Sa’adda ya nufi hanyar gadan-gadan a tare ita da shi ɗin suka riƙe numfashi cak suna jiran ganin abinda zai faru. Wani abun mamaki shi ne yana nan da ƙarfinsa, bai kwanta lakaf kamar lagwani ba. Ya tashi tsaye ƙyam a matsayin jarumin nan Mukhtar.
A tare ita da shi ɗin suka sauke wata iriyar nannauyan ajiyar zuciya. Bawan Allah Mukhtar sai hawaye. A fili da zuciya yake kabbara, haihala yana godiya ga Allah. Kwanaki bakwai ya kwashe yana tsayuwan dare kan Allah yasa a samu nasarar magance matsalar nan, ga shi kuwa Allah maji roƙon bawa ya amshi addu’arsa. Lallai duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. A wannan dare albarka kam Fareeda ta sha shi kwando-kwando daga bakin Mukhtar. Da wani kewa, zakwaɗi, ɗoki, farin ciki, zafin nama yake aikata komai.
A ɓangarenta duk da ta ji daɗin samun warakar matsalar da ke tsakanin su biyun, ta ji daɗin ganin yadda ko ina na jikinsa ke rawa yana ƙara rirriƙeta. Ta ji daɗin jin yadda yake ta shi mata albarka. Ko kaɗan bata nuna mishi jin daɗinta a fuska ba. Aka ce haihuwa ɗaya horon mahaifa. Ta yafe mishi tabbas, kuma a cikin kwanakin tana ganin yadda yake ta ƙoƙarin canzawa daga wancan Mukhtar ɗin mai murɗaɗɗen hali zuwa wani mai sanyin hali. Ƙudurtawa tayi a ranta baza ta sakar mishi fuska lokaci ɗaya kamar wata sakarya ba, ya zama dole ta ja ajinta, ta kame mutunci da kimarta don ƙara sama ma kanta girma da kwarjini. Amma fa hakan ba yana nufin za ta dinga wulaƙantar da shi bane.
Ko bayan kammaluwar komai haka ya riƙe ta a jikinsa yana sharar ƙwallah. Zuciyarsa cike da wani irin rauni da fargaba. Daman ya sani, shi da Fareeda kamar hanta ne da jini, baza’a taɓa raba ɗaya da ɗaya ba.
Har ta fara gyangyaɗi ya tashe ta a hankali, yana riƙe da ita a gefen kafaɗunsa suka ƙarasa banɗaki. Wanka suka yi sannan suka koma kan gado, hannayensa biyu ya buɗe ya saka ta a ƙirjinsa.
Akai akai yake sauke ajiyar zuciya, wani irin riƙo ne yayi mata, kamar wanda ke tsoron za’a ƙwace mishi ita. Bai matse ta yadda za ta wahala ba, amma yayi wani irin kanainayeta da hannayensa ta yadda ko ita ce tayi yunƙurin ƙwacewa baza ta iya da gaggawa ba. Ba tare da ɓata lokaci ba wani nannauyan barci ya kwashe su biyun, a lokacin sha biyu da rabi na dare. Agogo na buga ƙarfe huɗu na dare Fareeda ta farka, tun tana saka alarm a wayarta yanzu ta daina. Yau da kullum ta fi ƙarfin wasa, tashi a daidai irin wannan lokacin har ya bi jikinta.
Tana tunanin yadda za ta motsa da jikinta wayar Mukhtar ta fara ƙarar Assalatu khairun minannaumi. A take shi ma ya buɗe idanu, karaf idanunta suka faɗa cikin nasa. Tsawon daƙiƙu biyu suna kallon juna a cikin madaidaicin hasken ɗakin sai ya haske ta da tattausan murmushi.
Bata mayar mishi da martani ba, ta ɗan kawar da fuskarta gefe sannan ta ce,
“Zan tashi, ɗan sassauta min.”
Babu musu ya sassauta riƙon da yayi mata. Da basmala a bakinta ta miƙe zaune, salatin Annabi SAW tayi da addu’o’i sannan ta miƙe zuwa banɗaki. Tana fitowa bai ɓata lokaci a kwance ba ya shiga ya ɗauro alwalar, tana gefe yana gefe kowa ya fuskanci gabas suna kai kukansu ga rabbil Izzati. Wani ikon Allah kamar haɗin baki, a wannan dare ita da shi gaba ɗaya addu’arsu ta tattara ne ga Allah ya musu maganin damuwoyinsu, ya haɗa kansu, ya raya musu zuri’arsu, ya kawar da shaiɗan a tsakaninsu.
******
Kwanci tashi ba wuya a gurin mai kowa mai komai. In da rai da lafiya komai mai zuwa da wucewa ne. Haka zalika babu wani laifi da baza’a iya gyarawa ba, sai dai in shi wannan bawan bai ɗauki aniyar gyara tsakaninshi da mahaliccinshi ba.
Mukhtar yayi niyyar gyara, ya haɗa da addu’a. Sai Allah ya taimakeshi akan ƙudurinsa, a hankali yana danne zafin kishi da zuciyarsa yana kuma addu’ar Allah ya tama mishi sai ga shi an samu gwaggwaɓar canji da cigaba tsakaninshi da Fareeda. Yanzu wani irin tsarin zama ne suke yi na gaskiya da gaskiya, ba ɓoyo ba ƙumbiya-ƙumbiya. Sukanyi musayar ra’ayi cikin mutunta juna, ƙauna da girmama juna. A yanzu manyan turakun da suke riƙe da zamantakewarsu uku ne.
Ƙauna
Haƙuri
Uzuri ga juna.
Waɗannan matakai su suka samar da wata sassanyar zama mai daɗi da armashi a tsakaninsu. Tsawon watanni biyu kenan cif Fareeda da Fatima basu sake ganin juna cikin ido ba, da yake Fatima ce mai yawan leƙe ta window tana yawan hangen Fareeda idan za ta fita unguwa ita kaɗai ko kuma ita da Mukhtar.
Ga Fareeda kuwa ta manta da wata Fatima, ko a cikin tunani ta shafe babinta. Kuma duk tsawon lokacin nan bata taɓa sani akwai rikici tsakanin Mukhtar da Amaryarsa ba.
Kwanakin girkinta su kaɗai yake ba ta, ranar da ba nata ba tun magrib yake mata sallama ya koma ɗakin baƙi. Bata taɓa mayar da hankali ta lura da abinda ke wakana ba, to ko ma ta lura meye ruwanta a ciki? Har a sallah addu’a take Allah ya mantar da ita Fatima da lamuranta.
A ɓangaren Fatima da Mukhtar kam lamarin ƙara tsami yayi sosai. Tun da ya mata wannan korar karen ta janye jikinta, bata ƙara gigin zuwa ɗakin baƙi ba. Amma ta mayar da shi kamar wani Atm na tatsar kuɗinta, kwana ɗaya biyu za ta tura mishi saƙon ta kwana bata yi barci ba, ya bata kuɗi za ta asibiti. Ta haɗa da akawun ɗinta na banki ta tura mishi.
Da yake ƙoƙarin canja halayensa yake yi ta ko wane ɓangare na rayuwarsa bai taɓa ƙorafi ba. Sai dai yayi murmushi kawai, ya tura mata dubu uku ko biyar ya haɗa da addu’ar Allah ya shiryeta. A cikin duk kwanaki biyu na girkinta sau ɗaya rak yake leƙawa ya duba lafiyarta, shi ɗin ma ba wata magana da take shiga tsakaninsu.
Duk in ta tura mishi saƙo za ta unguwa, bai taɓa hana ta ba. Amsarshi ɗaya da zai bata shi ne.
“Allah ya tsare.”
A take zai tura mata 1k ya rubuta kuɗin napep.
Duk wannan yaji da Mukhtar yayi ma Fatima har yanzu Allah bai sa ta fuskanci inda yake so ta fuskanta ba. Tsanar Fareeda kullum ƙara ninkuwa yake a zuciyarta, kullum addu’arta ɗaya shi ne Allah ya bata dama ko ɗan yaya ne tai yaga-yaga da Fareeda.
Mukhtar kuwa tara shi take yi, ta barshi ne har zuwa sadda Allah zai sauketa lafiya. Ta san da ta haihu yaga kyawawan jarirai a gidansa tana zaune zai fara bikonta, a lokacin ne za ta gwada mishi lallai shiru-shiru ba tsoro bane, gudun magana ne.
******
Tana shiga cikin ɗakin ko zama bata yi ba ta fara zazzaga bala’i kan shariyar da ƙannenta suka mata, sun ganta amma suka nuna kamar basu san wacece ita ba.
“Inna kina kallon yarannan ko? Yanzu saboda Allah da Annabi ni ba ni da alfarmar da zan shigo gidannan su miƙe su tarbeni cikin farin ciki da nuna ƙauna? Miye laifina? Ko don an ga yanzu ba ni cikin daular da nake ciki ada? Sunnar Annabi SAW da na raya shi ne abinda zai janyo min tsana da hantara a gurin ku?”
Sai kuma tayi takwaf-takwaf da fuska kamar za ta saka ihu.
“Aure ne nayi fa Inna ba karuwanci na tafi ba. Don Allah don Annabi ki yafe min. Ki fahimce ni mana. Kinga fa saboda fushin da kike yi da ni har yanzu na kasa cimma abinda nake burin cimmawa a aurennan. Rabo ne tsakanina da Mukhtar Inna, ƙaƙƙarfan rabo. Ni abinda nake so ki dinga tunawa wani bai taɓa auren matar wani, ni da Fareeda tun fil-azal Allah ya ƙaddara sai mun auri miji ɗaya. To menene laifina don rubutacciyar ƙaddara ta tabbata a kanmu…?”
“Ba ki da laifi Binta, ko kusa ba ki da laifi.”
Uwar ta faɗa idanunta a ƙasa tana cigaba da ƙullah kukan miya da take sayarwa.
“Rabo kuma da kike magana akai Allah ya kawo masu albarka…”
“Ai ya ma kawo Inna”
Sai kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi.
“Ciki nake da shi Inna, Wata uku kenan”
Tsam Inna ta ɗaga kanta tana kallon Fatima. Sai kuma ta jinjina kai, ta ɗan muskuta tana mamakin cikin da Fatima ta ce tana da shi. Lallai iko sai Allah Al’musawwiru.
Tsawon wasu mintuna shiru ne a tsakaninsu. Can sai Inna ta katse shirun da cewa
“Ya Fareeda da ƴaƴanta? Ina fatan duk suna nan lafiya?”
Yamutsa fuska tayi jin an taɓo inda yake mata ƙaiƙayi, sai ta nemi guri a gefen gadon ɗakin ta zauna.
“Inna Fareeda tana ɓangarenta ina nawa. Babu wacce ta san ya lafiyar ƴar’uwarta take. Domin ku ne kuke mata kallon wata mutuniyar arziki, wallahi kwanaki daga ɗan faɗa ya haɗa mu kar kiso kiga yadda ta zage ni ta uwa ta uba…”
“Duk da ba ni na haifeta ba na san haliinku ɗaya bayan ɗaya. Idan za ki dafa Alƙur’ani ki rantse bazan taɓa yarda ta zage ki ba tare da ke ce kika janyo rikici a tsakaninku ba. Ni dai na faɗa miki, ba baki nake miki ba Binta. Ba kuma fushi nake yi da ke ba. Wallahi matuƙar baki tsarkake zuciya kin nufi kowa da alkhairi ba matsala baki ga komai ba, duk wacce kike ciki somin taɓi ne.
Ni na haife ki Binta. Baza ki taɓa layance min ba. Tun kina ƴar ƙanƙanuwarki ako wane lamari da zai taso ke macece mai bala’in son kanki. Idan za ki dafa Alƙur’ani ki rantse bazan taɓa yarda bayan son raya sunnar aure babu wani abu a zuciyarki ba game da auren mijin aminiyarki ba.
Aure tsakaninki da Muntari ko kusa babu haramci a cikinsa. Amma ni abinda naso, da kinyi haƙuri kin kawar da kai, da idanun duniya basu dawo kanki haka ba. Da kin nuna ƙin al’amarin a fili ko da zuciyarki tana tsananin so, da bakunan da za suyi Allah wadarai da al’amarin basu kai yawan haka ba. Da kin nuna ma Fareeda da alkhairi da zuciya ɗaya kika shiga gidanta, da danganta a tsakaninku bata yi tsami haka ba. To amma Binta duk baki bi waɗannan hanyoyin ba, ana nuna miki Annabi kina runtse idanu, duk wanda yaso nusar da ke sai ki fitittike kiyi ta zuba rashin mutunci, kina ganin nema ake a hana ki auren Mukhtar da kike tsananin so da ƙauna. To an ƙyale ki kin aure shi, kin ga Mukhtar shi ma ya ganki, sai ku cigaba da zama. Allah ya bada sa’a. Fatana da addu’ata ako wane lokaci Aniyar kowa ta bi shi a cikin ku ukun!!”
Wani irin ƙunci da ɓacin rai mai tsanani ne ya lulluɓeta a sanadiyyar jin kalamin da ke fita daga bakin Innarsu. Ita da ta je gidan da niyyar yini har yamma lis, saboda tun da tayi aure bata taɓa zuwa gida ba sai a ranar. Ko minti uku bata ƙara ba ta tattara komatsanta a cikin jaka ta fice a gidan, fuskarta a ɗaure.
Da murmushi uwar ta raka ta. A zuciyarta ta bi ta da addu’ar shiriya.
Daga nan tayi niyyar zuwa gidan Inna Rabi, har ta ce ma mai mashin ga inda zai kaita sai kuma ta canza shawara.
“Malam kai ni Askulaye. Na manta zan je dubiyar mare lafiya.”
Ƙasa-ƙasa yaja tsaki, jin ta ce dubiya za ta je shiyasa baiyi ƙorafi ba. Nan take ya juya akalar mashin ɗin ya fara wani irin tuƙi na ganganci yana walagigi da ita a tsakiyar hanya.
Daga can tsallaken titi da saurin gaske Idriss ya taɓo Mukhtar yana nuna mishi, Fatima da suke tsakiyar titi wani mai mota ya kusa kwashe su ya watsar tsakiyar hanya, Allah ya taƙaita dai hatsarin bai faru ba. Shi ne fa mai mashin ɗin ya tsaya yana ta zazzaga bala’i da masifa don ganin suntumemiyar motar da ta kusa kwashe, ciyarsa cike da fatan ya ƙwamuso wasu miyagun kuɗaɗe a hannun Alhajin. Ita kuwa Fatima da zuciyarta ɗaya take taya mai mashin zazzaga tsiya, go slow har ya fara taruwa, ga jama’a sun tsaya kallo gefe da gefe.
“Mukhtar? Wancan ba amarya Fatima bace?”
Ko kafin ya ɗago kai sai da gabanshi ya faɗi. Kallo ɗaya yayi mata ya kawar da kanshi, yana jin wani irin muzanta da kunya na lulluɓe shi.
“Idriss pls bar maganarta. Ita ce ko ba ita bace ba abinda ya shafe ka bane. Muje don Allah.”
Ya ƙarasa maganar daƙyar kamar wanda ya haɗiyi taɓarya. Wai yanzu shi ne matarshi a ke hayaniya da ita haka a tsakiyar hanya? Uhmmm! Ba komai, rayuwa ce wata rana sai labari. Ya ayyana hakan a ransa, yana jin yadda zuciyarsa ke suya da tafarfasa.
*****
A gaban madubi ta tsaya kamar yadda aka umarce ta. A hankali ta zuge zip ɗin jakarta, ta ciro ƙullin ruwan maganin da tun a hanya take riƙe jakar cikin lallaɓa da tarairaya kamar wacce ta ɗauko ɗanyan ƙwai.
Rashin ganin motar Mukhtar a tsakar gidan ba ƙaramin farin ciki tayi ba. Da zafi zafi ake bugun ƙarfe, gara tun yanzu tayi amfani da maganin tunda sharaɗin shi ne ta tabbatar mijinta ba ya gida.
Ruwan maganin ta huda ta tsiyaya a hannu ta kurkura bakinta sau uku! Sannan ta wanke fuskarta da ragowar maganin. Ta fuskanci kudu, ta runtse idanunta ta kira sunan Fareeda sau goma sha shida.
Ta gumtse baki tsam ta fita daga ɓangarenta. Kai tsaye gurin Fareeda ta nufa, zuciyarta cike da yaƙinin babu abinda zai hana wannan magani aiki kamar yadda malam mai gani har hanji ya faɗa mata. Duk yadda Ramlah tai ta kururuta mata shaharar malamin bata wani yarda ba sai da suka je ta gani ma idanunta. Irin manyan matan da tags suna mishi layi yasa taji a ranta lallai ta zo inda za’a share mata hawaye. Nan take ta watsar da duk wani ɗari-ɗari da tsoron me zai je ya dawo ta miƙa ma Malam imani da yardarta ɗari bisa ɗari.
Tana kama hannun ƙofar Fareeda ta murɗa kofar ta buɗe, da saurin gaske ta cusa kai cikin falon tana zare-zare idanu.
Fareeda na zaune akan kujera tana ɗaye gam ɗin da tayi ƙunshin gargajiya a yatsunta sai murɗa ƙofarta ta jiyo, ko kafin ta ce komai sai ganin Fatima tayi tsaye a kanta tana ƙare mata kallo.
Ƙirjinta ne ya buga dam!!! da sauri ta runtse idanu tayi addu’o’i. Cikin ƙarfin hali ta buɗe baki daƙyar ta ce
“Lafiya za ki shigo min ɗaki…”
“Fareeda tashi yanzunnan ki fita a haukace tuburan ki bar min mijinki Mukhtar har abada.!!!”
Fatima ta faɗa da ƙarfi sosai kamar yadda Malam mai gani har hanji ya kwatanta mata.
A karo na biyu ƙirjin Fareeda ya buga daram!! A zabure ta miƙe tsaye tana jin yadda kanta ya fara wani irin juyawa, ta fara ganin komai bibiyu.
“Inna… lillahi… wa.. inna.. ilaihi… raji’un…”
Ta finciko da ƙyar daga can ƙasan maƙoshinta, wani ƙaƙƙarfan jiri ne ya rufe mata idanu. Ta tafi yuuuuu za ta faɗi ƙasa da gudun gaske Mukhtar da ya fito daga cikin ɗaki ya tare ta.
Abinda Fatima bata sani ba shi ne. Tunda Mukhtar ya hangeta a kan titi tsakiyar maza tana kumfan baki hankalinsa ya gaza kwanciya. Daman ba wannan ne karo na farko da take ce mishi za ta unguwa sai ya hangeta a inda bai taɓa zato ba. Na yau ne dai ya fi bashi haushi. Wankin mota ciki da waje suka kai shi da Idriss, motarsa bata bushe da zai iya hawa ya tuƙa zuwa gida ba, ga shi kanshi ya fara ciwo yana buƙatar kwanciya. Kawai sai ya hau napep zuwa gida bayan sunyi sallama da Idrees ya ce da yamma zai je ya ɗauki motarsa.
“Ddddddddddama kkkkkkkkkana ggggggggidah?”
Fatima ta tambayeshi bakinta na rawa, hankalinta a bala’in tashe. Tana nuna shi da yatsarta manuniya.
Matuƙar kika yi kuskuren aikata abinda aka umarceki a kunnen mijinki duk abinda kike taƙama da shi a aurenku zai zo ƙarshe.
Maganar Malam ya faɗo mata arai.
“Na shiga uku!”
Ta faɗa da ƙarfi a tsorace tare da ɗora hannunta biyu akai, sai kuma ta fashe da ihun kuka ta fara ja da baya da baya, jikinta babu inda baya rawa kamar wacce ake kaɗawa ganga. A haukace ta juya za ta fice da saurin gaske Mukhtar ya ce,
“Fatima, na sake ki, saki uku!”
Cak ta tsaya guri ɗaya kamar wacce aka yi ma umarni. Lokaci ɗaya mararta yayi wani irin murɗawa mai ƙarfin gaske, kafin ƙiftawa da bismillah jini a guje ya fara gangarowa ta ƙasan ƙafafunta.
Ganin jinin da ke zuba yasa ta ƙwallah wani gigitaccen ihu. Hankali a bala’in tashe ta tallabe mararta da hannu biyu.
“Gudajin jininmu Mukhtar!!! Ka gani, za kasa muyi asararsu. Na rantse da Allah baka isa ka sake ni ba. Idan ka isa shegiya nake. Ni da kai mutu ka raba don ubanka!”
Tayi maganganun a ruɗe cikin ficewar hayyaci.
Mukhtar ko kallonta baiyi ba. Yana tallabe da kan Fareeda da ko kaɗan ba ta a hayyacinta, hankalinsa a ɗugunzume yana tofa mata duk addu’ar da tazo bakinta.
Fatima a ruɗe ta fice da sassarfa zuwa ɓangarenta, kamar idan ta je can ɗin tana da wani abinyi. Hannayenta duk biyu dafe da mararta tana rusa ihun kuka, kai tsaye banɗaki ta wuce. Bata damu da yadda duk ta ɓata tile ɗin falo zuwa cikin ɗakinta ba. Kamfai ta cire ta durƙusa a tsakiyar bayin don ƙara tabbatar ma da kanta wai jinin nan daga ƙasanta yake fita? Ai kuwa kamar jiran ta tsuguna ake yi nan take guda-guda ya fara biyo bayan jinin da yake bin ƙafafunta. Ga mararta da ya ƙara riƙe mata da bala’in ciwo kamar za ta mutu, sai ihu take ƙwallawa gwanin ban tausayi.
“Fareeda kin ci nasara a kaina, Allah ya isa tsakanina da ke!!! Ramlah shegiya gantalalliya, Allah ya tsine miki albarka. Mukhtar mugu macuci azzalumi, Allah yai fata-fata da namanka!”
Bayan gama faɗin maganganun zaman ƴan bori tayi akan gudajin jinin, ta ɗauke wuta ɗif!
******
Bayan wata biyar abubuwa da dama sun faru, Masu daɗi da akasin haka. Ga Mukhtar da Fareeda dai abubuwa masu daɗi sun fi yawa. Yanzu hankalinsu a kwance yake sosai har ma fiye da farkon aurensu, wata iriyar zama ce suke yi ta ƙauna, soyayya, tarairaya. Har rige-rige suke wajen faranta ma junansu rai. Suna rainon cikinsu da yai wani irin bala’in girma, a wasu lokutan ma idan ta zauna sai an taimaka mata gurin tashi, duk kuma yadda cikin yayi girma sun ƙi yarda a faɗa musu ƴaƴa nawa ne a cikin, sun ce idan Allah ya sauketa za su gani, abu ɗaya da likita ya tabbatar ma da Mukhtar shi ne ba ɗa ɗaya bane a cikin. Ko kaɗan Fareeda ba ta sha’awar mai aiki, duk yadda Hajiyarmu tayi ta nacin Fareeda ta koma gidanta da zama tunda cikin ya tsufa Mukhtar zillewa yayi ta yi, a ƙarshe dai ƙanwar Hajiyarmu wacce mijinta ya daɗe da rasuwa ke zaune da ita.
Yau tunda ta tashi da asubah Mukhtar yana lura da yanayinta, sai cije baki take yi tana yamutsa fuska. Ƙafarta ɗaya ya riƙe ƙam, tayi ta motsa ta kasa, sai shi ne ya taimaka mata daƙyar suka isa bayi, a tsaye tayi fitsari saboda yadda cikin ya takure ya cure waje ɗaya ta ƙasan mararta.
“Ammatana, ko dai in yima Inna Halima magana mu tafi asibiti…?”
Wata ƙaƙƙarfan damƙa tayi ma kafaɗunsa sanadiyyar wata masokiya da ta taso daga ƙasan mararta ta cake ta a gadon bayanta.
“Abee, kamar kashi nake ji, kama ni in gani ko zan iya in hau masai.”
Ta faɗa daƙyar tana runtse idanu tana buɗewa, ta haɗa zufa tayi kashirɓin.
Har zai taimaka mata ta hau ta zauna tayi kashin sai kuma tunanin kar a haifa mishi ƴaƴa a cikin masai ya faɗo mishi arai.
“Kiyi haƙuri Babyna, sannu! Kila fa haihuwar ce, kin ga muje ɗaki ki zauna, idan ma kashin ne kiyi a ɗakin sai in gyara gurin.”
Ya faɗa bakinsa na rawa.
Da ƙyar, da dabara, da salati da sallallami ya iya taimaka mata daƙyar suka koma cikin ɗaki. Zanin jikinta tuni yayi nasa gurin, daga ita sai rigar barci doguwa har gwuiwa, a dabarance tana wash-wash ya zaunar da ita akan kafet ɗin da yake bakin gado.
Jikinsa na rawa ya fice kiran Inna Halima, suna sawo kai cikin ɗakin kukan jariri na musu maraba. Har suna bangaje kafaɗun juna saboda rige-rigen su shiga ɗakin.
Naƙuda ce ta taho ma Fareeda gaba ɗaya da zafi-zafinta. Ko da yaro namiji ya faɗo wani azababben ciwon ne ya sake turnuƙeta. Idan tayi salati, tayi nishi sai ta kama maimaita ayar Summas sabeela yassara. Minti uku tsakanin faɗowar Hassan duniya Usaina ta biyo baya da kukanta inyaaaa inyaaaa fiye da na ɗan’uwanta. Nan take mahaifa ta faɗo. Fareeda sai aka koma sauke numfashi a hankali saboda yadda take jin ta sakayau, kamar an zare mata ƙaya a maƙoshi.
Inna Halima hawaye Mukhtar hawaye. Sun jera mata sannu ya fi baki dubu. Sai hamdala suke yi suna kirari ga mahaliccin sammai da ƙassai. Jiki na rawa ta fara ƙoƙarin yanke cibiyar ƴaƴan Mukhtar yana taimaka mata da miƙo min wannan miƙo min wancan. Cikin awa ɗaya da rabi ƴaƴan da uwar sun fito shar da su, Mukhtar ya kwashe su a mota zuwa asibiti don ƙara duba lafiyar jikinsu.
*****
A guje Jiddah ta faɗa cikin ɗakin tana numfarfashi, ƙiris ya rage ta taka ƙafar Fatima da sauri ta janye tana galla mata harara. Ba tare da damuwa da hararar Fatima ba ta mayar da idanunta kan Innarsu ta ce.
“Innah, kin ji Aunty Fareeda ta haifi ƴan biyu mace da namiji?”
“Da gaske? Alhamdulillahi Ma sha Allah!”
Inna ta faɗa cikin matsanancin farin cikin da ya gaza ɓoyuwa kan fuskarta.
“Wallahi da gaske, yanzunnan ta kira ni a waya. Wai don Allah in faɗa miki, kuma wai in baki haƙuri yau kwana uku da haihuwar bata sanar da ke da wuri ba. Kuma ta ce inje gidan Aunty Binto anjima in karɓo mana ankon suna turmi uku, ni ɗaya, salma ɗaya, ke ɗaya…”
“Har turmi uku Jiddah? Nawa suke? Allah yasa dai babu tsada?”
Innah ta tambaya da tunanin kuɗin atamfofin a wannan yanayi da ake ciki na rashin kuɗi.
Da karaɗin murna Jiddah ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta amsa ma Innar
“A kyauta fa ta bamu Innah, ta ce dai saura ni da Salma muƙi zuwa gurin taron suna za ta gamu da mu.”
“Allah sarki Aunty Fareeda. Baiwar Allah mutumiyar kirki, Allah ya saka da alkhairi.”
Salma ta faɗa da yanayinta na sanyin hali, fuskarta cike da murmushi.
Kyawawan addu’o’i na shi albarka, Allah ya raya zuri’a, Allah yasa a gama lafiya Inna ke ta jerowa ga Fareeda kawai sai ji suka yi Fatima ta ƙwalla ihun kuka, hannayenta biyu doɗe da kunnuwanta tana harba ƙafafu a ƙasa kamar ƙaramar yarinya. A Zuciyarta take ta tsine ma Mukhtar da Fareeda.
Da mamaki ƙannen da uwar ke kallonta. Tunawa da abinda take ma wannan borin yasa ƙannen kwashewa da dariya suka tafa hannayensu, ita kuwa Inna ficewa tayi daga ɗakin ta kama harkokinta, a zuciyarta take addu’ar shiriya ga Fatimar.
*****
Da gaske dai Mukhtar ya canza. Bayan ɗinkuna kala uku masu tsada da yayi ma Fareeda na fitar suna, bayan akwatuna uku da ya shaƙo da siyayyar kayan babys, bayan manya-manyan raguna guda huɗu da ya siya na raɗin suna. Naira dubu ɗari biyu ya tura ma Kamfanin Hds jawelleries and more ya ce a haɗo mishi zannuwan da zai sa ma Fareeda a kayan goyo. Ya kuma gargaɗi Sister Hadiza 08144965394 kar a kuskura a saka mishi zanen ƙasa da dubu ashirin.
A bayan siyayyar da Mukhtar yayi mata ita ma Fareeda bata tsaya sanya ba wajen fitar da kuɗi a ribar da ake tura mata na kiwon kaji ta ce Aunty Hadiza ta fitar musu da zani mai matsakaicin kuɗi na anko.
Kasancewar duk kaya a gurin Hds jawelleries and more 08144965394 kan farashin sari suka fi bayar da shi sai ga kwaɗeɗiyar zani an fitar mata da shi na anko. Ko da ta ce zanin yayi nan take aka buga lissafi Aunty Binto ta ƙara akan kuɗin da Fareeda ta bayar suka siyo zannuwan da yawa. Da yake Fareeda ta mutane ce kwana biyar da haihuwa zannuwan sun ƙare tas har ana nema.
Fareedan Mukhtar fatan ayi taron suna lafiya a tashi lafiya
Alhamdulillahi Alaaa kulli halin!! Anan na kawo ƙarshen labarin RABON AYI. Idan kuna ƙaunata ni Fareeda Abdallah kuma kuna ƙaunar rubutuna cikakkiyar ƙaunar da za ku nuna min shi ne kuyi Reg da bakandamiya Hikaya kuyi sub na 500 ku karanta labarina mai taken LOKACI. Idan baku iya Bakandamiyar ba ku tuntuɓeni zan koya muku yadda ake yi, biyo ni a tafiyar labarin LOKACI shi zai tabbatar min da lallai ana tare.
Godiya ta musamman ga duk waɗanda suka bi ni wajen karatun labarin RABON AYI. Na gode, na gode, na gode.Gaisuwar fatan alkhairi, da fatan haɗuwarmu da juna. Waɗanda na ɓatawa rai a labarinnan don Allah su yafe min, fahimta fuska ce kowa da irin tasa, kuma ɗan adam ajizi ne.