amatsayin ya da Zama uba agareta bashi zai share ko goge mummunan bakin fentin da take dashi ba kamar yadda mutane ba zasu taba maida Kai mahaifinta ba duk da cancantar da kayi saboda sun riga sun San komai”. Ta Kara kallonsa tace ” don haka mu daina yaudarar kanmu kawai yarinyar nan mu fito mu gaya Mata gaskiya tun kafin damuwa ta salwantar da ita”. Malllam Umar yace ” hakane Hajara nima ayau Naga kysutuwar mu gaya Mata gaskiya amma har sai na Sami Zama da mallam Hamza wanzami, don ina fatan mu Sami sulhu ” Hajara tace ” Allah dai yasa ya fahimceka duk da abin da kamar wuya”. Malllam Umar yace ” ràshin Kabir agun muhseena ba karamar asara bace domin shine nake da yakinin zai rike ta cikin aminci da kauna da soyayya yaro ne nagartacce Wanda zai iya Zama abin alfaharin duk wani Wanda ya same Shi amatsayin suriki, ina matukar yi Mata sha’awar aurensa”. Hajara ta nisa ahankali tace ” Allah dai ya kawo mana mafita.”
Haka suka cigaba da tattaunawa har muhseena ta dawo daure da alwakarta.kai tsaye ta dau hijabin ta tasa gami da shimfida tabarma ta shiga sallah nafila domin Samun sassauci daga masifar da take ciki.
Hakan yasa Mallam Umar ya fice zuwa dakinsa cikin dimbin tashin hankali.
A dakinma ya rasa abinda ke masa dadi sai dai ya Kai gauro ya Kai mari.hakika Yana matukar tausayin Hajara in da Yana da halin sauya kaddarar ta hakika daya canja.yau gashi muhseena zata sa takalmin da Hajara ta cire tarihi Yana kokarin maimaita Kansa.
Ya koma ya zauna akan Dan karamin gadonsa shin ta ina zai kamo lamarin nan ta yaya zai mallakama muhseena abinda take so.haka yayi ta tunane tunane Wanda suka sa Shi tuna shekarun baya daya taba tsintar Kansa a irin wannan yanayin da Kabir yake ciki yanzu.
Washegari mallam Umar bai saurari komai ba, yayi ma gidan mallam Hamza wanzami tsinke dai dai karfe goma da rabi na safe ya tura yaro cikin gidan yayi sallama da Shi.
Ba’a dauki wani dogon lokaci ba mallam Hamza wanzami ya fito Yana dube duben son ganin me yin sallama dashi, ganin mallam Umar yasa yayi gaggawar tsinke annurin fuskarsa.
Malam Umar ya Mika masa hannu sukayi musabaha sannan yace ” mallam Hamza wajenka nazo ina son muyi wata yar magana”. Malllam Hamza ya Kara tamke fuska yace ” to ina jinka Allah dai yasa lafiya” ya gyara tsaiwarsa yace ‘ lafiya lau,illa dai nazo ne akan maganar Yara da suke son junansu”. Yace ” wane Yara fa Kenan?”
Duk da mallam Umar ya fahimci akwai nau’i na wulakanci acikin maganar mallam Hamza to hakan baisa ya ji haushi ko ya nuna damuwa a fuskarsa ba yace “Yara Dan wajenka Kabir da yar wajena muhseena “. Yayi masa wani irin kallo yace ” yar rukonka da dai ba yarka na” mallam Umar yace ” koma dai menene, to Akan maganar su nazo” ya shafi gemunsa Yana dubansa yace ” to me ya faru kazo.”
Mallam Umar yace ” muna da bukatar aurar da ita ne shiyasa nace bari nazo muyi magana, atakaice ma dai na ba Kabir auren muhseena “. Mallam Hamza yayi gaggawar cewa ” aah bamu Karba ba , don me zaka zo kace kaba Kabir ita sai kace wata kosai ko dabino, ko an gaya maka muna da bukatar aura ma Kabir ita ne” mallam Umar yace ‘ haba mallam Hamza me ya kawo wannan maganar daga magana me dadi ” yace Yana kokarin kallonsa ” wace magana ce me dadi , don anzo ance an ba danka Yar shege shine abin dadi , to ina son Ka saurare ni ba Kabir ba muhseena take ko wa, bashi ba ita na raba tsakaninsu, saboda haka don Allah kabar wannan maganar anan kaje idan ta Sami wani Mijin tayi aurrenta amma ba dai da na ba.”
Mallam umar yayi dif haushi fa da takaici suka kama Shi ,yace ” Amma ban ta ba tsammanin Jin wannan maganar daga bakinka ba, meye ya kawo maganar yar shege bayan kunsani duk abinda ya Sami mahaifiyar yarinyar nan tsautsayi ne da kaddara Kuma babu Wanda ya wuce Allah ya jarafce Shi” yayi masa kallon tsaf yace ” tsautsayi da kaddara ko son abin duniya da kwadayi” yace ” haka dai kuke gani tunda ba Kwa yima kowa Uzuri ba Kuma Kwa son ku yima mutane kyakkyawar shaida ” mallam Hamza yace ,” nifa babu abinda ya dameni kawai dai Kabir dans bazai auri muhseena ba fakat magana ta kare” mallam Umar yace cikin raunanniyar murya” don Allah mallam Ka tsaya Ka fahimceni yaran nan suna son junansu ayi hakuri kusa albarka ayi auren nan ” ” har abada babu aure tsakanin Kabir da yarinyar da bata da nasaba, kaga mallam Umar don Allah Ka wuce Ka tafi Allah ya kiyaye hanya “. Yana Gama fadin hakan ya juya ya shige gida Yana bambancin fada.
Mallam Umar yayi jugum takaici da mamakin bakin halin mallam Hamza ya kama Shi ya kasa Ciba kafarsa ya bar kofar gidan.
Har Kabir ya fito da sauri daga cikin gidan da alama mallam Hamza ya gayá masa abinda ya faru . Har kasa ya durkusa ya gaishe shi cike da girmamawa, mallam Umar ya amsa shima idanun sa na bayyanar da kaunar Kabir acikinsu.
Mallam Umar ya dago Shi Yana kallonsa yace ‘ Kabir me yasa Ka boye mana abinda ke faruwa har sai da abu yayi nisan da baza’a iya gyarawa ba”. Cikin rawar murya yace ” saboda Bana son na muhseena a damuwa duk Kuma yadda zanyi Naga na gyara Nabi Nabi Amma babu wani canji, mahaifana sun riga sun dage dole sai dai na rabu da ita, bayan Kuma zuciyata ita kadai take so”
Cike da tausayi mallam Umar yace ” sai dai kayi hakuri Kabir amma a yadda Naga mallam Hamza ya dauki maganar Bana Jin zai sakko ya karbi wannan maganar don yama ki tsayawa ya saurareni.”
Kabir ya numfasa yace ” ni Baba ko awane yanayi muhseena ta tsinci kanta aciki Zan iya aurenta Bana ko bukatar Jin gaskiyar maganar saboda ni ita nake so”. Mallam Umar yace ‘ nasani , Kabir nasan kana son mujaheeda Shi yasa nake son Ka aureta domin Kai kadaine zaka iya jiyar da ita dadi da farincikin data rasa” yayi kasa da murya yace ” don Allah Baba Ka taimakeni” ya dafa kafadarsa yace ” Ka Sami nutsuwa Ka kwantar da hankalinka Allah zai kawo mafita” Kabir yace ‘ gobe Zan bar garin amma har zuwa yanzu babu wata alama da take nuna mahaifina zai sakko daga kujerar nakin da ya hau.”
Mallam Umar yace ” kaje kayi ta addua” ya juya zai tafi asanyaye Kabir yace ” Baba yaya muhseena?” Ya juyo ya dube Shi yace ” Kada Ka damu yarinya ce jaruma me tsananin tawakkali don haka komai zai zo Mata da sauki”. Daganan ya wuce ya tafi yabar Kabir tsaye cikin matukar damuwa.komai ya Kara kwance masa.
Cikin matukar damuwa mallam Umar ya shiga gida da Ande Dije ya Fara kacibis tana kokarin zuwa turken awakinta, ta dakata tana yi masa kallon tsaf sannan tace ” meye duk Kabi Ka fita hayyacinka wani abunne ya faru da Naga gaba daya duk Kabi Ka sukurkuce*. Ya numfasa Yana kallonta yace ” gaba daya abubuwanne duk sun cabe Ande ” ta Kara dubansa tace ” to meya faru” sannu ahankali ya kwashe duk abinda ke faruwa ya gayá Mata ya Kara da cewa ” to yanzu ma daga gun mahaifinsa nake gaba daya ya tsayama ya saurareni Kiri Kiri mutumin nan yaki, Shi kawai dansa ba zai auri muhseena ba.”
Ta saki tsaki tace ” Kai ko kana da abin mamaki yanzu meye lefin mallam Hamza ko Kaine tsakani da Allah zaka yarda danka ya auri mara asali kayi fa adalci don haka ni banga laifinsa ba , Kuma ma ai babu wata asara tunda daga uwar har yar sun ci kudinsa sun ci kayansa babu adadi Allah ma yasa Kada ace su biya” sosai mallam Umar yasan idan ya cigaba da tsayawa yana sauraren Ande Dije babu abinda zai karama Kansa sai damuwa hakan yasa ya wuce zuwa dakin Hajara.
Zaune ya tadda Hajara tana danna ma muhseena tsumma a Saman goshinta . ” Meya sameta” ya tambaya a gigice , Hajara ta waiwayo tana dubansa tace ” zazzabi ne da ciwon kai me zafi ya kamata.”
I love your books