"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku!!!"
Fareeda ta faɗi haka idanunta a warwaje, hannu bibiyu ta ɗora akai wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata. Babu abinda take hangowa a idanuwanta da ji a kunnuwanta sai masifar da Mukhtar zai sauke mata, ba shi da haƙuri ko kaɗan.
Balaƴaƴƴe ne na bugawa a jarida idan aka yi kuskuren shiga gonarsa, ba shi da uzuri ko misƙala zarrah. Har wani kirari yake yi wa kansa cewar"Ni fa kamar kunama nake, a taɓa ni aji ɗau."
Da waɗannan tunanin. . .