Skip to content
Part 9 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Ba tare da ɓata lokaci ko wata damuwa a fuskarsa ba ya shige cikin motarsa. Zuciyarsa cike take taf da farin ciki.

Duk yadda Fareeda tayi jarumta wajen ɓoye tashin hankalin da ta shiga da jin sunan wacce zai aura shi kam ya gani, ai an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Ƙarara ya ga tashin hankalin da zuciyarta take ciki zane ɓaro-ɓaro kan fuskarta.

“Kaɗan ma kika ji kuma kika gani Yarinya.”
Ya faɗa haɗe da yin ƙwafa, babu tausayinta ko kaɗan a zuciyarsa.

Wannan wankan da ya ɗauka daman don Fatima yayi, tsawon sati biyun da suka kwashe suna zuba soyayya ta waya shi kam ɗari bisa ɗari ta yi masa, ya gamsu zai samu abinda yake so.

Irin alƙawurran ladabi, biyayya, gata, kogin so da ƙaunar da take ta ƙara kwaɗaita mishi idan suka yi aure shi kam ya amince ko bata kai haka a tsarin halitta ba zai iya auren ta.

Yo daman me ake biɗa a auren? ba kwanciyar hankali bane? A wannan matakin da yake kai na jin zafin irin ƙunci da baƙin cikin da Fareeda ta daɗe tana ƙunsa mishi ko tsohuwa ce zai iya aurenta matuƙar za ta bi tsarin da yake so, kuma su zauna lafiya ƙalau.

Yana gaf da ficewa daga cikin layinsu sukai clashin da motar Yaa Mustapha, da alamun gidansa suka nufa. Rage gudu Mustapha yayi da niyyar su gaisa, Mukhtar ya kawar da kansa ya ƙara ma motarsa wuta ya wuce a guje, ko fitila baiyi musu ba, kamar ma bai san motar waye ba.

Da mamaki Yaya Mustapha yake hangenshi ta mirrow har ya ɓace ma ganinsa.

“Wai wancan motar da ta wuce ba ta Mukhtar bane?”
Aunty Murja da take zaune gefen mai zaman banza ta tambaya, itama fuskarta na nuna mamaki.

“Shi ne. Ina ga bai ganmu bane.”
Ya amsa yana ƙara gudu don isa gidan. Babban burinsa yayi tozali da ƙanwarsa, Shekaran jiya da ya kirata ta tabbatar mishi har ranar Mukhtar bai zo garin ba.

Yadda ya ganshi yanzu ɗinnan da yadda ya sharesu bayan sun haɗa idanu ya alamta mishi tabbas akwai matsala.

Bayan shigarsu cikin gidan sallama suke ta kwaɗawa a ƙofar falon, amma shiru suke ji. Duk su ukun kuma sun kira wayarta amma babu wanda ta ɗaga.

Cikin ɗan damuwa da ƙila wa ƙalan lafiya ko ba lafiya ba Aunty Murja da ƴar’uwarsu Rahama wacce ta kawo musu ziyara daga Rigacikun suka sa kai cikin falon don duba halin da ake ciki. Shi kuma Yaya Mustapha matsayinsa na namiji ya tsaya a bakin ƙofa hankalinsa a tashe yana jiran su gano halinda Fareeda ke ciki, domin tamanin bisa ɗari na tunaninsa ya tafi kan ba lafiya ba.

“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ke Fareeda? lafiya? me yake faruwa?”
Ya ji muryar su biyun sun faɗa cikin da wani irin karaɗin tashin hankali.

Ko kafin ya banke ƙofar falon ya shiga a sittin zuwa inda suke sai jin muryar Aunty Murja yayi ta fashe da wani irin ƙaƙƙarfan kuka.

Ganin Fareeda kwance shamɓar a ƙasa bayan gyara ta daga sujudar da tayi ba rai babu alamunsa a jikinta yasa shi ya tafi taga-taga zai kife, Allah ya taimake shi hannunsa na hagu ya dafe bango. Cikin ɗaukewar hankali da tunani ya tafi a slow motion ya zauna daɓar a ƙasa ya zuba ma gangar jikinta idanu, na wasu daƙiƙu ƙwaƙwalsa ta tsaya cak daga sadarwar saƙonni.

Rahma, wacce su Fareeda ke kira Baby saboda tsananin gayu da yanga irin nata, ƴar’uwa ce ta kusa sosai a gurinsu. Karatun aikin jinya tayi, duk da tashin hankalin da take ciki na ganin aminiya kuma ƴar’uwarta cikin wannan hali tunaninta bai ɓace kamar nasu ba. A nutse ta dudduba Fareedar sai taga ba rasuwa tayi ba, suma tayi.

Da gaggawa ta nufi kicin, gorar ruwa mai matsakaicin sanyi ta ɗauko ta dawo. A nutse ta zauna ta fara tsiyaya ruwan kaɗan a hannunta tana shafa mata a fuska, ta shafa sau uku a na huɗun Fareeda ta ja wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke.

Da saurin gaske kuma a firgice ta buɗe idanunta, ido biyu da sukai da Baby yasa ta miƙewa zaune a zabure da wani irin ƙarfi a jikinta ta ruƙunƙumeta, lokaci ɗaya kuma ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka mai tafe da saƙon baƙin ciki da takaici tun daga can ƙarƙashin zuciyarta.

Kukan da ta fashe da shi shi ya zama kamar yarfin ruwan ƙanƙara ga Aunty Murja da Yaya Mustapha.

Da murna mai tsanani ganin ta farfaɗo suka matsa kusa da sauri, Aunty Murja ta ruƙunƙume su biyun itama tana nata kukan na farin ciki. Farkowar Fareeda ba mutuwa tayi ba ya kore mata duk wani damuwa da fargaba, a ganinta duk abinda zai biyo baya mai sauƙi ne.

Shi kuwa Yaya Mustapha gefe ya rakuɓe kamar ƙaramin yaro yana ta sassauke ajiyar zuciya a jejjere, zuciyarsa cike da farin ciki, babu abinda yake furtawa da murya ƙasa-ƙasa sai
“Alhamdulillahi alaani’imatihi tatimmussalihat.”

Ganin kukan yana ƙara tsawo ya ƙi ƙarewa yasa Baby ta fara raɗa mata tausasan kalamai a kunnenta.
“Ya isa haka Besty, pls ya isa haka. Ummm?! Ba ga mu ba? ko ma wane al’amarin damuwa ne za mu fuskance shi tare, muna tare da ke, kin ji ko? duba kiga Aunty Murja riƙe da ke, kuka take saboda irin kukan da ta ga kina yi. Kin ga Yaya Musty zaune a gefenki shi ma cikin tashin hankali, kiyi haƙuri kin ji? kiyi ta maimaita Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ko wane bala’i ne in Allah ya yarda zai zo mana da sauƙi kin ji?”

A hankali take ta rage ƙarfin kukanta, har tayi shiru gaba ɗaya, sai sauke ajiyar zuciya irinna wacce ta daɗe tana kuka.

Har wannan lokacin kanta na kwance a kafaɗar Baby. Mustapha da Murja sun matsa kusa da ita suna riƙe da hannayenta a cikin nasu, a fuskokinsu tana kallon matsanancin damuwa da tashin hankali saboda damuwar da take ciki.

“Mukhtar… zai… ƙara aure…”
Tayi maganar a rarrabe.

Su ukun gaba ɗaya buɗe baki sukai cikin tsananin mamaki suna kallonta, ƙara aure a daidai wannan lokacin shi ne abu na ƙarshe da za suyi tunanin Mukhtar zaiyi, ba don komai ba sai don ganin matsananciyar soyayya da shaƙuwar da ke tsakanin masoyan biyu.

Tuna komai lokaci ne kuma muƙaddari daga Allah yasa Mustapha rufe baki a sanyaye. Ya haɗiye wani kakkauran miyau, ya rasa da wace kalami zai fara amfani wajen kwantarwa da ƙanwarsa hankali.

Ya buɗe baki zaiyi magana Fareeda ta katse shi ta hanyar cewa
“Ya tabbatar min da zai ƙara aure, kuma babu wacce zai aura sai ƙawata… Fatima ƙawata… Fatiman Mama Laure.”
Ta ƙarasa maganar da saukar wasu zafafan hawaye a idanunta.

“Kan ubancan kayyasa.”
Baby ta lailayo wani ashar ta maka saboda yadda maganar ta bugi zuciyarta.

Duk su ukun babu wanda bai san Fareeda da Fatima ba, abin mamaki ne ƙwarai da jinjinawa a ce Mukhtar zai auri Fatima ƙawar Fareeda.

“Amma ita Fatiman ta amince?”
Aunty Murja tayi ƙarfin halin tambaya fuskarta na harhaɗewa da wani irin matsanancin ɓacin rai.

“Ƙwarai! Ya tabbatar min ta amince. Kuma daman sati biyu kenan ko na kirata a waya ba ta ɗauka, daga bisani ma sai ta kulle ni na daina samunta…”

Aunty Murja da Baby ne suka haɗa baki gurin cewa
“Kutmelesi…”

“Menene kuke yi haka kamar wasu ƙananun yara? Kun manta babu haramci ko kaɗan a cikin aurensu?”
Mustapha ya katse su da faɗin haka.

“Haba Yaya Mustapha, ai ana barin halas ko don kunya. Sai ka ce muna garin gaɓa-gaɓa(marasa hankali)?”

“Uhmmm! Baby kenan! ke dai kawai Allah ya iya mana. Amma muna cikin wani zamani ne wanda da yawanmu bamu ɗauki cin amana a bakin komai ba.”

Lura da yayi maganganun matan babu abinda suke yi sai ƙara rura wutar kishi da baƙin ciki a zuciyar Fareeda duba da yadda take share hawaye akai-akai. Yasa Mustapha matsawa kusa da ita sosai ya fara rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.

*****

“Wai yanzu ƙawata kina nufin wannan ɗan mitsitsin turaren shi ne zan shafa a goshi na muyi tozali da Aban twince? Ni wlh na raina…”

Da saurin gaske ƙawar ta rufe mata baki, sai zazzaro idanu take yi hankali tashe kamar wacce taji za’ayi saɓon Allah.
“Ki iya bakinki. Na rantse da girman Allah ki iya bakinki. Ba’a tantama ko raba ɗayan biyu a kayan Hajiya Zainab Harka gaskiya da gaskiya. Idan ba haka ba kuwa ina tabbatar miki za kiyi biyu babu, ke ba ga biyan buƙata ba, maƙudan kuɗaɗen da kika kashe basu dawo ba.”

“Hmmm! Allah na tuba. Shi kenan Ramlah. Na gode. Zan gwada sai fatan Allah yasa mu dace.”

“Yauwa ko ke fa Hajiyata. Ai duk abinda zan karɓo miki gurin matarnan ina tabbatar miki kiyi amfani da shi kawai da dukkan ƙwarin gwuiwarki. Magungunanta ƴan gaske ne, manyan malamai gareta waɗanda kafin ta fara siyar da ko wane magani nata sai sun kwana sittin suna sauke izu sittin.”

“Taɓɗijan!”
Fatima ta ambata cikin mamaki da jinjina girman al’amarin.

“Da gaske fa, amma na tabbatar duk abinda zan faɗa miki a yanzu baza ki yarda ba. Sai kinga Mukhtar ya zama tamkar takalmin takawarki. Fareeda kuwa ko rantsuwa nayi ba kaffara kina shiga gidan zaiyi waje road da ita…”

“Hehehehe!”
Ta fashe da wata ƙaƙƙarfar dariya na jin daɗin maganganun ƙawarta.

Sai kuma ta gyara zama a gefen gadon, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa. Da dukkan gaskiyarta ta kalli ƙawar ta ce
“Kin san Allah? ni kuma ba na burin ya saki Fareeda. So nake cikin sanyi da wani irin taku na kissa in soya mata ɗanyar gyaɗa a hannu, ta wulaƙanta na ƙarshen ƙarshe, tana ji tana gani mijin da take tunƙaho da shi ya fi ƙarfinta, ya zamo sai hange daga nesa. Shi yasa Wallahi Tallahi Billahi ko nawa ne zan kashe don gyara kaina…”

A tare ƙawayen biyu suka fashe da wani ƙaƙƙarfan dariya haɗe da tafa hannayensu.

“Daman fa Hajiyarmu tana cewa burin kishiya abu uku ne. Ko ta fita ta bar miki gidan, ko ta mutu ta bar miki duniyar, ko tayi mummunar wulaƙantar da kare ma sai ya fita daraja a gurin mijin. Ki dage ƙwarai ƙawata ki tabbatar da ɗaya daga cikin maganganu ukun nan.”
Ramlah ta faɗa da wani irin salon zuga da tunzurah zuciyar Fatima, ta kuwa samu nasara, nan take ta cigaba da shan munanan alwashi kan Fareeda.

Suna wannan halin Mukhtar ya kirata a waya ga shi a ƙofar gidanta.

<< Rabon A Yi 8Rabon A Yi 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×