Lallausan murmushi ta saki jin cewar yana ƙofar gida. Mai gadin gidan ta kira, tayi mishi umarnin a buɗe ma babban baƙonta ƙofar gida ya shigo da motarsa.
Sai kuma ta kira ɗaya daga cikin ƙannenta biyu da suke zaune tare da ita da ƴaƴanta ta bata umarnin ta shigo da baƙonta cikin falon. Daman tun tuni ta sa sun ƙalƙale ko ina an baɗe shi da turaren wuta.
Tun ɗazu ta yi wanka, zaman jiran ƙarasowarsa take yi Ramlah ta kai mata saƙonta.
Tun da ya shigo cikin kaduna ya faɗa mata ya iso, ko da ya ce mata gida zai fara zuwa yayi wanka har da kukanta na kissa.
Cikin shagwaɓa ta roƙe shi to don Allah idan ya je gida kar ya daɗe, tun ɗazu ta gama shirya mishi kayan abinci ta yi kwalliya zaman jiranshi kawai take yi.
Ta sake ƙasa ƙasa da murya tana ɗan jan hanci, kamar har lokacin kuka take yi ta ce
“Aban Twince, ka ganni zaune hannuna a kunci, idanuna sun ƙure ƙofar shigowa da kallo, babu abinda suke so da buri sai suyi tozali da kyakkyawar fuskarka mai cike da annuri da haske, irinna mai riƙo da Addinin musulunci.
Hancina a buɗe yake, babu abinda yake muradi sai ya shaƙi daddaɗan ƙamshin da jikinka ke fitarwa Nawan.”
Kunnuwana a burbuɗe suke, babu abinda suke kwaɗayi sai suji saukar sautin tattausan muryarka mai cike da amo da kwarjini na ingarman namiji.
Don Allah ka tausaya ma zuciyar da kullum take ta tsallen daka tana jiran isowar abokin soyayyarta.
Kar ka bari Aunty Fareeda ta tsare ka da surutunta har mu bushe ni da abincin da na shirya maka wajen zaman jiranka.”
Daga haka ƙit ta katse wayar, tana jin shi yana ta sauke numfashi sama-sama tsabar yadda kalamanta suka rugurguza ɗan ragowar kuzarinshi.
Da yake ɗan halas ne, ko da ta kalli agogo yanzu sai ta ga mintuna arba’in da bakwai kenan da gama wancan wayar tasu. Lallai Mukhtar za’a je da shi.
Ashe ma bashi da wahalar sha’ani kamar yadda kullum Fareeda take cewa,
“Ke ƙyale ni, Mukhtar murɗaɗɗen mutum ne. Lallaɓawa nake yi ina haƙuri don mu zauna lafiya.”
Tunanin Fareeda a wannan gaɓar da tunanin irin maganganun da suke yi a lokuta mabanbanta yasa ta jan tsaki ƙasa-ƙasa.
“Ƙawata lafiya kuwa?”
Ramlah ta tambayeta.
“Ba komai ƙawata. Wani banzan tunani ne ya faɗo min arai. Ki jira ni anan pls in sallami Aban Twince, idan ya tafi sai in baki cikon kuɗin.”
Ta miƙe da hanzari ta fara sabunta kwalliyarta, a fuska kaɗai za’a kalli Fatima asan tana cikin matsanancin farin ciki.
Cikin lokaci kaɗan ta rambaɗa wani ubansun kwalliya, kamar wacce za ta je gasar fitar da sarauniyar kyau ta jihar kaduna. Ta ɗauko wani ɗan ubansun leshi da aka yi mata ɗinkin doguwar riga, daga sama ya kamata tsam, daga gurin gwuiwarta zuwa ƙasa sai rigar ta baje. Ta ɗauko wani siririn gyale da zai shiga da leshin ta rataya a kafaɗa, ta yi kyau sosai.
Ƙawarta Ramlah sai zabga mata kirari take yi ita kuma kanta yana ƙara kumbura. Daga bisani ta fice daga ɗakin da salon tafiyar za tayi baza tayi ba, tana wani rangaji kamar reshen bishiya a iskar damina, hannunta riƙe da wannan turare wanda Ramlah ta karɓo mata.
A ƙofar shiga cikin falon ta tsaya ta buɗe turaren ta zuba fiye da rabi a jikinta, nan take gurin ya ɗume da wani irin ƙamshi mai tafe da ƙauri-ƙauri.
Ita kanta ƙamshin baiyi mata ba, amma kasancewar turaren magani ta san dole za’a ji haka, wataƙila a hancin wanda aka siya turaren dominsa tattausan ƙamshi mai matuƙar kwantar da hankali zai shaƙa.
Tunanin hakan ya sa ta sakin murmushi. Ta maƙale muryarta ƙasa sosai da wani irin salo na jan hankali tayi masa sallama, ta jira ya amsa sannan ta yaye labulen ta sa kanta ciki.
Suna haɗa idanu a tare su biyun suka sakarma juna wani lallausan murmushi, ta ƙarasa a hankali da wannan salon tafiyar nata har zuwa kusa da inda yake zaune, kan kujera mazaunin mutum uku.
A maimakon ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye falon, sai ta tsuguna a ƙasa, cikin ladabi da ƙanƙan da kai ta sauke idanunta ƙasa kamar baiwa a gaban ubangidanta.
“Haske nah, ina maka barka da zuwa akurkin muhallina a karon farko. Na ji daɗi matuƙa gaya, yau ɗin ta kasance rana mai matuƙar muhimmanci a cikin tarihin rayuwata. Barka da zuwa, ya hanya? ina fatan ka iso lafiya?”k waɗannan maganganun da take yi tana yi ne da wani irin salo na jan hankali, ga miji mai matuƙar son girma da biyayya na ƙarshe irin Mukhtar. “Mace mai ladabi duniya ce Alaji.”
Mukhtar ya faɗa a zuciyarsa. Daƙyar ya iya mazewa don kar ya bada kanshi a karon farko ya amsa gaisuwarta.
Umarni yayi mata kan ta tashi ta hau kan kujera, buɗar bakinta sai cewa
“Miji fa tamkar Ubangida yake a gurin mace mai wayau. Taya zan iya hawa saman kan kujera in goga kafaɗa da kai alhalin kana saman kujerar? A ganina babu ladabi ko kaɗan a cikin haka. Ka barni haka Aban Twince, nan ɗin ma ya isa.”
Sai ta ɗan muskuta ta gyara zama a kan kafet nan gabanshi, ta tsura mishi idanu tana kallon tsantsar kwarjini da zatin da Allah ya zuba a fuskar wannan bawan Allah.
Tunanin ko ruwa bata gabatar mishi ba yasa ta nemi afuwarsa a marairaice.
“Yi haƙuri Haske nah! kallon kyakkyawar fuskarka na neman shagaltar da ni in gabatar maka da ababen motsa bakin da na shafe tsawon yini guda ina shiryawa musamman domin kai Mijina. Ina sake neman afuwa a karo na biyu.”
Lallausan murmushi kawai ya sakar mata, shi fa ya ma kasa magana. Babu abinda yake hasasowa a zuciyarsa sai irin kyakkyawan zamantakewar da za suyi shi da Fatima. Lallai wannan ita ce abokiyar burminsa.
Sai bin ta da kallo yake yi tana jera wasu ƙayatattun kulolin cin abinci a gabansa, bayan ta janyo wani ɗan madaidaicin teburin da ake ɗora abinci a tsakiyar falo idan ba’a sha’awar zuwa dining table.
Sai da ta kwaso kayan abincin tas, da wani jug ɗin gilashi mai cike taf da kakkauran zoɓo da yasha kayan ƙamshi.
“Haske nah! Ka yi min izinin in zuba maka abincin?”
Ta tambayeshi a ladabce.
A wannan karon ma ya kasa magana, sai kai ya iya ɗaga mata alamar yayi mata izini.
Martanin lallausan murmushi ta fara sakar masa, kafin ta fara buɗe kular miya tana satar kallonshi.
Daddaɗan ƙamshin miyan agushin da ya daki hancinshi yasa shi buɗe hanci sosai ya shaƙi ƙamshin, ya lumshe idanunsa. Kafin daga bisani ya buɗe idanu ya sauke kan kayan abincin, a daidai lokacin da ta ɗauko malmala ɗaya na sakwarar da ya daku luƙwui-luƙwui ta saka masa a faranti.
A wannan gaɓar kam ya kasa shiru, sai da ya ce
“Fatina? ya aka yi kika san abincin da na fi so a rayuwata?”
Ya tambayeta yana mamaki.
Far tayi masa da idanu, ta rausayar da kanta gefe guda. Muryarta ƙasa-ƙasa da rangwaɗa ta gilla mishi ƙarya da cewa
“Haske nah! Sakwara da miyar agushi nima shi ne abincin da na fi so a rayuwata. Kawai zuciyata ce ta raya min, idan da gaske so ya kai so tsakanina da kai tabbas zai kasance abinda nake matuƙar so kaima kana son sa. Abinda nake ƙi kaima za ka ƙi shi Aban Twince, kasancewar hakan shi ne cikar soyayya.”
A zahirin gaskiya a gurin Fareeda taji yana matuƙar son sakwara da miyar agushi. Idan ta je gidan a mabanbantan lokuta tana tarar da ita tana daka sakwara. Ita kuma Fatima abinda bai dameta ba kenan, idan ta fara ƙorafi ita ko wahalar daka ba ta ji kai tsaye take faɗa mata Mukhtar na tsananin son sakwara, ko laifi tayi masa idan tana so ya huce da sauri to tayi masa sakwara miyar agushi da busasshen kifi ko kuma da naman rago. Ta yi amfani da haka ne don ƙara saye zuciyarsa._
Shi kuwa tsananin farin ciki da jin daɗi ba kunya ya tare hannunsa a baki ya sumbata, sannan ya hura mata a cikin iska.
Lumshe idanunta tayi tana dariya ta ɗan rufe gefen fuska irin alamun ta ji kunyar nan, me ta tuna kuma oho! sai ta buɗe fuskar da sauri ta saka idanunta cikin nashi. A tare suka sakarwa juna murmushi.
Sosai ta zuba mishi miyar agushin da ta ji naman rago ya dahu luguf a gefen sakwarar.
Ko kafin ta miƙa mishi har miyan bakinshi ya gama tsinkewa. Don haka bai ɓata lokaci ba yayi bismillah ya fara ci a nutse, yana yaba ɗanɗanon girkin a fili da zuciyarsa.
Tagumi ta buga da hannu biyu ta gyara zama a ƙasa nan gabansa tana sake ƙare masa kallo.
‘Wato lallai Allah Al-musawwiru ne. Ashe akwai rabon yin aure wataƙila ma har da yara tsakaninta da Mukhtar? Ba tun yanzu ba yake bala’in burgeta. Auranta na farko dattijo ta aura, wanda ya auri wata matar kafin ita ta haifa masa ƴaƴa uku duk mata sai Allah yayi mata rasuwa. Ko da ya aureta ya aura ne da sa ran za ta riƙe masa marayun ƴaƴansa, da farko kuma rigiɗi-rigiɗi kamar zaman zaiyi daɗi a tsakaninsu. Daga bisani ta tasa su gaba da makirci da bita da ƙulli rikici ya ɓalle tsakaninta da manyan yaran biyu. Duk sa ido irin na mijin kuma ya rasa gane mare gaskiya a tsakaninsu._
Daga ƙarshe dai dole a zaman ƴaƴan ya koma gaban yayar mijinta Hajiya Zainab, wacce ko ƙanƙani babu shiri tsakaninta da Fatima. Aure da rabo kuma wata goma sha ɗaya ta sunkuto ƴarta mace, aka saka mata sunan marigayiya uwar mijinta, Sa’adiyya, sai suke kiranta da Ummee. Wata shekarar na zagayowa ta sake haifo ƴa mace. Wannan haihuwa biyu da tayi a jere shi ya kawo sauƙin ƙiyayyar da Yar mijin ke mata, har sukan zauna inuwa ɗaya ba tare da ta caccaɓa mata baƙaƙen maganganu ba._
A gefe guda kuma duk da waɗannan ƴaƴa biyun da ta haifa shaiɗaniyar zuciyarta bata daina bugawa duk sa’adda za tayi tozali da Mukhtar mijin Fareeda ba. A wani lokacin har baiken kanta take gani, tana ga kamar tayi sauri wajen zaɓin mijin aure. Tunda ita ta fara aure da shekara ɗaya da rabi kafin Fareeda tayi. Wata ƙil da bata yi gaugawa ba, ita Mukhtar zai gani ya ce yana so ba Fareeda ba, tun da duk inda ɗaya za taje tare take da ɗayan.
Kwatsam kuma sai ga rasuwar mijinta bayan ta haifa masa ƴaƴa huɗu. Idan ta ce bata ji rasuwar mijinta uban ƴaƴanta ba ta yi ƙarya. Amma bayan kwaranyewar komai ta ci gaba da rayuwarta cikin walwala tare da ƙannenta biyu waɗanda ta ɗauko daga gida don su tayata zama. Da ƴaƴanta huɗu, tunda kafin rasuwar mijin ya bar wasiyar ta riƙe mishi ƴaƴanshi a gidanshi, idan za tayi aure ta ba Yayarsa Hajiya Zainab yaran ta haɗa da na hannunta ta riƙe har zuwa aurensu.
Bayan shekara guda da rasuwar mijinta sai wannan shaiɗaniyar zuciyar ta sake yunƙurowa ka’in da na’in take ƙawata mata Mukhtar. Duk sa’adda taje gidan Fareeda ta gan shi ta dinga kwainane kenan da sunƙe-sunƙe na neman samun shiga, shi kuwa a lokacin ko kallo bata ishe shi ba.
Ashe ba tare da sanin su biyun ba ƙaddarar aure zai iya shiga tsakaninsu a lokacin da basu taɓa tsammani ba. Lallai Allah da girma yake…
“Tunanin me kike yi?”
Ya tambayeta da kulawa bayan ya gama cin abincin, ƙaramin kofin da ya tsiyayi zoɓo ne a hannunsa yana kurɓa a hankali yana lumshe idanu.
“Ikon Allah kawai nake tunani Aban Twince. Ummm nace ba? Ka faɗa ma Aunty Fareeda za ka aure ni?”
“Ke tsaya, wai Fareedar ce kike ce mata Aunty?”
Ya tambayeta yana dariya.
“Uhmmm ba dole in ce mata Aunty ba? Ko da na ɗan girme mata da ƙananun watanni kuma Aminiyata ce ai gaba take da ni a gidan miji, ka ga girma dole in bata a matsayinta na uwargidan farin cikin zuciyata.
Ni dai don Allah Aban twince”
Tayi ƙasa da idanunta ta haɗe hannayenta biyu alamun roƙo.
“Duk da na san ƙawata akwaita da bala’in taurin kai, duk abinda ta so kuma zuciyarta ta kitsa mata ko ba daidai bane shi take aikatawa. Na san za ka ga tashin hankali da masifarta idan ka faɗa mata maganar aurennan, don Allah kar ka biye mata.
Ka bi ta a sannu, idan tayi haƙuri ni ba da tashin hankali zan shiga gidanta ba. Alkhairi da albarka nake so mu haɗu mu gina bisa jagorancinka Haske nah! Kayi haƙuri da haukarta pls”
Lallai bahaushe yayi gaskiya, duk girma da shekarun namiji ƙaramin yaro yake zama a gaban mace. Duk tsauri da taurin Mukhtar sai ga shi salon da Fatima tayi amfani da shi ta bala’in tafiya da shi.
Bai bar gidan ba sai misalin ƙarfe tara da rabi na dare, ko sallar isha’i bai halarta ba. Ya tafi ne bayan sun gama tsara za suyi aure nan da sati uku! in dai sun samu yadda suke so babu daɗi ba ƙari.
******
Ido a buɗe Hajiya Aisha take kallon babban ɗan nata da mamaki, bayan gama sauraren duk irin maganganun da ya taho mata dasu a wannan dare. Daƙyar ta iya buɗe baki ta ce
“Aure nan da sati huɗu Malam? (Haka take kiranshi saboda kasancewarsa ɗan fari.) To wace yarinya za ka aura a cikin wannan taƙaitaccen lokacin?”
“Fatima, Fatima zan aura Hajiya. Don Allah ki saka albarka kar ki ce min a’a.”
Ya ƙarasa maganar a marairaice, da damuwa sosai a fuskarsa.
“Wata Fatima kenan?”
Ta tambayeshi ba tare da damuwa da yanayin fuskarsa ba. Ita zancen auren ne ke ta bata mamaki, to wani rikici ke tsakaninshi da Fareedar da ita basu faɗa mata ba?
“Za ki santa ma yarinyar, Fatima ƙawar Fareeda. Wacce mijinta ya rasu kwanakin baya can…”
“Fatima dai Yaya? amma kam ta tabbata gagarumar munafuka kuma maciya amana ta ƙarshen zamani.”
Ƙanwarsa Zubaida da tayi luf akan kujera kamar tana barci ta faɗi haka bayan ta wuntsulo daga kan kujerar ta faɗo ƙasa saboda yadda maganar ta jijjigata.
Idanu ya zazzaro mata yana galla mata harara
“Wa ya kasa da ke a wannan maganar ƴar sa’ido? Ɓace min daga nan kafin in tattaka ki.”
“Yarinyar da auranta za ka taka ta Malam?”
Hajiyarsu ta tambayeshi tana jinjina kai alamun ƙarin mamaki. Sai kuma ta mayar da kallonta wajen Zubaida da ta daskare a zaune tana kallon Mukhtar.
“Shiga cikin ɗaki ki jira ni.”
Tsam ta miƙe tsaye bayan ta ɗauki wayarta da ke ajiye a hannun kujera. Kamar baza ta sake cewa komai ba, sai da ta kusa shiga ɗaki ta jiyo ta kalli Mukhtar, da ɗaurarriyar fuska ta ce
“Yaya, gaskiya baka yi ba. Amma fa ka sani, duk wanda yaci amana ko ba jima ko ba daɗe tabbas amana sai ta ci shi. Fatan alkhairi.”
Da saurin gaske ta shige cikin ɗaki ta banko ƙofar ganin ya miƙe a zafafe yana muzurai.
“Hajiya kina ganin Zubaida…”
“Zauna.”
Uwar ta bashi umarni fuskarta a ɗaure.
A sanyaye ya koma inda ya tashi ya zauna, ya saukar da kanshi ƙasa, zuciyarsa cike da addu’ar Allah yasa dai kar Hajiyarsa ta hana shi auran Fatima, don gaskiya ba ya jin zai iya bin umarninta a wannan karon.
“Me Fareeda tayi maka?”
“Ba komai.”
Ya amsa kai tsaye.
Girgiza kai tayi, kafin ta sake cewa
“To me yasa za ka auro mata ƙawarta ko in ce aminiya a matsayin kishiyarta?”
“Hajiyaaaa…. wannan auren fa ba haramun bane. Banzar magana ce kawai ta Malam bahaushe da yake wani cewa ana barin halas ko don kunya. A matsayina na namiji mijin mata huɗu na ga Fatima tayi min, ina niyyar auranta. Kuma na faɗa ma Fareeda bata tayar da hankalinta ba, har tayi min fatan alkhairi. To don Allah Hajiya menene kuma na wani damuwa ko ƙananun maganganu?”
“Babu! Fatan alkhairi Malam. Hmmm! Allah ya jiƙan Alhaji (Mahaifinsu Mukhtar da ya rasu shekaru shida baya tun Fareeda na amarya) Idan ka bar nan sai kaje gurin ƙanin mahaifinka yayi maka jagora.”
Ta faɗa har lokacin babu walwala a fuskarta.
Ya buɗe baki zaiyi magana ta ɗaga mishi hannu alamar dakatarwa.
“Maganar da ka zo don muyi mun gama ta, kana iya tafiya. Dare yayi, kwanciya zanyi. Allah ya bamu alkhairi.”
“Ameen.”
Ya amsa jikinsa a sanyaye, yana ta kallonta amma ta hana shi sake magana. A dole ba don yana so ba ya miƙe ya kama hanyar fita daga falon.
“Malam”
Ta kira sunanshi.
Ya juyo da sauri zai dawo ta sake dakatar da shi.
“Ka tsarkake zuciyarka, kayi komai don Allah. Idan ba haka ba tabbas ƙarshen ko wace gaugawa da-na sani ce da cizon yatsa, don daga shaiɗan take. Ka gaida Fareeda, sati mai zuwa ina nemanta.”