Mamaki mai tsanani ne ya lulluɓe shi ganin Fatima kwance kan doguwar kujera a falon Hajiyarmu. Ƙam ya tsaya guri ɗaya yana ɗan murza idanunsa, da tunanin ko tsananin caja mishi kai da take yi ne yasa ta fara yi mishi gizo.
Ganin bata ɓace ba yasa shi tabbatar da Fatima ce a gaske.
“Me ya kawo ki gidannan?”
Ya tambayeta cikin tsawa da ɓacin rai.
A kasale ta miƙe ta zauna tana yamutsa fuska. Tunda tayi amannan har yanzu ƙarfin jikinta bai dawo ba. Ta buɗe baki za tayi magana da saurin gaske ya dakatar da ita.
“Tashi ki fita! Wai ke wace irin mayya ce? Na zaci har ƙofar gidanku na kai ki amma shi ne kika sake biyo ni nan? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ya Allah kayi min tsari da wannan bala’i…”
“Mukhtar!!!”
Ta kira shi da asalin sunanshi, abinda ta daɗe bata yi ba.
“Ka yi hauka ne? Iyalin taka ce kake kira da bala’i?”
Hajiyarmu ta tambayeshi da tsawa sosai a muryarta.
Ya kasa amsawa, sai sunkuyar da kanshi ƙasa yayi yana jin yadda ranshi ke ƙuna da raɗaɗi.
A hankali Hajiyarmu ta tako cikin nutsuwa har zuwa kusa da su biyun. Da yatsarta manuniya ta nuna su, fuskarta a ɗaure tamau.
“Ku biyunnan, ku kuka ga junanku kuka nace kuna so ba tare da son ran mu iyayenku ba. Don haka, Mukhtar duk wani fate-fate na azaba da Fatima za ta dama maka dole kai kaɗai za ka sharɓi abinka. Ke kuma”
Ta nuna Fatima da yatsarta manuniya, kafin ta cigaba da cewa
“Ina da labarin duk irin tsiyatakun da kika tsula ma mutane kika nace har sai da aka ɗaura wannan aure. Cikin waɗanda kika bijere ma har da mahaifiyarki, don haka kuka baki ma fara ba tukunna! Bazan hana ki zuwa gidannan ba, amma daga yau kar ki kuskura ki sake zuwa min gida da wani ƙara ko ƙorafi. Ku ji da kanku ku biyun, kun ce kun ji kun gani, don haka mun barku da junanku.”
“Hajiya…”
“Ban nemi ƙarin bayani ba. Ba na son jin komai. Riƙe maganarka a cikinka. A cikin ko wace irin zamantakewa haƙuri, kawar da kai, yi ma juna uzuri su ne ja-gaban da suke kai ma’abota zamantakewar ga tudun mun tsira.
Don haka kuje kuyi ta haƙuri da juna, wata rana sai labari. Ɗauki matarka ku tafi.”
Hajiyarmu ta katse Mukhtar da ya kira sunanta a raunane yana niyyar yi faɗa mata abinda Fatima tayi masa.
Hankalinsa ne ya ɗugunzuma jin ta ce ya ɗauki Fatima su tafi. Tsananin tashin hankali bai san sa’adda ya zube gwuiyawunsa a ƙasa gaban Hajiyarmu ba. Ya kalleta cikin ido, idanunshi ciccike da ƙwallah, ji yake kamar ya ɗora hannu biyu akai yai ta rusa ihu ko Hajiyarmu za ta bashi dama yayi mata abinda yake faruwa.
Tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah. Yanayinsa ya taɓa mata zuciya, amma alƙawari ne tayi ma kanta tun sa’adda ya cije ma auro Fatima baza ta taɓa shiga al’amarin su biyun ba. Ko kwanaki da tayi magana don lamarin ya shafi su Sayyid ne.
Kawar da kai tayi, ta ɗan sassauta fuskarta kaɗan sai ta dawo da kallonta gare shi.
“Sai ka fara tanadi. Ɗazu Aunty Jimmalo ta tabbatar da ciki a jikin Fatima…”
“Ciki? Na shiga uku!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!!”
Ya jero maganganun cikin tashin hankali da ɗimuwa. Ƙasa ya duƙar da kanshi. Wani abin mamaki da Hajiya baza ta iya tuna lokaci na ƙarshe da taga faruwarsa a fuskar Mukhtar ba shi ne saukar hawaye a idanunsa, kawai ɗiɗɗigarsu ta gani a jikin farar yadin boyel ɗin da ke sanye a jikinsa.
“Uhmmm!”
Ta faɗa cikin mamaki da tu’ajjibi. Hannayenta ta fara tafawa tana sallallami, sai kuma ta riƙe haɓa ta ce
“Kuka kake yi don na faɗa maka masoyiyar maƙwallaton zuciyarka na ɗauke da ciki? Halan ku biyun abu ne da baku taɓa tsammani ba? Itama nan ta gama sussunne kai tana sharar ƙwallah. Madallah! Ɗan so ko ƴar so an tabbatar da ƙyanƙyasan ƙwayayensu ai dole kuyi kuka. Amma a shawarce ba kuka ya kamata kuyi ba. Godiya ga Allah za kuyi da addu’ar Allah ya raba lafiya. Ɗauki matarka ku tafi, aji tsoron Allah a dinga kiyaye adalci tsakanin mata biyu.”
Mukhtar sai da ya ɗauki tsawon mintuna uku yana matsar hawaye kamar mace. Sannan ya iya miƙewa tsaye, idanunsa sun kaɗa sunyi ja sosai. Ya ɗan duƙa kaɗan ya ce
“Hajiyarmu a huta gajiya. Na gode. Allah ya kara lafiya da nisan kwana.”
Ya ƙarasa gurin Fatima ya jefa mata wani kausasshen kallo da idanunsa sannan ya ce
“Tashi mu tafi.”
A tsorace ta kalle shi, sai kuma ta kalli Hajiya. Ta sake kallonshi ta kalli Hajiya. Marairaice fuska tayi idanunta na kan Hajiyar ta ce
“Hajiya don Allah ki barni anan…”
“Wa ce za ta barki anan? Allah ya kiyashe ni. Tashi tsaye maza sawunki a likkafa ki bi mijinki ku sha soyayya. Yadda aka ƙyanƙyashi ɗan so ai ya kamata a reni wannan ƙwai cikin tsananin soyayya da tarairaya.”
Da saurin gaske Fatima ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya. Kalaman da ta faɗa ma ƙawarta ɗazu a waya cewa ita da Haskenta sun jajurce a cikin kwanaki ƙalilan sun ƙyanƙyaso ƙwayayen ƴaƴan soyayya shi ne Hajiyar take saƙa mata su. Ko kaɗan bata zaci Hajiyar na jin ta ba, da baza ta saki baki tai ta surutu haka ba.
Kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi aka cire haka ta miƙe a ɗarare ta bi bayan Mukhtar. Daƙyar ta iya buɗe ƙofar mota ta shiga ciki, ta matse jikinta guri ɗaya ta duƙar da kanta a ƙasa.
Tsabar tayi nisa a lissafin dokin rano ko kusa bata san sun isa gida ba, sai da taji ya kashe motar, ya buɗe ƙofa ya fita haɗe da buga ƙofar motar da ƙarfi.
A kasale ta buɗe ƙofar ta fita, tana kallonshi ya shige ɓangaren Fareeda. Haka taja ƙafafunta a sanyaye zuwa ɓangarenta.
*****
Agogon bangon ɗakin ya kalla, ƙarfe uku da minti arba’in da biyu na yammaci. Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa cikin ɗakin ya haye kan gadon. Barci take yi, hankalinta kwance, irin barcin nan da a kallon bawa za’a gane barci ne na nutsuwa, kuma ana jin daɗin barcin nan.
Baya son tashinta, amma a daidai wannan lokacin ba shi da yadda ya iya. Ita ɗin kawai yake buƙatar jin ɗumin jikinta. A hankali jikinsa na rawa-rawa ya ƙarasa jikinta ya ruƙunƙumeta da ɗan ƙarfi. Lokaci ɗaya hawayensa ya dawo.
Cikin barci kamar a mafarki Fareeda ta ji an rungumeta, da fari ta zaci mafarki take yi. Amma daga baya da ta tabbatar da gaske ne ga kuma ƙamshin turaren Mukhtar da har ya fara kama jikinsa kawai sai ta fara mutsu-mutsu tana ƙoƙarin ƙwacewa, idanunta a rufe.
Da saurin gaske ta buɗe idanu jin kamar ana jan shessheƙa. Mukhtar ne ke kuka, Mukhtar ɗin da ta sanshi a mutum mare haƙuri, Mukhtar mai juriya da jajurcewa. Jaruminnan da abu ɗai ɗai ne ke nasarar karya mishi zuciya, wai yau shi ne ke riƙe da ita yana kuka. Matsanancin mamaki ne ya lulluɓeta, sai take tunanin kamar ba kukan gaske yake yi ba. Domin share ma kanta tantama da saurin gaske ta ɗaga fuskarsa da hannunta na dama. Hawaye ne ta gani, ga su nan kace-kace a fuskar
“Wwwwwwwa ya rasu?”
Tayi mishi tambayar bakinta na rawa.
Daƙyar ya iya girgiza mata kai alamar babu kowa ya sake mayar da kansa jikinta ya cigaba daga inda ya tsaya. A hankali ta ɗan sauke ajiyar zuciya, sai tayi luf tana saurarensa, ita bata cigaba da yunƙurin ƙwacewa ba sannan bata tambayeshi me ya same shi yake kuka ba.
Tun tana jin shessheƙarshi har ya koma sauke ajiyar zuciya, can kuma sai ta ji shi yayi shiru, yana sauke numfashi a hankali.
Ɗan motsawa tayi kaɗan bayan ta yi tunanin zai iya yin barci.
“Zan yi sallah, lokacin sallar la’asar yayi.”
A hankali ya fara sassauta riƙon da yayi mata, har ya sake ta gaba ɗaya. Yana kallonta ta sauka akan gadon har ta shige banɗaki. Tsoro ne ya kama shi, ganin babu wata damuwa a fuskar Fareeda. Yaushe yayi kwantan da har kukanshi bazai jefa ta cikin tsananin ruɗani da tashin hankali ba? Lallai ya tafka kura-kurai da dama a ginanniyar zamantakewar da suka faro ta da ƙaƙƙarfan tubali na gaskiya da riƙon amana.
Lallai ya kamata ya gyara tun kafin kwaɓar ta idasa yi masa ruwa. Sai ya tuna irin yadda a baya, kafin shigowar Fatima cikin rayuwarsu, ko damuwa a fuska ya fita ya dawo mata da shi hankalinta ba ya taɓa kwanciya sai taga walwala a fuskarsa.
Yana wannan tunanin ta fito daga bayi. Ko kallonshi bata yi ba, gurin kayanta ta nufa kai tsaye ta ɗauki doguwar riga da hijabi ta saka ta shimfiɗa sallaya ta fuskanci gabas. Sai a lokacin ta ɗan waiwaya ta kalleshi da fuska ba yabo ba fallasa.
“A masallaci dai har an idar da sallah. Gara ka miƙe ka sauke farali, bayan nan idan kwanciyar za ka cigaba da yi sai ka koma gurin matarka…”
“Kora ta kike yi?”
Ya katse ta, da muryarsa a sanyaye.
“Ai kam dai korarka nake yi Mukhtar. Ban ga dalilin da zai sa kazo kayi min kwance da ranar nan alhali ba girki na bane. Ni zanyi sallah.”
Kafin ya ce wani abu har ta fara tayar da iƙama.
Shi ma bai cigaba da kwanciyar ba, banɗakinta ya shiga bayan gama biyan buƙatarsa yayi alwala. Bai fita daga ɗakin kamar yadda ta so ba ya ɗauki sallaya ya shimfiɗa nesa da ita kaɗan ya tayar da sallah.
Tana zaune tana lazimi har ya idar. Bayan istigfari da gajeren addu’a juyawa yayi gaba ɗaya ya fuskanceta.
“Don Allah, ki shafa addu’a ki ɗan bani minti biyar daga cikin lokacinki. Don Allah ba don ni ba…”
Haka nan ba don zuciyarta na so ba ta bi umarninsa. Fuskarnan a ɗaure, baki a gaba. Allah ya sani a yanzu ta tsani ko ɗan yaya ne ya matse mata guri. Bakinnan a gaba ta tsattsare shi da idanu tana jiran jin abinda zai ce da ita.
“Fareeda, a yanzu na gane kuma na tabbatar a zamantakewar auren da muka yi a baya kafin in ƙaro aure, kashi sittin da biyar cikin ɗari na irin saɓanin da muka yi ta samu ba kowa ne ya janyo haka ba face ni. Amma da yake a wancan lokacin ina kan wani ɓigiri ne da Malam bahaushe yake kira ƙaramin sani ƙuƙumi. Don girman Allah kiyi haƙuri ki yafe min, irin yadda nayi ta ƙuntata rayuwarki a baya tun daga aurenmu har zuwa yau ɗinnan da nake miki magana.
Fareeda, na rantse miki da Allah ban auro Fatima don in tozarta ki ba. Ina son ki har gobe Fareeda, a tunanina auren Fatima da zanyi shi ne abu na ƙarshe da zanyi wanda zai sa ki shiga hankalinki da gaggawa.
Ban gane ni ɗin ba ni da wayau ba, kuma na tafka gagarumin kuskure sai tsakanin jiya da yau da wata irin nutsattsiyar tattaunawa ta shiga tsakanina da wani mai buɗaɗɗe kuma wayayyen tunani. Ashe ba maganin matsala na ɗauko ma kaina ba, wata gaggarumar matsalar mai zaman kanta na ɗauko na ɗora ma kaina.
Ban gane ni ɗin ba mai godiya ga ni’imar da Allah yayi mishi bane sai ayau ɗinnan.”
Ya duƙar da kanshi, wata sabuwar ƙwallar ta cicciko a idanunsa. Babu abinda yake tunani a zuciyarsa sai Fatima da cikin da aka ce tana ɗauke da shi.
Aka ce a nemawa ƴaƴa uwa ta gari. A cikin kwanakin zamantakewarsu yayi ma Fatima wani irin karatu ne na nutsuwa, ya gane duk yadda yake tsammaninta ta shallake tunaninsa. A haƙiƙanin gaskiya ma tsoro take ba shi, ta ina zaiyi farin cikin haɗa zuri’a da Fatima?
Da ƙyar ya iya haɗiɗiye ƙwallarsa ya kamo hannunta guda ɗaya cikin nashi, a raunane ya cigaba da magana bayan yayi ƙoƙarin kawar da tunanin Fatima daga zuciyarsa.
“Duk wani dogon bayani a yanzu ba shi da amfani Fareeda. Na san duk abinda zan faɗa a yanzu za ki dinga kallonshi a ihu ne bayan hari.
Amma a karo na barkatai zan ƙara roƙonki, ki bani dama ta ƙarshe don darajar iyayenki da suka rigayemu gidan gaskiya. Don Allah SWT, don darajar Fiyayyen halitta SAW abinda ya wuce ki barshi a wanda ya wuce. Mu fuskanci gaba, ki ajiye duk wani baƙin ciki da ɓacin rai da na cusa miki cikin ƴan kwanakinnan da waɗanda suka gabace su. Ni kuma ina tabbatar miki in Allah ya yarda za ki same ni a sabon Mukhtar ɗin da baki taɓa tsammani za ki gani a cikin taƙaitaccen lokaci haka ba. Don Allah…”
Me nace ka yi ne Mukhtar? Ni fa ban ce kayi komai ba balle ka dinga haɗa da girman Allah da Manzonsa. Ban ƙullace ka ba, kawai na kame kaina ne daga duk abinda zai janyo min ɓacin rai da shiga tashin hankali, ko ka manta yanayin da nake ciki? Tunda dai har Allah yasa ka gano kuskurenka Alhamdulillah! Nima ina roƙon ka yafe min irin saɓa maka da nai tayi a baya. Amma don Allah ka tsahirta min, ko mun ƙi ko mun so tunda kiɗa ya canza dole tsarin rawarmu ya canza. Kaje ka ji da matarka, yau ba girkina bane. Idan da sauran magana gobe in Allah ya kaimu sai a ƙarasa.”
A sanyaye ya fice daga ɗakin ta raka shi da idanu. Yana fita daga ɗakin ta taɓe baki ta cigaba da tasbihin da take yi.
Kai tsaye ɗakin baƙi ya nufa daga na Fareeda, buɗewa yayi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya zage ya gyara ɗakin ƙal. Sai da ya gamsu ɗakin yayi yadda yake so sannan ya fice zuwa ɓangaren Fatima.
Ko da ya shiga tana zaune akan kujera. Ta yi wankanta har da kwalliya a fuskarta. Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke, ko sannun da take mishi bai amsa ba. Ɗakin barcinta ya shige, ita dai tana zaune sai ganinsa tayi yana fitowa da suturunsa da yake cikin akwatinta.
Gabanta ne ya faɗi, da saurin gaske ta miƙe tsaye hannayenta dafe da ƙirji. Bai ko kalleta ba ya fice da kayan a hannunsa, da saurin gaske ta bi bayansa ta leƙa, a zatonta ɗakin Fareeda zai kai kayan, sai taga ya nufi ɗakin baƙi da su.
Da ƙyar ta iya komawa mazauninta ta zauna a lokacin da yake daf da dawowa cikin ɗakin, haka ta dinga raka shi da idanu har ya gama kwashe suturunsa tas da duk wasu muhimman kayansa da suke cikin ɗakinta ya mayar ɗakin baƙi.
Sau takwas tana yunƙurin yi mishi magana sai ta rasa ta inda za ta fara, har yayi fita na ƙarshe da tunda ya fita bai dawo ba.
Ciki? Chakwakiya kenan dai
Yanzu kam babu ko wani rabuwa