Skip to content
Part 3 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Duk da mota ɗaya suka shiga wajen komawa gida zaman ƙuda ne a tsakaninsu, kamar ma waɗanda basu taɓa sanin juna ba.

Ko wacce ta jingina kai da ƙofar mota ne suna kallon can waje.

Ita Fatima babu wani fargaba da damuwa a tattare da ita, babu nauyin miji a kanta balle ta shiga ɗimuwa, shekarar mijinta biyu da rasuwa, shi yasa take dama kununta yadda take so.

Ganin yadda Fareeda ta ɗaure fuska ta juyar da kanta ɓangaren ƙofa ne yasa itama tayi hakan, don kar ƙawartata taga kamar bata damu da halin da take ciki ba.Gidan Fareeda aka fara isa, da wata muguwar kasala ta buɗe ƙofar motar tana ƙoƙarin fita, hannunta ɗaya da Fatima ta riƙe yasa ta juya a hankali ta kalleta.”Na san duk inda Mukhtar yake ya dawo duba da yadda yaita kiranki akai-akai, ko in raka ki cikin gidan in taya ki ba shi haƙuri?”Murmushin yaƙe tayi, ta zare hannunta a hankali.

“Babu komai, ki ƙarasa gida kawai. Zanyi masa bayani, babu abinda zai faru sai alkhairi in Allah ya yarda. Za muyi magana a waya”

Bata jira komai ba ta mayar da ƙofar ta rufe, ta juya ta nufi ƙofar gidanta da sassarfa ƙirjinta yana luguden daka. Bakinta ɗauke da addu’o’i kala daban-daban.Ganin ƙaramar ƙofar gidan a buɗe saɓanin rufewar da tayi kafin ta fita shi ya ƙara tabbatar mata da Mukhtar ya dawo, ko da ta shiga cikin gidan sai ta rakuɓe a jikin ƙofar.

Idanunta tsaye ƙyam akan motarsa da yake fake a tsakar gidan, jikinta babu inda ba ya rawa.

Mara gaskiya aka ce ko a ruwa gumi yake, duk da sanyin iskar hunturu da ya fara kaɗawa bai hanata jiƙewa sharkaf da gumi ba.

Ta lumshe idanunta, wasu zafafan hawaye suka silalo daga idanuwanta, zuciyarta cike da takaici da Allah wadai na wannan taurin kai da rashin jin magana irin nata.

Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba sun sha samun saɓani da Mukhtar kan fita unguwa mara muhimmanci.

Ya sha zaunar da ita yayi mata karatun dalla-dalla kan ra’ayinsa na rashin son ganin matarsa tana fita unguwa barkatai.

Ko sha’anin ƴan’uwanta ko nasa idan ba mai matuƙar muhimmanci bane bai cika barinta ba, ballantana sha’anin ƙawayenta waɗanda kai tsaye yake kiransu da tarkace.

Ta kai tsawon mintuna biyar a gurin tana tufka da warwara ba tare da samun hanyar da zai ɓulle da ita ba, daga bisani kawai sai tayi shahadar ƙuda ta mayar da ƙofar ta rufe, ta nufi cikin gidan ƙafafunta na harharɗewa saboda rashin gaskiya.“Daga ina kike?”

Ta jiyo fusatacciyar muryarsa yana tambayarta cikin tsawa.Ƙam ta tsaya guri ɗaya, a hankali ta ɗaga idanunta ta kalleshi, yana zaune kan kujera mazaunin mutum ɗaya yana fuskantar ƙofar shigowa. Ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karkaɗawa, alamun da ke nuna tabbas tsiya yake ji.Ƙyifƙifta idanu tayi, lokaci ɗaya suka cicciko da hawaye.
“My de…””Na ce daga ina kike?”
Ya katse ta tun kafin ta ƙarasa faɗin abinda tayi niyya.Runtse idanu tayi, ta haɗiye wani kakkauran miyau sannan tayi ƙarfin halin cewa
“Daga gidansu Jiddah…””Na je har gidansu Jiddar ban same ki ba, ban tarar da kowa a gidan ba. Ki faɗa min gaskiyar daga ina kike yanzu Fareeda, idan ba haka ba Wallahi tallahi zan nuna miki wani ɓangare nawa da baki taɓa sani ba.”Idanunta ta sauke ƙasa, cikin sanyin murya ta kora mishi bayanin zallar gaskiyar daga inda take a halin yanzu. Tun daman can ita ba gwana bace a ƙarya, ko tayi nan da nan ake ɓaro jirginta, shi yasa ako wane irin hali ta gwammace ta faɗi gaskiya duk abinda zai faru ya faru.”Ofishin ƴan sanda? Ke Fareeda? daga Ofishin ƴan sanda kike yanzu? Taɓɗijan! Lallai ma!!!”
Ya faɗi kalaman da wani irin yanayi mai bayyana kaiwa ƙololuwa a takaici da baƙin ciki haɗe da mamaki. Fareeda ta goge mishi hadda, ko da ya dage ta faɗa mishi daga inda take yayi tsammanin za ta faɗa mishi sun fito gidan walimar Amarya ce.Matarsa a ofishin ƴan sanda sanadiyyar fita da tayi ba tare da izininshi ba shi ne ƙarshen tozarci da cin mutuncin da Fareeda ta taɓa yi mishi mai bala’in ƙuna a iya zamantakewar aurensu na shekaru shida.Tabbas zai ɗau mataki, ya zama dole ya ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan Fareeda, ta yadda nan gaba ko da da amincewarsa ba ko wane karabitin unguwa za ta dinga tambayarsa ba.Tsam ya miƙe tsaye daga kan kujerar da yake zaune, hannayen rigarsa ya fara nannaɗewa yana yi yana ciccije baki.Idanu warwaje take kallonsa
‘Rufe ni da duka zaiyi?’

Ta tambayi kanta a zuciya.A iya zamantakewar aurensu duk bala’in Muktar ko dungurinta da ƴar yatsa bai taɓa yi ba. Lallai yau ta kai ƙololuwa wajen ɓata masa rai.A tsorace ta zube ƙasa ta ɗora hannaye biyu a kanta ta runtse idanu haɗe da fashewa da ƙaƙƙarfar kuka. Cikin kukan ta fara magana tana yi masa magiya
“My dear… don girman Allah da darajar fiyayyen halitta SAW ka yi haƙuri… ka yafe min don Allah, wallahi in Allah ya yarda daga rana mai kamar ta yau bazan sake fita ba da izininka ba, kayi haƙuri don Allah kar ka duke ni…”

“Yi min shiru Fareeda!!!”Ya katseta ta hanyar daka mata wani gigitaccen tsawar da yasa ta fara sakin fitsarin da tun ɗazu yake cike dam da mararta.
“Na yi shiru, wallahi na yi shiru, don Allah ka yi haƙuri…”

Wani murmushi mai bayyana matsanancin takaicin da zuciyarsa take ciki ya sakar mata, kan hannun kujerar da ya tashi ya ɗan ɗofana mazaunansa, da hannu yayi mata alamun ta tashi daga ƙasa ta hau kan kujera.

Da rawar jiki ta cika umarninsa.

Tsawon daƙiƙu casa’in yana ƙare mata kallo, Allah ya sani yana tsananin son Fareeda, soyayya kuma ba na wasa ba. Daidai gwargwado akwai zaman lafiya da kyakkyawar fahimtar juna tsakaninshi da ita.

Babban abinda yake haɗa shi da ita taurin kai ne da rashin jin magana, ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ya sha sanar da ita yawan yawon zuwa gidan biki da suna shi ba shi a tsarin rayuwar zamantakewarsa da iyalinsa. Idan tana so su cigaba da tafiya cikin farin ciki da ɗasawa to tabbas ta bi abinda yake so, a lokacin za ta ce ta ji, har ma ta ƙara da ƙasƙantar da kanta ta bashi haƙuri, ta kuma ɗaukar mishi alƙawarin in Allah ya yarda baza ta sake ba. Wannan ba shi ne karo na farko da ta fita ba da izininsa ba, ta sha yin haka babu adadi, lallai wannan karon idan bai ɗauki hukunci mai bala’in tsaurin da zai jijjiga duniyar Fareeda ba baza ta san Annabi ya faku ba.

“Ba dukanki zanyi ba Faree, a iya tsawon zamantakewarmu na taɓa dukanki?”

Da sauri ta girgiza kai alamar a’a!

“Kuma ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kina ƙetare iyakar dokokin da nake gindaya miki ko?”

A kasalance ta ɗaga kai alamar eh!

“Ki buɗe bakinki ki amsa min.”

“Eh! Don Allah…”

“Saurara Fareeda, ki daina haɗa ni da Allah, na yi haƙuri, na kuma yafe miki.”

Da mamaki ta ɗaga idanunta tana kallonshi baki buɗe.

“Eh tabbas na yafe miki. Rufe bakin.”

Kamar wata sakarya ta rufe bakinta, wani tsinkakken miyau da ya taho mata ta haɗiye da sauri.

“Ki shiga cikin ɗaki yanzu kiyi wanka, kiyi alwala, ki gyara jikinki kiyi sallar magriba. Sai ki nemi abu mai sauƙi ki dafa min, rabona da abinci tun karin safe.”Yana gama faɗin haka ya naɗe hannuwansa a baya, da wani irin taku na ƙasaita ya nufi cikin ɗakinsa, saɓanin ɗakinta da in dai yana gari anan suke gudanar da kusan komai na rayuwarsu.

Ko da ya shige ta fi minti biyu tana kallon hanyar da ya bi, mamaki take yi, mamaki mai matuƙar yawa. ‘Me yake damunsa ne? kai ko dai ba shi lafiya? Duk faɗa irinna Muktar shi ne za ta mishi irin wannan laifin kai tsaye ya ce ya yafe mata? Me yake faruwa?’

Ire-iren tunanin da ke cikin zuciyarta kenan har ya ɗauro alwala ya fito ya tarar da ita a inda ya barta.

Idanu ya buɗe da mamaki ƙarara a fuskarsa.“Menene haka kuma Sweety? Na faɗa miki fa yunwa nake ji.”

Yayi maganar da sanyin murya idanunsa a kanta.

“Yi haƙuri, yi haƙuri Dear, yanzu zan samar maka abinda za ka ci.”Tayi maganar cikin sauri, a zabure ta miƙe tsaye ta ɗauki jakarta da mayafin da ya faɗi ƙasa ta nufi cikin ɗakinta da sauri, har tana harɗe ƙafafu.

Tana ɓacewa ganinsa ya ɗaure fuska tamau, yayi ƙwafa, ya cije gefen bakinsa na dama ya ƙanƙance idanu. Hannun rigarsa da ya naɗe don yin alwala ya warware sannan ya nufi hanyar fita daga ɗakin don zuwa masallaci.

Tunani yake, tunanin irin matakin da zai ɗauka akan Fareeda. Lallai ya kamata ya ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki, zai buge ta irin bugun daga kai sai me tsaron gida, ta inda zai lallasata tayi laushi, laushi kuma na har abada.

Wani tunani da ya kurtso zuciyarsa lokaci guda ya saka shi sakin wani tattausan murmushi, ya girgiza kai alamun samun gamsuwa.

<< Rabon A Yi 2Rabon A Yi 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×