Ƙaƙƙarfan tsaki ta ja, ta gallawa wayar harara kamar shi ne Habeebi da’iman ɗin da ya katse wayar ba tare da ya ƙarasa jin bayanin halin da budurwarsa take ciki ba. Don ita duk a tsammaninta Fareeda budurwa ce.Tana niyyar mayar da wayar cikin jaka wani kiran ya sake shigowa, ta zaci na farko ne ya sake kira, sai taga saɓanin wancan sunan, wannan an rubuta ‘Luvly Bro’ ne da manyan baƙaƙe.Ko da ta ɗauki wayar bata tsaya sauraren wani rainin hankali irinna wancan ba, bayan hello kai tsaye ta cigaba da cewa
“Mai wannan wayar fa ga ta nan kwance a gadon asibiti ta samu hatsari…””Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”
Ya Mustapha ya katseta cikin tashin hankali.”Ɗan’uwa lafiya? ina Fareedar?”
Aunty Murja da Masrura suka haɗa baki gurin tambayarsa, a hankali yanayin farin cikin haihuwar ɗa namiji da Aunty Binto tayi ba tare da an tsaga ta ba ya ɓace daga fuskokinsu.Tsuru suka yi suna sauraren Mustapha da yake ɗan safa da marwa hankali tashe da waya a kunnensa, yana sauraren Baby Mardy da take mishi kwatancen ɗakin da aka kwantar da su a asibitin Barau dikko.”Ok! Na gane, ganinan zuwa yanzu.”
Maganar da yayi na ƙarshe kenan tare da katse wayar. Shaf ya ma manta tsaye suke da ƴan’uwansa saboda tashin hankali, har ya kama hanyar wucewa daga gurin da sauri Murjanatu ta riƙo hannunsa na dama, sai a lokacin ya tuna tare da su yake tsaye.Duk da kasancewarta mai ƙwarin zuciya har idanunta sun canza kala, ƙwalla ya cicciko daga cikinsu. Daga yadda ya amsa wayar duk sun fahimci wani mummunan abu ne yake faruwa da Fareeda, ƙanwarsu abar son zuciyarsu, yarinya mai bala’in faram-faram da gudun ɓacin ran kowa a cikinsu. Ita kuwa Masrura kasancewarta ƙarama kuma mai rauni har ta fara hawaye.”Ɗan’uwa ina kake shirin zuwa? Me ya samu Fareeda?”
Ta tambayeshi da sanyin murya, idanunta ciccike da hawaye.Hannunsa na hagu ya ɗaga ya ɗan bugi goshinsa, ya ɗan tattare naman goshin ya huro wani zazzafan iska daga bakinsa. Murmushin yaƙe yayi, don ya ƙarfafa musu gwuiwa.
“Fareeda ta ɗan samu hatsari ne a napep a hanyarta zuwa nan, mai keken ya gudu, wata baiwar Allah ce ta taimaka mata. Amma dai ta tabbatar min da sauƙi sosai, shi ne zanje in ga halin da take ciki…””Ka je ko mu je? Ai sai mu tafi gaba ɗaya kawai.”
Murjanatu ta katse shi da faɗin haka tana gyara zaman mayafinta.”Idan muka tafi can gaba ɗaya ita kuma Aunty a barta da wa? Ke kiyi haƙuri ki zauna, ni bari inje da Masrura mu duba halin da take ciki. Tunda Alhaji Baba ya je tahowa da Hajiya da su Aunty Balaraba idan sun ƙaraso sai ke ma kije ki gano halin da take ciki.””To shi kenan. Don Allah duk yadda kuka tarar da ita mu dinga waya, duk da mun fita daga fargabar Aunty Binto hankalina bazai kwanta ba idan ban san halin da ƴar ƙanwata take ciki ba.”
Ta ƙarasa maganar fuskarta a dame.******Yadda suka tarar da fuskarta a suntume kamar mai keken ta kai ya dinga sukuwa da tayoyinsa ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba. Jiki a sanyaye suka zauna kan kujerun da Mardy ta miƙa musu.Masrura kam rufe fuska da hijabi tayi tana jan shessheƙar kuka, yau dai kam sun gode Allah. Tashin hankali daga wannan sai wannan, sun samu fita daga fargaba da ƙila wa ƙala kan Auntynsu yanzu ga kuma abinda ya samu Fareeda.
Da wanne za su ji?Mustapha ma duk da yake namiji duƙar da kanshi ƙasa yayi, wani dunƙulallen abu ya tsaya mishi a maƙoshi, shi bai sauka ciki ba shi bai fito waje ba. Ina ma shi ne yake kuka kamar ƙanwarsa ko zai samu sauƙin zafi da raɗaɗin zuciyarsa?Sau takwas yana ɗaga idanu ya kalli Mardy, ya kasa buɗe baki yayi mata godiyar irin taimakon da tayi ma gudan jininsu saboda tsananin damuwa da tashin hankali.Sai ita Mardiyyar ce ta karya shirun da cewa
“To tunda Allah ya kawo ku ƴan’uwanta ni kam na yi abinda zan iya, tafiya zanyi. Sai ku ɗora daga inda na tsaya, duk wani abu da baku gane ba idan likita ya shigo zaiyi muku ƙarin bayani. Allah ya kyauta gaba, ga jakarta da wayarta nan. Idan na samu sarari ko zuwa jibi zan zagayo in duba jikinta.””Mun gode, Allah ya saka da alkhairi.”
Masrura ta faɗi haka da ƙyar, tana jan shessheƙa.A gefen gadon da Fareeda take kwance ta ajiye jakar da wayar, ta nufi hanyar fita daga ɗakin hannunta riƙe da wayarta tana kiran Langes, amma yana ta ringing bai ɗauka ba. Bata san Mustapha yana biye da ita a baya ba sai da ta kusan fita daga asibitin, kamar daga sama ta ji muryarsa a tausashe yana cewa”Muna godiya ƙwarai da taimakon ƴar’uwarmu da kika yi, ina roƙon Allah ya saka miki da mafificin alkhairi.””Ah ba komai Luvly Bro”
Ta ƙarasa kiranshi da sunan da Fareeda tayi saving tana wani dariya irinna gogaggun ƴan duniya.Ba a wannan layin yake ba, kuma don taimakon da tayi ma ƙanwarsa bai isa ya sa shi sakar mata fuska ba, ba ma shi a cikin yanayin fara’a da sauƙin zuciya. Fuskarnan a ɗinke ya zura hannunsa a aljihu ya zaro dubu biyar ya miƙa mata da cewar ta hau keke. Ya ƙara yi mata godiya.Ganin ba fuskar latsawa a dole ta kama kanta, ta kalli kuɗin ta kalle shi, wani irin kwarjini yayi mata sosai har ta ji baza ta iya mayar da hannun kyautarsa baya ba. Amma in banda haka mecece dubu biyar a gurinta?Kawar da kanta tayi tana ɗan taɓe baki, sai ta karɓi kuɗin tayi mishi godiya a taƙaice da harshen nasara.
“Thanks”Bai jira ko za ta ƙara cewa wani abu ba ya juya cikin asibitin da sassarfa. Ita kuwa ba ta da zaɓin da ya wuce bin bayansa da kallo har ya ɓace ma ganinta, ta ja tsaki ƙasa ƙasa ta cigaba da tafiya.Ko da ya koma ɗakin ya tarar Fareeda ta farka, Masrura ta kira likitan da yake aiki a wannan lokacin yana ƙara duba jikinta.Wani abin da ya ɗaure musu kai kuma ya ƙara ɗaga musu hankali shi ne, ganin yadda wasu siraran hawaye ke fita daga kwarmin idanunta yana gangarawa cikin kunnuwanta.Likitan na fita da sauri suka rufu a kanta, cikin kulawa da ƙauna suka rirriƙe hannayenta ɗai ɗai a cikin nasu suna tambayarta me ke mata ciwo? kukan me take yi? ko akwai inda ta bugu a cikin jikinta ne ba’a sani ba. Kamar suna yi da kurma ko dutse, uffan bata ce musu ba, bata kuma buɗe idanu ta kalle su ba. Wani irin zafi da raɗaɗi ne zuciyarta ke yi, idan ta buɗe kumburarren bakinta da nufin yin magana babu ko shakka ƙaƙƙarfan kuka ne zai ƙwace mata, sai kawai ta cigaba da sharɓen hawaye.Waigawa hagu da dama Mustapha yayi ko zai ga tissue yayi amfani da shi gurin share mata hawaye, da bai samu ba sai kawai ya tattare ƙasan rigar shaddar jikinsa ya cukwuikwuiye ya nufi idanunta da niyyar goge hawayen da har lokacin basu daina fita ba. Lura da abinda yake shirin yi ga shaddar tasa mai ruwan madara da sauri Masrura ta dakatar da shi.Ɗankwalin kanta ta ciro ta miƙa mishi, a hankali da fuska mai cike da tausayi yake ƙare mata kallo yana goge hawayen da har ɗan taruwa suka yi ta cikin kunnenta. zuciyarsa cike da mamakin shatin yatsun da yake gani ɓaro-ɓaro kwance a kumatukanta.
‘To ko dai bayan hatsarin mai keken ya mammareta ne?’
Ya tambayi zuciyarsa.
‘Ko shakka babu waɗannan shatin yatsun na mari ne.’
Ya buɗe baki zaiyi magana sai ya ji Masrura tana cewa.”Aunty Faree, wai kukan na menene haka don Allah? na zaci murna da godiya ga Allah ya kamata kiyi tunda kin farfaɗo cikin hankalinki? Don Allah kiyi shiru, ki daina kuka, kin san kuwa Aunty Binto ta haifo baby boy ƙato ba tare da anyi mata aiki ba…?”Da farko damƙe hannayensu biyun tayi da ƙarfi jin maganganun Masrura da yake sauka a nutse cikin kunnuwanta. Amma da ta ji kalmar ƙarshe ai bata san lokacin da ta buɗe jajayen idanunta ta zuba akan su biyun ba.Da ƙyar ta iya buɗe kumburarren bakinta da yayi mata wani irin nauyi kaman an ɗora mata dutse ta ce,
“Da gaske? ta haihu?””Wallahi da gaske”
Mustapha ya amsa fuskarsa cike fal da murmushi.”Kuma ita da jaririnta duk suna cikin ƙoshin lafiya.”
Masrura ta ƙara da faɗin haka itama fuskarta taf da murmushi.”Alhamdulillah.”
Ta faɗa a hankali, ƙoƙarin yin murmushi take yi amma ta kasa, a maimakon murmushin ya fito sai ta wani irin yanƙwane fuska kamar ƙonanniya, ta ko ina fuskarta zafi yake yi kamar an bubbuga mata duwatsu, a dole ta haƙura da murmushin, tayi shiru tana sauraren yadda ƴan’uwan suke ta bata labarai na farin ciki da ban dariya don dai su ƙara kwantar mata da hankali.Amma a zahirin gaskiya ƙarfin hali kawai suke yi, zukatansu cike yake taf da bala’in tausayinta. Gaba ɗaya halittar fuskarta ya sauya, wanda ya ganta ɗazu sadda ta fito daga gida idan ba farin sani yayi mata ba zai iya rantsewa da girman Allah ba ita ce Fareedar nan ƴar ƙwalisa ba.A ƙoƙarin saka ta farin ciki har Vidio call ta whatsapp suka yi da Aunty Murja da Aunty Binto, tana kallon yadda suke kawar da kai gefe suna share hawaye, amma ita farin cikin ganin ƙatoton jariri kuma fari sol kamar ɗan larabawa da Auntyn ta haifa musu ya kore mata kaso sittin cikin ɗari na damuwa da ƙuncin da zuciyarta ke ciki.Kaso arba’in na damuwarta Mukhtar ne. Duk hirar da take yi da ƴan’uwanta tunaninsa da tunanin girman laifin da ta aikata yana kwance malala can ƙarƙashin zuciyarta.
‘Me za ta ce masa idan ya dawo ranar juma’a ya tarar da ita cikin wannan halin? wani ƙarya za tayi masa ya gamsu ba da gangar ta fita ba? Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! ita kam satar fita bai ƙare ta da komai ba sai bala’i da masifa. Me ya kaita? me yasa bata yi haƙuri ta zauna a gida kamar yadda ya umarce ta ba? Dubi fa yanzu harkar zumunci za ta sadar, bata taɓa tsammanin wani mummunan abu makamancin wannan zai faru da ita ba, sai ga shi in banda tsarewa da taimakon Ubangiji lokacin da bawa bai taɓa tsammani ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba…'”Fareeda, tunanin me kike yi haka? Me yake damunki? Kinga, tun bayan farfaɗowarki na san akwai abinda yake damunki amma kina ƙoƙarin dannewa. Menene shi? Daman akwai ƴar ɓoye-ɓoye ne a tsakaninmu?”
Mustapha ya tambayeta da kulawa a murya da fuskarsa. Tun bayan farkowarta daga irin kukan da take yi yasan akwai abinda yake damunta, akwai abinda ke cin zuciyarta amma tana ƙoƙarin ɓoyewa. Ita saƙonsa ce, akwai shaƙuwa na musamman a tsakaninsa da ita, tana da fahimta sosai, duk wasu matsaloli nasa da zai rakito kafin ya tunkari sauran ƴan’uwansa da maganar ita yake fara tunkara, ta bashi mafita, da kuma sassauƙar hanyar da zai bi wajen bayyana maganar ga yayyensu.”Ya Mustapha, ina da damuwa. Kuyi min addu’a don Allah. Amma ina roƙon alfarma, a halin da nake ciki yanzu ba lokacin yin maganar bane, zan faɗa maka idan Allah yasa na ƙara samun sauƙi.”
Tana gama faɗin haka ta lumshe idanunta, ta cigaba da sauke numfashi a hankali.Duk su biyun idanunsu a kanta yake, kowa da irin saƙar da zuciyarsa take masa, amma dai sun share komai kamar yadda ta buƙata, tabbas! babu adalci su tilasta mata faɗin damuwarta a irin wannan halin da take ciki.*******Ya ɗauki tsawon wasu daƙiƙu yana jan fasali bayan ya amsa gaisuwar da ta gama yi masa cikin karaɗi da rangwaɗa. Kamar zai katse wayarsa, amma sai zuciyarsa ta cigaba da azalzalarsa tana tabbatar masa da cewar shawarar da ya yanke fa shi ne daidai, mafitarsa kenan. Ƙwaƙƙwaran hanya ce mai ɓullewa ya samar ga matsalolin da suka daɗe suna addabar duniyarsa.
“Za ki aure ni?”
Wani sabon suna da ta raɗa mishi yanzu-yanzu saboda zakwaɗi, zuciyarta cike da fatan tabbatuwar abinda ta ji kamar ya ce da farko.”Cewa nayi, za ki aure ni?”
“Eh! Eh!! Ehh!!!”
Ta amsa bakinta na mazari. Wayyo Allah daɗi, tsananin farin ciki da murna ta ma rasa inda za ta tsoma ranta, ta miƙe, ta zauna, ta sake miƙewa, ta zauna, daga bisani sai ta miƙe zumbur ta fara zagaye ɗakin da sassarfa. Bakinnan kamar zai yage saboda dariya, lallai yau larabar tata ce. Da alamun juma’arta za tayi kyau tun daga yau laraba ta zo da haske.”Idan na aure ki, wani irin tanadi kika yi min?”
Ya tambayeta da murya ƙasa-ƙasa, kamar ba Mukhtar ɗinnan da idan tana gaida shi yake amsawa a ciccije ba.”Zan baka farin ciki, zan tsunduma ka a kogin farin ciki, zan shayar da kai wata zallar ɗanyar tatacciyar madarar soyayya mare algus. Za ka samu har fiye da abinda kake burin samu a gurin matar aurenka…”Lumshe idanu yayi yana saurarenta, zuciyarsa cike da gamsuwa, yana ji ko a iya waɗannan alƙawuran da tayi mishi ya samu za su gamsar da shi. Zai ƙyale Fareeda, taje can da yawarta.