Ko da suka shiga cikin ɗakin da yake falle ɗaya, sai suka tarar da kujeran zama mazaunin mutum uku ita kaɗai ce a ajiye ta bakin ƙofa.
Can daga cikin ɗakin gado ne, a gefe guda da sauran tarkacen kayayyaki. Kan kujera Baban Murad yayi musu umarnin zama, shi kuma ya ƙarasa gefen gado ya zaunar da Maman Murad. Jikinsa na rawa ya ƙarasa kusa da fanka ƴar tsaye ya kunna ya matsa da fankar kusa da Maman Murad da tayi wata dagwalooo kamar wata wawuya ta ƙura ma guri ɗaya idanu.
Fatima ce ta ɗan ɗofana mazaunanta kan kujerar, kamar ace ƙyat ta zura a guje. Shi kuwa Mukhtar tsaye yayi a bakin ƙofa ya harde hannaye a ƙirji, fuskarsa a ɗaure tam yana kallon abinda dattijon ke yi.
“Maryam, Maryam, kina ji na?”
Baban Murad ya tambayi Maman Murad bayan ya tsuguna a gabanta, ya riƙe hannayenta biyu cikin nashi.
Tsawon wasu daƙiƙu kamar baza ta motsa ba. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya a zabure ta damƙe hannayen mijinta da ƙarfi. Idanu warwaje take kallonshi, sai kuma ta kalli Mukhtar a tsorace ta nuna shi da yatsa manuniya tana surutai
“Baban Murad kana ganin ya kafta min mari da hannunsa mai kama da dutse baka rama min ba? A gabanka za’a ci zarafin uwar ƴaƴanka baza ka ɗauki mataki ba? Ashe haka soyayyar da kake ikirarin yi min…”
“Maryam! Saurara don Allah! Ki nutsu ki fahimci abinda zan faɗa miki. Kinga wannan mutumin ba da wasa yazo ba. A matsayina na mijinki, ina mai baki shawara tun kafin hukuma su shigo cikin zancennan ki kira Kawu Bello yanzu ki faɗa mishi ya warware aikinnan.”
“Hukuma kuma Malam? Me kuma ya kawo hukuma a cikin wannan maganar?”
Ta faɗa jikinta a sanyaye.
“Ƙwarai kuwa hukuma. Ashe ɗazu baki ji abinda na ce ba kenan? Ke na ga ma kina neman ɓata min lokaci, bari in kira kawai azo a tattara min ke zuwa can, shi ma kawun naki duk inda yake a ƙasar nan cikin ƙanƙanin lokaci za’a damƙo shi”
Har ya fara daddana wayarsa da saurin gaske Maman Murad ta ce
“Dakata Alhaji, Allah ya huci zuciyarka. Don girman Allah maganar ba sai ta je gaba ba. Yanzu zan kira Kawun nawa.”
A duniya idan akwai abinda Maman Murad take tsoro bai wuce harkar hukuma ba.
Duk baki da tsananin bala’i irin nata ko fadar mai unguwa aka kaita ta dinga rusa kuka kenan tana bayar da hakuri. Ko da kuwa ita ce da gaskiya, balle ace gurin ƴansanda? ba ta fatan ko maƙiyinta a jarabceshi da zuwa gurin ƴansanda.
Duk da kawun nata ya sha sanar da ita irin wannan aikin bai da makari. Haka nan ta ɗauki wayarta ta kunna, ta lalubo lambarsa ta danna mishi kira, a amsa kuwwa ta saka wayar don Mukhtar ya ji da kunnensa abinda kawunta zai faɗa.
Ringing ɗaya, biyu, ya ɗaga daga can ɓangaren. Duk da jiya ta bar gida, amma ba ya ganin kiranta yaƙi ɗagawa ko me yake yi, saboda ita ɗin abokiyar cin mushensa ce. Hajiyoyi take amso ayyukansu daga birni tana kai mishi yana samun na cin abinci.
“Assalamu alaikum! Mariya? Daɗa in ce kau kin koma gida lahiya? Wallah tun jiya nika biɗat nambarki ba ni samu, nicce ko shigiyat abinga ta sadarwar garinmu tayi mana tsiyat da ta saba…”
“Kawu kana ji na?”
Tayi gaggawar katse shi sanin da tayi shi ɗin uban surutu ne. Yana amsa yana jin ta ta cigaba da cewa,
“Ina wannan matar Maman Ummee da nicce maka ita uwarɗakina ce? Har nihhaɗaka da ita ga waya kun kayi magana ta ƙara whaɗi maka yadda taka biɗar aikin da za’ayi ga kishiyarta ya kasance. Ka tuna ta?”
“Ƙwarai kuwa na tuna ta Mariya. Ta ina zan manta wannan muguwar mata da tacce tana biɗat inyi gagarumin aikin da kishiyatta za tayi muguwar wulaƙanta irin wulaƙancin da bata taɓa ganin wata ƴa mace tayi a duniya ba. Ko ba ita kika magana ba? Wacce har tacce sunanta Fatima kau? sunan mijin da za ta aura Mutari, sunan uwargidan nata Fidda’u take ko Fareeda? Na dai manta. Mi shinka faru? Ko wani aikin taka biɗar a sake yi mata? Kin san dai ko ga wancan lokaci na whaɗi miki ita wannan kishiyar tata ba ta taɓuwa sai wani ikon Allah. Macece mai yawan Ibada da addu’a, ko aikin salamta kasa yi niyyi ga ita, daɗa shi nassa nayi aikin langwai ga mijinta yadda ko kusa ba shi iya kusantar ita matar tasa…”
“Kawu ka saurara mana.”
Maman Murad ta katse shi, idanunta ciccike da hawaye. Tana kallon fuskar wayarta tana satar kallon Mukhtar da izuwa yanzu sai girgiza ƙafafu yake yi, tana ganin yadda yake ta dunƙule hannu a fusace kamar zai kai naushi sai kuma ya buɗe hannun.
“Kawu, ita wannan Fatima da ta baka aikin, Ga ta zaune a gefe na ita da mijinta wai ba ta buƙatar aikin. Don Allah kawu ka taimaka min, ka warware wagga aiki da kayyi kan mijinta Mutari, ka ganshi nan tsaye bisa kaina riƙe da bindiga mai jigida a hannunsa. Ɗazu da ya kafta min mari ina rantse maka da Allah tsawon lokaci nikkasa tantance shin a duniya nike ko har na mace ne an whara min hisabi ga munanan ayyukan da niyyi. Daɗa Kawu ashe shi mijinta soja ne, ya ce idan baka warware wagga aiki ba zai kashe ni sannan ya zo har nan garinmu ya kashe ka da duk iyalinka. Daɗa ga Baban Murad yayi maka ƙarin bayani. Don girman Allah kawu ka taimaka min.”
Hannunta na rawa ta miƙa ma mijinta wayar. Wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanunta, ta kalli Fatima da duk ita ce ta janyo mata wannan bala’in tana zaman zamanta ta galla mata wata matsiyar harara, har yanzu ɓangaren kumatunta da Mukhtar ya mara bai daina raɗaɗi ba.
Fatima dai bata san tana yi ba, ta rasa inda za ta tsoma ranta ne. Tunda ta ji Malam Bello ya faɗi irin aikin da tace a yi kan Fareeda bata san sa’adda ta sauka daga kan kujerar da take ɗofane ba, ta tsuguna a dandaryar sumintin tsakar ɗakin kamar mai jin kashi.
Hannunta na hagu ɗore a tsakiyar kanta. Idanunta a rufe amma hawaye ne ke tseren gudu a kumatunta. Zuciyarta cike da wani iri da-na sani mai bala’in yawan da ko kusa baki bazai iya baiyanawa ba. Bata taɓa tsammanin lamarin zai juye haka ba, bata taɓa zaton Malam Bello kawun maman Murad mutum ne mai masifaffen surutu har haka ba. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ita dai tata ta ƙare, ta san yau babu abinda zai hana Mukhtar ya lakaɗa mata tsinannen duka sa’annan ya sake ta saki uku!!
Baban Murad ya san halin Malam Bello da taurin kan riƙe amanar aikin bokancin da yake yi. Don haka ya cigaba da ɗorawa kan inda matarsa ta tsaya, sosai ya cigaba da tsoratar da Kawu bello ta hanyar tabbatar masa lallai fa ga Mariya nan an rutsa kanta da bindiga mai jigida. Matserar rayuwarta kawai a warware wannan aikin ne.
“Daɗa amma wannan mata Fatima anyi walakantacciya. Ita ta san mijinta soji ne tammiƙo sunanshi garen da cewa in mata aiki akan matarshi? Ni wha ko lokacin na ga Mutarin mai bala’in zafin zuciya ne. Ni Bello na ga ta kaina, yanzu ya zanyi? ta ina zan whara aikin warware wagga aiki da ban taɓa yi na kunce ba…”
“Au!!! Don abu kaza-kazanka baka san ta inda za ka fara warware aikin ba ko?”
Mukhtar yayi maganar a fusace cikin tsawa bayan ya lailayo wata ƙatuwar ashariya ya maka ma malamin. Da takalmin ƙafarsa ya taka har inda mijin Maman Murad yake ya fincike wayar a hannunsa.
“Wallahi, Tallahi, Na rantse da girman Allah yinin yau da gobe kawai kake da. A daren gobe zan tabbatar ka warware aikin ko baka warware ba? Idan ka cika ɗan halas kar ka warware, za kaga yadda safiyar jibi ba ƙauyenku na Maru kaɗai ba jihar zamfara gaba ɗaya za ta san ka taɓo musu tsuliyar dodo.”
Cikin fushi yayi hurgi da wayar ta maku da bango, ya aika ma Maman Murad wani fusataccen kallo kamar mai niyyar haɗiyeta, da saurin gaske ta sunkuyar da kanta ƙasa, a tsorace, jikinta sai makyarkyata yake yi.
Juyawa yayi zuwa inda Fatima ke tsugune ya damƙi kafaɗarta guda ya ɗaga ta tsaye.
“Wuce mu tafi.”
Yayi mata maganar da tsawa.
Har sun isa ƙofar fita daga ɗakin sai ya waiga ya kalli matar da mijin da suka yi tsuru-tsuru, bayyanannen tashin hankali da tsoro ƙarara a fuskarsu.
Wani taƙaitaccen murmushi da ƙarara yake nuna na mugunta ne ya sakar ma Maman Murad.
“Idan kin so, kina iya gudu daga yau zuwa gobe. Hhhh! Don Allah ina so ki gwada haka. A lokacin ne za ki gane asalin wanene Mutarin da kuke kira, don Allah kar ki saka mugun Kawunki ya warware ƙullin da yayi min ki gane. Muddin kika bari na sake dawowa ɗakinnan…”
Yayi ƙwafa, ya karkaɗa mata ƴar yatsarsa manuniya. Ya sake ƙwafa a karo na biyu, ya girgiza kai sannan ya finciki Fatima da saurin gaske suka fice daga ɗakin.
Saboda yadda hankalinsa yake a ɗugunzume ko damar saka takalmi bai ba Fatima ba. A haka yaja hannunta suka ratsa cinciron matan gidan da suke tsaye cirko-cirko suka fice daga gidan. Bai sake hannun Fatima ba sai da ya buɗe ƙofar ɓangaren mai zaman banza ya hurga ta ciki ya rufe ƙofar da sauri.
A haukace ya figi motar suka bar unguwar, ƙiris ya rage ya kaɗe wasu yara uku da suka zo wucewa Allah ya taimaka ya ci burki da ƙarfin gaske, su kuwa yaran da bala’in guda suka ƙarasa wucewa da karaɗin ihu irin na waɗanda suka tsallake rijiya da baya.
A tsorace Fatima ta zaro idanu tana kallon abinda ya kusa faruwa. Ganin Allah ya tsare yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta kalle shi da raunanan idanunta da har lokacin ruwan hawaye basu daina tsiyaya ba ta ce
“Has… Aban Twince don Allah…”
“Idan kika sake min magana a cikin motar nan na rantse da Allah zan baki mamaki.”
Ya katse ta da faɗin haka a fusace.
Gudu ya cigaba da shananawa, ita dai Fatima tun tana hawaye bata san sa’adda ta jingina kanta da kujeran mota ta fara gyangyaɗi ba.
“Sauka”
Ta ji muryarsa yana faɗin haka kamar a mafarki.
Ko da ta ɗaga idanunta da tunanin barcinta yayi nisa har sun isa gida bata sani ba gabanta ne ya rugurguje ya faɗi. Ba gidanshi ya kai ta ba, gidan ƙanwar mahaifitarta ce in da tayi taron bikinsu. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, tun kafin tayi magana hawayen da ta samu suka tsaya daƙyar sanadiyyar gyangyaɗin da ta fara yi suka sake ɓalle mata. Ta ma manta kashedin da ya mata na kar ta sake mishi magana a cikin motar.
“Mukhtar…”
“Ki sauka min a mota. Ki shiga gidanku. Kije ki ƙaro tarbiyya da ilimin yadda ake zama da mutane tsakani da Allah a ƙauna ce su da zuciya ɗaya. Idan kin gyara, ko nan da wata tara ne da yiwuwar in duba in gani, kila, kila, kila in iya zama da ke. Amma a yanzu kam bazan iya ba, kina buƙatar saiti na gaban iyaye Fatima, kin shallake duk yadda na tsammace ki.”
Da kanshi ya zura hannu ta jikinta ya buɗe mata ƙofar.
“Fita”
Ya sake bata umarni a karo na biyu.
Maganganun Mukhtar sun daskarar da ita, ko motsi ta kasa yi, Sai hawaye da take kamar an buɗe famfo.
“Za ki fita ne ko sai na ja ki da ƙarfi na fitar da ke?”
Ya tambayeta. A ƙarshe dai ƙin fita tayi, shi da kanshi ya zagaya ta inda take zaune ya fitar da ita, ko da ya sake hannunta sai ta tafi taga-taga kamar za ta faɗi yayi kamar bai gani ba. A dole ta koma ta tsaya, tana ji tana gani yaja motarsa a guje yabar unguwar bayan ya baɗa mata ƙura.
Zaman daɓaro, shi ne abinda Fatima tayi a ƙofar gidan Innarta. Zuciyarta cike da tunanin mafita da hanya mai ɓullewa. Ga hawaye har lokacin bai daina zuba a idanunta ba. Tana cikin wannan halin sai ga Nura ɗan gidan Inna ya fito daga gidan, ya kalli Fatima ya ƙara kallah.
Sai kuma ya kama haɓa cikin mamaki ya ce
“Aunty Fatima lafiya? Me yake faruwa? wa ya rasu? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”
Duk yadda yake ta magana hankali tashe yana jijjaga kafaɗarta ta kasa ce mishi uffan! Afujajan ya koma cikin gida don kiran mahaifiyarsu, ko kafin su fito har Fatima ta tare mai mashin ta haye, suna fitowa sai bayanta suka hanga ana ɓanana wuta da ita akan mashin.
“Allah ya kyauta. Ko ma menene za muji daga baya. Yanzu dai kai ka tafi gurin harkokinka. Idan na shiga gida zan kira Yaya (Mahaifiyar Fatima) duk abinda yake akwai zan ji, idan na tashin hankali ne zan kira in sanar da kai.”
*****
Mai mashin ɗin da ya ɗauketa bai aje ta ako ina ba sai a ƙofar gidan Hajiyar Muktar, can unguwar dosa. Ta hanga ta hango a daidai wannan gaɓar da take ciki Hajiyarmu ita ce last hope ɗinta. Tunda dai Allah yasa har Mukhtar ya sauke ta bai furta mata kalmar saki ba, to lallai aure tsakaninta da shi mutu ka raba. Indai wannan girman laifin bai sa shi sakinta ba bata ga wani laifi da za tayi mishi a duniya ya sake ta ba.
Haƙuri ta ba mai mashin ɗin ta shiga cikin gidan gurin Hajiyarmu ta amso dubu ɗaya ta kai mishi.
Ko da ta koma cikin gidan da fuska ƙozai-ƙozai sai kallonta Hajiyarmu ke yi. Da ganin fuskar Fatima za’a gane ta sha kuka. Bayan gaisuwa da ya shiga tsakaninsu da yake Hajiyar ba macece mai son shiga abinda ba’a kasa da ita ba sai bata fara tambayar Fatima abinda ke faruwa ba.
Fatima ce ta gaji da mutsu mutsu ta sake muskutawa a inda take zaune. Tayi rau-rau da idanu nan take suka tara tuwan hawaye, ta buɗe baki za tayi magana sai ga Sayyid ya fito daga kicin ɗin Hajiya hannunsa riƙe da ɗan ƙaramin faranti an ɗora soyayyiyar indomie da ƙwai akan farantin. Lokaci ɗaya ƙamshin abinci ya game falon gaba ɗaya.
Lokaci ɗaya zuciyar Fatima ya fara tashi, cikinta ya fara hautsinawa. Ta buɗe baki za tayi magana kawai sai amai ya taho mata. Ai kuwa da bala’in gudu ta miƙe ta shige bayin falon da ta san da zamanshi tun zamanin tana rako Fareeda idan wani abu ya faru a gidan.
“Lafiya kuwa? Me yake damunki haka?”
Hajiyar ta tambayeta da kulawa, ganin irin aman kumallo da tayi sa’anna ta zauna ta dafe kanta da cewar yana mata ciwo kamar zai faɗi.
“Hajiya kaina… kaina… wayyo Allah na…”
Abinda Fatima take iya faɗe kenan tana runtse idanu da cije baki.
Aunty Jimmalo babbar nurse ce a unguwarsu Hajiyarmu. Gida biyu ne tsakaninta da Hajiyar, akwai kyakkyawar mu’amala tsakaninsu. A ƙarshe dai dole ita Hajiya ta kira ta duba Fatima.
Bayan duk wasu gwaje-gwaje da ya kamata ayi a gaggauce sakamako ya nuna Fatima tana da shigar ciki.”
Wannan ciki da aka tabbatar ma da Hajiyarmu Fatima tana ɗauke da shi, shi ne abinda ya sanyayar da jikin Hajiyar gaba ɗaya. Ta zauna kan kujera tayi shiru tana jinjina ƙarfin iko irinna Ubangiji.
Wato ƙaƙƙarfan rabo ke a tsakanin Fatima da Mukhtar! Iko sai Allah.
Lokaci bayan lokaci takan tashi daga falon ta leƙa ɗakin da Fatima take kwance tana barci cikin nutsuwa. Awa biyu ta ɗauka cif tana barci kafin ta farka da wani gigitaccen yunwa, daƙyar ta iya wanke baki ta fita falon gurin Hajiya.
Bayan tambayar ya jiki teburin cin abinci Hajiyarmu ta nuna mata da yake ɗauke da kayan tea da dafaffen abinci. Cikin ɗaki Hajiyar ta shige don ta ba Fatiman damar cin abinci a nutse ba tare da takura ba.