Washegarin asabar karfe biyu da rabi, na rana aka daura auren Taufiq Yusuf lamido da mujaheeda sulaiman a babban masallacin jumaar dake unguwar.
Farinciki wajen mujaheeda baa magana.
Hankalinta bai tashi ba sai da zaa kaita gidanta Haj murjanatu ita ke rungume da mujaheeda tun daga mota har cikin katafaren gidanta.
Gida komai yaji sai dai fatan zaman lafiya.
Saida Haj murjanatu zata tafi ita da sauran Yan rakiyar ta sannan ta Ciro makullin sabuwar mota ta mikama mujaheeda wacce take ta aikin kuka ta rike hannunta ta saka Mata makullin motar tace “Ga makullin sabuwar motarki nan.”
Mujaheeda ta juya ta rungume mahaifiyarta tana cigaba da kuka me karfi, hakan yasa itama Haj murjanatu ta fashe da kuka.
Shin duk duniya idan ba aure ko mutuwa ba me zai rabata da gudan jininta mujaheeda.
Sun ci kuka har sun gaji daga bisani daker mujaheeda ta saki Haj murjanatu ta samu ta tafi cikin matsananciyar damuwa.
Tana adduar Allah ya hada mujaheeda da dukkan farinciki agidan aurenta.
Bata taba Jin damuwar ràshin Kara haihuwa ba tun daga mujaheeda irin na yau, domin dai tana cikin matukar kewar yarta har ta Kai gida kuka take Mai ratsa zuciya.
Ita ma can mujaheeda ba karamar wahala Taufiq yasha ba wajen ganin ya kwantar da hankalin ta saboda yadda take kuka kamar ranta zai fita.
Daker Taufiq ya samu ya shawo kanta ta hakura. Aranar ya maida mujaheeda cikakkiyar mace, ta Kuma Sami karin martaba da daraja agun Taufiq kasancewar ta Kai budurcinta dakin mijinta.
Kwana uku da aurensu Taufiq ya dauki mujaheeda ya kaita gidansu.can yabarta ya wuce office.
Sosai Haj saratu ta Kula da ita sai dai abu daya ta Lura dashi shine mujaheeda babu abinda ta iya sai kwanciya.
Hatta abinci da aka kawo Mata nan ta tsakura tabarshi atsakiyar falon Haj saratu ta kasa koda kauda kayan ballefa tace zata tashi tadan Mata wani aikin ko ba yawa. Tana nan dai akwance bata da wani aiki Saina danna waya.
Wanda Haj saratu batayi màmaki ba idan akayi laakari da irin gatan data fito ciki, sai dai ta wani bangaren zuciyarta ta Sami kanta da tausayama Taufiq domin dai tasan abubuwa da dama da Mata yakamata tayima mijinta bazai samu ba.
Ko da yazo tafiya da ita haka Haj saratu tayita binsa da kallon tausayi.
Ita Kam mujaheeda ta tabbatar tayi dacen surukai don yadda suka dauketa tamkar su suka haifeta musamman Àlh Yusuf lamido da ya fito sosai a matsayin mahaifinta ya tabbatar mata duk abinda Taufiq yayi Mata ya kasance shine mutum na farko da zata zo ta gaya masa zai tsaya Mata zai kare kimarta ba Kuma zai tabs yarda Taufiq ya zalunceta ba ko yaya ne.
Idanta tuna maganganun Àlh Yusuf lamido takan ji wani irin sanyi aranta.
Masu aiki uku Haj murjanatu ta kawoma mujaheeda.babu abinda take yi sai dai taci ta koshi ta kwanta tana aikin chatting.
Duk bukatun Taufiq tun daga Kan abinda zai ci, wankin singileti da gajerun wandunansa da kawo masa abinci duk masu aiki ne sukeyi masa babu ruwan mujaheeda.
Duk da Taufiq bai jindadin hakan to ya danne saboda Yana ganin abin a farko kila don bata Saba bane Amma Yana ganin nan gaba kadan zata karbi ragamar gidanta da Kuma kulawa dashi yadda ya dace.
Yau asabar Wanda yayi dai dai da makwanni hudu da auren Taufiq da mujaheeda, Haj murjanatu ta bukaci ganinsu.
Karfe uku da kwata na rana duka suna cikin falon Haj murjanatu.
Wani farinciki ne ke ratsa mujaheeda data ganta agida duk da kasancewar zuwanta na biyu kenan tun bayan aurenta , haka zalika itama Haj murjanatu tana zuwa kusan duk bayan kwanaki hudu don taganta taga Kuma halinda take ciki.
Haj murjanatu ta dubi Taufiq sosai sannan tace , ” Wata muhimmiyar maganace tasa nayi kiranku.”
Mujaheeda tadan sassauta da danne dannen wayarta tana kallon mahaifiyarta, yayinda Taufiq ya gyara zamansa ba tare da yayi magana ba, sai dai zuciyarsa na adduar Allah yasa ba wata fitinar bace zata bullo da ita, tunda bata gajiya da tsurfa.
Tadan muskuta sannan ta cigaba da cewa ” sanin kankane mujaheeda tayi karatunta har zuwa matakin degree ta Kuma fita da sakamako mai kyau” ya gyada Kai alamar hakane , ta cigaba da cewa,” saboda haka duk da mujaheeda bata rasa komai arayuwarta ba hakan bashi zaisa a dankwafeta acikin gida ba a matsayin asalin matar aure, dole itama tana da bukatar ta fita tayi mu’ amala ta cudanya da mutane saboda ko babu komai shima karin ilimi ne Kuma zai rage Mata zaman gida bayan kaima Ka tafi office.”
Mujaheeda ta danyi murmushi har kullum tana mamakin yadda mahaifiyarta take saurin gane abinda zai sata farinciki. Ta yaya ta gane zaman gidan baya Mata dadi musamman idan mijinta baya nan , bata saba rayuwar kulle ba duk inda taso zuwa tana zuwa, don haka maganar mahaifiyarta gaskiya ne babu dalilin dunkufewa agida bayan kowace mace yanzu kokari take ta tashi tsaye.
Haj murjanatu ta katsema mujaheeda tunaninta ta hanyar cewa ” hakan yasa nayi tunanin maida mujaheeda shugabar daya daga cikin kamfanonin mu , Wanda Zan bata takardun Duka kamfanonin ta bisu daya bayan daya ta zabi Wanda take ganin zata iya jagoranta,”
Ta juyo ta dubeshi Ido cikin Ido tace ” Kai Kuma aikin kane Ka yarda Ka amince Mata tayi aiki saboda duk karuwar kanka ce “.
Kan Taufiq yayi nauyi hakika bai taba tsammanin Jin hakan ba don da yayi zaton hakan da tun farko ya sanar dasu baida shaawar matarsa tayi aiki amma bazai hanata yin kasuwanci daga gida ba.
“Kayi shuru” cewar Haj murjanatu, ya dago Kansa ya dubi murjanatu yayi mamakin yadda ya hango farinciki a makale a fuskarta Wanda hakan ya tabbatar masa da cewa tana goyon bsyan maganar mahaifiyarta.
Ya dauke kallonsa akanta Yana saka abubuwa da dama acikin zuciyarsa, zahiri baya son matarsa tayi aiki Kuma bazai iya barinta ba saboda baiga dalilin yin aikin nata ba don kuwa babu abinda ta nema ta rasa don haka babu dalilin yin aikinta.
“Kai nake saurara ” akaro na biyu Haj murjanatu ta Kara yi masa magana.
“Yaya Taufiq kayi magana mana amincewarka kawai mummy take nema.”
Ya numfasa ahankali sannan yace ” mummy ni a tunanina babu wani amfanin aiki ga mujaheeda, tunda bata nemi komai ta rasa ba.”
Nan da nan mujaheeda ta canja fuska tana kallon Haj murjanatu ganin yadda fuskarta ta nuna yasa Haj murjanatu ta tabbatar ma kanta cewa mujaheeda fa tana bukatar aikin nan , don haka ta dubeshi tace ” kaji wata magana, Dama ana yin aikine idan aka Rasa wani abu ai ana yin aiki KO don Samun ilimin rayuwa bawai kasasshene yake yin aiki ba Kuma yanzu don kawai babu abinda ta nema ta rasa sai ta kasa fitowa tayi aiki aah kadaima ma wannan maganar mujaheeda dole zatayi aiki.
Ya dubeta sosai ysce ” idan na amince ko ?” Cike da mamakin maganarsa duk suka dubeshi.
Haj murjanatu tace ” shiyasa na kiraka saboda Ka amince din.”
Ya girgiza Kai yace ” To gaskiya mummy bani da raayin matata tayi aiki shiyasa bazan iya barinta tayi aiki ba, Amma Zan iya barinta tayi kasuwanci tana daga gida tunda yanzu akwai cigaba tana zaune zata saya Kuma ta sayar.”
Mujaheeda ta turo Baki cike da sangarta tace ” Amma ni yaya Taufiq nafi son aikin fiye da kasuwanci idan Kuma kace haka to Zan hada Duka nayi aikin da kasuwancin.”
Ya girgiza Kai yace ” kada kijama kanki damuwa ba gaira ba dalili domin dai ni bazan barki kiyi wani aikin kamfani ba, bayanni banga wani dalili ba.”
A fusace Haj murjanatu tace ” aah wai yayane Naga kana wani zakewa Kana nuna wata isa Ko don kawai kana ganin yanzu ikon mujaheeda ya dawo hannuna” ya girgiza Kai yace “ba isa nake nunawa ba, ikon mujaheeda Kuma daya dawo hannuna bani na ba Kaina ba Allah ne ya bani, haka zalika iya gaskiya ta na shaida Miki bazan iya barin mujaheeda tayi aiki ba gaskiya.”
Nan da nan ran mujaheeda ya Fara baci tayi saurin kallonsa tace ” Amma kasan mummy fa kake gayama wannan maganar.”
“To menene aibun maganar dana fada, don an rokeni abun da bazan iya badawa ba.”
Haj murjanatu tace rai abace ” ta yaya kuwa zakaga aibun maganganun da kake fada bayan kafi kowa sanin dai dai , waye Kai dazance Ga abinda zanyi da yata kace aah , mujaheeda zatayi aiki fakat babu sauran magana.”
Taufiq shima zuwa lokacin ransa ya Fara baci , hakan Yana ya tashi Yana cewa ” ba wani bane illa Mijin mujaheeda, Kuma na riga na yankema Kaina cewa mujaheeda ba zatayi aiki ba” ya wauwaya ya dubi mujaheeda ba damu da fushin dake makale akan fuskarta ba yace ” ina waje ina jiranki idan kun gama.”
Yana Gama fadin hakan bai saurari komai ba ya fice Haj murjanatu ta bishi da Ido cike da mamaki.
Ta dubi mujaheeda tace ” zo nan * a shagwabe ta taso daga wajen zamanta ta fada Kan cinyar mahaifiyarta ayayinda ta cigaba da shafa Saman bayanta tana cewa ” kinga irin ràshin darajar da mijinki yake nuna min KOe? Bai damu da ya nuna biyayya agareni ba ko bani na haifeki ba iya ràshin Kimata da zai dinga gani kenan” cikin bacin rai mujaheeda tace ” na gani mummy, Kuma duk duniya babu abinda nake so sama da Ku dinga Samun jituwa atsakaninku.”
Haj murjanatu tayi Dan Jim tana tunani ga dama ta samu na yarda zata kawo sabani tsakanin mujaheeda da Taufiq.
Tace ” yanzu me kika fahimta da abinda Taufiq ya aikata” ta girgiza Kai alamar bakomai, Haj murjanatu tace ” ya nuna baya son cigabanki, hakan ya tabbatar min da cewa Yana cikin sahun mazan da suke bakinciki da cigaban matansu, ta yaya bazai Miki bakinciki ba kina hawa motar data fi tashi kina kashe kudin da bazai iya kashewa ba to ta yaya Kuma zai barki a kiraki da manajan kamfani da zakiyi aiki ba a karkashin kowa ba,
Bayan Shi yana can ya kare a karkashin wani Yana kamfanin aikin hanya ana turasu suna wahala oganninsu na can suna shan raba.
Don haka yasanya bakinciki aransa.”
Mujaheeda tayi tsam da ranta tana son yarda da maganar mahaifiyarta amma son Taufiq na kokarin hanata dora masa wannan mummunar dabiar , duk da dalilan da mahaifiyarta ta bayar zasu iya Zama gaskiya Amma ta kasa yarda,.
Sai dai abu daya ta sani wannan Karon sun Sami bambanci ra’ayi tsakaninta da Taufiq domin dai tabbas tana son yin aiki, dole Kuma zatayi,
Haj murjanatu ta dago Kan mujaheeda tana kallonta tana son ganin tasirin da maganganun ta suka yi a wajenta ,tace ” saboda haka ya rage ruwanki kiyi yaki ki kwaci yancinki tun kafin abin yayi nisa aiki dai tunda kina so sai kinyi Shi , saboda haka ki nemi hanyar dazai amince ,domin idan lokaci yayi ina son ki sani ko ya amince ko bai amince ba zaki yi aiki .”
Ta gyada Kai tace ” Bakomai mummy zanyi magana dashi.”
Ta gyada Kai ta zuba Mata Ido tace ” akwai matsala ne ” ta girgiza Kai tace ” bakomai mummy ina godiya.”
Tayi murmushi tace ” babu godiya atsakaninmu duk abinda kike so ko meye wahalarta ki fada zaayi Miki.”
Tayi dariya har gefen kumatunta suka lotsa tace ” Allah yabar min mummy na.”
Sosai mujaheeda ta dauki lokaci kafin ta fito domin zuwa lokacin Taufiq ya kawo wuya saura kadan ya tafi ya barta sannan ta fito yadda ya hade rai itama haka ta hade rai, harta shiga motar yaja suka tafi babu Wanda yacema wani uffan.