Skip to content
Part 20 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

A karo na farko a rayuwar shi da ya rike jaka a hannun shi batare da yasan abinda zai zuba a ciki ba.

“Kana da passport Bajjo, Daada ma nata baiyi expire ba, da kai ya kamata ku tafi, zan biyo ku daga baya dan kar a bata lokaci.”

Abinda Julde yace mishi kenan, yana kallon gamsuwar da su Khalid sukayi da maganar Julden a cikin idanuwan su tun kafin ma su furta. Shisa yayi shiru, yanda duk ya so ya girgiza wani ya fada mishi cewa ba yajin zai iya tafiya shi kadai, bayajin yana da karfin halin da zai kula da Daada batare da zuciyar shi ta rarrabu kashi-kashi a cikin kirjin shi ba, sai ya kasa. Kai kawai ya daga musu cikin yarda shima. Hadiye tsoron da fargaba yayi har sai da ya koma gida a ranar, ya saka mukulli yana kulle dakin bayan ya shiga sannan ya budema Murjanatu zuciyar shi yana jin rashin ta fiye da kowanne lokaci.

“Bana jin zan iya Jaan, Daada ce, yau dana ganta a kwance babu abinda naji ina so inyi sai in zauna a gefen ta inyi kuka har sai ta bude idanuwanta tace mun komai zaiyi dai-dai… Ban taba kula da ita ba, ita ta saba kulawa da ni, taya zan fara yanzun?”

Ya karasa yana jan wani irin numfashi hadi da fitar da shi cike da nauyin da yake ji a kirjin shi, saboda yanda yayi maganar batare daya ba kanshi damar numfasawa ba.

“Waya yace kai kadai zaka kula da ita? Ba India kace ba? Zaka sameni a filin jirgi ina jiran ku Gidado…idan na kula da kai zaka iya kula da ita? Zan so ince maka zan kula da ku duka biyun, amman Daada ce, zaka so kayi komai daya dangance ta da kan ka… Na san hakan, kaima in ka nutsu ka duba zuciyar ka zaka ga hakane…”

Numfashin dai ya sake ja yana fitarwa.

“Babu abinda ba zaka iya ba in dai akan Daada ne, in baka yarda da kan ka ba, ka yarda dani, kasan ba zan maka karya ba, duk da ina sonka.”

Baisan murmushi ya kwace mishi da kalamanta na karshe ba sai da yaji alamar shi har a zuciyar shi da nauyinta bai ragu ba, amman numfashin da yaja ya kai mishi har ciki.

“Kinsan bangane komai da kikace sosai ba…komai ya kare ne da yanda kika ce kina so na.”

Dariyar da tayi sai da ta kara fadada murmushin shi.

“Ina son ka… Ina son ka Gidado.”

Kai ya jinjina, ya sani, saboda yanda bata gajiya da nuna mishi duk rana haka bata gajiya da fada mishi tana son shi. Wasu ranakun in ta fada sai yaita kallon ta, musamman labbanta da yanda kalaman suke fitowa kamar basu da wani nauyi a wajen ta. Da shi bahaushe ne, daya boye a bayan yaren yace shisa fada mata yana son ta a duk rana yake mishi wahala. To shi bafullatani ne, babu kunya a tsakanin su, sun wuce wannan matakin tuntuni, bashi da abinda zaiyi amfani da shi a matsayin kariya.

Amman kalmomin suna masa nauyin furtawa, zai iya kirga lokuttan daya fada mata su, yana dai kokarin ganin a rana ya zama dalilin da zatayi dariya ko sau dayane, yana kuma kokarin kyautata mata dai-dai iyawar shi, fada mata yana son ta na mishi wahala, amman nuna mata abune mai sauki saboda ta cancanci fiye da hakan a wajen shi, ta bashi abubuwan da zai dauki lokaci idan an bashi dama yana bayanin su.

“Wai har yanzun kana nan tsaye Bajjo?”

Khalid da ya turo kofar yana katse ma Nawfal tunanin shi ya furta.

“Na rasa abinda zan dauka, Murjanatu ta shiryamun jakata da zan taho.”

Gira daya Khalid ya daga.

“Nasan kana da aure Bajjo, ban manta kana da mata ba.”

Dariya Nawfal yayi.

“Yi hakuri ba haka nake nufi ba.”

Labban shi Khalid ya matse waje daya yana jinjina kai, cikin yanayin dake fassara “Ka dai cigaba Allah yana kallon ka.” Dariya ya sake na Nawfal.

“Da gaske na rasa abinda zan dauka”

Numfashi Khalid ya sauke.

“Me yasa kake fadamun? Ka kira Murjanatu mana sai ta fada maka abinda ta shiryo maka sanda zaka taho ka sake daukar su.”

Kai Nawfal ya jinjina cikin yarda da shawarar Khalid din yana nufar inda wayar shi take ya dauko.

“Me zakai?”

Cewar Khalid yana bude baki cike da mamaki.

“Kiran Murjanatu mana?”

Dafe kirji Khalid yayi yana samun waje kan gadon ya zauna.

“Me ka dafe? In zuciyar ka ce ba’a bangaren dama take ba, saika dan matsar da hannun ka tsakiya…”

Wani irin kallo Khalid yake ma Nawfal din daya cigaba da fadin.

“Daga bangaren haggu kadan.”

Ta baki Khalid ya furzar da numfashi yana sauke hannun shi.

“Baka ga kallon da nake maka ba ko? Ba zakayi shiru ba.”

Dariya Nawfal yake yi.

“Da gaske, wannan ai son kunyata Hamma Salim ne, ace baka san inda zuciyar ka ta ke…”

Robar ruwan da Khalid din ya dauka na sa sauran kalaman Nawfal din makale mishi tare da dariyar da yayi niyyar yi.

“I dare you Nawfal Bukar…”

Khalid ya fadi muryar shi babu alamar wasa.

“In kira Murjanatun ko…”

Kallon, “Magana kake har yanzun” da Khalid ya watsa mishi yasa shi daga hannun shi cikin saranda yana mayar da wayar ya ajiye. A duniya dai yasan in ta bangaren samun yan uwa ne Allah ya gama masa komai, ko da ace dama aka bashi zai wahala ya zabo irin su Khalid. Shisa yake kara godema Allah da kyautar su da Ya yi masa a cikin rayuwar shi. A cikin mintina kadan Khalid kan saka shi yaji yanda zai iya jure duk wani abu da zai faru da shi a cikin kowacce rana. Numfashi da bai san yana rike da shi ba ya sauke. Kananan abubuwa ya fara tattarawa kamar su brush da cajar waya da duk wani abu da yake tunanin zai bukata.

“Ba zance maka Daada zata zauna tare da mu har karshen rayuwar mu ba Bajjo, amman komai zai faru Allah ba zai dora mana abinda ba zamu iya dauka ba, daga karshe komai zaiyi dai-dai… In shaa Allah”

Khalid ya fadi muryar shi na fitowa da wani sanyi da yasa nauyin da Nawfal yake ji a kirjin shi karuwa. Baice komai ba, kayan shi ya cigaba da hadawa, ko ya so ya fadi wani abu bai san me zaice ba.

“Hamma yaje ya dauko su.”

Khalid ya fada dan ya rage musu nauyin shirun da ya lullube su gabaki daya, kai kawai Nawfal ya jinjina batare da yace komai ba, mikewa Khalid yayi tare da fadin

“Matar ka kake son kira, na bar maka dakin Bajjo.”

Murmushi Nawfal yayi, ba dan zai kira Murjanatu bane ya fita, abinda ya zo ya fada mishi ne ya gama fada shisa ya bashi waje yayi tunanin duk da yake bukata

“Na gode Hamma…”

Ya furta a hankali duk da Khalid din ya rigada ya fita daga dakin. Kayan shi ya cigaba da hadawa zuciyar shi da kan shi cunkushe da abubuwa mabanbanta.

*****

Da yawa kance lokaci sakarai ne, idan ya wuce baya dawowa. Ta kuma ga hakan a al’amura daban-daban. Ta ga sauri da rashin saurin lokaci musamman idan tana jiran wani abu. Kwanaki bakwai dai basu taba zuwa sun wuce mata haka batare da ta rike wani abu guda daya mai muhimmanci da tayi a cikin su ba. Tayi kuka har sai da ta fara tunanin anya ba duk rana ake halitta ma bawa sababbin hawaye ba? In ba haka bane ba tasan ta inda take samun hawayen fitarwa bayan tarin wanda ta zubda ba.

Ta sha jin labarin kadaici, har ma take tunanin idan ta runtsa idanuwan ta a wasu ranakun takan ji shi, takan ji kewar iyayen da ko fuskar su bata sani ba. Ashe wannan ba kadaici bane ba, yaudara ce da zuciyar ta take yi mata, asalin kadaici na cikin ranar da Khalid ya maida ta gida dan ta dauko kayanta. Yanda ta shiga cikin gidan tana tunanin ta inda zata fara inda ace ta rasa Daada, lokacin ne ta duba tsakar gidan da yayi mata fadi kamar duka duniyar ta ce ta tattaru a waje daya, ta kuma ganta ita kadai a tsaye. Ranar ne ta fara sanin menene kadaici, yanayi ne da yayi matukar firgitata, ranar kuma ta hango maraicin da bata fatan ya kusanto inda take.

Tun jiya aka sallame su, tunda daman sun kara barin Daada ne dan a tabbatar ta samu saukin da zata iya zaman jirgin tunda an riga an gama kammala duk shirye-shiryen da za’ayi da ya danganci tafiyar ta su. Ita dai ce take ta hada kayanta tunda ance gidan Julde zata zauna har su Daadar suje su dawo, ta so ta tambaya me yasa ba za’a tafi da ita ba, me yasa za’a barta, waye zai kula da Daada bayan bata tunanin akwai wanda yasan abinda Daadar take so da wanda bata so fiye da ita.

Amman tunda take bata taba ganin damuwa karara a fuskar Julde ba irin wannan karin. Yau ma da yazo gidan idanuwan shi duk sun kumbura kamar wanda yayi kuka. Maganar shima a shake take fitowa, shisa ta rasa kwarin gwiwar da zata tsare shi da wasu tambayoyi. In da zata iya daukar dakinta kacokan din shi da haka zatayi, saboda komai da yake ciki bukatar shi takeyi. Bata taba kwana wani waje ba bayan asibiti tare da Daada tunda take.

“Kwana nawa zakuyi Hamma?”

Tayi ma Nawfal tambayar da ta kasa yiwa Julde, amman kafadu ya daga mata cike da rashin sani kafin ya amsa da.

“Ba zance ga exact kwanakin ba Madina…zan fada miki da na san kwana nawa zamuyi.”

Kai kawai ta iya jinjina mishi, tana ture tunanin can kasan zuciyarta saboda bata son hasaso kwanakin da zatayi batare da Daada ba. Ba zata taba daukar duk abinda take da bukata ba, ta sani. Shisa ta rufe jakar kawai tana daukarta ta fito da ita falo ta ajiye. Dakin Daada ta nufa ta sameta a zaune in da tayi sallar la’asar, karasawa tayi ta zauna a gefenta tana matsawa sosai yanda zata iya jingina da jikin Daadar, bata da lafiya, amman tana bukatar hakan ko na yan mintina ne ko zuciyar ta zatayi mata sanyi.

“Allah ya baki lafiya Daada Am… Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya… Zanyi kewar ki”

Madina ta karasa maganar muryarta na fitowa a karye, hannu takai ta dan daga gilashinta tana sa yatsa ta goge hawayen da take jin ya taru a gefen idanuwan ta. Numfashi Daada ta sauke, akwai ciwo na daban da zuciyarta take fama da shi da yafi karfin ganin duk wani likita a fadin duniya.

“Kina da tambayoyi Madina, na san kina da tambayoyi masu yawa… Nagode da yanda baki taba tsare ni da in fada miki ba”

Sake shigewa jikin ta Madina tayi tana jin zuciya ta na kara karyewa

“Dan Allah kibar maganar nan Daada… Ke dai Allah ya baki lafiya, in akwai abinda ya kamata in sani ai ba saina tambaya ba na san zaki fadamun”

Cewar Madina, tana jin gaskiyar kalaman har ruhin ta. Koma menene bashi da muhimmancin lafiyar Daada a wajen ta. A yanzun ma gabaki daya babu wani abu da take so sama da ganin Daada ta dawo lafiya, an duba ance babu sauran abinda yake damun ta. Murmushi Daada tayi, murmushin da ya fito daga wani tsagi na zuciyar ta da har ya daina bugawa tare da yan uwan shi ba zai daina godema Allah da kyautar su Madina ba, akan su ta kara yarda da yanda Allah yake fitar da mai kyau a cikin mummuna.

Sallamar da suka ji na sa Madina mikewa, a daki ta baro wayar ta, tasan da zai wahala Salim ya shigo gidan. Zai kira ta ne yace mata yana kofar gida, tana fitowa falon kuwa ta ganshi a tsaye, kallon shi tayi tana ganin yanda yafi kofar tsayi. Salim dogo ne, irin dogayen da ko a cikin masu tsayi zaka duba da yawa baka sami kalar shi ba.

“Hamma…”

Ta furta yana sauke mata numfashin da yake rike da shi a matsayin amsa kiran sunan shi da tayi, kallon ta yakeyi da gajiya kwance akan fuskar shi, kasan idanuwan shi ya danyi duhun da in baka san shi ba zaka dauka haka suke. Madina ta san rashin wadataccen bacci ne.

“Ina ta kiran ki…”

Salim yayi maganar yana daga mata karamar wayar shi da yake rike da ita.

“Nabar wayar a daki, amman ga jakunkunan mu nan, na hada komai, bari ince ma Daada ta fito sai mu tafi.”

Kai Salim ya dan daga mata yana shiga cikin dakin sosai ya dauki jakunkunan nasu kamar basu da wani nauyi ya fice daga dakin. Ita kuma ta koma tana fada ma Daada ta fito su tafi. Sai da ta shiga dakin ta ta dauko wayarta sannan ta fito, tana kallon yanda Daada take daga kafarta tana saukewa dakyar, amman ba zata yarda ka kamata ba, in dai zata samu ta mike to zatayi tafiya ko yaya ne. Ita ta kulle ko ina tana sauke numfashi bayan ta fita kofar gida taga ta kulle nan ma. Tana juyawa ta ga Salim ya fito daga motar yana zagayowa ya bude ma Daada gidan baya ta shiga.

Ya mayar ya rufe sannan ya zagaya yana komawa mota, sanda ta taka ta shiga, tana rufe kofar taji yace ma Daada.

“Ya jikin naki Daada? Kan baya ciwo yau?”

Cikin yaren Fulatanci.

“Alhamdulillah, gashi ka ganni garas.”

Dan murmushi ya yi.

“Allah ya kara lafiya.”

Ya furta da hausa wannan karin, yana jan motar tunda daman yayi kwana kafin ya ajiye ta. Shi Madina take kallo tana son gane abinda yake damun shi a kwanakin nan, rashin maganar shi ya karu, sai suyi zaman awa daya baice mata komai ba, duk hirar da zatayi sai dai in idanuwanta nakan fuskar shine zata kula da yanda yake amsa ta da gira, kai ko nashi idanuwan da zai lumshe ya sake bude mata a kasalance. Salim najin idanuwan Madina da suke yawatawa a jikin shi kamar tana son budo duk wasu sirrikan shi.

Yana jin yanda kallon nata ke sa wani abu amsawa a cikin kirjin shi. Sharewa yayi kamar bai san tanayi ba har suka karasa gida. Kamar wanda yake kan kaya haka ya fice daga motar da sauri. Shi ya bude ma Daada da tace mishi.

“Da ba sai na fito ba tunda zamu juya ne… Ko ba yanzun za’a tafi ba?”

A kasalance Salim ya kalle ta.

“Ki fito Daada, ko ruwa ki sha, ki dan mike kafafuwan ki kafin kowa ya shirya, ba zakiyi ta zama a mota ba.”

Har zuciyar ta zaman motar zata zaba in da wani abu a muryar Salim ya bata damar hakan. Amman tsaye yayi yana jiranta, dole ta sauko da kafafuwanta daga motar. Rabonta da gidan tun bikin Adee, shima ba dadewa tayi ba. Tunda har gida mijin Adeen yaje ya gaishe da ita, ko yanzun yakan biyo lokaci zuwa lokaci, bai taba zuwa mata hannu biyu ba. Zatace yana da kirki, amman ta san kirkin na shine ya hadu da yanda Adee ta nuna mishi darajarta. Sai da yaga ta fito ya rufe murfin motar. Madina ma fitowa tayi ta zagayo suna jerawa da Daada.

“Jakar ki Mug…wacce ce jakar ki?”

Salim ya tambaya ganin ta bi Daada.

“Babbar…”

Ta amsa mishi a takaice batare da ta juyo ba tunda ta san zai biyo su. Tare suka shiga har falon gidan suna dan hira da Daadar. Madina ce tay sallamar da Saratu ta fito tana amsawa, fara’ar da take fuskarta na ragewa da ganin Daada.

“Ina wuni…”

Ta furta a hankali tana dorawa da.

“Ya karfin jikin? Ku zauna mana Madina.”

Zaman Daada tayi sannan ta amsa gaisuwar da Saratu tayi mata, Madina na gaishe da ita.

“Ina jakar?”

Dan juyawa Madina tayi dai-dai shigowar Salim da yayi sallama cikin sanyin murya. Saratu ta karasa tana kai hannu zata karbi jakar hannun Salim din.

“Ina zan kai?”

Da hannu ta nuna mishi hanyar dakin da nashi ne a cikin gidan kafin ya bar bangaren ya koma in da yake yanzun. Can kuwa ya nufa ya kai jakar ya dawo falon

“Ina Daddy?”

Ya bukata, dan murmushi Saratu tayi.

“Yanzun zaka ga ya shigo.”

Ta kirashi bai dauka ba, daman bata sa ran zai dauka ba, idan da ta kira fiye da sau daya zai san dole akwai wani abu muhimmi. Ace kai da mijin ka ba zaka kira kaji lafiyar shi ba, ba zaka kira ka tambaye shi wani abu ba balle kasa ran zakuyi hira idan yayi maka nisa. Bakowa bane zai fahimci ciwon abin sai macen da take cikin irin halin da take ciki.

“Madina a zubo muku abinci mana.”

Saratu tace tana maida hankalinta kan su, kai Madina ta girgiza,

“Ko zaki ci Daada? Baki ci wani abu mai yawa ba fa.”

Kai Daadar ta girgiza a hankali.

“Ni kam banajin yunwa fa.”

Numfashi Saratu ta sauke.

“Bari a kawo ruwa to.”

Tayi maganar tana nufar hanyar kitchen, bata jima ba ta dawo da ruwa da kofi, Madina ta karba ta zuba ma Daada tana mika mata. Karba tayi ta dan kurba ba dan tana jin kishi ba, ta ajiye kofin a kasa. Sai lokacin Madina ta kula da Salim ya bar dakin, sai Saratu da ta samu kujera can nesa da su ta zauna. Wani irin shiru marar dadi na lullube dakin, su duka ukun an rasa wanda zai ce wani abu. Sai dai motsin Madina da kan gyara zamanta lokaci zuwa lokaci. Ta ji dadi da Saratu ta mike ta kunna kayan kallon da suke cikin dakin tana daukar emote ta koma in da ta tashi ta zauna.

Sai ita da Madina suka maida hankali kan labaran, Daada kuwa kara shigewa tayi cikin kujerar da take zaune, kanta cunkushe yake da tunani kala-kala. Ko shigowar Julde bata ji ba sai muryar Madina da take gaishe da shi.

“Daada kun gama shiryawa ko?”

Ya bukata yana murmushin da kallo daya zakai mishi kasan na karfin hali ne, kai Daada ta daga mishi a hankali tana mikewa. Sai take ganin kamar ta dade bata kalle shi ba, kamar duk shekarun nan akwai wani labule a tsakanin idanuwan ta da shi da yake hana mata ganin shi irin yanda take ganin shi yau. Ba Julden da yake da mata da yara ba, ba Julden da ake ma kallon babban mutum a wajen kasuwan ci da cikin unguwa ba. Julde take kallo shi kadai batare da duk wannan abubuwan ba, dan ta take kallo yau tana jin littafin da ta dade da rufewa a cikin kanta yana budewa kafin ya tsaya a wani shafi da yake da muni a rayuwar su gabaki daya.

Duk shekarun nan, watannin da suke a cikin shekarun, ranakun da suka dinga zuwa suna wucewa bata san dalilin da sai yau ba, sai yau ta zabi ta kalli Julde da idanuwan da tayi mishi alkawarin ta kauda su da kan shi har abada.

“Allah ya tsine maka albarka Julde. Allah ya kunyata ka a idanuwan zuri’ar ka yanda ka zame mun abin kunya!”

Idanuwanta ta runtsa, gabaki daya kirjin ta na daukar dumi kamar an hura mata wuta a ciki.

Me yasa sai yau? Shine tambayar da bata da wanda zai amsa mata. Ta kuma kasa daina kallon shi. Ko da ta runtsa idanuwan, tana bude su akan shi suka sauka, sai dai yanzun taga kamar yana cikin wani abune mai kama da kwallon kafa, amman duhun abin bai hanata ganin shi a tsaye a ciki ba, kamar yana tsaye ne a cikin tsinuwar mahaifin shi da take jiran cikar lokaci ta fashe tare da shi. Da Madina bata riketa ba da kafafuwanta sun kasa daukar ta saboda firgicin da ya ratsa ruhinta.

“Daada ba dai jikin bane ba?”

Madina ta bukata cike da kulawa da kuma damuwa, kai kawai Daada take girgiza mata, addu’ar duk da tazo mata karantawa takeyi tana neman samun nutsuwa. Haka suka lallaba suna fita waje. Saratu daga bakin kofa tayi musu fatan Allah ya kiyaye hanya, lokaci ya koya mata kama kanta da kinyi musu abinda ta dauka a matsayin shisshigi a cikin rayuwar su. Tun farko Daada bata karbeta ba, tayi biris da cewar ko da bata auri Julde ba jinin da yake yawo a jikin ta yana yawo a jikin shi, ita din dangin shi ce ko da aure bai hada su zumunci ba.

*****

“Hamma kana soka mun kashin hannun ka a hakarkari na fa.”

Nawfal yai maganar yana sake gyara zaman shi. Motar da Julde ya so su dauka ya manta rabon da ya hau ta, kin tashi tayi, Daada, Madina da Salim baya suka shiga su. Khalid ya bude ta bangaren da Salim yake ya watsa mishi wani kallo da yasa shi mayar da murfin yana rufewa hadi da furta.

“Allah ya baka hakuri.”

Ta kasan makoshi, zagayawa yayi ya koma gaba in da Nawfal yake zaune.

“Ka dauko motar ka mana, matsewa fa zamuyi anan…dan Allah ka dauki mota Hamma.”

Amman Khalid yaki sauraren shi.

“Zaka matsa ko sai na kwade ka.”

Nawfal turo labba yayi yana kallon Julde da ya shiga mazaunin direba ya rufo kofar.

“Daddy kace Hamma ya dauki motar…”

Bai rufe baki ba yaji Khalid din ya turmotso rabin jikin shi akan na Nawfal.

“Kasheni zakayi ne wai, ka tsaya in matsa maka mana.”

Ya karasa yana ture hannun Khalid har yana gabje hanci da murfin motar da yake kokarin jawowa ya rufe.

“Wai dan uban ka Bajjo ni sa’anka ne?”

Sake tura shi Nawfal ya yi.

“Daddy kaji Hamma na zagi ko?”

Da kyar Khalid ya rufe murfin motar, yanda suke tutture juna zaka dauka yarane yan shekara bakwai ko kasa da haka. Murza kan shi da yake ciwo Salim yakeyi tun da suka fara.

“Bajjo ku fita daga motar nan.”

Ya furta babu alamar wasa a muryar shi, nutsuwa sukayi.

“Ba ku jini ba kenan.”

Ya sake maimaitawa.

“Daddy kace ya barmu dan Allah, ba munyi shiru ba.”

Khalid ya fadi, numfashi kawai Julde ya sauke, ya riga da ya koyi shiru ya kyale su, tuntuni kamar suna Khalid da Nawfal na ganin hanjin juna wasu lokuttan, sun girma, Nawfal harda mata amman ba zasu daina fada kamar yara ba. Da Salim yakan bar su tunda can ma. Yau bashi da karfin surutun kwata-kwata shisa yaja motar suka tafi. Da suka ga an hau hanya shine suka cigaba.

“Wallahi zaku sauka a hanya ku biyo mu a napep. Maganar da zan karayi akan ku sai kun sauka daga cikin motar nan.”

Salim ya fada, saboda Daada na tare da su, kuma a tsakiya take zaune. Madina ce ta bangaren da su Nawfal din suke zaune, daga inda yake zai iya mika hannu ya kai musu duka, amman baya son su duka su gwada hali a gaban Daada. Kan shi har juyawa yake saboda surutun da sukeyi. Amman dan su san da gaske sauka zasuyi shisa ya rantse suka ji, yana kallon Nawfal na ture hannun da Khalid yake kara dora mishi. Madina kanta murmushi takeyi, tana son ganin Khalid da Nawfal a tare, fadan su nishadi yake sakata, ko yanzun ma sun saukaka mata damuwar da take ciki.

Su dukan su basu kara nutsuwa ba sai da suka fita suka shiga cikin filin jirgin, suka tsaya inda zasuyi sallama da su Daada, lokacin tsoron da yake tare da Nawfal ya fito shimfide akan fuskar shi.

“Kace zaka biyo mu Daddy?”

Yayi maganar yana kallon Julde da ya daga mishi kai, Madina karasawa tayi ta rungume Daada tana jin wasu hawaye masu dumi na zubo mata.

“Karki karya ni Madina.”

Sake riketa tayi gam tana jin kamar ace in ta raba jikinta da na Daada zata taho da dumi da kamshin Daadar a tare da ita, iya wanda zata rike har sai ta dawo.

“Allah ya dawo mun dake cikin aminci Daada… Ina son ki sosai… Kin sani ai ko?”

Kai Daada ta daga tana kama Madina ta rabata da jikin ta.

“Bajjo zai kira mun ke ta hoton nan yanda naga kunayi.”

Hannu Madina ta sa tana goge fuskarta, sai da ta dan ja hanci sannan tayi murmushi.

“Video call Daada”

Dan daga idanuwa Daadar tayi.

“Oho ni ban san sunan shi ba.”

Dariyar karfin hali Madina tayi, wasu hawayen na sake zubo mata, hawayen da Salim yake ji har kasan ran shi. Shisa ya saka hannuwan shi cikin aljihu saboda kaikayi suke mishi, kaikayin ya rikota ya hadata da jikin shi ya lallasheta ta sigar da yafi kwarewa.

“Hamma sai mun dawo.”

Nawfal da yake tsaye gefen Daada ya fadi yana sa Salim janye idanuwan shi daga kan Madina yana mayarwa kan shi.

“Allah ya tsare…komai zaiyi dai-dai ka sani ko?”

Kai Nawfal din ya jinjina mishi, sallama suka kara yi gabaki daya, su suka fara juyawa suna barin Daada da Nawfal a tsaye. Madina ce ta juya tana daga ma Daada da taji zuciyar ta ta tsinke hannu, lokaci daya taji tsikar jikinta ta mike. Murmushi Madina tayiwa Nawfal da suka hada ido, sai dai zuciyar shi tayi nauyin da ya kasa mayar mata da martani har ta juya, yabi bayan ta da Kallo, da yanayin tafiyar ta.

Kallon ta Nawfal da Daada sukeyi.

Kallon ta Nawfal yake yi batare da ya san kaddarar da take bibiyar su ta kusan cika ba.

Kallon ta yake batare da ya hango doguwar igiyar da take shirin kulle su a waje daya ba.

Haka ya ga Salim yayi dabarar tsayawa Madina ta karasa suka jera tare, yanda ya juyar da kai na tabbatar ma da Nawfal din magana yayi ma Madina.

Salim magana yayi mata kamar ba su da wata damuwa da ta wuce jiran dawowar Daada. Nawfal ya fara juyawa ya na ba Daada passport din su ta rike, ya dauki jakarta ya dora kan akwatin shi yanda zasuyi mishi saukin ja, sannan ya kama hannun ta yana fadin,

“Muje Daada…”

Tana tunanin me likitoci zasu gani idan sun bude kirjin ta saboda zuciyarta na tare da su Madina, gabaki daya zuciyarta da ta kasa nutsuwa na tare da su. Haka tabi Nawfal suna tafiya, tana jin littafin da yake cikin kanta yana bubbudewa yana komawa shafin farko, takun duk da zatayi da nufin barin garin na zamar mata adon da yake janta don ta waiwayi in da komai ya fara..!

Allah ya sadamu da alkhairin shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 19Rai Da Kaddara 21 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×