LITTAFI NA DAYA
2002
Kamar ko da yaushe a ranakun da Nanna ce takan zo daukar su daga makaranta, yau ma yana leko kai yaga motar ta ya koma cikin makaranta. Mintina kusan sha biyar ya bayar a tsakani kafin ya fito, yasan babu wanda zaice ya neme shi sai Khalid, shima Nanna zatayi nasara akan shi bayan wasu yan mintina dole ya hakura su tafi. Titi ya nufa ya tari mashin da zai kaishi Hotoro daga nan makarantar su ta Greenfield da take cikin Sharada. Bai wahalar samu ba kuwa, shi yaune ranar shi ta karshe ma na zuwa makarantar tunda ya kammala jarabawar aji uku ne, duk da yaji suna cewa zasuyi musu wata jarabawar bayan sati daya da zasuyi amfani da ita wajen canza musu aji ba sai a jira fitowar JSCE din ba.
Kusan hakan shine tsari na makarantun kudi, bai wani damu ba tunda ba’a nan zai cigaba ba. Sun riga da sun gama magana da Daddy akan Science and technical zai tafi ya cigaba acan kuma har ya amince. Bakin titi ya sauka ya sallami mai mashin din ya taka zuwa kwanar da zata hada shi da gidan nasu. Ko kadan baya son komawa, ba zaiki yayita zagaye layi har bayan Magriba ba, idan dai-dai lokacin shigowar Daddy yayi sai ya dawo su shiga tare. Amman bashi da wani zabi, ba abokai yake da su ba balle yace zai wuce wajen su.
Kwankwasa gidan yayi, dattijon maigadin su ya bude mishi.
“Nawfal, an dawo kenan.”
Baba Isa kamar yanda suke kiran maigadin ya furta da fara’a a fuskar shi da tasa Nawfal yin dan gajeran murmushi yana amsawa da.
“Na dawo Baba Isa, sannu da kokari.”
Sannan ya wuce cikin gidan, bangaren su da yake wajen gidan, wanda dakuna ukune na bacci a ciki, kowanne da bandakin shi, falo sai kitchen matsakaici ya nufa. Mukulli ya zaro a aljihun wandon uniform din shi ya saka a jikin kofar yana budewa. Daddy yace bangaren nasu ne su hudu lokacin da suka dawo wannan gidan watanni hudu da suka wuce, a gaban shi a gaban kowa yayi maganar, amman shi kadai yake kwana a bangaren, ko da Daddy ya sani bai taba magana ba. Shima kuma ba damuwa yayi ba, ya rigada ya saba rayuwar kadaici ba tun yanzun ba.
Sanin ba kowa bai hana shi shiga cikin gidan da sallama ba. A falo ya ajiye jakar da take rataye a kafadar shi yana takawa zuwa dakin daya zaba a matsayin na shi ya wuce bandaki, ranar da akeyi ba ta wasa bace ba, shisa ya watso ruwa harda alwalar sallar la’asar ya dauro sannan ya fito. Riga da wando ya saka, yana son kamshin a rayuwar shi, tun zai iya tunawa ko turare ya gani dakin Daddy zai tambaye shi ya dauka. Shisa Daddy baya rabo da siyo mishi turaruka, kala-kala, wasu ko bude su baiyi ba ma, yanzun kala biyu ya fesa a jikin shi sannan ya baro dakin baccin yana fitowa falo inda yaci karo da Khalid da yake rike da kofi a hannun shi sai filet a dayan hannun da Nawfal yaga kamar cincin ne a ciki.
“Jalof Nanna tayi…”
Cewar Khalid din yana mikawa Nawfal kofin daya karba yana dubawa, shayine da akewa laqabi da ice-tea a turance, dan kankaru ne a ciki. Khalid ne kadai yasan baya hada hanya da duk wani abu me zafi, ko abinci ne saiya ajiye shi ya huce sannan yake ci. Zai iya cin abincin da ka fito da shi daga fridge amman ba zai iya cin wanda ka zubo daga tukunya ba sam. Amman kowa a gidan yasan baya cin yaji, idan yace baya cin yaji sai mutane su dauka abincin da yayi yaji da yawa ne baya so. A nashi yanayin ba haka bane ba, ko attaruhu daya kasa ka gabaki daya miyar ka zai mishi illa, cokali daya zaiji kamar ya zuba garwashin wuta a cikin bakin shi, awa daya ba za’ayi a tsakani ba kuraje zasu cika mishi baki, zai iya sati yana fama a haka.
Tun yana karami kowa yasan hakan, allergy ne yake da shi na duk wani abu daya danganci yaji. Duk da ya zamana dama ce da Nanna ta kara samu wajen gallaza mishi, da yake duka gidan kowa yana son abinci masu yaji har Daddy, a gaban Daddyn sai ta nuna abincin Nawfal daban take dafa mishi. Bai kuma taba karyatata ba, idan farin abinci ta dafa da miya zai diba ya saka mai da Maggi yaci, ranakun da yake da makaranta ma inya dawo baya bi takan abinci, da yaci sau daya shikenan zaici gaba da hidimar shi, kusan jikin shi ya riga da ya saba da yunwar.
“Ban san ko sugar din yayi maka ba, ka sha kaji.”
Khalid ya sake fadi yana mika mishi farantin cincin din.
“Nanna ta san ka dibo mata cincin?”
Nawfal ya tambaya, dan daga kafadu Khalid yayi.
“Abinda Nanna bata sani ba yana da yawa…”
Dan murmushi kawai Nawfal yayi, Khalid ya saba saka kanshi cikin hatsari saboda shi. Jibga ta Nanna babu wanda ya kai Khalid din shanta, kuma fiye da rabin lokuttan akan shine. Kurbar shayin yayi, sanyin shi yana saukar mishi da wani yanayi mai dadi, yana son kayan sanyi. Suna saka shi nutsuwar da ba zai iya misaltawa ba. Kai ya jinjina ma Khalid
“Komai yayi dai-dai… Nagode”
Sannan ya karbi filet din cincin din ya karasa yana samun kujera ya zauna ya ajiye shi akan hannun kujerar. Khalid dinma waje ya samu ya zauna
“Zanje gidan Daada idan nayi sallar la’asar. Kila in kwana acan. Ka fadawa Daddy idan ya dawo”
Kai Khalid yake girgiza mishi
“Kabari idan ya dawo yau sai mu fada mishi gobe kai baka da makaranta, ni ina da. Idan na dawo sai a kaimu nima ina so inje, na dade banje ba…”
Kallon shi Nawfal yake yi har ya gama maganar
“Ko Daddy ya barka Nanna ba zata bari ba, ka sani. Zan tafi yau, idan ka tambayi Daddy saika biyoni daga baya.”
Baki Khalid ya bude zaiyi magana Nawfal din yayi saurin katse shi.
“Zan tafi yau, ba zan kwana a gidan nan ba.”
Shiru Khalid din yayi, duk wani abu da zai fada yasan ta bayan kunnen Nawfal din zai wuce. Shisa ya zauna har ya gama shanye shayin, cincin din kwara budu yaci yana kallon shi. Yar karamar jakar shi Nawfal ya dauka. Tare suka fita masallaci sallar la’asar.
*****
Da sallama ya shiga gidan Daada, kallo daya zaka yiwa fuskar shi idan kagan shi awanni kalilan da suka wuce zaka ga sauyin da tayi. Idan zaka tona zuciyar shi mutane uku zaka samu a cikinta, Daada na daya daga cikin mutanen.
“Nawfal…”
Daada ta fadi itama da alamun jin dadi a muryarta bayan ta amsa sallamar tashi, anan bakin kofa ya zare takalman shi yana shiga cikin dakin, zaune take a kasa kan kafet, akwai kujeru a cikin dakin, zama a kan su bai dameta ba, sai tayi kwanaki bata hau kai ba, tafi jin dadin saman kafet din, idan ma wani ne yazo yayi mata magana takan ce,
“Ina zan iya zaman kujera, kafafuwana duk su tara jini, ga jikin tsufa.”
In Julde ne dariya yakan yi
“Daada idan kikace jikin tsufan nan sai wani ya dauka kin bawa shekaru tamanin baya”
Ita ma takan dara
“Ko dai banba tamanin baya ba ni din ba ta yau bace ba”
Yau din bata ma zauna falon ba sai yanzun nan, da yake tana zuwa Islamiyya anan cikin unguwar tasu ta Gadon kaya. Da karfe goma na safe zuwa sha biyu. Da ta dawo tana da miya, farar shinkafa ta dafa ta shige daki, bayan azahar bacci ta sha har uku da rabi.
“Ai kuwa gara da kazo, sai ka dauko mun Madina daga makaranta, yanzun nake shirin tashi naga hudu da rabin ta kusa”
Kallon Daada yayi
“Daga shigowata Daada? Kika san kalar gajiyar da na kwaso?”
Cewar Nawfal
“Raggwanci dai ba gajiya ba. Jakar nan zaka ajiye kaje ka dauko ta…”
Jakar ya sauke daga kafadar shi yana ajiye saman kujera, akan Madina ne kawai Daada ba zata saurari komai ba, yasan ba zata bar shi ya zauna idan ba zuwa yayi ya daukota ba. Makarantar da take din ba wani nisane da gidan Daada ba, da ka fita titi tsallakawa zakayi, hade take da islamiyya shisa ma take kaiwa har hudu da rabi, kamar yaji Daada na cewa ta kusan komawa tashi karfe shidda. Bai maida hankali kan zancen ba. Ka’ida irin ta makarantar su Madina sai da aka tsaya ana mishi yan tambayoyi, da Madina bata hango shi tace
“Hamma…”
Ba yasan zasu bata mishi lokaci, da gudunta kuwa ta karaso tana fadawa jikin shi hadi da zagaya hannuwanta a bayan kafafuwan shi. Dakyar ya bambarota yana rike hannunta suka fito daga cikin makarantar
“Yaushe kazo? A gidan mu zaka kwana?”
A shekarun ta har mamakin yanda take magana babu gargada yakeyi. Dan tsamin baki da yara sa’anninta sukeyi babu shi a Bakin Madina, babu kalmar da bata iya furtawa, sai dai wasu kalaman idan tayi saboda fulatanci da Daada takeyi mata kuma kusan dashi bakin nata ya bude zakaji fitar haruffan nata daban. Gashi tana cikin yaran da suke da surutu, sai dai fiye da rabin nata surutun akan tambaya ne, kome ta gani tana so ta gane. Idan gidan yazo bakin shi ba zai huta da tambaya ba sai tayi bacci.
“Hamma meye wannan? Hamma me yasa kasa wannan kayan yau?”
Tambayoyi kala-kala, yanda tambaya bata karewa a bakin Madina har mamaki yake bashi
“Idan zan kwana me zaki bani?”
Dan jim tayi sannan ta amsa shi
“Tuwo…”
Dariyar da ya kwana biyu baiyi ba ta kwace mishi
“Duk abubuwa masu dadi ki rasa me zaki bani sai tuwo”
Ya karasa maganar yana daukarta ya sabe a kafadar shi saboda titin da suka karasa
“Tuwo da dadi, Daada tana yi mana”
Tace da dukkan gaskiyar ta, ranta yana son tuwo fiye da komai a abinci, sai kuma nama, dan ko abinci zaka zuba ma Madina hannunta akan naman ciki zai fara sauka, sai ta cinye sannan ta fara cin abincin
“Saboda kina zaune da yar tsohuwa shisa tuwo yafi dadi.”
Da rashin fahimta take kallon shi yanzun
“Ni da Daada nake zaune ba yar tsohuwa ba.”
Dariya ya sake yi.
“Wacece yar tsohuwa Hamma?”
Numfashi ya sauke, dan har sukaje gida duk amsar da zai bata sai ta nemi tambaya a ciki. Yakan ji zuciyar shi da take tare da wani dutse danne da ita ko yaushe ya daga duk idan yazo gidan Daada. Wasu ranakun yana zuwa ko ba zai kwana ba, kamar yana da wani batiri na hakuri da komai da Daada ce kadai take da hanyar caza mishi batirin, shisa yake jin zuwa gidan nata ya zame mishi dole, tana saka komai yayi saukin dauka. Akwai mutum daya bayan Daddy da Khalid da suke kaunar shi, da suka damu da shi, hakan ba abu bane karami a wajen shi.
“Hamma kunnen ka manya.”
Sosai yake dariya.
“Madina dan Allah ki kyale kunnuwana su huta haka, ke kullum sai kince kunnuwana manya? Kamar naki ne”
Kai take girgizawa tana kama kunnen nashi ta lankwasa, hannunta ya ture
“Sakko wallahi tunda munzo gida.”
Sosai ta makale a jikin shi, sallama yayi yana shiga cikin gidan.
“Ai kuwa sai kin sakko tunda kunnena babba ne.”
Daada da take jinsu tayi murmushi
“Yarinya dai gaskiya ta fada, bata taba ganin kunnuwa irin naka bane shisa”
Fara’ar da bata bar fuskar shi bace ta sake fadada
“Daada kunnen Hamma ya kara girma”
Samu yayi yana saukota
“Kema kunnen ki babba”
Kan yar karamar hijabin da take jikinta ta saka hannunta tana taba nata kunnuwan
“Daada wai kunne na babba?”
Tayi maganar tana shiga cikin dakin ta zauna akan cinyar Daada da ta kamata ta gyara mata zama tana cire mata jakar makarantar ta ajiye a gefe, sannan ta kamo kafarta daya tana fara kwance igiyar takalmin don ta cire mata
“Ko dai zaiyi girma ba zai kai na Hamman ki ba, na shi kunnuwan daban suka zo”
Nawfal da ya samu kujera ya zauna yace
“Daada…”
Dariya tayi tana karasa cirewa Madina takalman
“In dauko riga ki sake mun?”
Kai Daada ta daga, da sauri kuwa ta mike daga jikinta tana rugawa da gudu.
“Karki janyo mun kayan nan Madina, ki dauko wadda hannun ki ya fara kaiwa.”
Ai da wahala ma idan Madina ta saurare ta, kai kawai ta girgiza. Doguwar rigace ta dauko kalar bula mai haske Daada ta saka mata. Kallon ta Nawfal yakeyi, rigarta na tuna mishi yanda yake son kalar bula, musamman mai haske kamar sararin samaniya, yana kuma son farin abu. In har Daddy zai sai musu kaya ya tambaya wacce kala zaice
“Sky blue ko fari.”
Duk da wani lokacin Daddy zai siyo mishi wata kalar daban. A cewar shi,
“Fiye da rabin kayan ka fari ne da blue Nawfal, gara ka sirka da wata kalar”
Yasan wata kalar a cikin kayan shi na dan wani lokacine, zai saka wata kalar saboda Daddy a yanzun, a gaba babu abinda wata kalar zatayi a cikin jerin kayan sawar da zai mallaka. Wajen shi Madina ta karaso.
“Hamma zan sha ruwa”
Ta fadi
“Da ban zo ba waye yake baki ruwan? Da nazo ba zaki barni in huta ba…”
Shagwabe mishi fuska tayi yana kallon kanta da yake dauke da kitso kwara biyu, wajen keyar gabaki daya babu gashi. Kamar an sude mangwaro
“Kunne na manya, amman jibi gashin ki kamar anci giginya ba wuka.”
Turo baki tayi
“Daada tace gashi na zai fito kamar nata.. Ko Daada? Nima dogo har bayana.”
Madina ta karasa maganar tana juyawa ta kalli Daada, kai Daada ta jinjina
“In shaa Allahu gashin nan zai fito har gadon baya, so nake ma yafi nawa idan ya tashi.”
Hankalinta ta mayar kan Nawfal tana mishi kallon kaji ko? Daman na fada maka, kafin ta sake cewa,
“Zan sha ruwa, kaji… Daada ta hanani bude fridge dinta, ka zo ka bani.”
Mikewa Nawfal yayi ta kuwa kama hannun shi, dole tare suka nufi kitchen din da yake hade da katon falon Daada din. Bin su tayi da kallo, wani abu na matsewa a cikin kirjinta. Tunda Nawfal ya shigo ta kula idanuwan shi sun fada yayi zuru-zuru kamar wanda baya ci yana koshi. Ta fi kowa sanin halin Saratu ba tun yanzun ba.
“Yaran nan amanata ne Julde, ina tsoron halin matar ka, ba tafiya da shi nake son hanaka ba, ka isa ka rike dan Bukar, da bana raye dole a cikin ku wani ne zai rike shi, amman ina nan, zan so ya zauna a hannuna.”
Kalamanta akan Nawfal shekarun baya suka dawo mata, ko yanzun in da zai dawo gidanta gabaki daya zata so hakan. Julde ya daure ta ne da kalaman shi, kalaman da har yanzun suke saka harshen ta yin nauyi wajen ce mishi Nawfal din ya dawo wajen ta, gashi bata da wata bayananniyar hujja tunda duk yanda zata tambayi Nawfal ya zaman su da Saratu yake zai ce,
“Daada lafiya kalau fa, ki daina damuwa dan Allah, muna zaune lafiya.”
Amman tasan karya yakeyi, alamun shi basu nuna haka ba, shatin duka a farko-farkon dawowar ta garin Kano da Nawfal din yakan ce mata dukan na makaranta ne, laifi sukayi amman tasan karya ne. Ta taba tambayar Khalid.
“Makarantar ku haka suke dukan yaran mutane Khalid? Na ga jikin Nawfal ko ina shatin bulala ne.”
Yanayin fuskar Khalid din tun kafin ya furta
“Duka kuma Daada? Ana duka a makarantar mu, amman ba da yawa ba, kuma Daddy na zuwa yayi magana idan mun fada, ba sosai ake dukan yan gidan mu ba”
Ta san Nawfal karya yayi mata, a yan shekarun shi a lokacin yasan ya adana damuwa a kirjin shi harya boye mata itama. A gidan ya kwana a ranar, da zazzabi ruf a jikin shi, zazzabin da sai da ta bashi magani, kuma tasan dukan ne. A lokutta da dama Nawfal ke karya mata alkawarin da ta daukarwa kanta na daina kuka akan su shida Madina, daga randa tasa kafa ta tsallake komai tayi nufin barin komai din a matsayin shudadden tarihi, sai dai ko tarihi yakan dawo maka lokaci zuwa lokaci, saboda akwai mutanen da labarin shi ba zai taba barin bakin su ba balle su barka ka manta.
Ita a nata bangaren ma bata bukatar wadannan mutanen, ko ya Madina zata gitta ita din babbar tunasarwa ce, ga Nawfal shima.
“Wani abu a zuciyata yana fada mun shi kadai ne kwan da nake da rabo a duniya Daada, ga amanar dana, gatan da na hasaso ma rayuwar shi mai yawa ne, ga amanar shi nan kafin in samu dawowa, dalilin da zaisa ni barin shi mai karfine…”
Nawfal amanarta ne, amanar da Bukar ya damka a hannunta, amanar da Julde ya karbe mata take ganin ya kasa tayata rikewa.
“Sai dai in har yanzun kina duba bayana, kina duba abubuwan da na bari, idan kin kasa mantawa ki daina kallona da halayen dana bari Daada waye zai daina? Ke kadai ce dalilina na shigowa garin nan, sai kuma Nawfal yanzun, idan kika hanani rikon yaron nan zanji kamar saboda kina dubana da abinda nake sa Allah ya shafe mun shi a littafina… Halayena ba zasu taba kulawar shi ba Daada, na rantse miki tarbiyar shi ba zata samu tangarda ba, kina kallon kaunar da take tsakanin mu, ko ita ki duba.”
Wannan kaunar kuwa ta ganta tun a ranar farko da Nawfal ya fara dora idanuwan shi akan Julde yana da shekaru uku a duniya, sati biyu bayan tafiyar Bukar, sati biyun da daga ita har Nawfal din sukayi su a matukar jigace saboda kukan Daddyn shi da yake yi mata. Amman yana ganin Julde ya ruga ya makale shi yana kiran.
“Daddy…”
Ta ga Julde da yaran shi, ta ga kalar kaunar da yake yi musu, amman yaro daya taga ya kalla da kallon da yake yiwa Nawfal, yaron da yayi sanadin komai. Har yanzun idan Nawfal da Julde na waje daya zaka ga yana kallon Nawfal din kamar shine tilon abu a duniya da yake cike mishi gurbin duk wani abu daya taba rasawa, kamar Nawfal ne hasken da ya yaye duk wani duhu daya taba samun rayuwar shi. Kome zata gani, ko me zatayi tunani bata da zuciyar da zata yiwa Julde maganar Nawfal ya dawo wajen ta, ko da ya yarda bata da tabbas akan Nawfal din zai amince, yanda Julde yake kallon shi, haka take ganin Nawfal din na kallon shi shima, kamar duka duniyar shi ta tsaya ne duk inda Julden yake.
Dawowar da su Nawfal sukayi falon da surutun Madina na katse mata tunanin da takeyi, bata san ya akayi daga rike hannun Nawfal Madina ta koma kan wuyan shi ba. Dariya takeyi cike da wani irin farin ciki da zuwan Nawfal kadai yakan bayyana shi a fuskarta.
“Da shiriritar nan da kukeyi da zuwa kayi kayo mun cefane ka siyo mun kifi”
Kafin ya amsa Madina ta riga shi da
“Zan bika Hamma, dan Allah zan bika”
Saukota yayi a hankali
“Je ki dauko hijabin ki da takalmi…”
Da gudunta ta tafi, Daada ya kalla
“Ina kudin?”
Itama mikewa tayi tana bin bayan Madina zuwa dakin baccin su. Ita ta dauko mata takalmi da yake mai madauri ne sai da ta saka mata, ta bata hijabin a hannun ta, bata jirata ba ta fita da gudu, haka Julde yake kwaso mata su, duk yawancin takalmanta irin sune. Kudi ta dauko ta fito ta same su a tsaye suna jiranta, bashi tayi ta kuma fada mishi na yanda take so. Yana rike da hannun Madina suka fita, Daada na tsaye tana kallon su. Zuciyarta da adanannen tunanin da takeyi akan su, jikokinta biyu da suka fi har ‘yayanta matsayi a zuciyar ta.
Amanar ta
Kaddarar ta
Sai dai taya zata san abinda kaddara ta tanadar musu yasha bamban da tunanin ta?
A lokacin da ta hade Madina da Nawfal a waje daya
A lokacin da ta hango su karkashin inuwa daya suna tayata rike amanar junan su
Kaddara ta rubuta musu yin hannun riga da juna
Inuwar guda daya ce kamar yanda Daada ta hango
Amman hannun rigar da zasuyi da juna dole mutum daya inuwar zata bi
Dole dayan su zaiyi gararamba a ranar da babu tabbacin samun inuwar fakewa.
Masha allah
Inason karanta littafanku
To masha Allah muna godiya, Malama Maryam. Ga takardu nan sai wanda kika zaba.
inason inkarasa amma narasa inda xansamu
Rai Da Kaddara paid book ne sai kin yi subscribing za ki iya karanta shi duka. Ki je menu ki latsa ‘subscribe,’ sannan ki bi sauran process, duk akwan bayanin a can.
Ki nemi marubuciyar ta wannan lamba+234 903 572 3778
Gwanata.
Hmmmm