Skip to content
Part 5 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Cikin wani irin matsanancin tashin hankali da fargaba ta dira ƙasa daga kan gadon, hannunta na hagu ɗore akai, hannun dama kuma riƙe da wayarta tana bin bayan kiran ƙanwarta, amma sam ya ƙi shiga, amsa ɗaya kwamfuta yake bata, wayar a kashe take.

Sai daga bisani ne tayi tunanin kiran yayansu Mustapha, ta kira shi kuma sau uku wayar tana ringing amma ba’a ɗauka ba.

Hankali tashe ta kira Aunty Murja. A ɗakinsu su Biyar ne, kuma iyayensu sun rasu tun kafin suyi aure, Aunty Binto ce kawai aka aurar da ita kafin rasuwar iyayensu.

Da yake mijin Aunty Binto mai halin dattako ne, shi ya tayata riƙon ƙannenta har zuwa aurar da su. Shi yasa Binta kamar uwa take a gurinsu, ta wahala da su, ba ƙaramin ƙauna da shaƙuwa ke a tsakaninsu ba, da wannan dalilin yasa idan abu ya samu ɗaya ji suke kamar ya samu dukkansu ne.

Hankalinsu bai kwanciya sai an samu maslahar wannan matsalar. Aunty Binto yaran da ta haifa a cikinta biyu ne kacal, wannan cikin shi ne na uku, ta same shi ne a lokacin da ta daɗe da fitar da tsammanin sake haihuwa.

Kuma cikin sai ya zo mata da matsaloli, da farko taita zubar da jini kamar bazai zauna ba, sai kuma Allah yasa cikin ya tsaya bai fita ba, saboda wannan zubar jinin da tai ta yi akai-akai yasa cikin ƙara watanninsa, yanzu cikin yana cikin wata na goma sha uku ne.

Dukkansu cikin zakwaɗin hauhuwar suke, hankalinsu a ƙumba, duk addu’arsu Allah ya sauketa lafiya. Ba’a kwana ɗaya biyu basu kira ta a waya sun ji lafiyarta ba. Ba ƙaramin shiri suke yiwa wannan haihuwa ba, saboda an daɗe ba’a yi ba.

Fatima wacce kakanninsu suke kira da Bintoto ita ce babbansu, sai Aunty Murjanatu, sai Yaya Mustapha, sai Fareeda, da autarsu Masrura.

Irin yadda ta ji muryar Aunty Murja a sanyaye tayi sallama bayan ɗaga wayar shi ne abinda ya ƙara ɗugunzuma hankalinta, a bayan sallamar kuma duk surutu irin na Aunty Murja shiru tayi, bata ce komai ba.

Sai Fareedar ce kiɗime ta ce
“Aunty Murja ya mai jikin? ta haihu kuwa…?”

“Har yanzu dai Fareeda, sai dai mu cigaba da tayata da addu’a, haihuwa ta ƙi zuwa sai uban wahala take sha. Likita ta ce nan da minti arba’in idan bata haihu da kanta ba sai dai ayi mata aiki a cire babyn…”

“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un”
Tayi salatin jikinta na rawa, kasancewarta mai saurin kuka nan take idanunta suka cicciko da hawaye, babu abinda take tunawa a ranta sai yadda tun farkon samun cikin Aunty Binto ta yanke tsammani da rayuwar duniya, gani take kamar sanadiyyar ajalinta take ɗauke da shi.

“Ba komai, mun dogara ga Allah, za ta haihu lafiya in sha Allahu, kina hanyar zuwa ne asibitin ne?”
Murja ta tambayeta.

“Eh! gani nan zuwa yanzu. Allah ya sauketa lafiya.”
Tayi addu’ar da wani irin sanyi a muryarta, lokaci guda hawayen da suke cikin idanunta suka gangaro zuwa kuncinta.

A ɗarare ta nemi gefen kujera ta ɗosana mazaunanta, kamar mai ciwon baya, saboda yadda jiki da hannayenta suke rawa daƙyar ta iya lalubo lambar mijinta ta kira.

Kiran biyu tayi mishi bai ɗaga ba, kafin ta kira na uku sai shi ya biyo bayan nata kiran.
“Paradise”
Ya kirata a tausashe, da ɗaya daga cikin kyawawan sunayen da yake kiranta da su.

Sai da ta ɗan ja shessheƙa sau biyu, sannan a kasalance cikin hawaye ta faɗa mishi abinda yake faruwa.

“Kukan ya isa haka don Allah, kiyi shiru, ki kwantar da hankalinki matata. Kin ji ko? Za ta haihu lafiya in sha Allah. Zan taya ki yi mata addu’a…”

“Hubbyna, don Allah, ka barni in je dubata a asibitin.”
Ta ƙarasa maganar a marairaice.

Daga can ɓangarensa ɗif ya ɗauke wuta, kamar tana ganinsa lokaci ɗaya yayi kini-kini da fuska.
“Idan kin je me za kiyi mata a daidai wannan gaɓar da take ciki?”
Ya tambayeta da cusasshiyar murya.

“Duk su Aunty Murja fa suna can, har da Ya Mustapha, ni kaɗai ce ba na nan. Don Allah ka bar ni in je ko fargaba da tashin hankalin da nake ciki zai ragu…”

“Look Fareeda, a daidai wannan lokacin addu’arku ita tafi buƙata. Kuma ko daga ina za ki iya yi mata ya iske ta, su ma su Mustapha suna can ne kawai ba don za su iya sakawa ko hanawa ba. Don haka kiyi haƙuri, babu inda za ki je ayau, idan ta haihu lafiya na yarje miki gobe da misalin 11am ki shirya kije ki duba ta a gida ko asibiti. Faƙat!!!”
Ƙit ya katse wayar, ba tare da ya jira ko za ta sake cewa wani abu ba.

A kiɗime ta ɗaga idanunta ta kalli agogon falon, ƙarfe sha ɗaya da minti hamsin na safe.

Idan ta tuna ya hanata fita, kuma Aunty Binto da take matsayin uwa a gare su ita ce kwance a gadon asibiti, ƙafarta ɗaya a duniya ɗaya a lahira, amma mijinta ya hanata fita. Ƴan’uwanta duk suna can, ita kaɗai ce anan, tana zaune ba tare da sanin halinda ƴar’uwarta take ciki ba.

Kawai sai ta ɗora hannu biyu akai ta fashe da wani balaƴaƴƴen ƙaƙƙarfar kuka, a daidai lokacin kiran Ya Mustapha ya shigo wayarta, sai tayi cilli da wayar kan kujera ta cigaba da rusa ihu, hannu biyu akai, sai bubbuga ƙafafu a ƙasa take yi kamar ƙaramar yarinya.

“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! Me zan gani haka ni Fatee? Fareeda lafiya? Wa ya rasu?”
Fatima da shigarta gidan kenan ta tarar da ita cikin wannan mawuyacin halin ta jero mata tambayoyin fuskarta na bayyana matsanancin tashin hankali.

A irin yadda ta tarar da ita ta sa a ranta kawai rasuwa aka yi, rasuwar ma irin mai matuƙar muhimmancin nan.

Sai da ƙyar ta samu ta rarrashi Fareeda tayi shiru sannan ta sanar da ita abinda yake faruwa, kafin ta ce komai kicin ɗinta ta wuce ta buɗe frig ta ɗauko gorar ruwa mai matsakaicin sanyi da kofi, falon ta koma ta tsiyayi ruwan ta kafa mata kofin a baki.

Ba ta da zaɓin da ya wuce shan ruwan, sai sauke ajiyar zuciya take yi a jejjere irin na wacce ta daɗe tana kuka.

A gefenta Fatima ta zauna, cikin rashin damuwa ta fara cewa
“Ke kam Fareeda na ga ranar da za kiyi wayau. In banda rashin wayau irin naki ai da bari kikai sai kin isa asibitin sannan ki kira Mukhtar ki faɗa mishi abinda yake faruwa. Kinga a lokacin kin riga kin fice, ko ya ce ki dawo gida kin dai riga kin gano halin da ƴar’uwarki take ciki. Amma ni a ganina ko yanzu bai ɓaci ba, ba kin ce yau ya koma gurin aikinsa ba?”

A kasalance ta ɗaga kai, alamar eh!

“To ga shawara, amma fa idan kina so, kuma idan kin ga dama…”

“Wace shawara ce ƙawata?”
Ta tambayeta cikin zakwaɗi, da tunanin za ta sama mata mafita cikin sauƙi kamar yadda ta saba samar mata a baya.

“Ba kin ce yau Mukhtar ya koma gurin aiki ba?”

“Eh! Ɗazu da safe.”
Ta sake amsawa a ƙagauce.

Fari da idanu Fatiman tayi, ta buɗe jakar hannunta ta ɗauki cingam guda ɗaya ta ɓare ta jefa a baki, ta yasar da ledar nan tsakar falon cikin rashin damuwa.

Hannunta da ta yar mata da ledar cingam a tsakar falonta da yake gyare tsaf ta bi da kallo, sannan ta kalli ledar cingam ɗin, ta cuna baki gaba, idan akwai abinda ke yawan shiga tsakaninta da ƙawartata ƙazanta ne, ba ta kiyaye inda ya kamata ta yasar da datti.

Ƙoƙarin danne ɓacin ran da yake yunƙurin taso mata take yi, ta haɗiye miyau sau biyu a jere.
“Kin fara magana kuma kin yi shiru.”
Tayi maganar tana kallon yadda take tauna cingam ɗin cakal cakal babu aji ko misƙala zarrah, kamar ba ɗiya mace ba.

“Hajiyata ai kawai ki fice abinki, maganin dai tsinuwar mala’iku kina tafe kiyi ta istigfari. Aunty Binto ta fi ƙarfin komai a gurinku, ba ma kamar ke, ki tuna yadda duk cikinku ta fi shaƙuwa da ke da fifitaki? sau nawa tana ba ki abu ba tare da ta ba sauran ba? Dubiyar mare lafiya za ki je da sadar da zumunci, Allah ma bazai kama ki da laifi ba. Amma fa kar ki daɗe, kiyi sauri ki dawo ɗakinki.”

Shiru tayi cikin tunani, a yanayin da take ciki Allah ya sani hankalinta ya fi karkata kan tafiya a bisa zaman. Ta san zance ne kawai na Fatima da ta ce maganin tsinuwar mala’iku istigfari, amma dai ko ba yau ba za ta roƙi mijinta ya yafe mata. Ta san in sha Allahu har za ta fita ta dawo ba tare da ya sani ba, tunda yau ya koma gurin aiki, babu yadda za ayi ya dawo balle har yasan ta fita, za ta je ta dawo lafiya ba tare da ya sani ba, idan ya dawo ko cikin hira ne za ta roƙi ya yafe mata ba tare da ta faɗa masa laifin da tayi ba…

Tana wannan tunanin Fatima ta katse ta da cewa
“Kin ga ni fa daman kasuwa zan tafi siyayya na ce bari in leƙo mu gaisa ko kina da saƙo? kin tuna kuɗinnan da Baban Jiddah ya bamu? ko za ki sayi wani abu a kasuwa? ni kam wata haɗaɗɗiyar doguwar riga na gani a jikin Nabila, irinta zan siyo.”

“Taɓ! Ai ni babu abinda zan siya. Kina ganin hidimar kuɗi ya taho min, zagewa zanyi inyi ma Aunty Binto hidima ta bajinta, Allah dai ya sauketa lafiya.”

“Ameen ya Allah”

Da haka suka yi sallama, Fatima ta fice daga gidan, ita kuma ta fara shirya tafiya duba ƴar’uwarta a gaggauce, ta rasa dalilin da yasa ƙirjinta ke yawan bugawa akai-akai, amma wannan fita ta riga ta yi niyya, babu abinda zai hana ta zuwa.

Tana kulle ƙofar falonta kiran Mukhtar ya shigo wayarta, ƙirjinta ne ya sake wani ƙaƙƙarfan bugun da yasa ta tsuguna a ƙasa tana jan inna lillahi, daƙyar ta iya daidaita kanta sannan ta ɗaga wayar, da cusasshiyar murya mai bayyana matsananciyar damuwa.

“Matata? ya Auntyn tamu da jiki? kin samu labarin ta haihu kuwa? na kira Mustapha in ji ya mai jikin amma bai daga ba.”

“Da sauƙi dai, har yanzu basu kira ni ta haihu ko aikin za’a shiga da ita ba.”
Ta jera mishi maganganun a hankali, ƙirjinta na cigaba da bugawa.

“Za ta haihu lafiya da yaddar Allah. Ki kwantar da hankalinki kin ji ko?”
Yayi maganar da kulawa.

“Tam! Allah yasa.”

“Kiyi haƙuri Baby, na san kina jin babu daɗi na hana ki zuwa, idan kin duba ko kin je ba abinda za ki iya yi. Ki cigaba da yi mata addu’a daga gida kin ji?”

‘Hmmm! Dole ka ce haka tunda ba ƴar’uwarka bace.’
Ta faɗi hakan a zuci, a fili kuma sai ta ce.
“Ba komai, na gode mijina. Allah ya huta gajiyar tafiya.’

“Ameen”

A zahirin gaskiya da wannan wayar da suka yi jikinta yayi sanyi da fitar, kamar ta haƙura ta zauna, amma shaiɗan ya cigaba da azalzala mata kan ta fita. Yana ƙara tunasar da ita muhimmancin yayarta a gare ta. Da saƙa mata wasu tunanika na banza da wofi.
‘Ba fata take yi ba, yanzu idan Auntyn ta rasu fa? shi kenan duk ƴan’uwanta sun gana da ita itace basu haɗu ba? saboda wani umarni na namiji da ba shi da tabbas? mijin da za ta iya canza shi amma baza ta iya canza ƴar’uwarta ba’

Kawai sai ta miƙe tsaye, ta kalli jikinta, ɗinkin doguwar rigar atamfa ce, ta yafo babban gyale a kai. Sai ta buɗe ƙofar falon ta shiga cikin ɗakinta ta aje gyalen akan gado ta ɗauki hijabi ta saka. Da sassarfa ta fice daga gidan bayan ta kulle ko ina.

******

“Langes, hanga ta arewacin gabar kaga wata fatsa da take tahowa, idan ba gizo idanuna suke min ba sai naga kamar rangaji take tamkar reshen bishiya a cikin iskar damina.”

Da jajayen idanunsa ya waiga zuwa inda abokin nasa yake magana, sai yayi arba da ita, duk da hijabi ne sanye a jikinta bai ɓoye asirin ƙirar jikinta ba, hijabin ya kwanta a jikinta, ƙirjinta ya taso sosai ta gaban hijabin, duk da tashin hankalin da take ciki ba bazar-bazar take tafiya ba, a nutse take tafiya, ga wanda bai santa ba zai iya cewa yanga take yi, amma a zahirin gaskiya haka yanayin tafiyarta yake.

“Kai, gaskiya ni fa na fola, miyau na ya tsinke. Ya kamata in mayar da kwaɗayina ta hanyar ɗanɗanawa…”

“Kai fa Villa ɗan iska ne, ba ka da mutunci, don Allah ka ƙyaleta ta tafi…”

Ko kafin abokin nasa ya rufe baki har ya fita daga cikin napep ɗin ya nufi gurinta.
“Hajiya ya? tafiya ne?”

Manyan idanunta ta ɗaga ta kalleshi a kaikaice, sai tayi arba da napep ɗin da yake fake a can bayanshi.
“Eh! shatar napep nake nema zuwa asibitin garkuwa.”

Saukar tattausan muryarta a kunnuwansa yasa shi lumshe idanu kamar tsohon kwarto, ya haɗiye tsinkakken miyan bakinshi, ya fara magana da yanayi mai baiyana farin cikin da zuciyarsa take ciki.
“Hajiya kiyi murna kakarki ta yanke saƙa, zo muje kawai.”
Yayi maganar yana wani irin dariya da ta rasa gane inda ya dosa.

“Nawa zan baka?”

“Haba kar ki damu Hajiya, bazai gagareki ba in Allah ya yarda.”
Ya juya ya nufi napep ɗin tana biye da shi a baya, signal yayi ma abokin nasa da yake zaune a bayan napep ɗin da sauri ya fice ya koma gaba, bayan ya kakkaɓe mata kujerar bayan.

Ba tare da tunani ko fargabar komai ba tayi basmala ta shiga ta zauna, tana ƙara rungume jakarta a jikinta.

“Hajiya kiyi haƙuri, abokina zai ɗan raɓe nan kusa da ni zan sauke shi can babban titi…”

“Ba damuwa.”
Ta amsa idanunta na kallon waje, zuciyarta cike da tunanin yanzu ko a wane hali yayarta take?

<< Rabon A Yi 4Rabon A Yi 6 >>

1 thought on “Rabon A Yi 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×