Ya daɗe tsaye yana sauke zafafan numfashi a tsakiyar falon. Idan ya kalleta, sai ya kalli cikin falon ya sake kallon irin kujeru da labulayen da ta zuba, waɗanda ko makaho ya laluba ya san ba masu tsada bane.
Da sassarfa ya taka ya shige kicin ɗin, wani jiri da ya nemi kayar da shi da saurin gaske ya rirriƙe Cabinet da hannu bibiyu, yana ta sauke numfashi sama-sama.
Ƴan kayayyakin kicin ɗin da ta zo dasu duka-duka ga su nan babu yawa, idan aka tattara su duka baza su cika buhun suger ba, idan kuwa sun cika baza su taɓa fin buhun suger ba.
Kuloli masu sauƙin kuɗi guda biyu, sai farantan cin abinci dozen ɗaya, kwandon kifa wanke wanke, kwandon tsane shinkafa, tukwanen tower guda uku, jug da ƙananun kofunansa, tarkacen cokula da ludaya, bahon wanka babba da ƙarami, bokiti guda biyu, sai wasu manya kofuna na ɗidan ruwa, ga abin girkin gawayi nan babba da ƙarami ajiye a gefe guda. Ko flask Allah baisa idanunshi sunyi katarin hangowa ba.
Da wani irin sanyin jiki da na gwuiwa ya fice daga kicin ɗin ya koma falo. Tana tsugune a inda ya barta, irin yadda take zare idanu ya tabbatar mishi a bala’in tsorace take, kamar ya ce kyat! ta zura da gudu
Kujerar da ke kusa da ita ya laluna ya zauna a hankali, yayi tagumi da hannu bibiyu yana kallonta. Can dai ya buɗe baki daƙyar, muryarsa na fita a hankali ya ce
“Fatima!!! me yasa kika yi min ƙarya?”
“Banyi maka ƙarya ba! Wallahi banyi maka ƙarya ba!! Na rantse da Allah banyi maka ƙarya ba!!! Haskenah don girman Allah kayi haƙuri…”
Ta jero maganganun cikin sauri tare da saukar wasu zafafan hawaye a idanunta. Laɓɓan bakinta sai rawa suke yi saboda tsananin tashin hankali.
Kallonta yake yi, mamakinta yake yi da har ta iya rantsewa da girman Allah bata yi mishi ƙarya ba.
Ya sauke ajiyar zuciya, ya gyara zama ta hanyar miƙar da ƙafafunsa, ya kalleta, ko kaɗan kukan da take yi bata bashi tausayi ba.
“Satin da ya wuce, ina gurin aiki kika kira ni da zancen ga ki a kasuwan barci. Da na tambaye ki me kika je yi kika ce min dubu ɗari uku ne kika je rage siyayyar kayan kicin, ga shi kinyi siyayyar kuɗin hannunki sun ƙare gaba ɗaya babu kuɗin da za ki biya me motar da zai ɗaukar miki kaya. A take na tura miki da dubu goma kuɗin mota. Anyi haka ko ba’a yi ba?”
Hawayenta ne suka ƙara ƙarfin sauka, a kasalance ta zame daga tsugune ta zauna a ƙasa. Ta saukar da idanunta ƙasa sosai ta amsa da,
“Anyi haka! Kayi hakuri, dubu hamsin ne naje siyayyar da su ba dubu ɗari uku ba. Tabbas anan na faɗa maka ba daidai ba…”
“Kin kuma yi min ƙarya ta hanyar kwaɗaita min za ki sai mana kayan ɗaki masu ƙoluluwar tsada. Tsakani da Allah ni kuma na saka rai, saboda ɗabi’a ce irinta ɗanAdam duk sa’adda aka ce za’a yi mishi wani abu dole ya saka rai.
Sai yanzu kawai na ganki da waɗannan sakarkarun kayayyakin da a kallonsu kawai za’a gane na hannu ne. Saboda Allah Kin san ba ki da kuɗin sayen kaya masu tsada me yasa kika ce min za ki siya?”
Lallai baki shi ke yanka wuya, a wannan gaɓar ta kasa magana, ina ma ƙasa za ta tsage ta shige don kunya?. A zuciyarta ta tsine ma yar mijinta da ta sa aka raba gado kuma aka hana ta kason ƴaƴanta ya fi sau ashirin.
Da ta rasa abinda za ta ce don kare kanta sai kawai ta ƙara ƙarfin kukanta, daga sharɓen hawaye zuwa jan shessheƙa da jiniyar kuka ƙasa ƙasa.
“Kinga, Fatima ni ba na son ƙarya. A rayuwata na tsani ƙarya, na tsani maƙaryaci. Sam Fareeda ba ta min ƙarya, za ta faɗa min gaskiya ko da ɗacin gaskiyar zai sa in kwana in yini in ɗauki tsawon sati biyu ina mata masifa.
Haka kuma na tsani yaudara da munafunci. Waɗannan munanan halayen guda uku wallahi na tsane su, na tsani masu yin su.
Kin ga daga fara tafiyarmu da har yau bamu yi wata biyu ba, kinyi min ƙarya ta hanyar kayan ɗaki, abinda kika ce za ki zo da su ba su na gani ba.
Kin yaudare ni ta hanyar yin ciko na abubuwan da ko kusa ba ki da su. Fisabilillahi me yasa za kiyi haka? Da kika ga da gaske aure za muyi me yasa ko sau uku ne baki fito babu kayan ciko don in ɗan fahimci yadda kike kamar 1 a cikin riga ba?
Bazan ɓoye miki ba. Wallahi raina yayi bala’in ɓaci kan wannan yaudarar da kika yi min. Ki auna lamarin ke a karan kanki, da ace ni ne nayi miki ƙaryar ina da wani abu sai da muka yi aure kika tarar ba haka ba fa?
Wannan yaudarar da kika yi min da zan kai zancen kotu tsaf alƙali zai raba aurenmu, saboda nayi hidimar mallakar wayar Samsung ne na tsinci waya rakani banɗaki a cikin kwalin Samsung ɗin da aka bani. Alƙali zai tilasta ki duk da wani abu ya shiga tsakaninmu zai sa ki biyani kaf abinda na kashe na hidimar auren ki…”
“Kayi hakuri! Don Allah kayi haƙuri. Kar ka kai ni kotu, don Allah kar ka bayar da dama a raba aurenmu. Mukhtar wallahi tallahi ina son ka, irin tsananin soyayyar da babu wata ƴa mace da ta taɓa gwada maka irinsa, ka bani dama ko ɗan yaya ne, wallahi zan yi maka biyayya kamar baiwa da ubangidanta! Duk abinda kake so zan so shi ko da zuciyata ba ta so.
Don Allah kar ka sake ni. Bazan sake yi maka ƙarya ko yaudara ba, nayi maka alƙawarin wannan.”
Ta ƙarasa maganganun tana rusa kuka gwanin ban tausayi, zuciyarta sai wani irin bugawa take yi fafafat!
Kalmar rabuwa tsakaninta da Mukhtar kalma ce da ko a mugun mafarki ba ta fatan ya taɓa wanzuwa. Idan ya sake ta ina za ta jefa kanta? Magauta za suyi mata dararraku ba dariya ba. Ko a gurin Fareeda da mutanenta ai ta shiga uku, ƙaryarta ta ƙare.
“Hmmm! Allah yasa hakan! Ni dai na faɗa miki ki kiyaye. Kin ganni nan ba ni da haƙuri ko ƙanƙani, ɓarna dubu gyara dubu. Kamar kunama nake a taɓa ni ko da kuskure ne aji ɗau! Idan kina son zamanmu ya ɗore lafiya ki kiyaye duk abinda zai janyo mana saɓani.”
Yana gama faɗin haka ya miƙe tsam ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, har ya kusa bakin ƙofar sai ya dawo ya tsaya daidai ƙafafunta, ya nuna mazaunanta da ƙirjinta da yatsarsa manuniya.
“Sannan cikon da kike yi anan da can kar ki kuskura ki ƙara yi min amfani da su a gidannan. Ki tsaya a iya halittar da Allah ya baki.
Kashaidi na ƙarshe da zanyi miki akan ciko kenan. Na hana daga yanzu, ba na so, ruwanki ne ki nemi magungunan da za su sa ki ɗanyi kumari, ruwanki ne ki tsaya a bushe. Ciko dai na hana daga yanzu. Ke ni ko sha ka fashe za ki nema can matsalarki, ni dai kar ki kuskura ki ƙara yi min kwalliya da kayan da ba naki ba. Na faɗa miki!!”
Bai jira ko za ta ce wani abu ba ya fice daga ɗakin.
Ya so yaje ɗakinshi na ɓangaren Fareeda yayi wanka, amma haka nan ya haƙura. Ya shiga motarshi ya fice daga gidan.
Ƴan kuɗaɗen da suka rage masa a cikin acc ya cire ya shiga kasuwa, dangin kayan abinci ya loda babu laifi, duk wani abu da yasan mace za ta nema wajen yin girki ya saye shi.
Sai da ya gama siyayya tsaf sannan ya sai ma Fatima ƙaramin gas, 6kg. Ya sai mata ƙaramin flask, yaja motarsa zuwa gida.
Bayan ya ajiye motar ɓangaren Fareeda ya wuce. Ya tarar da ita cikin ƴaƴanta sun sha kwalliya gwanin ban sha’awa. Suna zaune akan teburin cin abinci suna karyawa, dankalin turawa ne da soyayyen ƙwai, ga kofin tea a gaban ko wannensu.
A gefe guda kuma ga faranti nan shaƙe da dubulan da alkali, irin yadda suka yi kyau a ido kawai sun isa bayyana irin daɗin da za suyi a baki.
Da sauri yaran suka tashi suna mishi Oyoyo. Har ƙasa ya durƙusa ya rungume su yana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da suke fitarwa a jikinsu.
“Abee ina kwanna”
Suka haɗa baki gurin gaishe shi da muryarsu na yarinta.
Cikin jin daɗi ya amsa musu sannan ya ja su zuwa kan teburin.
“Iyyeee! Madam irin wannan kayan daɗi haka babu ko tayi?”
Ya faɗi haka idanunsa cikin na Fareeda, fuskarsa taf da murmushi. A zuciyarsa yake yaba irin kyawun da tayi cikin doguwar rigar atamfar da ke jikinta.
Sai da tayi faree da idanu da murmushi a fuskarta ta amsa mishi
“Haba Oga! Kai da ke da Amarya ai kayan daɗi sai dai a gani a gurinku. Mu kam abinda ya samu ne kawai muke ɗan lasawa don mu kauda tsamin baki.”
Idanunsa idon alkaki sam ba ya wuce tayi, a yanzu ma hannu ya miƙa ya ɗauki guda ɗaya yakai baki ya gutsura. Lumshe idanu yayi yana jin wani irin garɗi da daɗi da ya ratsa bakinshi gaba ɗaya,
“Ummmn! Gaskiya duk wacce tayi alkakinnan ta cancanci a bata tukwuici. Ba ƙarya ta iya.”
“Kai dai santi kawai kake yi Oga, bari in saka maka waigi…”
“Da gaske nake fa.”
Yana gama cin na hannunsa ya sake ɗaukar wani. Sannan ya fara faɗa mata abinda ya kawo shi.
“Kayan abinci ne na siyo, ina so a ɗiba ma Fatima ta ajiye a gurinta, sauran sai ki ajiye anan! Tunda yanzu ga yara na san cin abincin zai ƙaru sosai akan na da.”
“Haka ne! Allah ya ƙara buɗi da arziki mai albarka.”
“Idan kin gama muje ki gani mana.”
Bata gama ba, amma saboda ba ta son ya cika daɗe mata a gurinta sai ta miƙe tsaye.
Su Shahid ma suka miƙe da sauri ganin iyayen za su fita su barsu su kaɗai.
“Abee”
Sayyid ya faɗa yana ɓata fuska alamun zai saka kuka.
Da sauri ya dawo ya ɗauke shi, ya riƙe hannun Shahid suka nufi ƙofar fita daga falon.
Suna fita suka tsaya jirab fitowar Fareeda, tana fitowa suka jera, tafiya suke cikin nutsuwa zuwa gurin motarsa.
Sayyid da aka ɗauka sai surutu yake yi yana ba uban labari, iyayen fuskokinsu cike taf da murmushi, a kallonsu kawai za’a gane kyakkyawan iyali ne da suke cike da farin ciki.
Fatima tana tsaye kan kujera tana gyara ƙarfen labulenta na gurin window, ɗan lanƙwashewa yayi kamar zai karye. Shi ne ta taka kujera ta hau tana ƙoƙarin gyarawa, kamar ance ta kalli harabar gidan, kwatsam idanunta suka yi kyakkyawan gani.
Saboda tsananin firgici da baƙin cikin da lokaci ɗaya ya turnuƙe zuciyarta ƙiris ya rage ta faɗo ƙasa, Allah ya taimaketa tayi saurin faɗawa kan kujera.
A maimakon kuma ta nema ma kanta salama ta hanyar wucewa daga gurin ta daina kallon abinda ke ƙona mata zuciya, sai taja ta tsaya. Ta buɗe labulen sosai tana kallonsu, zuciyarta sai tafarfasa take yi da kishi da baƙin cikin Fareeda.
Ta kalli yadda tayi kyau cikin doguwar rigar jikinta, fuskarta babu kwalliya sosai amma ko maƙiyinta bazai ce bata yi kyau ba.
A daidai lokacin Shahid ya ɗauki wani abu da bata san ko menene ba a cikin boot ɗin motar Mukhtar ya ruga da gudu, a yangace Fareeda ta bishi da ɗan gudu-gudu da niyyar ta kamo shi, a fili take kallon yadda mazaunanta sai saɓar saɓar suke a cikin riga.
Ƙanƙance idanu tayi sosai ranta yana ƙara ɓaci, a hankali ta miƙa hannu ta shafo nata shafaffun mazaunan, sai taja tsaki.
Ganin yadda Mukhtar yayi wani dagalo yana bin Fareeda da kallo yadda suke ta zagaye motar ita da ɗan, shi yaƙi tsayawa, ita kuma ta ƙi daina bin shi. Sayyid da Mukhtar sai dariya suke musu.
Ita kuma Fareeda sai tura baki take yi a shagwaɓe tana bin yaron tana maganar da sam ba ta jin me take cewa.
“Sakarya kawai wawuya.”
Ta faɗa cikin jin haushi. A zuciyarta ji take kamar ta janyo Fareedan ta zauna a ruwan cikinta tai ta ɗibga saboda baƙin cikinta da takaicinta.
Caraf taga Mukhtar ya cafke yaron, ya amshi abin hannunsa ya miƙa ma Fareeda, ta karɓa tana ƙara tura baki haɗe da ɓata fuska.
Tana ganin yadda Mukhtar da ƴaƴan suka haɗa hannuwa alamun bata haƙuri suke yi.
Ita kuma ta ɗan kama kumatun ƴaƴan biyu ta ja, ta aika ma Mukhtar hararan wasa sannan ta saki murmushi. Hannun ƴaƴan ta kama suka ja da baya.
Mukhtar ya fara fito da kayayyakin abinci daga cikin boot ɗin. Tana tsaye tana ganin yadda Fareeda take nuna mishi yana ajiyewa guri daban daban har ya gama fitar da kayan boot ɗin gaba ɗaya.
Ya buɗe kujerun baya ya fito da gas da kwalin ƙaramin flask ɗin. Kusa da Fareeda ya matsa da su ya ce
“Kiyi haƙuri Madam! Na san yanzu haƙƙoƙin duk ku biyun ya rataya a wuyana ne. Amma ni a ganina babu laifi don ka sai ma wacce ba ta da abu wani abin da bai taka kara ya karya ba.
Kamar yadda kema wata rana zan siyo miki abinda kike buƙata ba tare da na sai mata ba. A ganina wannan shi ne adalci. Babu laifi ko?”
Murmushi tayi, kuma ko kaɗan bata ji ba daɗi a ranta ba. A ganinta yadda ya faɗa ɗin shi ne adalci na gaskiya, tabbas itama wani lokacin za ta buƙaci abinda zai sai mata ba tare da ya haɗa da Fatima ba.
“Babu komai Oga. Allah ya ƙara arziki.”
Martanin murmushinta ya mayar mata sannan ya ajiye Gas da flask ɗin a gurin kayan abincin da ba shi da yawa.
Izuwa wannan lokacin ɓacin rai da baƙin cikin Fatima ya kai ƙololuwa, ta kasa daure ma zuciyarta. A fusace ta ɗauki tsintsiya da abin kwashe shara ta buɗe ƙofar falonta ta fita waje, cikin hikima ta fara ƴan kakkaɓe kakkaɓen dattin gurin, alamun dai shara za tayi.
Mukhtar na juyawa zai fara kwasar kayan abinci mai yawa zuwa ɓangaren Fareeda sai ya hangi Fatima tana shara.
“Fatima, Fatima, Ke Fatima”
Ba tare da wani yanayin ƙauna ko girmamawa ba ya buɗe murya ya dinga ƙwala mata kira.
Bata amsa ba, sai ɗagowa da tayi a fusace ta zuba mishi ido.
Hannu yasa ya yafito ta, ya ƙara da cewa
“Zo nan”
Tsintsiya da abin kwashe sharar ta ajiye gefe ɗaya, ta fara tafiya a ɗan tattale ta nufi gurinsu tana wani nannarke idanu.
Kallo ɗaya Fareeda tayi mata ta kawar da idanunta daga kanta.
Yanzu ta canza kayan jikinta, daga na turawa zuwa leshin akwatinta da ta ɗinka tayi fitar biki. A cikin kayan turawa babu cikon da Mukhtar ya hana ta sakawa sosai ramarta ke fitowa, shi yasa ta yi ma kanta ƙiyamullaili ta canja kayan, ko babu komai kaurin leshi zai hana ramar armashi a idanun mai kallonta.
Akan kayan abincin da suke rabe ta fara sauke idanunta, cikin ladabi ta ɗan duƙa ƙasa ta ce,
“Haskenah barka da dawowa. Ga ni.”
Bai amsa ba sai nuna mata kayan abincin da bai da yawa yayi ya ce
“Ki ɗauki abinda za ki iya cikin kayayyakinnan kije da su ɓangarenki. Idan na shigar da waɗannan zan shigo miki da ragowar.”
Kafin ta amsa sai da ta sauke idanunta akan wancan kayan mai yawa da yake ajiye gefen Fareeda, ta haɗiye wani maƙwallato na ɓacin rai.
Ta ƙaƙalo murmushi ta sakar ma Mukhtar, ta durƙusa har ƙasa ta ce
“Na gode Haskenah. Allah ya saka da alkhairi. Allah ya ƙara buɗi, Allah ya jiƙan Babanmu ya ƙara ma Hajiyarmu Lafiya, Allah ya…”
“Ameen! Ameen!! Ameen!!!”
Ya katse ta da sauri. Umarnin miƙewa tsaye yayi mata.
Har ya sunkuci buhun shinkafa a kayan da zai kai ɓangaren Fareeda kamar wanda aka matsa bakinshi sai ya kalli Fatima ya ce
“Daga yau kar ki sake durƙusa min gwuiyawunki a ƙasa. Malamai da yawa sun haramta haka, kuma ko ba haramun bane ni ba na so!!”
A tare mata biyun suka bi shi da kallo. Fatima kallo ne take mishi na rauni da kunya haɗe da takaicin gwasaleta da ya tsiri yi yau a gaban Fareeda. Ɗazu yayi mata, yanzu ma ya ƙara wani, idanunta ne suka cicciko da hawaye.
Ita kuwa Fareeda kallo ne take mishi na yadda a wasu lokutan ba ya iya tauna magana, sakinsu yake kamar ya ci kashi. Fisabillahi ina daɗin irin wannan? Tunanin ba abinda ya shafeta bane yasa ta watsar da abin a ranta ta kawar da kanta gefe ɗaya.
Itama Fatima ba yadda ta iya haka ta mutsuke idanunta, ta ɗauki ƙananun ledojin da suke cikin cefanenta taja ma Fareeda dogon tsaki ta wuce tana karkaɗa ƴan ƙananun mazaunanta. Ko ta manta babu ciko ne oho mata!!
Ita Fareeda abin ma dariya ya bata, ta bi Fatiman da kallo tana jinjina ƙarfin halinta. Ita ta rasa gane wannan al’amari, ita ce ya kamata tayi mahakacin kishi da Fatiman da bata duba sanayya ba ta aure mata miji ko kuwa ita Fatiman ce ya kamata tayi mahaukacin kishi da ita?
Ko da ta ƙara kallon bayan Fatiman taga ƴan ɗuwaiwakan da take kaɗawa ta kasa hana kanta darawa.
“Ke kuma da wa kike dariya?”
Mukhtar da ya isa gurin hannunshi riƙe da alƙaki yana taunawa ya tambayeta.
“Kai dai Oga kana da son jin magana. To Ni da matar mijina ne.”
A tare ita da shi suka sake kallon Fatima da take gaf da isa ɓangarenta, har lokacin kuma bata canza yanayin tafiyarta ba.
Da ɗan ƙarfi Fareeda ta ƙyalƙyale da dariya, shi kuma yaja tsaki ƙasa-ƙasa.
Bai sake cewa komai ba ya cigaba da jidar kayan abinci har ya gama kaima Fareeda nata. A lokacin taja ƴaƴanta bayan tayi mishi sannu da aiki suka shige ɓangarenta.
Tsaf ya kwashe na Fatima ita ma ya loda mata a store ɗinta. Bai ganta a falo ba, bai nemeta ba ya fice zuwa ɓangaren Fareeda.
Tashar da ake karatun yara ya tarar ta kunna ma su Sayyid, ita kuma tana kicin tana wanke-wanke.
Ɗakinsa ya wuce kai tsaye, suturunsa masu ɗan yawa ya ɗiba ya fice da su zuwa ɓangaren Fatima. Sai a lokacin ya tarar da ita cikin falon, tana zaune kan kujera tayi tagumi, idanunta sun kaɗa sunyi jaaa.
“Haɗa min ruwan wanka.”
Ya bata umarni ba tare da ya bi takan yanayin damuwar da yake gani kwance male-male kan idanunta ba.
Cikin ɗakinta ya shige, ya zuba kayan akan gado. Ita kuma ta wuce bayi ta haɗa mishi ruwan wankan, tana fitowa kafin ta ce ta haɗa ya kalle ta da yanayin rashin jin daɗi ya ce,
“Ke gadon ma ko arzikin sif baki samu ba, yanzu a ina zan zuba kayan sakawa na?”
“Kayi haƙuri. Bari in kwashe kayan babban akwatin can sai ka zuba kayanka a ciki.”
Kallo ɗaya yayi mata ya shige banɗaki.
Ita kuma ta janyo akwatunan da yayi mata na aure ta kwashe kayan cikin babban akwatin ta loda a ƙananan da babban ghana must go ɗin da ta zubo tsofaffin kayan sakawarta.
Tana kwashe kayan zuciyarta cike da tunanin inda za ta samu kuɗi da gaggawa ta sayi sif ta biya a gyara mata katakon shimfiɗar gadon da ya ɓalle da hannayen kujerun da suka ɓalle.
Ya fito banɗakin ya tarar da ita har ta gama shirya mishi kayanshi a cikin akwatin. Gaban madubi ya wuce yana goge gashin kansa zuwa wuyansa da tawul. Da murmushi a fuskarsa yana kallonta ta cikin madubi ya ce
“Na ci alkali mai daɗi a gurin Fareeda. Ni fa mayen alkaki ne, gara ki hana ni nama da kiyi min rowar alkaki. Ina nawa?”
“Alkaki?”
Ta tambaye shi da mamaki a fuskarta.
“Eh! Ba ke kika bata ba?”
“Ni wallahi ban bata wani alkaki ba. Kila dai a wani guri ta samo.”
Ta amsa da dukkan gaskiyarta.
A ɗofane ya ɗora mazaunansa gefen gadon, bai manta karyewar da yaji ɓangaren da ya zauna da ƙarfi yayi jiya da daddare ba. Ya juyo da fuskarsa yana kallonta ya ce
“Alkaki fa nake nufi irin na kayan gara da amare suke zuwa gidan miji da shi. Ba ke kika bata ba?”
“Eh!”
Ta amsa a raunane, sai kuma ta saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa tana murza yatsun hannunta na dama cikin na hagu. Domin kawo ƙarshen duk wasu tambayoyinsa ma sai ta ce
“Kayi haƙuri. Ba ni da kuɗi ban samu yin komai na ciye-ciye ba. Rabon gadon su Ummee aka yi kuma ƴan’uwan babansu duk sun riƙe komai. Shi yasa komai ya zo min a hagugunce…”
“Au! Wai daman da kuɗin gadon ƴaƴanki kika so ki ƙayata min gida?”
Bakinsa a buɗe yayi mata tambayar.
Kamar wacce aka ɗinke mata baki. Kai kawai ta iya ɗaga masa alamar haka ne.
Shi ma dai ba shi da zaɓin da ya wuce yayi shiru. Amma a zahirin gaskiya Fatima ta sane masa, lamarinta a birkice yazo mishi, irin yadda ko a mummunan hasashe bai taɓa tunanin lamarin zai zo musu ita da shi a haka ba.
*****
A bala’in maneji ko in ce a daddafe Mukhtar ya gama kwanaki ukunsa a ɓangaren Fatima. Lamarin dai ga shi nan… Ƙarerayin da tayi mishi ya rusa armashin komai.
Har Fareeda ta lura da babu wani rawar kai ko girigiɗishin amarci daga duka ɓangarorin biyu. Ita dai nata idanu, su ta kawo ta zuba musu ta cigaba da harkokinta da ƴaƴanta hankali kwance.
A yammacin da zai koma ɓangaren Fareeda jikinsa har rawa yake yi. Sosai murnarsa ta gaza ɓoyuwa, har Fatima ta lura da haka, wannan yasa jikinta ya ƙara sanyi, zuciyarta ya ƙara cika da tumbatsa da tsanar Fareeda.
A karo na biyu ya sake haɗa su a falonta Fareeda matsayinta na uwargida. Nasihar a zauna lafiya yayi musu, sannan ya faɗa musu shi ba ya sha’awar matanshi su raba girki.
“Girkin karin safe ne kawai na yarje ma kowa tayi a ɓangarenta. Amma girkin rana da dare duk mai girki idan tayi ta ɗiba ma wacce bata da girki a wadace yadda zai ishe ta.
Da za ku haɗa kanku ma ta hanyar yin girki tare da cin abinci tare ba ƙaramin farin ciki da jin daɗi zanyi ba. Kuma zan samu nagartaccen kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyata.”
‘Ashe kuwa baza ka taɓa samu ba Mukhtar’
Fareeda ta faɗi haka a zuciyarta. A fili kuwa fuskarta cike taf da murmushi.
“Fatima kin gama kwanakinki uku da addini ya baki. Yau da yamma zan koma ɗakin…”
“Oga minti biyu don Allah! Zan iya magana?”
Fareeda ta katse shi, daa muryarta a sanyaye kuma cikin ladabi.
“Ina jin ki”
Ya amsa yana tsatsareta da idanu.
Itama Fatima kai ta ɗaga ta kalleta, a sace ta gallah mata harara.
Karaf a idanun Fareeda. Murmushi ta saki cikin rashin damuwa. Idanunta ta mayar cikin na Mukhtar, da dakiya a muryarta ta ce
“Oganah, rannan kai da amarya Fatima kun nemi alfarmar in ƙara muku kwanaki. To nima dai daga baya nayi tunanin inyi ƙoƙarin kasancewa cikin uwaren gida masu adalcin da ta ambata kai kuma ka maimaita min.
Don haka na ƙara muku wata uku, sati goma sha biyu, kwanaki casa’in. Waɗanda addini ya basu kwanaki uku na ninninka muku uku sau talatin ai na ɗan kyautata ko…?”
“Kan’uba!!! Fareeda Wallahi baki isa ba!!!”
Mukhtar ya katse ta cikin fushi haɗe da miƙewa tsaye a fusace…