Skip to content
Part 6 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Ta kasa kiran ko ɗaya daga cikin ƴan’uwanta a waya, bata san wane irin labari za ta ji kan Auntynsu ba, mai daɗi ko akasinsa? Da wannan dalilin yasa ta zaro wayarta a jaka ta kashe, aka ce zuwa da kai ya fi saƙo, gara ta je ta ga halin da ake ciki da idanunta.

“Langes, yanayin iskar garin ya canza, ɗan fesa min turarennan ta baya-baya ko za mu shaƙi iska mai daɗi.”

Kalaman da kunnuwanta suka jiyo daga bakin direban napep ɗin kenan, ko kafin ta ce wani abu ko yunƙurin yin wani abu kawai sai jin feshin wani irin turare mare daɗin ƙamshi tayi a fuskarta.

Cikin fushi da ɓacin rai ta buɗe baki za tayi magana kawai ta ji jikinta ya mutu, gaɓoɓinta suka yi sanyi gaba ɗaya, ko ɗan yatsarta ta kasa ɗagawa. Cikin ƙasa da minti ɗaya idanunta suka yi wani irin nauyi sosai, lokaci guda wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita.

Kusan a tare abokai biyun suka waiga baya suna kallonta, lokaci guda suka haɗa idanu sukayi murmushi, sai kawai ya cigaba da ɓanana wutan napep ɗin don zuwa inda suka nufa.

_Langes da Villah taƙadiran matasa ne da suka addabi unguwarsu da sace-sace, neman mata, shaye-shaye. Duk yadda suke waɗannan tsiyatakun an sani ba wai ba’a sani ba, amma an kasa ɗaukan wani ƙwaƙƙwaran mataki a kansu. Ko ƴan sanda sun kama su basa wuce kwanaki biyu a kulle, saboda ɗaurin gindin da suke da shi a gurin Ciyaman ɗin ƙaramar hukumarsu._

_Bisa shawarar mai unguwa da dattijai a cikin unguwa sai aka yanke shawarar nema musu sana’ar yi, wataƙil hakan ya zama sanadiyyar shiryuwansu. Kafin tunkararsu da batun sana’a sai da aka ɗauki sati uku cur ana jan su a jiki, yi musu nasiha, tare da nunar musu da illar munanan ayyukan da suke aikatawa, aka kawo musu manyan misalan da ya tabbatar musu Chairman fa ba gata yake musu ba, yana amfana da su ne don ya cimma manufa ta ƙashin kansa, ba don ya tallafi rayuwarsu a matsayinsu na matasa ba. Sai da aka fahimci sun fara laushi sosai, hankali ya dawo jikinsu, sannan aka bijiro musu da tambayar wace irin sana’a suke so suyi? su faɗa in dai jarin da suke nema bai zarce naira miliyan ɗaya ba in Allah ya yarda za’a ba su._

_Bayan shafe sati guda suna shawarwari a tsakanin su biyun sannan zukatansu ta tsayu akan a sai musu keke napep. Babu ɓata lokaci kuwa aka siya musu, amma an aje musu sharaɗin cewa duk bayan kwana uku za su dinga bayar da balance a fadar mai unguwa har su tara kuɗin da za’a sake siyan wata napep ɗin, su mallaki kowa ɗai ɗai. Suka ce sun amince._

_Da farko sun fara aikinsu da zuciya ɗaya, kamar abin arziki. Kuma sai Allah ya tarfawa garinsu nono, balance ɗin da suke kaiwa har ya zarce adadin kuɗaɗen da aka yanka musu da farko. Komawarsu ruwa tsundum a ɓangaren zina ya biyo bayan wata Kilaki ce da suka ɗauka, tun daga kawo har zuwa maraban rido, da suka nemi ta basu kuɗinsu sai ta ce sai dai ta biya da albarkatun jikinta, idan kuma sun yafe to ba damuwa. Langes har ya kawar da kai shi kuwa Villah ya ce sai ya ɗana kuɗinsa._

_Tun daga wannan rana kuma sai abun ya zame musu jiki, tun suna haka da ballagazun matan da suka amince har suka fara tsallakawa kan waɗanda basu ji ba basu gani ba, ana haka har wata rana Villah ya ratsa gonar yarinyar da ta zame masa alaƙaƙai kuma ƙarfen ƙafa, ganin irin abubuwan da suka faru tsakaninsu da wannan yarinya yasa Langes shan alwashin in Allah ya yarda bazai ƙara ba, yanzu haka ma dai shi aure yake nema._

_Fareeda da suka ɗauketa a tudun wada basu ajiyeta ba sai da suka je can unguwar rimi, inda suke da ɗaki na musamman don gudanar da lamari irin wannan. Ɗakin ɗan ƙarami ne, kuma unguwar irin lungunnan ne da babu zirga-zirgan mutane sosai, ko napep ɗinsu daƙyar suke raɓata ta shige cikin lungun._

Fareeda bata buɗe idanunta ba sai da ta ji ana kici-kicin cire mata hijabi, kamar a mafarki haka take gani da jin komai. Ko da ta fahimci a ina take da kuma mummunan abinda yake shirin faruwa da ita a firgice ta make hannuwansa, idanu warawaje ta buɗe baki cikin ƙaraji tana faɗin
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Malam me kake ƙoƙarin yi min? na shiga uku!! ina ne nan kuka kawo ni?”
A zabure tasa hannuwa biyu ta hankiɗa shi baya ya faɗi ƙasa daga kan ƴar yaloluwar katifar ita kuma ta miƙe tsaye da sauri.

Ba tare da damuwa da rashin hijabi a jikinta ba ta nufi ƙofa da gudu shi kuwa yasa mata ƙafa ya taɗiyeta, ta faɗi ƙasa yaraf, bakinta da goshinta suka daki dandaryar sumintin tsakar ɗakin. Ihu ta ƙwala saboda azabar zafin da ya ratsata har ƙwaƙwalwarta.

Kafin ta dawo hayyacinta ya ɗaga ƙasar katifan ya ɗauko wata sharɓeɓiyar wuƙa, sai ƙyalli take yi a cikin ɗan madaidaicin hasken ɗakin, saitin wuyanta ya nufo gadan-gadan da wuƙar idanunshi a zazzare ya ɗora yatsarsa manuniya kan laɓɓansa alamun tayi masa shiru ko ya yankata.

A tsorace cikin wani masifaffen tashin hankali da ya ƙara lulluɓeta ta ɗauke kukan da take yi ɗif, ta ɗora hannu biyu akai hankali tashe sai murgina kan gefe da gefe take yi tana wani irin nishi mai kama da gurnani, kamar mai naƙuda.

“Dan ubanki ni kika ture na faɗi ƙasa?”
Ya tambayeta da wata ƙatuwar murya mai bayyana ɓacin ran ture shi da tayi.

Da sauri ta girgiza kanta alamar a’a! ta haɗa hannuwanta biyu alamun bada haƙuri tana yi tana jan shesshekar kuka, hawaye wasu na korar wasu kamar an buɗe famfo.

Gefen katifar ya laluba ya zauna, har lokacin bai ɗauke tsinin wuƙar daga saitinta ba, kallonta yake yi yana mamakin farkawarta a daidai wannan lokacin. Maganin da suke amfani da shi wajen fesawa mata mai kama da turare yana da ƙarfin da har su kusan gama komai da yarinya ba ta iya farkawa, ko ta farka za ta buɗe idanu ne kawai, amma jikinta shakaf za ta ji shi babu ƙarfi ko na sisin kwabo, ko ɗan yatsa ba’a iya ɗagawa balle har yarinya tayi ƙoƙarin yi musu gardama ko tayi yunƙurin ƙwatar kanta. Ita kuwa wannan sai ga shi ta farka da ƙarfin jiki da na zuciya, wannan wace irin yarinya ce?

Sassauta ɓacin ransa yayi, ya ɗan rage ƙarfin muryarsa, ya kawar da wuƙar daga saitinta ya fara magana ba tare da fushi ko hargagi ba.
“Kin ga, ki kwantar da hankalinki. Wannan kukan da kike yi ba na son shi. Ban saba ina biyan buƙatata ana min kuka ba kamar mai aikata fyaɗe ba, ba na so. Kin gane?”

Da sauri ta dinga ɗaga kai alamar eh, ta ɗaga ya fi sau goma, saboda tsananin tashin hankali da ɗimuwa, kuma har lokacin hawayen basu daina tsere daga idanuwanta ba.

“Ki buɗe baki ki amsa min, ba na son maganar kurame…”

“Don Allah, don girman Allah, don darajar Fiyayayyen halitta SAW ka rufa min asiri ka ƙyale ni, ka barni in tafi ba tare da ka keta min rigar mutunci na ba… Wallahi tallahi ni matar aure ce…”

“Ni ma ai mijin aure ne.”
Ya amsa kai tsaye, fuskarsa na nuna rashin damuwa da magiya da roƙonta.

“Na shiga uku…”

“Baki shiga ba tukun za dai ki shiga, don wallahi tallahi babu yadda za’ayi ki fice daga ɗakinnan ba tare da na kashe ƙishin ruwan da arba da tsayayyun ƙirjinki ya haddasa min ba. Matso nan in duba ma ko ciko kika yi, don matan yanzu bala’in yaudara gare ku, har mazaunai na acuci kuke sakawa, matso salin-alin in duba ta yadda za ki daɗi nima zanji, idan kuma ba haka ba ko da tsiya-tsiya sai na duba, sannan in damuƙa, in yamutsa, in tsotsa yadda nake so…”

Duk abinda yake faruwa a tsakaninsu Langes yana zaune ta waje a ƙofar ɗakin yana ji, hankalinsa a ɗugunzume, zuciyarsa cike da matsanancin tausayin wannan matashiya da ko sunanta basu sani ba. Basu taɓa ɗauko yarinyar da tun a karon farko ya ji zuciyarsa bai nutsu a ratsa gonar mutuncinta ba irin wannan. Waya ce riƙe a hannunsa yana ta dokawa wata lamba kira, tun ɗazu an ɗaga ta kuma ba shi tabbacin ga ta nan zuwa da gaugawa amma har yanzu bata iso ba.

Yana wannan zaman ya ji bala’ƴaƴƴen dambe da buge-buge ya kaure a cikin ɗakin, sai kuma ya fara jin ƙarar saukar mari tas tas ba ƙaƙƙautawa, muryar Villah na tashi cikin hargagi yana zagin Fareeda ta uwa ta uba yana faɗin shi za ta ciza har ta zubar mishi da jini?

“To sai na yi yaga-yaga da mutuncin naki sannan in kashe ki inga uban da ya tsaya miki a garinnnan.”

Hankalinsa ne ya ƙara mugun ɗugunzuma, duk iskancin da suke aikatawa a baya basu taɓa kashe rai har lahira ba. Idan Villah ya kashe wannan yarinya da basu san ko wacece ba ina za su kai hakkin rai? A zabure ya miƙe tsaye da niyyar buɗe ɗakin don ya shiga ya dakatar da Villah kawai sai yayi ido biyu da ita, saboda tashin hankalin da yake ciki ko tsayuwar ɗan mashin ɗin da ya kawota bai ji ba.

Riga da wando matsattsu ne a jikinta, sun matseta tamau, sun fitar da duk wasu siffa na shape ɗin jikinta. Kimono mai shara-shara ta ɗora akan kayan, duk da haka bai ɓoye girman tuma-tuman mazaunanta ba sadda ta juya baya da nufin magana da mai mashin ɗin da ya kawota.

_Mardiyya wacce gayu yasa ta yanke sunan zuwa Baby Mardy irin ɗima-ɗiman matannan ne, ga tsawo ga ƙiba. Ita ce alaƙaƙan da Villah ya haɗu da ita, duk da kasancewarta ta daɗe da rabar ma gayu mutuncinta kan titi shiga gonarta da Villah yayi abu ne da bai faru bisa amincewarta ba, ta kira abinda yayi mata mummunan fyaɗe na cin zatafi, ko da ta dawo hayyacinta shaƙeshi tayi sai da ƙyar ta sake shi bayan Langes ya zube mata duk kuɗaɗen da ke jikinsu. Kafin tafiyarta ta sha musu alwashin daga kanta Villah ya gama ratsa gonar da ba tasa ba, kamar motar kwana-kwana haka take musu dirar mikiya ta kashe wutar zinar da suke niyyar aikatawa ba zato ba tsammani, duk sadda ta bushi iska zuwa take ta karɓe kuɗaɗen da ke hannunsu. A bayan idanun Villah ta ritsa Langes da bindiga ta rantse da girman Allah duk sadda suka ɗauko wata mace idan bai kirata ba sai ta kashe shi har lahira. Wannan ne abinda ya tsorata Langes, ya daina biye ma Villah, yayi ma kanshi karatun ta nutsu ya fara neman aure._

Wani uban ihu da Fareeda ta ƙwallara lokacin da Villah ya riƙe gashin kanta ya buga fuskarta da bango shi ne abinda ya ɗaga ma Langes da Baby Mardy hankali suka buga ƙofar da ƙarfi tare da afkawa cikin ɗakin a guje.

Fareeda ce yashe a ƙasa a sume cikin jini, shi kuma Villah yana tsaye a kanta yana huci, lokaci guda kuma yana cire Belt ɗin wandonsa.

Kimonon jikinta ta cire tayi hurgi da shi, ko kafin ya gama kallonsu fuskarsa na bayyana mamakin shigowarsu a daidai lokacin da yake gaf da cimma mummunar buƙatarsa ta kaima mararsa wani irin naushin da yasa shi ƙwallah ihu ya durƙushe a ƙasa, hannuwansa biyu dafe da inda ta nausa yana runtse idanu haɗe da cije baki.

“Da na faɗa maka tun da ka zura gugarka a cikin rijiyata ka yi ƙarya ka sake yin ninƙayi a cikin wata rijiya balle har ka ɗebi ruwa ka zaci wasa nake ko? To ka jira ni zuwa anjima, duk inda ka shige zan lalubo ka. Zan lalata gugar taka ta yadda ko kyauta aka umarci ka shige cikin wata rijiya sai dai ka kawar da kai.”

Gurin Fareeda ta nufa da sauri hankalinta a tashe, ganin yadda ya fara samun nasarar yaga wani sashe na gaban rigar Fareeda har wani ɓangare na ƙirjinta ya baiyana a fili yasa ta jan tsaki, siririn gyalen da ta yafo a kanta ta cire. Da sauri ta ɗanyi dabara ta rufe gurin, har za ta ɗauke ta a haka sai ta hangi hijabin Fareeda da jakarta yashe can gefe ɗaya.

Langes ne ya kamata suka mayar mata da hijabin, ta maƙala jakarta a kafaɗa suka fice da ita hankalinsu tashe, tunaninsu da addu’arsu ɗaya ne.
‘Allah yasa bata mutu ba.’

******

Ko da suka isa asibiti sai da ƙyar likitoci suka karɓeta saboda yanayin jikinta. Sun dage sai an sako ƴan sanda cikin case ɗin, tunda sunyi ƙaryar hatsari tayi. Sun karɓe ta ne bayan Mardy ta kira wani saurayinta ƙusa a jiharnan, shi yayi magana da likitan, ya ɗura masa wasu ƴan kuɗaɗe sannan aka karɓeta da gaugawa.

Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci suka rufu akan Fareeda, aka yi mata duk wani abu da ya kamata, ta cigaba da barci da taimakon alluran da aka ɗura mata a cikin ruwa.

Idan ka kalli Fareeda sai ta bala’in baka tausayi, saboda yadda siffar jiki musanman na fuskarta ya canza gaba ɗaya, goshi da bakinta sun kumbura suntum, idanunta duk da a rufe suke sun tasa luhu-luhu. Shatin yatsu kwance ɓaro-ɓaro a kuncinta hagu da dama.

Daga bayanan da Langes yayi wa Mardy sam bata ji makaman da za su riƙa don gano ahalin Fareeda ba. Lokaci na farko da zuciyarta ya kitsa mata duba cikin jakarta, ko za su samu wani abu da zai sauƙaƙa musu gano inda ahalinta suke kafin ta farka.

Wayar da ta fara cin karo da ita yasa ta sauke ajiyar zuciya, kunna wayar tayi, ntwk na hawa wayar kiran Mukhtar na shigowa.

“Alloooo…”
Mardy ta faɗa da wani irin murya da yasa Mukhtar cire wayar daga kunnensa a can ɓangaren, ya duba lambar ya tabbatar dai tabbas Matarsa Fareeda ya kira ya ji wata baƙuwar murya, kamar ya katse kiran, amma sai ya sake mayar da wayar kunnensa yana tambayar ina mai wayar?

Gyatsine baki tayi, da jin muryar gayen a wani cuccushe zaiyi jin kai da ɗagawa, bai burgeta ba sam, amma sunan Habeebe Da’iman da ta ga anyi saving ɗin lambar ya tabbatar mata yana da muhimmanci a gurin mare lafiyar nan.

“Ita asalin mamallakiyar wannan wayar da ka kira, ga ta nan kwance a asibitin Barau Dikko, ta samu hatsari ne a cikin kekenapep. Mai napep ɗin ya gudu bayan yayi mata kwatsa-kwatsa da fuska, ni kawai taimaka mata nayi…”

Ƙit kiran ya katse daga can ɓangaren Mukhtar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 5Rabon A Yi 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×