Washegari jikin mujaheeda yayi sauki sosai, sai dai kallo daya zaka Mata Ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa. Haj murjanatu kuwa sam bata jindadin irin kallon da mujaheeda take yi mata mai cike da tuhuma da dora laifi.
Ta tashi daga inda take zaune ta dawo kusa da mujaheeda ta zauna tana kallon ta cike da kulawa, ta Kara Ciro wayarta ta Kira Taufiq karo na kusan goma sha daya kenan data kirashi tun daga wayewar gari amma babu kiranta daya Wanda ya daga.
Ta Kara kallonta tace ” Na Kira Taufiq sama da sau goma amma yaki daga wayata.”
Mujaheeda ta waiwayo ta dubeta sosai tace ” me zaiyi Miki kike kiransa” ta dan hadiye yawu sannan tace ” Zan bashi hakuri ne ” agaggauce ta Kara kallonta ta maimaita maganar ” zaki bashi hakuri?” Ta gyada Kai tace ” kwarai da gaske matukar yin hakan zaisa ki Sami natsuwa da kwanciyar hankali to Zan bashi hakuri, Amma Kiri Kiri yaki daga wayata saboda dole sai nuna bani da kima ko daraja agunsa.”
Dai dai lokacin Àlh Mustapha labaran ya shigo cike da jindadin yadda yaga mujaheeda ta sami sauki kai tsaye ya wuce bakin gadon Yana kallonta ” mujaheeda yaya kike Jin jikin naki” ta gyara kwanciyar ta ahankali tace ” Naji sauki daddy.”
Yace ” Alhamdulillah Allah ya Kara lafiya, Kuma ina son ki daina sama kanki damuwa wacce kinsan damuwar ba zata gagara na warware Miki ita ba , saboda Auranki da Taufiq insha’Allah babu abinda zai hana Shi kasancewa.”
Cike da shagwaba tace ” Naji daddy Amma fa har yanzu bai kirani ba.”
Ya girgiza Kai yace ” Kada ki damu bai kiraki bane saboda bai San kina asibiti ba”
” Ta yaya zaisan tana asibiti bayan yaki daga Kirana babu irin Kiran da banyi masa ba Amma yaki dagawa.”
Gànin idanun mujaheeda sunyi rau rau alamun son tayi kuka yasa Àlh Mustapha labaran ya dubi Haj murjanatu yace ” Haj zo” ya Fadi maganar Yana fita daga cikin dakin ayayinda Haj murjanatu ta bishi abaya.
Daya daga cikin kujerun dake girke a waje Haj murjanatu ta zauna ayayinda Àlh Mustapha labaran ya cigaba da tsayuwa Yana kallonta sannan yace” Ràshin daga wayarsa ba wata damuwa bace tunda kina da damar da zaki iya zuwa har gidansu Taufiq ki basu hakuri” da sauri ta juyo tana kallonsa tace” gidansu Taufiq na basu hakuri?” Ya gyara tsaiwarsa yace” eh babu wani abu ni Zan iya daukarki muje ki basu hakuri komai ya wuce, bana Jin Kuma zai Zama matsala kema agareki idan akayi laakari da kema kina bukatar kwanciyar hankalin mujaheeda kina son kiga ta bar kan gadon asibiti ba tare da damuwar komai ba.”
Haj murjanatu ta yi ajiyar zuciya tana jinjina abinda Alh Mustapha labaran yake son ta aikata , sannan tayi masa kuri da Ido,
Tace ” idan na aikata abinda kace shin yaya girmama kaina zai kasance ? Yaya makomar martabata da kimata? Shin yin hakan daga min daraja zaiyi Ko durkushe darajata zaiyi?
Ya girgiza Kai yace” Babu abinda zai samesu domin kin yi abinda ya dace kiyi ne Bana Jin zai Zama matsala Ko ga tsakaninki da Taufiq illama ya sassauta al’amarin zaki Kuma Sami wata martaba wacce Baki samu ba da agidansu Taufiq,
Ina tabbatar Miki wannan abinda zaki aikata zai Zama sanadiyyar gyaruwar abubuwa da dama.”
Shuru tayi tana cigaba da tunanin maganarsa , ayayinda ya cigaba da cewa ” haka zalika mujaheeda zata jidadin faruwar hakan matuka, akalla Kuma nasan zaayi auren nan cikin kwanciyar hankali.”
Asanyaye cikin ràshin zabi ta gyada kanta tace ” shikenan babu damuwa.”
Yadanyi murmushi kadan yace ” to shikenan, mujaheeda taji sauki saboda haka idan an sallameta saimu tafi gidansu Taufiq din” Kai kawai ta gyada.
Daga bisani ta tashi ta koma cikin dakin ayayinda da Àlh Mustapha labaran ya fice zuwa harabar asibitin ya Kira Taufiq ya sanar dashi duk yadda sukayi da Haj murjanatu ya Kuma tabbatar masa da cewa mujaheeda taji sauki sosai, hakan ba karamin sanyaya ran Taufiq yayi ba saboda tun jiya daya ji labarin ciwon nata bai kara samin nutsuwa ba gani yake tamkar komai laifinsa ne.
Adaran ranar aka sallami mujaheeda bayan samun saukinta.
Àlh Mustapha labaran da Kansa ya Kira Alh Yusuf lamido ya sanar dashi suna nan zuwa shida Haj murjanatu Alh Yusuf lamido yaso Jin dalilin zuwan nasu amma Àlh Mustapha ya sanar dashi yayi hakuri har sai sun zo.
Azahiri Haj murjanatu ji take kamar zaa rabata da wani bangare na jikinta ko kadan bata kaunar zuwa gidansu Taufiq amma babu yadda ta iya idan har tana son ta dawo dai dai da yarta dole tayi hakan,
Amma can cikin karkashin zuciyarta sosai take Jin ta Kara tsanar Taufiq.
Washegari Àlh Mustapha labaran da Kansa ya tuka Haj murjanatu zuwa gidan Àlh Yusuf lamido zuciyarta cike da bakincikin abinda take Shirin aikatawa mutanen da take ganin su abanza wai sune zata je ta rokesu don kawai dansu ya auri yarta gidan yaron mijinta zata je ta bada hakuri duk isarta da izzarta.
Sun Sami kyakkyawan tarba agidan su Taufiq a falon Àlh Yusuf lamido aka saukesu hade da duk Kan wani kayan ciye ciye Amma babu abu daya da Haj murjanatu ta taba , zuciyarta na cike da alhinin abinda zata aikata Wanda dai dai yake da barin mutuncinta.
Haj saratu babu wani cikakken kwanciyar hankali atare da ita kaancewar bata San abinda ya kawosu gidan ba.
Kujerar kusa da Haj murjanatu ta samu ta zauna tana adduar Allah yasa lafiya.bata dade da Zama ba Taufiq yayi sallama ya shigo Kai tsaye kasan kafet din ya samu ya zauna.
A kaiksice Haj murjanatu ta watsa masa harara haushinsa take ji sosai aranta.
Cikin girmamawa ya gaishesu bayan sun amsa ne.
Alh Mustapha ya gyara zamansa yace.”
Abubuwa sun faru marasa dadi musamman Kan lefen da aka kawo , Wanda abinda ya biyo bayan kawo lefen yayi sanadiyyar da Taufiq ya tabbatar ma da mujaheeda cewar ya fasa auren ta hakan yayi sanadiyyar tashin ciwon mujaheeda harda kwanciya a asibiti jiya aka sallamota.”
Haj saratu da Alh Yusuf lamido suka saki salati, Alh Yusuf lamido yace cikin ràshin jindadin abinda yafaru yace ” subhanallah,yaya jikin nata yanzu” ,Alh Mustapha labaran yace ” aah ta Sami sauki Alhamdulillah, dalilin da yasa kenan Muka taho saboda Haj tana da abinda take son ta fada muku.”
Nan da nan Haj murjanatu taji tamkar an dora Mata dala da gwauron dutse aka musamman yadda taga duk sun zubo Mata idanu, daker bakinta ya iya budewa tace ” maganar fasa aure bayan saura Bai wuce mako daya da wani abu ba bai taso ba, dalilin da yasa kenan nace Zan zo na ba da hakuri,”
Cikin matukar mamaki Haj saratu da Alh Yusuf lamido da Taufiq suka shiga kallon kallo na mamaki, ta cigaba da cewa ” saboda haka Taufiq kayi hakuri Ka janye wannan maganar ,Kuma ina son Ka sani duk abinda nayi yanzu saboda yata nayi saboda ina bukatar Samun natsuwarta, tunda Allah ya jarafceta da sonka ya Zama dole nayi hakuri na rungumi hakan amatsayin kaddarar rayuwa ta.”
Alh Yusuf lamido ya gyara zaman gilashinsa a Ido sannan yace “haba Haj don wannan har sai kin zo kin bada hakuri bayan irin wautar da Taufiq yayi da gsnganci ai wannan auren idan kinga bai tabbata ba to sai dai wani hukuncin ubangijin don haka babu komai ai dama baku zo ba.”
Alh Mustapha labaran yace ” aah gara da muka zo tayi laifi ta Kuma zo ta bada hakuri hakan ya wadatar Allah yasa ayi damu Allah Kuma ya kauda duk wata fitina dake ciki” gaba daya suka amsa da Amin ,Haj saratu tace ” komai ya wuce Haj babu damuwa ai mun riga mun Zama daya,”
Ita dai Haj murjanatu tunda tayi shuru bata Kara cewa komai ba saida ta Mike ta dubi Àlh Mustapha tace ” mu je ko?”
Daganan tayi musu sallama fuskarta babu yabo babu fallasa.har mota Alh Yusuf lamido da Taufiq suka rakasu haka zalika saida suka ga tafiyar su sannan suka dawo gida.
Suna shigowa Haj saratu ta dubesu cike da mamaki tace ” lalle Haj murjanatu tana matukar son mujaheeda ai Bana Jin duk duniya Akwai Wanda ya isa ya take izzar Haj murjanatu harta tsaya bada hakuri, ko banza yau mun kafa tarihi gara da kayi haka Taufiq”
Alh Yusuf lamido yace ” aah baiyi dai dai ba Kuma Kada Ka sake yin hakan ko da wasa, yanzu da wani mummunan abin ya samu yarinyar nan wa zaa rike a matsayin sila idan ba Kai ba ,nace Kabi komai ahankali tunda yarinyar tana sonka angama me wahalar na Kuma sha gaya maka bazan taba yarda Ko barin yar Alh sulaiman ta wulakanta ba duk yadda zanyi zanyi domin ganin na kare kima da darajata,”
Ya dubeshi sosai Ido cikin Ido yace ,” Na rantse maka Ko Kai zaka wulakanta mujaheeda Ko Ka bata Mata Zan iya mamcews da cewa Nina haifeka Zan iya bata maka fiye da yadda baka tsammani, don har abada bazan tabs mantawa da abinda mahaifinta yayi min ba arayuwa.”
Ya Kara kallonsa sannan yace ” don haka Ka shiga taitayinka duk ranar da Ka Kara Zama sanadiyyar tashi ciwon mujaheeda zaka hadu da fushina matuka “
Yana gama fadin haka ya shige falonsa ayayinda Haj saratu da Taufiq suka bishi da kallo.
Haj saratu Kam tasan yadda maigidanta ya dauki Mahaifin mujaheeda bai hadashi da kowa ba kamar yadda yake kallon mujaheeda tamkar yar da ya haifa tabbatas tasan abinda ya fada haka yake zai iya batawa da Taufiq akan mujaheeda,
Kai wannan aure na mujaheedan da Taufiq akwai kalubale acikinsa, ita Kam Haj saratu tana tare da danta duk inda yafi Samun natsuwa nan take babu yadda zaayi taki danta saboda mujaheeda.
Har Taufiq ya koma bangarensa maganganun mahaifinsa nayi masa yawo akunne shin wane irin matsayi mahaifinsa ysba mujaheeda da har yake iya Jin zai iya bata masa akanta.
Batun yau yake ma Kansa wannan tambayar ba amma dai abinda yasani ne shine mahaifinsa na matukar son mujaheeda adalilin kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da mahaifinta.
*****
Karfe takwas na dare Taufiq ne zaune cikin falon gidan Haj murjanatu cikin kawatacciyar kwalliyarsa sai tashin wani kamshi yake na musamman.
Gefensa mujaheeda CE kallo daya zakayi mata kasan Tasha wahala nan da nan duk ta rame.
Duk maganganun da Taufiq yake yi batace komai ba , sai da GA bisani ta dube Shi cike da so da Kauna tace
“Zan rokeka wata alfarma daya ?” Ya kafeta da tsararrun idanunsa yace ” ina jinki” ta maida bayanta ta kwantar sosai Kan kujera tana kallonsa sannan tace ” don Allah don son Annabi ina rokonka da cewa Ko zuwa gaba Kada Ka Kara kokarin hukuntani da Kalmar rabuwa atsakaninmu, ina son Ka sani babu wasu munanan kalmomi agareni da suka wuce kace zaka rabu da ni da Kuma zaka min kishiya don Allah na rokeka Ka taimaka min Ka hana kunnuwana Jin wadannan kalaman har abada.”
Taufiq yayi shuru Yana cigaba da kallonta ,ba tare daya Ce uffan ba ta cigaba da cewa” ina son Ka sani ina yi maka son da bazan iya rabaka da wata mace ba ina matukar kishinka bazan taba iya yarda Ka hada ni da wata acikin zuciyarks ba, kamar yadda bazan iya jurar Jin cewa Ka fasa aurena ba ” ta tsaida idanunsa sosai akansa tace ” kaga wadannan kalaman guda biyu ,zaka rabu da ni da zaka min kishiya to suna iya yin sanadiyyar rasa rsyuwata,,,,,,?
A gaggauce ya dakatar da ita Yana kallonta , yace ” ki daina furta Kalmar mutuwa Kan abinda kinsan bazan iya aikatawa ba, Kalmar bazan aureki ba damuwa CE tasa ni fadar haka amma bana nufin hakan har cikin zuciyata , Kalmar Zan Miki kishiya Kuma ki ajeta a gefe saboda ni ba me raayin auren Mata biyu bane ke kadai kin isheni rayuwa.”
Mujaheeda ta lumshe Ido cike da farinciki da jindadi tace ” nagode ina rokon Allah yabarmu tare.”
Hira suka cigaba da yi sosai suna cigaba da tsara yadda sha”anin bikin zai kasance. Sai da dare yayi sosai sannan sukayi sallama ya tafi.
Sosai yake Jin kaunar mujaheeda na Kara Samun matsuguni acikin zuciyarsa. Haka itama mujaheeda ranar kwana tayi tana farinciki idan ta tuna Taufiq yace ita kadai ta isheshi bazai taba yi Mata kishiya ba ta yarda da maganarsa ta Kuma dasata aranta. Tikisa !.
An Gama komai a sabon gidan da Taufiq zai zauna da mujaheeda yayi matukar kyau kwarai da gaske.
Sannan anyi Mata danki na garari na gani na fada duk kayan da aka sa Mata babu Wanda aka saya a Nigeria hakika an kashe dukiya a dakin mujaheeda.
Duk wani shirye shirye angama na daurin aure .zuwa lokacin kuwa mujaheeda ta Sami lafiya sosai.
Tun ranar talata aka fara shagalim biki . Sai ana gobe daurin aure da daddare Haj murjanatu ta bukaci ganin Taufiq wani karamin falonta suka zauna daga ita sai Shi .
Ta dube Shi tace ” Taufiq na bukaci ganinka ne saboda wata muhimmiyar magana da nake son mu tattauna ” yadan gyara zamansa yace ” ina jinki”
Ta muskuta taca ” Nasan baka da bukatar na sanar da Kai irin son da nake ma mujaheeda domin kasani , hakan yasa nake son na tunatar da Kai mujaheeda ta rasa mahaifinta bata da kowa sai NI sai mijina sai Kuma Kai Wanda nan gaba kadan zaka iya kwace duk wani gurbinmu agurinta, haka zalika kasan irin lalurar da mujaheeda take da ita tun tana yar karamarta lalurar ciwon zuciya Wanda hakan Yana daya daga cikin abinda yake tilsta min wadata ta da duk abinda take so da Kuma korar damuwarta tare da shawo Kan matsalolinta,
Saboda Kada ciwonta ya tashi ko ya Kara Samun wani sabon salon.”
Ta numfasa sannan ta cigaba da cewa ” na ba yata dukkan gata na Kula da ita da bukatunta don haka Bana son ta nemi wani abu ta rasa arayuwarta agidanka don haka na kiraka domin kayi min wani alkawari.”
Yayi saurin kallonta yace ” alkawari? Wane irin alkawari kenan.”
Ta dubeshi Ido cikin Ido tace ” tunda mujaheeda ta mallaki hankalin kanta na fahimci tana cikin sahun Mata masu matukar kishi musamman akan abinda take so duk duniya Kuma babu wani abu da take so sama da Kai, hakan yasa kullum nake kwana na tashi da tunanin yadda zaayi mujaheeda ta rayu agidanka ba tare da kishiya ba.”
Ta muskuta sannan tacigaba da cewa ” shiyasa nake son kayi min alkawarin ba zaka tabs yima mujaheeda kishiya ba matukar tana raye zaka yi hakuri Ka rayu da ita ba tare da kishiya ba.”
Duk da Taufiq baida sha”awar Zama da Mata biyu tofa hakanan yaji ya samu Kansa da faduwar gaba da ràshin natsuwa.
“Bakace komai ba.”
Ya numfasa gami da kokarin tattaro hankalinsa guri daya yace ” Haj Shi Kara aure ai kaddara ce daga cikin kaddarorin da Allah yake kaddarama bayinsa……?
Tayi saurin katse Shi tace ” kawai alkawari na roka kayi min basai kayi min wa”azi ba” ya gyada Kai yace” ni Bani da shaawar auren Mata biyu ban taba ma wannan tunanin ba “
Haj murjanatu ta dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu lokaci daya ta Mike zuwa jikin wata kyakkyawar durowa ta bude tasa hannu ta Ciro wata tskarda hade da biro ta dawo kusa da Taufiq ta Mika masa tace ” tunda baka da ra’ayi to Alhamdulillah ga tskarda nan kasa min hannu.”
Ta Mika masa takarda ya Karba ita Kuma ta koma ta zauna tana kallonsa.
Ya bude takardar Yana karantawa takarda CE me nuna cewa bazai taba yima mujaheeda kishiya ba gashinan a rubuce sa hsnnunsa kawai ake bukatar.
Hakanan yaji zufa tana karyo masa duk da sanyin da ake yi.
Tace ” idan har da gaske ne abinda Ka fada ,to ga tskarda nan kasa hannu, idan Kuma har Ka fada da ysudara ne to Ka Miko min takarda ta”.
Shin me yasa baya son sa hannu atakardar bayan har cikin zuciyarsa yasan abinda ya fada gaskiya ne?. Taufiq yayima Kansa tambaya.komai ya tsaya masa , tunaninsa ya tsaya cak!
Amma duk da haka baisan dalilin da yasa ya Sami Kansa da sa hannu Akan takardar ba.
Haj murjanatu ta cika da farinciki bayan ya miko Mata takardar ta amsa tana murmushi , tace ” yanzu na tabbatar da kana son mujaheeda, Allah yasama aurenku albarka”
Asanyaye ya amsa cikin ràshin karfin guiwa , ta dubeshi tace ” shikenan kana iya tafiya.”
Ahankali ya tashi yayi sallama da ita ya fita hakanan yaji damuwa da danasanin sa hannu a takardar suna son su kamashi , duk da yaso ya tsaya yaga mujaheeda hakanan ya wuce ya tafi gida saboda ràshin jindadin zuciyarsa Wanda ya rasa dalilin hakan.
Kai ma ai ka yi mistake ka sa hannu, abin da ba karfin ka ba ne sai na Allah ai shi kadai ya san gaibu
Fatan alkairi agareku