Skip to content
Part 14 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Ta daɗe tsaye a tsakar gidan bayan tafiyarsu. Tunanin Mukhtar zai iya zargin ita ta kira Hajiyarmu ta faɗa mata wannan maganar yasa duk jikinta yayi sanyi. Lokaci ɗaya ta nemi matsanancin farin cikin da ya lulluɓe zuciyarta ta rasa.

Da taga dai tsayuwar bazai mata ba sai ta fara takawa a hankali zuwa cikin falon, hankalinta a tashe, zuciyarta a ɗugunzume.

Ko da tayi sallama bai amsa mata ba, yana zaune a inda suka barshi, har lokacin kanshi a ƙasa.

Saɗaf saɗaf ta kama hanyar shigewa ɗakinta.

“Fareeda”

Ya kira ta da wani irin murya da bata taɓa jin ya kira ta da irinsa ba.

Lokaci ɗaya idanunta suka cicciko da hawaye, daƙyar ta iya juyowa tana kallonsa, wani dunƙulallen abu da ya tokare mata a maƙoshi yasa ta kasa amsa kiran da bakinta.

Bai damu da rashin amsawar da bata yi ba. Ya miƙe tsaye da wani irin fusata kamar bajimin zaki, ya naɗe hannuwansa a baya. Fuska a ɗaure tamau kamar bai taɓa sanin wata aba wai ita dariya ba.

“Saboda na ce baza ki koma can ɓangaren bane kika haɗa ni da mahaifiyata? Yaushe muka fara haka a tsakaninmu?”

Kafin ta ce komai hawayen idanunta ne suka samu damar gangarowa, saukar hawayen da yayi daidai da ɗan matsawar wannan malolon da ya tokare mata maƙoshi. Ta haɗiyi wani kakkauran miyau, da rawar murya ta fara Magana.

“Wallahi, Tallahi, na Rantse da girm…”

“Akan ƙarya za ki rantse min?”

Ya katse a zafafe yana matsowa kusa da ita kamar zai kikkifa mata mari.

Da saurin gaske taja da baya, zuciyarta cike da wani irin bala’in tsoronsa. Tunda suka yi aure duk bala’insa bai taɓa dukanta ba, ba ta fatan ya fara daga yau.

“Saurareni ki ji da kyau! Don kin samu goyon bayan Hajiyarmu ta amincewa komawarki wancan ɓangaren ba shi zai sa in fasa auren Fatima ba.

Zan auro Fatima a matsayin matar aure na. Aminyarki ta ƙud da ƙud, wacce duk wani sirrinki na fili da ɓoyo a tafin hannunta yake.

Bari in faɗa miki abinda tun fara neman auren nan nawa ban faɗa miki ba.

Zan auro Fatima ne don kawai inga faɗuwarki Fareeda. Kin daɗe kina guma min takaici, kin daɗe kina ƙunsa min baƙin ciki, kin ɗauki lokaci mai tsawo kina gasa min ɗanyar gyaɗa a hannu ta hanyar ƙona min zuciya kina tsallake umarnina a matakai mabanbanta.

A yanzu lokacina ne. Lokacin da a sannu a hankali zan ɗauki fansar duk irin abubuwan da kika daɗe kina yi min. Kina ji kina gani wacce take zuga ki ta mayar da ke sakarya tana ƙara izaki wajen ƙetare umarnin mijinki.

Za ta shigo gidanki a matsayin matar mijinki. Za ta yi masa biyayya akan abinda ke kika kasa dannar zuciyarki wajen yi ma mijinki biyayya.

Za tayi amfani da sirrukanki da ta sani wajen rugurguza tubalin da kika daɗe kina ginawa…”

“Mukhtar !!! Ta katse shi ta hanyar ƙwalla kiran sunanshi. Mugayen baƙaƙen maganganunsa nema suke su saka zuciyarta mummunar bugawa.

Tunda ya fara maganganun wasu zafafan hawaye suke tsere a fuskarta. Idanunta sun kaɗa sunyi jajur, lokaci ɗaya fuskarta ta damalmale ta canja kamanni.

Ta ja shessheƙar kuka mai ƙarfi, ta sanya hannu biyu ta fara goge hawayen fuskarta da sauri, amma sam sun ƙi daina zubowa.

Ita da kanta ta bada tazara tsakaninta da shi, a yanzu da kanta ta fara haɗe tazarar da yake tsakaninta da shi, tana kallonsa da manyan idanunta da suke ta wani irin rawa rawa saboda kuka, sai wani irin numfarfashi take ja mai tafe da shessheƙar kuka sauri-sauri. Laɓɓan bakinta sai rawa suke yi, gwanin ban tausayi.

“Fatima ko Mukhtar? Ina sake maimaita maka ga ta ga ka nan! Ni Fareeda Allah ya sani, kuma yana ganin zuciyata, duk ku biyun da zuciya ɗaya nake zaune da ku.

Kuma ko da kuke shirin yin aure dai dai da sakan ɗaya ban taɓa yi muku wani fata saɓanin ta alkhairi ba.

Amma na lura duk ku biyun nema kuke ku hallakani. To ina so ku sani, wannan saƙo ne zan faɗa maka ka isar ma ita gimbiyar taka.

Ni Fareeda in Allah ya yarda ba dai mutum ba sai dai Allah. Alhaji Abdullahi Bawa kafin rasuwarsa hannayen mu ƴaƴansa gaba ɗaya ya dafa ya ce ƴaƴana, in Allah ya yarda a duniya baza ku taɓa taɓewa ba.

Hajiya Hajara Usman tana gargarar mutuwa da alƙur’ani a hannuna ina karanta mata suratul Yaseen, ta shafo kumatuna da tattausan murmushi a fuskarta ta ce Fareeda, idan anyi duniya don Manzon Allah SAW maƙiya sai dai su bi bayanki. Maƙiya su bi bayan Fareeda, Ya Allah ga Fareeda, ina roƙon maƙiya su bi bayanta.

Ta ƙara da cewa Ubangiji duk wanda zai so ganin bayan Fareeda da ƴan’uwanta Allah kasa sai dai su suga bayanshi. Ina damƙe da Alƙur’ani a hannun dama, hannuna na hagu na cikin nata na dama. Daga wannan maganar numfashi biyar ta ƙara ja mala’ikan mutuwa ya zare ranta.

Da waɗannan kyawawan addu’o’in na iyaye da hadithi ingantacce ya tabbatar da cewa yardarsu tana tare da yardar Allah kake tunanin za ku iya cin galaba a kaina?”

Sai ta saki wani tattausam murmushi da ya fito tun daga ƙarƙashin zuciyarta. Tana kallon yadda ya tsaya wani sagalau da baki yana kallonta, da wani irin yanayi mai kama da na mamakin ƙarfin halinta. Bata damu ba ta cigaba da cewa.

“Mukhtar tunda ba don Allah kake shirin auren Fatima ba, ba baki zanyi maka ba. Amma idan baka tsarkake niyyarka ba ko rantsuwa nayi babu kaffara tafiyar taku babu nisan da za tayi, idan kuma za tayi nisan za tayi ne duk ku biyun kuna cikin fige kazar wahalar da Rabbi zai yanka muku.

Amma har yanzu kana da sauran dama, lokaci bai ƙure maka ba. Ka koma ka gyara Tubalin ginin ƙarin aurenka, idan ka cigaba da tafiya kan wannan TUBALIN tokar lallai… Hmmm! Allah ya kiyaye.”

Da sassarfa ta shige ɗaki ta barshi tsaye a gurin.

Wani dogon tsaki yaja, duk waɗannan dogayen maganganun nata sam ko kaɗan basu girgiza zuciyarsa ba. Sai ma wani dogon tsaki yaja zuciyarsa cike da takaicin wannan girman kai da jiji dakai da bala’in bakin na Fareeda.

Ita a rayuwarta babu wani magana da zai saka jikinta yayi sanyi? Duk bala’insa ba ta tsoronsa, wai idan yana magana bakinta ya mutu? A’a ba dai Fareeda ba.

Idan tayi mishi shiru ya san tayi shiru ne kawai ba don tsoro ko bata da abin cewa ba. Yayi ƙwafa mai ƙarfi yana cije gefen baki, ya girgiza kai yana fitar da wani zazzafan huci daga bakinsa.

“Hmmm! Na san maganinki Fareeda. Za kiyi laushi, dolenki za kiyi laushi. A sannu zan dafa ki ki dahu luguf, ba dai mace kike ba? Za ki gane duk zafin kanki dole kiyi laushi ƙarƙashin ɗa namiji.”

A fusace ya banke ƙofar ɗakinsa ya faɗa ciki, banɗaki ya nufa kai tsaye ya fara watsa ruwa a gurguje. Dole yaje gurin Fatima a darennan, ya kamata ya sanar da ita an samu canjin tsari, tun kafin ta lodo kayyakin gadon ɗakuna uku cif gara ya faɗa mata ta sai na ɗakuna biyu ne.

Ba tare da tunanin a banɗaki yake ba a karo na barkatai ya sake jan tsaki. Tun kwanaki sun gama tsarawa ɗakuna ukun ɗaya nashi ne, ɗaya nata, ɗaya kuma na ƴaƴan da za su haifa.

Har kimanin kuɗaɗen gadajen da za ta siya ta sanar da shi, wani abu kuma da ya ƙara faranta mishi rai shi ne, gadon da za ta saka mishi a ɗakinshi ya fi nata da na ƴaƴansu masu zuwa tsada.

“Ina son ki Fateena”

Ya faɗa a fili cikin wani irin shauƙi na soyayya, har yana lumshe idanunsa.

*******

“Aban twince saurara don Allah! Ban… fahimce ka ba? Wai kana so ka ce min ginin da ka gama gyara min har aka auna yawan labulai shi ne yanzu Fareeda za ta koma ciki? Ita kuma ta bar min tsohon apartment ɗinta wanda ta gama zama ta mata shi da ƙazantarta na tsawon shekaru?”

Ta katse shi da faɗin haka cikin gatsali da ɓacin rai, bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana kwararo mata bayanin hukuncin da Hajiyarmu ta yanke.

A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalleta, yau babu ma wannan ladabin da take masa na zama a ƙasa. Tana zaune akan kujerar da ke fuskantarsa fuskarta a ɗaure tamau.

Sai karkaɗa ƙafafu take yi irin na rainin nan, daman a muryarta ya fahimci babu tausasawa da girmamawa ko misƙala zarratin.

Ranshi ne ya soma ɓaci, da sauri ya danni kansa da cewa

“Yi mata uzuri Mukhtar, dole ranta ya ɓaci. Ta saka ran a matsayinta na amarya ita ce da sabon gini sai kuma yanzu ace ba haka ba? Ya zama dole ka lallaɓata.’

Lumshe idanu yayi yana ƙara tattaro nutsuwa da kwanciyar hankali jikinsa. Ya haɗe yatsun hannayensa guri ɗaya yana ɗan matsawa.

Lallausan murmushi ya sakar mata wanda a kwanakin baya idan yayi mata lumshe idanu take yi alamun matsanancin jin daɗi, sai ta ɗan rufe fuska tana satar kallonsa irin alamun ƙara nutsewa a kogin soyayyar nan.

Wani abin mamaki yau sai yaga ta ƙara ɗaure fuska, ta kawar da kanta gefe ɗaya, ta tura baki gaba, idan ba kunnensa ne ma yaji gari ba sai yake jin kamar ƙaramin tsaki taja masa.

“Tsaki kika yi ne?”

Yayi mata tambayar don share tantama.

“A’a gyara zama nayi.”

Ta amsa da shaguɓe.

Bai ɗauka gatse tayi mishi ba. Ya kwantar da murya sosai alamun rarrashi da ban haƙuri.

Abinda bai sani ba a darennan Fatima kan dokin zuciya take. Abinda yayar mijinta ta ƙudurce yi mata wulaƙanci da tozarci ne na ƙarshe da bata taɓa tsammani ba a daidai wannan gaɓar.

Ga shi ƴan kuɗaɗenta dubu ɗari uku da take ajiyewa daga cikin kuɗin hidimomin yara duk ta gama ɓarnatar da su a wajen gyaran jikinta da siyan magungunan mallaka da maganin mata waɗanda Ramlah take amso mata.

Tsananin baƙin cikin fallasa za tayi aure da Ummee tayi bayan tafiyar Hajiya Babba rufe ɗaki tayi tama yaran tsinannen duka, kamar tana dukan manyan ƴaƴa.

Ga ƙannenta biyu duk sun gudu gurin Innarsu, daga ita sai yaran a gida. Babu mai ceto sai Allah da kanta ta gaji ta ƙyalesu bayan ta lallasu ligis, yanzu haka wahala ce tasa su barci.

Bata yi sallar magriba ba balle isha’i. Tana kan wannan tsinin ne yazo gidan.

“Fateena, kiyi haƙuri. Don Allah ki kwantar da hankalinki. Kamar yadda na faɗa miki, wallahi in banda umarnin Hajiyarmu ne wannan babu yanda za’ayi in ba Fareeda sabon gini…”

“Dakata Aban twince, don Allah saurara. Ka daina wani kwana-kwana, ko umarnin Hajiyarku ne ai kaine mai gidan. Kawai ka ce Fareeda ta mallakeka…”

Wani uban tsawa da ya daka mata saboda tsananin tsorata bata san sa’adda ta durgo ƙasa daga kan kujera ba.

A zafafe ya miƙe tsaye, duk wani ɓacin rai da yake dannewa tun daga wanda Fareeda ta kuntuka mishi lokaci ɗaya yayi fitar burtsu. Da yatsa manuniya ya nunata yana magana da wani irin ɓacin rai da bata taɓa sanin zai iya nuna mata ba.

“Ki tsaya iya matsayinki. Kar kiyi kuskuren sakin linzamin bakinki wajen faɗa min maganar banza. Ki sani, dalili ne zai sa in aure ki. Ko yanzu da zan samu tabbacin kwaranyewar wancan dalilin na aurenki wallahi tallahi bazan aure ki ba…”

Tsananin tashin hankali da firgicin kalamansa Fatima bata san sa’adda ta rarrafa ta damƙe ƙafafunsa ba.

“Na tuba, na bi Allah na bi ka. Don girman Allah kayi haƙuri, ka rufa min asiri. Ka yafe min, dan Allah kar ka fasa aure na Hasken zuciyata.”

Zuciyar maza ta riga ta motsa. Fincike ƙafafunsa yayi ya fice daga falon a fusace. Bai ɓata lokaci a tsakar gidan ba ya shige motarsa ya fice a fusace.

Ƙaƙƙarfan kuka ta fashe da shi bayan ta ɗora hannu biyu akai, sai kuma a haukace ta janyo wayarta ta fara jera mishi kalaman neman afuwa da ban haƙuri. Ko kafin ya isa gida ta aika mishi saƙonni

<< Rabon A YI 13Rabon A Yi 15 >>

1 thought on “Rabon A Yi 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×