Skip to content

Rai Da Kaddara 1 | Babi Na Biyu

5
(2)

<< Previous

Kamshin turaren shi ya fara cika mata hanci ta zo juya kwanciya, dan tana daya daga cikin mutanen da in har zasuyi juyi komin baccin da suke sai sun farka. Wani lokacin ma sai ta tashi zaune, kamar yanzun dinma haka ta faru da Saratu. Idanuwanta ta sauke akan Julde cikin shaddar shi ruwan toka da tayi matukar amsar farar fatar shi, agogon da yake manne jikin bango ta kalla tana ganin karfe sha daya harda wani abu na dare.

“Ina zaka cikin daren nan?”

Ta bukata tana jin wani abu da ya tokare mata makoshi. Sai da tayi tunanin ba zai amsa ba, dan har hula sai da ya saka sama kan shi batare da ya juyo ba ya ce,

“Yaushe inda zanje ko karfe nawa ya fara damun ki?”

Gyara zamanta tayi, dan batayi magana akai ba baya nufin abin baya damunta. Halayen shi kaf ta san su, zata rubuta littafi akan halayen nashi da ko shi ya karanta sai ya sha mamaki. Yau dinma bata san me yasa take son mishi magana kan fitar da zaiyi ba, tafi alakanta hakan da gajiyar da take jin tayi da halayen shi a satukan.

“Karfe sha daya na dare, idan ba maza masu aikin kwana ba, kowanne namiji mai mutunci yana tare da matar shi…”

Numfashi ya sauke yana dan tabe bakin shi, surutun ta ko a jikin shi, ita dinma bawai ta dame shi bane ba balle kuma abinda ya fito daga bakinta .

“Me kake tunanin Daada zatayi idan taji babu wani abu daya canza daga halayen ka? Sai ma abinda yayi gaba?”

Wannan karin juyawa yayi ya kalleta da murmushi dauke akan labban shi.

“Babu abinda zatayi tunani saboda ba zaki fada mata ba, saboda zaman ki a cikin gidana yafi miki komai muhimmanci, kuma fadama Daada abune da zaiyi barazana da zaman.”

Abinda yake tsaye a makoshinta take kokarin hadiyewa amman yaki wucewa, tana kallon shi ya dauki mukullin motar ya fice daga dakin hadi da ja mata kofar. Runtsa idanuwan ta takeyi tana bude su da sauri-sauri cikin son mayar da hawayen da suka cika su taf. Ta gama kuka akan Julde, ta gama zubar da hawayenta akan kishin shi, ba zai zamo karshenta ba. Bata san ko tun farko bata nuna mishi wadatacciyar soyayya bane shisa yanzun yake ganin duk wani abu da zatayi domin kudin shine, dan arzikin da yake da shi.

Ko kanta ba zata yaudara ba, tana son rayuwar hutu, tana jin dadin kudin da yake da shi, sauyin da rayuwarta ta samu a tare da shine babban cigaban da zata mutu tana alfahari da shi. Shisa bata son taga kwandala ta fita daga aljihun shi da sunan yiwa wani alkhairi bayan ita da yaran su. Har wani duhu take ji ya lullube mata idanuwa saboda bakin ciki. Amman hakan baya nufin bata son shi, tana son shi, tana jin soyayyar shi a ranaku mabanbanta, yau na daya daga cikin wadannan ranakun. Ko da ba zasu kasance da juna cikin raya daren ba taso duk juyin da zatayi taji shi a kusa da ita.

Kamshin shine gauraye da dakin, kamshin da zai cika dakin wata ko dakin otel a tare da wata da ba ita ba. Dumin shi da take son ji fiye da komai a daren shine wata zata kwana tana mora. Ta ya zata ce abin baya mata ciwo? Ance lokaci na sa ka saba da abubuwa da yawa, amman kullum Julde saiya karyata mata hakan, saiya nuna mata ba zata taba sabawa da halin bin matan shi ba. Duk yanda take kishin shi, duk yanda bata son wani ya rabar mata shi bai hanata tsugunnawa kan gwiwoyin ta ta roke shi daya kara aure ba.

“Idan uku zaka kara dan Allah ka karo, da wannan biye-biyen da kakeyi ka karo uku ka ajiye mu zama mu hudu, zamu isheka, mun isheka Julde, dan Allah…”

Murmushin da baka raba fuskar shi da shi yayi mata, ko ranshi a bace yake kuwa zaiyi murmushi.

“Ajiye mata hudu ba zai hanani hangen wasu ba Saratu, ke dinma ya na kare dake? Aure, yarana kawai da nake kallo suke hanani dana sanin zaman aure dake, ko dan irin wannan surutan da kike yawan yi mun. Zan sake maimaita miki in ba zaki iya zama dani ba furtawa kawai zakiyi…kiyi harkarki inyi tawa, zaki iya nemar mun shiriya idan kina da wannan lokacin, in baki dashi kibar ni da halina…”

Ba dan tana da wani ilimin addini ba, sallah da tsarki ma yanda zatayi su a tsarin addini a gidan Radio ta koya. Anan taji kalar kuskuren da take tafkawa a rayuwarta, amman zata iya cewa jahilci na daya daga cikin babbar cutar da take damun Julde. Watakila da yayi makaranta, ta boko ko ta addini zai rage wasu abubuwan. Yanzun ma lokaci bai kure mishi ba idan har yayi niyya, tunda ita ma takan saurari kasa-kasai da ta siyo na wa’azi kala-kala kuma tana karuwa. Shisa halayen shi suka hadu suna mata ciwo biyu yanzun, kishin shi da kuma matsayin abinda yakeyi ga makomar goben yaran su.

Komawa tayi ta kwanta, bata koyi kokarin share kwallar da take zubo mata ba. Sosai kirjinta yake zafi, musamman da zuciyarta ta shiga hasaso mata hotunan inda Julde yake da abinda yakeyi. Idanuwanta taji sun bushe rayau, ko alamun bacci babu. Tana jin hawayenta tun suna zuba har suka daina, banda ajiyar zuciya babu abinda takeyi, ko juya kwanciya batayi ba, ta dai ja jikinta sosai ta dunkule waje daya ko zata samu saukin zafin da kirjinta yakeyi. Ba duba agogo takeyi ba balle ta san ko karfe nawa, kawai dai taga daren yayi mata wani irin tsayi ne. Kiran sallar asuba kawai take saurare taji an turo kofar.

Tana jin kai kawon shi, tasan kayan jikin shi yake ragewa. Bata dai motsa ba, kwan dakin daya kunna kafin ya fita yaje ya kashe ya dawo yana hawa gadon. Jin da tayi ya rikota yana juyawa da ita ta fuskance shi ya sa ta fara kiciniyar kwacewa, sai dai karfin su sam ba iri daya bace ba, ko sirantaka irin ta yawancin fulani Julde ba shida ita, ba zaka kira shi namiji mai jiki ba, amman dogone na misali, ko ina a jikin shi bai nuna rama ba.

“Kina son gwada karfi dani Saratu, in kin ganni a irin yanayin nan ki daina mun gardama kar inji miki ciwo wata rana.”

Wasu hawayen ne masu zafi taji sun cika mata ido, da daudar zinar daya kwaso yake neman hada jiki da ita, ko wankan tsarki baiyi ba, lokacin da taji yanda zata tsarkake jikinta tayi kokarin ganin shima ya sani, kwanaki ta jera kullum sai ta karanta mishi yanda zai tsarkake najasar da yake yawo da ita, bai nuna mata alamar ya dauka ba, amman yaji ta, kuma tana fatan ya dauka din.

“Dan Allah ka kyaleni…”

Ta furta a raunane, ta san halin shi, abinda yayi niyya ba zai fasa ba, kuka takeyi sosai, kukan ta bai karu ba sai da bayan ya gama abinda yayi niyya ya juya mata baya cikin wani irin yanayi da ya fito da tsantsar kunar rai ya furta.

“Babu kamar Mero, har yanzun banji irin Mero ba.”

Kamar ita tayi sanadi ko ta zama dalilin da ya rasa Mero kuma ya kasa samun madadinta ba har yanzun. Kukanta kara mishi kunar rai yakeyi. Mata uku ita cikon ta hudu a dare daya amman ko kusa da natsuwar da yake samu da Mero basu kusanta ba balle su cike mishi ramin da ta bari. Akan yaran shi yasan menene soyayya, akan Nawfal yasan asalin kauna da dukkan zuciyar shi. Mace, ita din a wajen shi kamar riga ce da zai saka wadda yake so don biyan bukatar shi ya cire ya sauya a lokacin da yayi niyya. Me yasa Mero ta kasa barin ran shi? Zuciyar shi babu wajen kaunar wata mace banda Daada, amman yana jin wani rami a cikin kirjin shi inda baisan Mero ta zauna ba sai da tabar shi.

“Baka taba sona ba Julde, da akwai soyayyata a ranka ko yaya ne ba zaka zubar mun da mutunci har haka ba, ba zaka mayar dani abin nunawa a dangi ba…”

Maganar Mero ta dawo mishi tana saka shi runtsa idanuwan shi yana hango fuskarta, idanuwanta, jan bakin da baka raba labbanta da shi. Ita da kanta ta fada mishi baya son ta, me yasa zata manne mishi har haka? Mata nawa ya sani kafin ita? Mata nawa ya sani bayan ita, me yasa ta fita daban? Me take da shi da ya kasa samu tare da sauran? Kullum, tun bayan ita kullum saiya nemi gamsuwar da yake samu da ita a tare da mata daban-daban amman ya kasa samu. Baya bibiyar mata da yawa haka kafin Mero, ta sake bude mishi sabon shafin da babu kalaman da zasu iya fasaltawa.

Bai bude idanuwan shi ba har bacci ya dauke shi cike da mafarkin Mero, ya kuma bude su da wayewar gari cike da tunaninta. Da yake Juma’a ce shi yake kai yaran makaranta in ba wani babban uzuri ba, a gaggauce yayi wanka ya shirya sannan yayi sallar asubar da ba kullum ya damu daya sameta a cikin jam’i ba. Duk tare suka karya yana hira da yaran kamar bashi da wata matsala in har yana ganin su a kusa da shi. Salim ne dan shi na farko, Fadila da itace ta biyu kuma tana makarantar kwana ta Science and Technical da take nan garin Kano, Khalid sai Lukman.

Suna gamawa ya saka su a gaba suna fita tare, daya sauke sune ma Khalid yace mishi.

“Daddy idan na dawo zanje gidan Daada acan zamuyi Weekend tare da Bajjo…”

Khalid din ya karasa yana kallon Julde da yake girgiza kai.

“Har kwana biyu zaku je kuyi, ka dai je idan na dawo daga kasuwa da dare in biyo in dauke ku… Shima Nawfal din zan hadu da shi daya tafi bai fada mun ba.”

Gardama ba halin Khalid bace ba, duk a cikin yaran shi kadaine ba zai ja magana sau biyu da babba ba. Hakan yasa shi jinjina kai kawai yayi ma Julden sallama yana bin bayan yan uwan shi ya shige cikin makaranta. Julde kuma yaja motar shi yana nufar kasuwa, zuciyar shi tayi mishi nauyi fiye da kowanne lokaci.

***** *****

Yanda yake cin abincin Daada take kallo, ya tattara hankalin shi kamar bai taba yin wani abu mai muhimmanci kamar wannan ba. Tausayin shine cike da zuciyar ta, daren jiya da ta zubo mishi taliya da miyar kifin da tayi ta zallar tumatiri da albasa taga ya kalleta.

“Tumatir ne kawai da albasa Bajjo.”

Ta fadi tana kiran shi da sunan da ta makala mishi kasancewar shi da daya tilo a wajen mahaifin shi. Tana dadewa bata kira shi da Nawfal ba. Tana gani ya saka cokali ya fara dibar miyar da kifin yana kaiwa bakin shi, saida ya sauke numfashi tukunna ya fara cin abincin. Yau ma haka, kwano ta samu daban tana zuba mishi miyar da tayi saboda shi kawai.

“Daada abincin nan yayi mun dadi.”

Cewar Nawfal yana jin kamar ya samu waje ya adana dandanon abincin ya dinga daukowa yana tunawa a ranakun da zaici mai da yaji ko ya sha shayi saboda Nanna ba zatayi abincin da zai iya ci ba. Ya dade idan ya kalleta yana so ya tambayeta laifin shi, yana so yaji me ya taba yi mata mai zafi da ta dauki karan tsana ta dora mishi ba.

“Yarana da gidan uban sune ma abinda na dafa shi suke ci, ba zaka sakani girki biyu saboda baka cin yaji ba wallahi, ba zan iya wannan jidalin ba.”

Ta kan yawaita fada mishi, ko a makaranta Nawfal Bukar yake amfani da shi ba Isiyaku ba. Ya san bashi bane baban shi ko bata tuna mishi ba, amman shi din yake ma kaunar da ya kamata yayi wa baban shi da bai san komai game dashi ba bayan suna. Sai dai abu na farko daya fara koya bayan magana shine yin shiru, akan abubuwa da yawa, musamman abubuwan da suka fi karfin fahimtar shi, da kuma wanda suke damun shi. Shiru yafi komai saukin yi, furta wasu abubuwan baya kawo gyaran su, ya taba furtawa Julde cewa Nanna tace gidan ba gidan uban shi bane ba.

Fadan da sukayi a gaban idanuwan shi harya mutu ba zai manta ba, yana da tabon dukan da Saratu tayi mishi a bayan shi har gobe. Shiru yafi komai sauki a wajen shi, yanzun ya kara fahimtar duk abinda ake so yaji za’a iya fada mishi ba saiya tambaya ba, abinda yake son ji kuwa koya tambaya idan ba’a son fada mishi ba zaiji ba.

“Kar dai ka fado daga kujerar nan wajen santi.”

Daada ta fadi tana mishi dariya.

“Ba dai zai hanani yabon girkin nan ba dan yayi mun dadi… Idan zan tafi kika dibar mun miyar nan zata dade bata lalace ba?”

Kallon shi Daada tayi.

“Zata iya kwana biyu dai tunda ba sake dafawa zakayi ba, ko akwai fridge a dakin ku?”

Kai ya daga mata saboda ya cika bakin shi da shinkafa.

“To bari sai ka karo kayan miya da kifin in maka da yawa, idan kaje saika saka cikin fridge ka dinga diba.”

Murmushi yayi, matsayin Daada daban yake a wajen shi, ko ganinta yayi sai yaji wani sauki a cikin ran shi. Da duk wani abu da zatayi kuma da yanda take faranta mishi. Mikewa tayi tana shiga daki ta fito da hijabi a hannunta.

“Gara inje barkar nan sai ma in biya in taho da Madina…”

Cewar Daada tana saka hijabin ta.

“Kibari zanje in dauko ta.”

Kai ta girgiza mishi .

“Ba nisa da inda zanje… Sai na dawo.”

Kai Nawfal ya daga

“Allah ya tsare. A dawo lafiya”

Daada ta amsa tana ficewa daga dakin. Abincin shi ya gama ci ya dauke kwanonin ya kai kitchen, ya dawo ya zauna yaji sallamar Khalid daya amsa, uniform din da yake jikin Khalid din na tabbatar mishi daga makaranta kai tsaye nan din ya nufo.

“Da baka jirani mun taho tare ba gashi na zo ai.”

Dariya Nawfal yayi

“Ka kyauta. Daman bance ba zaka zo ba ai, kawai jiyan na so tahowa…”

Takalma Khalid ya cire yana sake yin sallama ya shiga cikin falon, jakar shi ya fara saukewa dan a cikin ya zubo duk wani abu da yake tunanin zai bukata, yaji me Julde yace, amman yasan wahalar dai yazo gidan Daada. Idan ta saka baki dole yabar su su kwana biyu. Fada ne Nanna zatayi idan ya koma, to ko bai zo ba Nannar shi ba zata rasa dalilin yin fada ba, shisa bai koma ta gidan ba yayi tahowar shi, zaice mata Daddy ne yabar shi.

“Ina Daada?”

Ya tambaya

“Wai zatayi barka sai ta taho da Madina daga makaranta kuma…”

Kai Khalid ya jinjina yana mikewa.

“Ni yunwa nake ji.”

Kitchen ya wuce ya zuba abinci iya wanda yake tunanin zai iya cinyewa yana hadowa da wani filet din daban ya dawo falon, kan kafet ya zauna ya ajiye filattan a gaban shi yana janyi jakar shi ya bude. Mangwaro ne manya guda biyu ya dauko.

“Mangwaron ne a jaka Hamma?”

Nawfal ya fadi yana dorawa da

“Ko dan meye ba za’a samu a jakar ka ba.”

Dariya kawai Khalid yayi, inda sabo ya saba jin suna mishi wannan surutun. Kawai yafi yarda da ya saka duk wani abu da yake tunanin zai iya bukata a cikin jakar shi ta makaranta. Har paracetamol zaka samu cikin jakar, inka tambaya zaice maka.

“Idan naji kaina yana ciwo fa? Tunda ba sanar dani zaiyi kafin ya fara ba.”

Akwai ranar da suke dawowa daga islamiyya takalman Salim suka tsinke. Khalid ya zage aljihun gaban jakar islamiyyar shi ya zaro takalma silifas yana mikawa Salim din yayi gaba abin shi. Su duka binshi sukayi da kallo na wasu dakika kafin su kwashe da dariya. Wata rana dan tsokana ko sabulu ne ya kare musu a bandaki zakaji suna.

“A duba jakar Khalid ba za’a rasa ba.”

Shiru yake ya kyale su kamar yanda yayi ma Nawfal din yanzun. Abincin shi ya gama ci ya tashi da filattan yana zuwa ya wanke mangwaron, a fridge ya saka saboda Nawfal ya siyo daman, ya kuma san ba zai sha ba sai yayi sanyi ko yaya ne, idan ma yayankawa akayi zai dauki na shi ya saka a fridge. Yanda Nawfal baya mura har mamaki abin yake ba Khalid, idan ya sha sanyin da Nawfal yake sha na rana daya a sati saiya kwanta gadon asibiti. Da ya fito ma bai zauna ba, dakin da suka saba sauka ya nufa, wanka yayi ya fito ya dawo falon daga shi sai gajeran wando.

“Geez Hamma…”

Nawfal ya fadi yana kare idanuwan shi, kallon kan shi Khalid yayi, yanda Nawfal din yayi wani zai iya zaton babu kaya Khalid ya fito, karamin tsaki yaja.

“Kasan shekara bata fi daya ba a tsakanin mu ko? Ba zaka daina ce mun Hamman nan kana dora mun girma ba.”

Batare da Nawfal ya sauke hannun shi daga kare idanuwan shi da yayi ba ya ce,

“Ka dai girmeni, zan daina in ka daina ce mun Bajjo.”

Wucewa kawai Khalid yayi abin shi. Mikewa shima Nawfal din yayi, sai da ya kara watsa ruwa, lokacin daya fito har Khalid ya gama shirin shi ya fita. Shima shiryawa yayi cikin farin yadi harda hula bula ya saka kamar takamin shi daya dauko. Kafin ma ya fito yaji dawowar su Daada saboda rakadin Madina da take kwala mishi kira, sanda ya fito Khalid na fadin.

“Lallai Madina, kamar baki ganni ba ko?”

Ko kallon shi batayi ba ta ruga da gudu tana fadawa jikin Nawfal hadi da zagaya hannuwanta jikin kafafun shi.

“Hamma na dauka ka tafi kabarni.”

Kanta ya shafa

“Nace miki ina nan har ki dawo makaranta ai… Masallaci dai zamu tafi ni da Hamma yanzun mu dawo, me zan siyo miki?”

Daga kai tayi tana kallon fuskar shi

“Biskit”

Khalid da yake zaune ya ce,

“Ni ina da biskit din ai, ba zan baki ba tunda baki kulani ba.”

Juyawa tayi ta kalli Khalid.

“Hamma na zai siyo mun ai dai, ko Hamma?”

Kai Nawfal ya jinjina yana dariya.

“Ki je ki cire uniform, Daada tayi abinci mai dadi.”

Murmushinta ne ya fadada.

“Tuwo ta dafa?”

Wannan karin har Khalid dariya yayi da Madina bata ga dalilin su nayin dariya ba. Nawfal yace anyi abinci mai dadi, shisa tayi tunanin tuwo ne.

“Shinkafa”

Lokaci daya fara’ar fuskarta ta dishe tana raba jikinta da Nawfal din.

“Shinkafa kuma”

Ta furta ranta a bace tana sake saka su dariya. Daki ta wuce harda jan kafafuwa a dole ranta ya baci da aka dafa shinkafa ba tuwo ba.

“Daada zama dake yarinyar nan kaf ta kwashe halin tsofaffi, ace ga shinkafa amman tuwo ne a ranta.”

Khalid yace yana dariya.

“Ku da bakuyi halin tsofaffin ba ai sai kuyita fama da shinkafar ku, amman ni tuwo zan mana anjima.”

Mikewa Khalid ya yi.

“Tafdin, aci tuwo lafiya…” Dan shi baya so, tuwo da danwake na cikin abincin da yunwar da zata saka shi cinsu ba karama bace ba. Sallama suka yiwa Daada suna fita masallaci.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.