Skip to content
Part 27 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Kwanansu Shahid biyu a asibiti aka sallamesu, Alhandulillahi sun warke garas, kamar ba su ne aka fice da su ranga-ranga ba. Daga asibiti kai tsaye Hajiyarmu gidanta ta wuce da su ba tare da neman shawara ko amincewar Mukhtar ba.

Shi ɗin ma dai bai ja da zafi ba, ganin yadda Hajiyar ke ciki da shi lallaɓawa yake yi su rabu lafiya. Bai gane tara shi take yi ba sai da aka sallamesu daga asibiti suka koma gida. Wankin babban bargo tayi mishi ƙal kan yadda ta fuskanci yana tafiyar da lamuran zamantakewar iyalanshi.

Ta kuma ƙara da faɗa mishi matuƙar bai zama jajurtaccen namiji mai iya danne zuciyarsa lokacin fushi ya dinga bincike a nutse lokacin da aka faɗa mishi faruwar wani abu tabbas zai rusa gidanshi da kanshi.

Sunkuyar da kanshi ƙasa yayi yana bata haƙuri har ya fahimci ta gama. Da gaske kuma ya gano kuren da ya aikata wajen yanke ma Fareeda hukunci, amma in Allah ya yarda zai kiyaye gaba wajen sake ɗaukar mataki da gaggawa kan duk abinda zai ji daga sama.

Acan gidanshi kuwa, wani irin zama ne ake yi mare daɗi ko kaɗan tsakaninshi da matan biyu. Gagarumin fushi yake yi da Fatima, duk yadda ta kwashe kwana tana jinyar shaƙan da yayi mata kallo bata ishe ba. Ya kulle duk wata ƙofa da zai bata damar da za tayi mishi wani bayani nata da yake ɗauka na ƙarya da rainin wayau.

Ɓangaren Fareeda kuma shi yake cusu cikin kwantai. So yake su shirya da gaske, ita kuma ta ƙi bayar da damar hakan. Bata kuma fito fili kai tsaye ta nuna mishi fushi take yi mai tsanani da shi ba, wani irin gashin ƙuma take yi masa sannu a hankali. Wasarere take yi da al’amarinsa kamar auren dole aka yi mata da shi.

Kai tsaye take yaɓa mishi duk irin baƙar maganar da tazo bakinta. Ya rasa ta yadda zai bi da ita, a ƙarshe sai ya koma ya saka mata idanu yana jiran yaga iya gudun ruwanta. Daman ai shi ma tayi mishi laifi, bai manta amfani da maganin da tayi don kar ya samu damar kusantarta ba. Yana dai bin ta ne don kawai irin hukuncin kai tsaye da ya ɗauka na maganar su Sayyid ba tare da ya bincika ba.

Yana kwana a ɗakin matan nashi, amma kashi tamanin da biyar cikin ɗari na rayuwarshi ya koma yi ne a ɗakin baƙi. Sai dare ya fara shiga sosai sannan yake tafiya ɗakin wacce take da girki ya kwanta.

Ga Fareeda dai wannan mataki ko a jikinta wai an tsikari kakkaura. Hankalinta kwance yake sosai fiye da ake tsammani. Tun daga faruwar wannan abin kuma ta daina ba Fatima abinci, itama acan ɓangarenta bata sake dafawa da ita ba. Tunda abin ya faru kuma har yau ita da Fatima basu haɗu ba.

A ɓangaren Fatima kam ta damu matuƙa gaya, hankalinta na tashe yake ƙwarai da fushin da Mukhtar yake yi da ita. Duk yadda ta so kalallame shi da kalaman ban haƙuri da daɗin baki kamar yadda ta saba a wannan karon ya ƙi bata fuskar haka.

Tun a ranar farko da ya shiga ɗakin ta zube a gabanshi cikin kuka ta haɗe hannayenta ta buɗe baki za ta fara magana ya daka mata wani gigitaccen tsawa ya ce idan ta kuskura ta ce za ta bashi hakuri igiyar da ta ƙulla tsakaninsu zai datse su a darennan. Saboda tsananin tashin hankali da firgicin jin abinda ya ce da jan mazaunai ta bar gabanshi ta koma can gaban madubi ta haɗe kai da gwuiwa tana rusa kuka.

Falo ya fice, bayan ya galla mata harara sannan yaja mata dogon tsaki. Tun daga wannan rana zaman doya da manja ne a tsakaninsu, idan zai shiga inda take kamar mai ciwon baki yake cijewa yayi mata sallama. Idan ta gaishe shi daƙyar yake amsawa.

Amma wani ikon Allah a maimakon ta rame sai ta yi kumari. Ingantaccen haɗin damun kunu na maganin nono da take sha wanda ta siya a gurin Farida ba ƙaramin karɓarta yayi ba. Kwantattun nonuwanta duk da basu taso sun tsaitsaya ba a hankali take jin suna ciccika, tuwon tsoka na cikowa ta cikin lamusassun fatan. Ganin wannan cigaba da aka samu yasa duk tashin hankalin da take ciki bata taɓa fashin dama kunun safe da dare ba. Farida ta faɗa mata za ta iya shan maganin sau ɗaya idan tana harkar maneji, idan kuma tana so taga cika aiki da gaggawa to ta dinga sha da sassafe kafin ta ci komai, da kuma daddare idan za ta kwanta. Shi yasa idan da hali tun farko in za ki sayi maganin idan da hali ki sayi bokiti biyu domin kar maganin ya yanke ba tare da kin sha na aƙallah sati biyu ko uku kamar yadda ake so ba *_👉🏽09077591726 lambar mai maganin nono.

Kullum idan ya shiga kwanciya haka za ta tasa shi gaba ta saka gwuiwa a ƙasa gaban gado ɓangaren da yake kwanciya tana hawaye. Ba ta taɓa tanka mishi har sai ta ji ya fara jan numfashi alamar yayi barci.

A tsorace take sosai, tunda ya ce idan ta kuskura tayi mishi magana kan abinda zai faru shi yasa take kiyayewa. Tsoronta Allah tsoronta Mukhtar ya ce zai sake ta, ita kam da tashin alƙiyamarta ta tsaya, kada Allah ya nuna mata wannan rana. Idan tayi tunanin haka har wani tuf-tuf take yi ta tofar da mugun miyau.

Shi kuwa Mukhtar kamar dutse duk yadda za ta tasa shi da koke-koke bai taɓa ɗaga ido ya kalleta ba. Idan ta ishe shi da jan shessheƙa ne sai ya juya mata baya, ya ɗauki filo ya danne kansa har barci ya ɗauke shi. Ranar da ƴan tsiyan ke kusa kuma tana fara kuka zai fatattaketa ya kora ta falo. A haka har suka kwashe sati biyu basu samu daidaito ba.

****

Tsawon lokaci Ibrahim yana kallon Mukhtar da wani irin maɗaukakin mamaki kwance ɓaro-ɓaro kan fuskarsa. Sau uku yana buɗe baki yana rufewa, ya kasa cewa komai don mamaki da takaici.

Daga ƙarshe dai yayi ƙumajin buɗe baki daƙyar ya ce,

“Ban taɓa sanin kai ɗin daƙiƙi bane sai yau Mukhtar. Yanzu saboda Allah da Annabi kai ka yarda da wannan tatsuniyar tunda kai ƙwaƙwalwarka dusa aka zuba a ciki?”

Da wani irin bala’in fushi da ɓacin rai Mukhtar ya ce

“Ni kake zagi kake tozartawa haka Ibrahim? Babu komai, ba laifinka bane. Laifina ne da na kwaso damuwata na faɗa maka don tunanin kai ɗin amini ne na gari. Ka ga tafiyata.”

Ya yunƙura zai miƙe tsaye a fusace Ibrahim ɗin ya janyo rigarshi da ƙarfi ya zauna jaɓar kan kujera.

“Ai wallahi baka isa ba. Yadda muka faro maganar nan sai mun ƙarasata. Dole ka zauna ka saurari duk abinda zan faɗa maka. Wai ni kam Mukhtar anya ma Fatimar nan haka ta barka? Tsohuwar mace duk ta sa ka susuce ka zama wani maloho da kai, sai wauta kake zubawa baka san ko cikin abokai ana zunɗenka ba? Hmmm! Ai babu komai Mukhtar, da irinku ne kuke ja mana mata suke yi mana kuɗin goro wajen cewa mu ba ƴaƴan goyo bane.

Yanzu kai ka manta irin matsananciyar ƙauna da soyayyar da Fareeda ta nuna maka tun zamanin neman aurenta har zuwa bayan aure? Ka manta irin yadda Fareeda tai ta haƙuri da murɗaɗɗun halayenka waɗanda ko mu abokanka ba ma iya haƙuri da su? Ka manta yadda na sha faɗa maka a zamantakewarku da Fareeda kai ke da kaso sittin cikin ɗari na matsalar zaman aurenku?

Bari in sake maimaita maka abinda na daɗe ina faɗa maka. Zamantakewar aure nau’i ne na zaman amana, yarda, musayar ra’ayi tsakanin juna. Ba wai zaman bautarwa ko takura ko ƙuntatawa ba. Ni ban baka shawarar ka saki Fareeda ta dinga fita sakaka ba, amma abubuwa da dama ya kamata ka ɗan buɗa mata.

Balancing ake yi Mukhtar, kai da iyalinka in dai ba zarginta kake yi ba, ya zama dole ka dinga kawar da kai kana sakar mata wasu abubuwan ko da zuciyarka ba ta son haka.

Ko ka ƙi ko ka so yanzu zamanin ya canza. Dole mu karɓi wannan canjin da rayuwa ta zo da shi. Irin yadda mata suka bautatu ma maza a baya, na yanzu sam baza su iya haka ba. Me yasa kaga yanzu sakin aure ba’a ɗauke shi a bakin komai ba? Saboda Maza masu cusasshen tunani da bahagon ra’ayi irin naka sun kasa gane yanayin zamantakewa, da kuma abinda ake nufi da zamantakewar shi kansa. Ni dai a ganina, a kuma irin karatun da nayi ma mace, wallahi banga wani abun tafi da ita kamar zuma da sai na yi ta shuna mata wuta ba.

Amma tunda dai kai ba ka jin shawara, kaje kayi abinda kake so Mukhtar. Tunda dai kai har ka yarda Fareeda da gaske ta yi amfani da maganin da ba ka iya kusantarka, to menene amfanin zamantakewar aurenku? Ka sallameta kawai ta ƙara gaba ka riƙe Fatimarka.”

Yayi wani dariya kafin ya cigaba da cewa.

“Ai wallahi da kana ji kana gani ɗan hakin da ka raina zai tsole maka ido. Mamaki sai ya kusa ajalinka kan irin mazan da za kaga suna gogoriyo wajen neman aurenta. Ina tabbatar maka ko cikin abokanmu ɗaiɗai waɗanda baza su sa kai ba, ko ni nan…”

“Ibro don girman Allah kayi shiru da waɗannan maganganun. Allah ma bazai sa haka ya faru ba in sha Allah, ni da Fareeda mutu ka raba takalmin kaza. Yanzu dai don Allah ka bani shawara, ya zanyi? Me zanyi? Wani mataki zan ɗauka don gano gaskiyar abinda yake faruwa?”

Ya ƙarasa maganar a marairaice.

Tunda Ibrahim yaga Mukhtar ɗin yayi laushi ya sauke kanshi ƙasa. Sosai ya saki jiki ya bashi shawarwari ƙwarara waɗanda ya bashi tabbacin in dai ya bi su kamar yadda ya karanta mishi, to nan da kwanaki ƙalilan babu abinda zai wanzu tsakaninshi da iyalanshi sai zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Da fara’a sosai a fuskarsa suka rabu da Ibrahim ɗin. Daman a cikin abokansu in dai ɓangare na gyaran zamantakewa ne tsakanin miji da mata Ibrahim shi ne gaba-gaba. Allah yayi masa wannan baiwar, in sha Allah da ya shiga cikin matsala ya tattauna da miji da matan cikin ƙanƙanin lokaci matsala za ta kau, a samu daddaɗan zamantakewa da kwanciyar hankali.

A wannan ranar ya kama girkin Fatima ne. Kai tsaye kasuwa ya shiga ya siya kayan ciki da yawa yayi cefane ya wuce gida. Da kallon fuskarsa kawai za’a fahimci yana cikin walwala.

Ganin wannan fara’a da ke shimfiɗe a fuskarsa yasa hankalin Fatima ya ɗan kwanta, da rawar jiki ta tarbeshi ta karɓi kayan hannunsa zuwa kicin. Ita da take tsoron yi masa magana sai ga shi da kanshi yake janta da zance cikin kulawa soyayya.

Kamar a mafarki take kallon lamarin, tun tana ɗari-ɗari har dai ta saki jikinta suka cigaba da hira cikin walwala. Shi ya taya ta suka raba naman gida biyu, ya ce tayi farfesun rabi, ta soya rabi. Cikin hanzari ta fara aikin yana kama mata da ƙananun abubuwa.

“Ina abincin Fareeda da nata farfesun?”

Ya tambayeta bayan ya ga ta gama komai bata ce mishi ga na Fareeda ba. A lokacin har an idar da sallar isha’i.

“Taɓ! Tuntuni fa mun daina girki tare, tun lokacin da wancan rikicin ya faru washe gari da girki ya koma kanta bata bani abinci ba, har girki ya fita kanta bata kawo min ba ni nake girka nawa. Ganin haka ni ma sai na daina dafawa da ita…”

“Ikon Allah! Me yasa baki faɗa min ba?”

Ya tambayeta cikin sanyin murya, kamar ba Mukhtar wannan mai yawan faɗa da hargagin ba.

“Kayi haƙuri. Na yi tunanin ko ita ta faɗa maka ne.”

Ta amsa a tsorace bayan ta saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa.

Bai ce komai ba. Miƙewa yayi ya shiga kicin ɗin ta. Duk abinda ta dafa sai da ya ɗiba ma Fareeda a wadace kafin ya ɗauki kulolin ya fice da su, bayan ya ba Fatima uzurin yana zuwa.

Ko da ya isa can abinci ya samu tana ci, da alamun hankalinta kwance. Idanunta na kan T.v tana kallon shirin taron ƙauna da ake haskawa a tashar arewa24.

Ko da yayi sallama ta amsa bata kalle shi ba. Nan gabanta ya ajiye kulolin abincin ya zauna a gefenta, sai kallonta yake yi. Ta ƙara wani irin kyau mai sanyi, daman ita haka ciki ke mata a farko-farko, kyau take yi sosai sai cikin ya kusa fita sai ta koma yadda take.

“Ƴanmata na. Ba tayi?”

Ya faɗa da murmushi sosai a fuskarsa bayan ya riƙe cokalin hannunta.

Tsai tayi da ranta, idanunta na kan hannunsa da ya riƙe mata cokali. Sai kuma ta ɗanyi murmushi, ta ɗago fuskarta ta kalle shi a sakalce tana ɗan jujjuya idanunta.

“Ƴanmata tana can ka baro ta a ɓangaren da ka fito. Miye wannan ka kawo min? Sarauniyar taka bata faɗa maka na daina karɓan duk wani jagwal da zai fito daga hannunta bane?”

“Ta faɗa min. Ina so ku cigaba da girki kamar yadda na tsara muku da farko, shi yasa na ɗauko wannan na kawo miki…”

“Bazan ci ba. Kuma na rantse da girman Allah bazan sake haɗa girki da wata mace a gidannan ba. Iya zallar gaskiyar magana kenan Mukhtar.”

Ta faɗa kai tsaye tana kallon cikin idanunsa ba tare da shakka ko tsoro ba.

Lallai giwa ta fara lafiya. A maimakon ya balbaleta da faɗa kamar yadda ya saba sai cewa yayi

“Allan ya baki haƙuri uwar huɗuna. Allah ya sauke ki lafiya.”

Yayi maganar da murmushi a fuskarsa. Ganin tana mishi wani irin kallo yasa shi faɗaɗa murmushinsa.

“Uwargida sarautar mata, Fareeda ikon Allah, ja gaba ki shige sauran mata sai dai su bi ki a baya. Duk namijin da bai da mai sunan Fareeda a cikin matanshi ina tausaya mishi kan mummunar asarar da ya tafka a rayuwar duniya.”

Kaɗa kai ta iya yi kawai ta kawar da kanta zuwa kan T.v da take kallo. Ita ɗin ba sakarya bace da zai zo yana mata wani daɗin baki da sam ba halinsa bane. Ta sanshi kamar yunwar cikinta, don haka bazai zo yana mata wasu tsamayen kalamanshi ta saurareshi ba. Abinda bai fahimta ba shi ne, gishiri ya sauka daga kan kaza, ta ajiye shi ne gefe ɗaya.

Ko ba’a rabu ba, ita a tsarin rayuwarya baza ta taɓa ajiye namiji a zuciyarta har ya haddasa mata wani mugun ciwo ba. Da igiyoyin aurensa da komai za ta yakice shi ta cigaba da rayuwa lafiya kalau.

<< Rabon A Yi 26Rabon A Yi 28 >>

1 thought on “Rabon A Yi 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×