Sosai kanshi ya ɗauki zafi, ɓacin ran Hajiyarsa ba abu bane da zai murje fuskarsa ya shanye kamar babu komai.
Daga yadda ta amsa mishi ya san ta dai amince ne kawai, don ba ta da yadda za tayi. To amma shi ya zaiyi ne? zancen gaskiya bai fara neman auren Fatima don ya fasa ba.
Shi sai yau da suka yi ido biyu maganganu suka shiga tsakaninsu ya ji tabbas aurenta wajibi ne a gare shi. Aurenta shi ne zai zamo babbar maslaha tsakaninshi da Fareeda.
Kawai dai zai kwantar da kanshi ya cigaba da lallaɓa Hajiya yana bata haƙuri, ita ba mace bace mai tsananin riƙo, ya san cikin ƙanƙanin lokaci za ta haƙura ta yafe mishi.
Ganin dare ya fara yi sai bai yi yunƙurin zuwa gurin ƙanin mahaifinsa ba, kai tsaye ya nufi gida. Gajiya ke nuƙurƙusarsa yana mazewa, da yake ya sa maganar auren a ranshi yana so ayi komai da zafi-zafi, yadda ya shawo doguwar tafiyarnan ai da babu abinda zai fitar da shi a yau dai sai zuwa masallaci, ko kuma larura wacce ba’a fatan samuwarta.
Ganin wutan falon a kashe shi ya alamta mishi Fareeda ta kwanta, ya taɓe baki, ko kaɗan bai ji ba daɗi ba yadda yake ji a baya idan yana gari ya fita ya dawo ya tarar ta kwanta bata jira shi ba.
Kai tsaye ɗakinsa ya nufa, yayi tunanin zai tarar da ita ciki sai yaga saɓanin haka.
“Ma sha Allah”
Ya furta a fili cikin jin daɗi.
Ya gaji ƙwarai, hutu yake buƙata. Kuma a yadda yasan halin Fareeda kamar yunwar cikinsa shirun da tayi masa ɗazu yasan akwai rikici da bala’in tashin hankalin da zai biyo baya, duk masifa irin tasa sam ba ta tsoronsa a wasu lokuta, kuma bakinta bai cika mutuwa akan ko ma menene ba, sai dai kawai tayi shiru ba don ta rasa abin cewa ba.
Ya shirya mata, bai jin tsoron komai, duk wani rikici da za ta girgizo dai-dai yake da ita. Ita tasan a faɗa da masifa ya dame ta ya shanye.
A darennan ne dai yake buƙatar hutu, gara da ta bashi iska sa haɗu da safe, in yaso suyi duk wacce za suyi, ko ta ware ko ta warwaraye, ya shirya ma ko wanne a cikin abu biyun.
A shekarunsa na tashen ƙuruciya bazai sake yarda ya ɗauki wani zafin taurin kai da rashin jin maganar Fareeda ba. Ya kai maƙura, iya haƙuri da kawar da kai yayi, yanzu lokacinsa ne na ɗaukar matakin da yaga ya dace.
A gurguje yayi wanka, ya canza kayansa zuwa na barci, ya bi lafiyar gado. Yana kwanciya kiran Fatima na shigowa cikin wayarsa, da mamaki a fuskarsa yake kallon kiran.
Ya rasa dalilin da yasa shi jin babu daɗi a ransa, me kuma take nema bayan ɗazunnan suka rabu?
Ƙasa-ƙasa ya ja tsaki, ya danna maɓallin rage ƙara ya juya ma wayar baya. Addu’ar kwanciya barci yayi ya shafe jikinsa gaba ɗaya, yana runtse idanu babu ɓata lokaci nannauyan barci yayi awon gaba da shi.
Tun da ya shigo da mota cikin gidan tana jin shi, a wannan lokacin tana zaune ne kan darduma tana jan casbaha, bayan ta idar da shafa’i da wuturi.
Buɗe ƙofar falon da yayi yayi daidai da wani irin bugawa da ƙirjinta yayi, da sauri tasa hannun hagu ta dafe saitin zuciyarta tana jan Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Sai wani bahagon tambaya ya shigo cikin zuciyarta.
“Yanzu fa Mukhtar ɗinta daga gurin Fatima yake ko?”
“Uhmmm!”
Ta faɗa a fili, zuciyarta na sake tuna mata tsakaninta da Fatima. Aminiyarta ta ƙud da ƙud!
Fatiman da a baya babu jituwa ko na kwabo tsakaninsu da Mukhtar, wai ita ce yanzu har suka ƙulla za suyi aure…
Numfashi ta fara ja tana saukewa sama-sama cikin sauri saboda wani irin bala’in zafin kishi da takaicin cin amanar da suka yi mata.
Ta lumshe manyan idanunta da daga yammacin nan zuwa dare suka kumbura sosai, ga wani irin nauyi da suke mata saboda yawan kukan da tayi.
Ita ba jahila bace, ta sani babu haramci a cikin aurensu. Amma tsakani da Allah sun ci amanarta, ta yarda da su biyun sosai da sosai, aure tsakaninsu biyun abu ne da ko a mugun mafarki bata taɓa hasashen zai iya faruwa ba.
Wasu zafafan hawayen suka sake silalowa daga idanunta. Zuciyarta cike da saƙe-saƙen tunanika da tambayoyi mabanbanta.
“To wai shin, ta yaya aka haihu a ragaya? ko dai daman tuntuni akwai kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu ita ce suke ninke ta a baibai saboda sun maishe ta sakarya?
Inaaa… Za ta iya rantswa Babu ! Duk da Fatima gwana ce gurin ɓoye-ɓoye, da iya yima ƙarya kwaskwarima don ta zama gaskiya.
Shi Mukhtar ba mutum bane mai fuska biyu, ya sha ce mata shi fa ya tsani Fatiman nan, ruwan munafukai gare ta. Kuma yadda yake maganar a kallo ɗaya za’ayi masa asan daga zuciyarsa ne, iya zallar gaskiyar abinda ke ransa yake faɗa.
Ko rantsuwa tayi babu kaffara a baya babu wata dangantakar arziki a tsakaninsu, a cikin kwanakin nan ne dai suka ƙulla dangantakar da har ta miƙa za suyi aure.
Saboda rashin jin maganarta ne Mukhtar zai auro ƙawarta don ya girgiza duniyar nutsuwa da kwanciyar hankalinta? Tayi wani murmushi mai ciwo, tabbas ya ci galaba a kanta.
Wani ƙaƙƙarfar kuka da ya ƙwace mata yasa da sauri ta cukwuikwuiye hijabinta ta cusa a bakinta, don kar sautin kukan ya fita har ya jiyota daga ɗakinsa.
“Ƴar’uwa, yanzu ba lokacin da za ki zauna kina ɓata lokacinki akan kuka bane. Ki tashi tsaye da ibada, ki ninka ki ƙara ninkawa a cikin nafilfilin da kike yi. Allah da ya halicce ki ya halicce su biyun shi za ki fuskanta ki kaiwa kukanki, idan akwai zalunci a ciki da gaugawa zai saka miki, domin shi Allah SWT mai saurin karɓar addu’ar wanda aka zalunta ne.”
Maganganun da ƴar’uwarta Baby tayi mata ɗazu gab da za su bar gidan suka dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta kamar a lokacin take faɗa mata.
“Fareeda shalelen ƙanwata, ki kwantar mana da hankalinki don girman Allah. Kishiya ko? Anyi ma dubu bata kashe su ba ke ma baza ta kashe ki ba.
Idan matsananciyar damuwa ta turnuƙo ki ki tuna mu ƴan’uwanki da muke tsananin ƙaunarki, idan kika bari wani mummunan ciwo ya kama ki mu muke da asara ba Mukhtar ba.
Ki yawaita istigfari domin Allah ya yafe miki kura-kuranki, wataƙil laifin da kika aikata ne yasa Allah ya jarrabeki da wannan lamari ko za ki hankalta ki dawo cikin hayyacinki. Ki tuba ma Allah, domin shi ɗin mai karɓar tuban bayinsa ne ako wane lokaci.
Ki dinga faɗin Hasbiyallahu wa ni’imal wakeel. Ki ta maimaita Lahaula walaa ƙuwwata illa billah. Kiyi kuka a gaban Ubangijinki Fareeda, ki kira shi da tsarkakan sunayensa waɗanda idan an kira shi da su yake amsawa. Ki roƙe shi da kyawawan sunayensa waɗanda idan an roƙe shi da su yake bayarwa. Ki yawaita maimaita Ya Allah ka jiɓanci lamurana, ka zama gata na, ka shirye ni shiriya madaidaiciya, ka kawo daidaito tsakanina da mijina. Ya hayyu ya ƙayyumu ka kawar da shaiɗan ko shaiɗaniyar da take tsakaninmu.”
Shawarwarin Aunty Murja gareta kafin su bar gidan.
Shi kuwa Mustapha murmushin ƙwarara gwuiwa yayi mata, ya riƙo hannunta na dama ya riƙe a cikin nasa.
“Fareeda, mu maza muna so idan za muyi aure matayenmu na gida su dinga hauka da nuna mana tsananin kishinsu, hakan yana sa muyi ta jin daɗi muna ƙara manna musu hauka. Duk zafin da za kiji a zuciyarki kar ki kuskura ki nuna ma Mukhtar kin ji ko?”
Daƙyar ta iya ɗaga mishi kai.
“Na san fa ƙanwata Fareeda za ta iya, don ita ɗin mai aji ce. Duk tsananin son abu da take yi idan ya bata haushi tana aje shi gefe ɗaya ta cigaba da harkokinta lafiya kamar wannan abu bai dameta ba. Ko ta canza daga wannan halin?”
A dole ta saki murmushin yaƙe ga hawaye kaca-kaca da fuskarta. Ta girgiza kai alamar bata canza ba.
“Yauwa Luvly Sister. To yanzu amfanin wannan halin ya zo, ki yi mishi biyayya, amma ki kawar da kai a lamarinsa kin ji ko? Akwai addu’o’in da zan tura miki ta whatsapp, ki dage ki tayi, mu ma za mu taya ki. Idan kika fuskanci Ubangiji tabbas zai fuskance ki Fareeda.”
Tunanin kyawawan maganganu da shawarwarin da ƴan’uwanta suka ba ta ɗazu kafin ficewarsu daga gidan yasa ɗif ta ɗauke kukanta.
A nutse ta miƙe tsaye, hijabin jikinta ta cire ta ajiye a gefen gado. Banɗaki ta koma ta sake ɗauro alwala.
A wannan dare, kusan kwana Fareeda tayi tana sallah, idan ta gaji, sai ta zauna tayi ta istigfari, hailala, tasbihi, salatin Annabi, sai ta cigaba addu’o’i cikin kuka take roƙon Allah ya daidaita mata al’amuranta.
Ƙarfe uku da minti biyar wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita nan kan darduma. Barcin da ya zo mata da wani irin nutsuwa, kwanciyar hankalin da bata taɓa tsammanin samunsa a cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Lallai da gaske ne duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa.
Ƙarfe huɗu da minti arba’in daidai ta farka da salati a bakinta, idanunta na sauka kan agogo tayi saurin miƙewa zuwa banɗaki ta sabunta alwalarta.
Malamin islamiyarsu ya taɓa faɗa musu lokacin ketowar alfijir lokaci ne na karɓar addu’ar bayi.
Da nutsuwa ta cigaba da nafilfili tana addu’o’i a cikin sujada har aka kira sallar farko. Ta miƙe tayi raka’atanul fijr, aka kira sallar asubah ta gabatar da ita. Tana cikin yin azkhar ɗin safe wani nannauyan barci ya dinga fisgarta, daƙyar ta iya ƙarasawa tayi addu’a tabi lafiyar gado. Tana jin zuciyarta sakayau, kaso tamanin cikin ɗari na tashin hankalinta Allah ya yaye mata.
******
Tana idar da sallar asubahi ko addu’a bata tsaya yi ba ta tafi ɗakin da ƙannenta suke kwana.
Ta tarar da su kan dadduma ne, suna Azkhar, tsananin zaƙuwar da tayi suyi maganar da ke tafe da ita ta kasa jira su gama, umarnin katse Azkhar ɗin tayi musu, ta ce magana za suyi.
Hankali tashe suka yi addu’a a gurguje, suka tattara nutsuwa da hankalinsu kaf zuwa gareta.
Cikin hikima da yi ma zance kwaskwarima ta faɗa musu maganar za tayi aure, kuma Mukhtar za ta aura. Ƙure su da kallo tayi tana jira taga yanayin da za su nuna da irin maganganun da za su furta.
Sai taga gaba ɗaya su biyun shiru suka yi suna kallonta da matsananciyar al’ajabi da mamaki a fuskokinsu, kamar sun ga wata sabuwar halitta, bakunansu a buɗe.
Haushin yadda suka tsaya kallonta bayan tsawon daƙiƙun da ta ɓata tana faɗa musu maganar aurenta kawai sai ta ja wani dogon tsaki, ta daka musu tsawa cikin fushi ta ce
“Wani irin iskanci ne za ku tasa ni gaba da kallo kamar baku sanni ba?”
A tare ƙannen nata suka yi firgigit kamar masu barcin da aka sheƙa ma ruwan sanyi, sai kuma wannan ta kalli wancan wancan ta kalli wannan, aka rasa wacce za ta fara cewa komai.
Cikin hargagi da masifa ta cigaba da cewa
“Wallahi tallahi idan baku ce wani abu ba sai na ci mutuncinku da asubahinnan…”
“Kiyi haƙuri Aunty.”
Suka haɗa baki gurin faɗin haka da damuwa a fuskokinsu.
Jiddah ce ta ɗan motsa tana jin yadda mazaunanta suka yi wani irin tauri kamar wacce ta shafe awoyi a zaune, ta kalli Fatima da take ta huci na ɓacin ran da suka guma mata, da sanyi a muryarta ta ce
“Aunty Fatee, Ni fa wallahi na yi shiru ne ina warware maganganunki, kamar ban fahimci me kike magana akai ba.
Wai kina nufin Yaya Mukhtar mijin Aunty Fareeda aminiyarki shi za ki aura nan da ƙanƙanin lokaci?”
Kafin ta amsa sai da ta ƙara haɗe gabas da yamma ta murtuke fuska don kar su kawo mata wargi, kar ma dai Jiddah ta ji labari. Gara Salma tana nuna jin tsoronta a wasu lokutan.
“Eh! ƙwarai! Mukhtar zan aura, shi ne yazo gidannan jiya da daddare…”
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Me ya shiga cikin hankalinki Aunty? Wannan wane irin mummunar saɓo ne kike ƙoƙarin aikatawa?”
Jiddah ta jefa mata tambayoyin fuskarta na ƙara bayyana matsanancin mamaki da firgici.
Kallon ƙasa da sama ta watsa mata, ta san halin Jiddah sarai, idan bata yi mata na mahaukata ba baza ta ƙyaleta salin-alin ta aikata hidimar gabanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba.
“Ubanki ne ya shiga cikin hankalina, Jiddah na ce Babanki ne ya shiga cikin hankalina. Ina ruwanki da rayuwata? Da kike cewa zan aikata saɓo uwar me muka haɗa da Fareedar da ya wuce ƙawance da zaman unguwa ɗaya? Ina haramci a cikin aurena da mijinta? Wallahi akan maganar nan na shirya ja da ko uban wanene, duk wanda yasan bazaiyi fatan alkhairi ba ya rufe min ɗoɗɗoyan bakinshi, idan ba haka ba kuwa za mu hau sama mu faɗo da ko wane ɗan iska. A duniyar nan kakaf ban cire miki hula ba babu wanda ko wacce ta isa haramta min abinda yake halas a gurina…”
“Kiyi haƙuri Aunty, Allah ya sanya alkhairi.”
Salma ta faɗi haka cikin sanyin murya, zuciyarta cike da tsoro da mamakin Yayar tasu.
Ita kuwa Jiddah tun da ta hangame baki ta ɗora hannu akai bata sauke ba har Fatima taja musu wani dogon tsaki ta fice daga ɗakin cikin fushi kamar za ta tashi sama.
“Amma dai wallahi ke banza ce Salma. Ina wani alkhairi a lamarin cin amana da har za ki ce mata Allah ya sanya alkhairi…”
“To me kike so in ce Jiddah? kina ganin yadda ta ɗauki zafinnan tsaf za ta iya rufe mu da duka. Kin ji dai ta ce ta shirya ja da uban kowa a duniyar nan. Ba gara da na faɗa mata hakan ta fice ba tare da tashin hankalin ya fi haka ba? Taje can da yawarta, kila rabon fige kazar wahala ke kiranta ga auren mijin Aunty Fareeda.”
“Ai Wallahi ƙarya take yi, maganganunta a cika baki da zancen banza na ɗauke su. Inna zan kira yanzunnan in faɗa mata halin da ake ciki, baza mu zuba idanu ta janyo mana zagi da tsinuwa a cikin gari ba.”
Jiddah tayi maganganun cikin ɓacin rai tare da janyo wayarta, ta buɗe wayar kenan buf Fatima ta dawo cikin ɗakin kamar an jefo ta.
Kai tsaye gurin Jiddah ta nufa a gaggauce ta fisge wayar hannunta, ta soke a haɓar zani sannan ta riƙe ƙugu tana kallonsu cikin wani irin fushi da basu taɓa ganin tayi irinshi ba.
“Ashe daman ku ɗin ƴan iskan yara ne matsiyata ban sani ba nake zaune da ku ina taimaka muku?”
Taja wani ƙaƙƙarfan ƙwafa, ta cigaba da cewa
“To duk maganganun da kuka yi ina laɓe a bakin ƙofa ina saurarenku.
Har da ke Salma da nake miki kallon mutumiyar kirki ashe tsohuwar munafukace ke? To ku jira ni, duk sai na ci ubanku ɗaya bayan ɗaya.
Bari in gama da Inna zan dawo ta kanku don ubanku.”
Wayar Salma da yake maƙale a caji ta cire a fusace ta fice da wayoyin a hannunta fuuuuu kamar kububuwa.
*****
Ba ita ta farka ba sai ƙarfe tara da rabi na safiya. Ganin lokaci ya tafi yasa ta bubbuɗe idanunta da mamaki.
A gurguje ta faɗa banɗaki tayi wanka. Wani abu da ya saka ta cikin farin ciki shi ne, ko da ta tsaya gaban madubi tana kallon fuskarta kumburin da idanunta suka yi duk sun saɓe, saura kaɗan.
Taƙaitaccen murmushi tayi, ta ƙara gode ma Allah kwanciyar hankali da nutsuwar da ya saukar mata. Bayan ta shafa mai da powder sai ta bi idanun da kwalli ɗan kaɗan, sauran kumburin sai ya ƙarasa ɓacewa.
Bata tsaya ɓata lokaci gurin daidaita girarta ba, ɗan tacewa kawai tayi sama sama, sai suka yi wani irin gazar-gazar, su basu kwanta ba basu miƙe a hargitse ba. Ta goga man baki kaɗan a laɓɓanta.
Wata doguwar rigar roba roba mai sauƙin kuɗi da ta siya a gurin maƙwafciyarsu ta saka a jikinta, rigar ta bi jikinta ta lafe, tudun mazaunanta suka taso sosai ta bayan rigar.
Hular rigar ta saka a kanta, shi bai rufe gashinta da bata cika son kitsa shi gaba ɗaya kuma bai bar suman da yawa a waje ba, sai tayi wani irin sanyin kyau sosai, irin yadda rigar ya zauna a jikinta idan ba sani aka yi ba sai a zaci mai bala’in tsada ne.
Kai tsaye kicin ta nufa ba tare da ta kalli ko ƙofar ɗakinsa ba. Dankalin hausa tayi sha’awar soyawa ta sha da lipton, idan shi ma Mukhtar yana ra’ayi za ta aje masa don fita hakki.
Tana da pure man ƙuli mai kyau, wanda idan ta soya dankali da shi ba ƙaramin ɗanɗano yake ƙara yi ba.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗebi dankalin iya yadda zai ishe su ta wanke, ta fara ferewa cikin hanzari, tana jin yadda yunwa ke sakaɗarta.
Sai a lokacin ta tuna jiya ko abincin dare bata iya ci ba saboda tashin hankali, ƙasa-ƙasa taja tsaki ta cigaba da aikin da yake gabanta.
A ɓangaren Mukhtar shi ma barci yayi wadatacce, ko da ya dawo sallar asubah kwanciya ya sake yi. Bai farka ba sai ƙarfe goma na safe, tun dare da ya juya ma wayarsa baya sai a lokacin ya waiwayeta.
Kiran da aka rasa ya gani da yawa, amma na Fatima su ne guda goma sha ɗaya. Da sauri yabi bayan kiran yana jin damuwa da rashin ɗaukar wayoyinta da baiyi ba, tun asubah ya kamata ya kira yaji yadda ta tashi a matsayinta na wacce take niyyar zama iyalinsa nan da lokaci ƙanƙani.
Ya kira sau biyu bata ɗauka ba, sai ya tura mata saƙon ban haƙuri da zafafan kalaman soyayya ya ajiye wayar ya shiga wanka.
A mintuna goma sha biyar ya gama shiryawa cikin ƙananun kaya. Ya ɗauki wayarsa ya nufi falo, yanzu kam ya shirya tsaf don tarbar duk wani tashin hankali daga matar gidan, shi yasa ko fuskarsa kadaran kadahan take.
Ba ta a falo, amma ya jiyo motsinta a kicin ga kuma ƙamshin man gyaɗa da yake tashi alamun tana soya wani abu.
Ba tare da fargabar komai ba ya nufi kicin ɗin. Ya ɗauki tsawon daƙiƙu ashirin yana ƙare ma bayanta kallo, ya haɗiyi wani kakkauran miyau, ya ɗaure fuska yayi sallama a daƙile.
“Ameen wa’alaikas salaam.”
Ta amsa da wani irin sanyi da yanga a muryarta.
A nutse ta juyo tana kallonshi, fuskarta a sake yake sosai, idan ba gizo idanunsa ke masa ba sai yaga kamar ma wani kwantaccen murmushi take yi.
Duk ƙwaƙwarsa ya kasa gano ɓacin rai ko kaɗan a fuskarta, ga wani irin annuri da kwarjini da fuskarta ke fitarwa.
“Ranka ya daɗe, barka da asubah! Ina kwanah.”
Ta katse mishi tunani da gaisuwa, har tana wani ɗan duƙawa kaɗan cikin salo alamun girmamawa.
“Lafiya ƙalau.”
Ya amsa daƙyar bayan yayi ƙumajin daidaita kansa daga mayataccen kallon da yake bin ta da shi, zuciyarsa cike da maɗaukakin mamakinta, sai kallon yadda tayi wani irin kwalliya na ɗaukar hankali kamar wacce ba ta a cikin wata damuwa.
Bai dawo hayyacinsa ba ta sake shayar da shi wani mamakin ta hanyar cewa.
“Ranka ya daɗe, ina neman afuwa. Yau ɗin wani daɗin barci ne ya kwashe ni har na makara, minti biyar za ka bani kacal in kammala haɗa maka abin karyawa. Afuwa plsssssss.”
Ta ja kalmar “Pls” ɗin da wani irin salon shagwaɓa da ya kusan kifar da shi a ƙasa yayi saurin dafe ƙofar kicin ɗin.
Kamar bata ga abinda ya faru ba, ta dallare fuskarsa da kyakkyawan murmushinta, ta ƙara tura tsukakken bakinta gaba tana mommotsa shi kamar za tayi sumba, ta ƙale mishi idanu ɗaya, ta ƙarke da sakar mishi Fari da idanun da ya saka shi ficewa da baya da baya daga cikin kicin ɗin baki hangame yana kallonta.
Tunani ɗaya ne a ransa. ‘Ko dai ta zaci wasa yake mata maganar aurenshi da Fatima? lallai kuwa idan haka ne ta yaudari kanta
Ya ake bude books dinki website din nan