Skip to content

Rai Da Kaddara 1 | Babi Na Hudu

3
(2)

<< Previous

Idan yaji ana cewa lokaci na gudu ada sai yayi ta mamaki, saboda shi sam baya ganin gudun lokaci. Musamman idan yana gida, yini daya sai ya zame mishi kamar yini biyu. Amman wannan karin zai saka baki idan ana maganar gudu na lokaci, saboda da gaske kamar idanuwan shi ya rufe a aji hudu ya bude su ya ganshi yana zana jarabawar gama sakandire ta aji shidda da ake kira da WAEC. Randa suka zana ta karshe sai yake jin abin kamar a mafarki, har Julde yaje ya dauko su bai dana jin shi kamar a mafarki yake yawo ba.

Sai dai ya koma kirga kwanakin da suka rage mishi a cikin gidan. Adee ta samu gurbin karatu a jami’ar Wudil, nisa ta sake yi musu.

“Ga BUK, me yasa sai Wudil? Quantity Survey din ne basu da shi a BUK?”

Ya tambayeta, bai taba zuwa Wudil ba, amman yasan kauye ce, kuma yaji wani a ajin su yana magana cewa babu mata da yawa a makarantar, duk wani abu da zata takura baya son shi sam. Murmushi kawai tayi.

“Ka ce mun BUK zaka je kaima Bajjo, in har can din zaka sai in hakura da Wudil…”

Shirun da yayi murmushin Adee kawai hakan ya fadad,a

“Idan kana gida zan dinga kokarin dawowa weekend in shaa Allah.”

Bai dai sake cewa komai ba, burin shi mai girma ne, bai kai da furtawa ba. Amman nisan da zaiyi wa gida da sunan karatu ba zai tsaya makarantun da suka sani ba. Ya fi kowa jin rashin Adee a cikin gidan, dan ma yanzun Julde kudin kashewa yake basu kusan kullum, ba zaici yana da matsalar abinci ba. Mai dadine kamar wanda Adee zata tsaya ta dafa mishi sai dai yaje gidan Daada yake samu. Islamiyya da ya koma yanzun bashi da lokaci mai yawa na zuwa gidan. Yanzun ma daya taso masallaci ya wuce yayi zaman shi yana nazarin darussan da akayi na ranar har sai da yayi sallar Magriba da Isha’i tukunna ya dawo gidan.

“Ina kaje tun dazun?”

Khalid da yake kwance cikin kujera ya tambaya,

“In da ka aikeni?”

Ya amsa yana wucewa, dakin su ya nufa ya ajiye jakar makarantar shi, ruwa ya watsa ya sake kaya sannan ya sake fitowa yana nufa kitchen, fridge ya bude yana ganin robobin ice cream din shi har biyu inda ya bar su tun daren jiya. Guda daya ya fiddo yana mayar da fridge din ya rufe ya karasa ya dauki cokulla har biyu ya dauraye su, yana daukar wani plate shima ya dauraye ya taka zuwa falon, teburin da ke tsakiyar dakin yaja zuwa kusa da kujerar da zai zauna ya ajiye plate din ya dora cokullan a sama yana ajiye robar ice cream din shi a gefe.

Sake komawa daki yayi ya dauko kifin gwangwani guda biyu tukunna ya samu waje ya zauna. Gabaki daya Khalid hankalin shi ya mayar kan Nawfal da yake bude kifin harya juye shi cikin plate, gani yayi ya bude robar ice cream din ya saka cokali a ciki, tashi zaune Khalid yayi.

“Jikin ka na shan wahala a hannun ka Bajjo, kifi da ice cream?”

In dai akan zabin abinci ne ya saba da surutun Khalid din, bude baki Khalid yayi zai sake magana shigowar Salim ta saka shi ya mayar ya rufe.

“Na dauka ba’a hada kifi da madara.”

Salim yayi maganar cikin sigar da bata bukatar amsa kamar yanda ya saba, kana iya amsa shi yayi maka kallon “Da kaina nake magana, me yasa kake amsawa?”. Kowa a gidan ya koyi zama da Salim, duk da haka kafadu Nawfal ya daga.

“Har yanzun ban ci da yawan da zai mun illa bane ina jin.”

Dan ba zaice ga ranar da yake hada shayi kuma da madara yaci da kifi ba. Kai Salim ya girgiza yana wucewa abin shi.

“Da gaske abin nan dadi yake maka?”

Hararar Khalid yayi yana cigaba da cin kifin shi hankali kwance. Yana gama cinye kifin ya mike ya dauke plate din ya kai kitchen, yana dawowa ya hangi Khalid da robar ice cream din shi ya dibo a cokali yana shirin kaiwa baki, da gudu ya karasa amman har Khalid ya kai cokalin cikin bakin shi.

“Ewww…Hamma…kace mun shine cokalin farko…”

Wuyan shi Khalid ya rike da alamu ke nuna dakyar ice cream din ya wuce ta cikin shi, fuskar shi a hade take gabaki dayanta, harya ciro cokalin kokarin tattara sauran dandanon ice cream din daya rage a bakin shi yakeyi amman ya kasa, hannu kawai ya iya dagawa Nawfal da ya dakuna fuska yana jujjuya robar hannun shi kamar zata sanar mishi idan Khalid din ya sha abinda yake cikinta fiye da sau daya. Kurkuro bakin shi Khalid yayi amman bai daina jin dandanon ba.

“Nawfal meye a robar nan?”

Asalin sunan shi da Khalid ya sa Nawfal din amsawa da,

“Ice cream”

Yana dorawa da

“Sau daya ka sha?”

Babu abinda ya tsana irin kurbi in kurba da abu a cikin kofi, ko kuma yana shan ice cream, ko yana cin wani abu kazo ka dauki cokalin ka ci da shi ka mayar a ciki, saiya ga kamar da sauran yawu a jiki ka mayar mishi. Idan Khalid na son ya bar mishi abu haka yake masa wannan rashin kirkin.

“Wanne irin ice cream ne wannan?”

Numfashi Nawfal ya sauke

“Chocolate mint… Me ya faru?”

Kai Khalid yake girgizawa, komai na Nawfal ya fita daban, kamar kullum dalilin da zai sake banbanta da mutane yake nema. Kamar McLean yayi kankara haka ice cream din yake.

“Sau daya na sha, na farko kuma na karshe da yardar Allah.”

Khalid yace muryar shi na fitowa a gajiye. Dariya Nawfal yayi

“Me ya samu ice cream din? Me ya faru? Ba dai zaka ce babu dadi ba.”

Wani irin kallo Khalid yake mishi

“Akwai dadi, a sha lafiya.”

Da murmushi a fuskar Nawfal ya nufi kitchen dan ya dauko wani cokalin, daga can dakin su ya wuce ba sai Salim ya dawo falon ya kore su ba. Ko da Salim ba zai fito ba lokacin baccin shi yayi, kome zaiyi da wuri yake yi ya gama, karfe tara idanuwan shi sun fara nauyi, har mamakin Khalid da zai iya kai karfe daya na dare zaune yana kallo yakeyi, kuma washegari ya tashi su tafi sallar asuba kamar lafiyar shi kalau. Shi kanshi zaiyi kamar an dora dutse, bacci na da muhimmanci a wajen Nawfal.

*****

“Daada…”

Ya kira muryar shi can kasan makoshi, hannu tasa tana share hawayen da suka kasa daina zuba daga idanuwanta, ya dauka da Julde zaifi samun matsala, sai dai soyayyar da ke tsakanin su da take tasiri akan Julde ko yaushe ita tayi nasara. Nawfal na ganin yanda tafiyar shi wani gari da sunan karatu ne karshen abinda Julden yake so balle kuma ace wata kasa.

“Cikin kudina, kai da Daada kunce ina da kudi, in dai zasu isa…”

Julde bai barshi ya karasa ba, da wani nauyi a muryar shi yace,

“Me yasa kake tunanin kudi ne matsala ta da tafiyar ka? Bajjo ina da kudin da zan fitar da ku dukan ku karatu kasar waje, ba kudin bane matsalata, nisan ka, nisan da zakayi ne damuwata.”

To ga damuwa fiye da wadda ya gani a tattare da Julde nan shimfide kan fuskar Daada, kukan da takeyi gabaki daya ya kashe mishi jiki, zuciyar shi daya ke tunanin ba mai raunanata kan tafiyar ce yake ji tana mishi rawa.

“Daada…”

Ya sake kira kamar hakan zai isar da sakon da baisan ta inda zai fara fada mata shi ba. Yana bukatar tafiyar, jin shi yake kamar yana cikin wata yar karamar kwalba, watakila tafiyar ta fito da shi daga cikinta, duniyar shi yar karama ce, haka ma mutanen da suke cikinta. Ba fadadata yake son yi ba, asalima yana jin wajen mutum daya ya rage mishi, daya cike shikenan. Yana dai son tafiya saboda da dalilai da ba zai iya rabawa da kowa ba.

“Daada makaranta ce kawai fa, zan dawo… Ki daina yi kamar na tafi kenan.”

Kai ta jinjina, zuciyarta na wani irin ciwo, tafiya ta rabata da mutane da yawa, tafiya tayi mata sanadin abubuwa da ba zasu lissafu ba. Idan tace ko sunan tafiya bata son ji wasu zasuyi mamaki, amman dalilanta masu karfine. Shi da Madina ne mutane biyu rak da suka rage mata da take jin in dai tana numfashi ba zata bar wani abu ya rabata da su ba. Ko da yace makarantar kwana zai tafi hankalinta ya tashi, sai da Julde ya fada mata makarantar a cikin garin Kano ne, duk da haka sai da taji duk satin duniya Julden na zuwa ya dubasu.

Amman baccin kirki batayi duk asabar din duniya sai Julde ya biyo ya sanar mata da cewa Nawfal din na lafiya take samu nutsuwa. Yanzun kuma yazo mata da zancen tafiya wata kasar amurka, yana tuna mata abubuwan da ba mantawa tayi ba, amman ta samu waje ta adana su idan ba ranaku irin yau ba basa kwacema adaninta sai ta basu damar hakan.

“Dan Allah Daada… Kina daga mun hankali.”

Hannu tasa tana sake dauke kwallar da ta taru cikin idanuwan ta

“Naji tafiya da sunan karatu Bajjo, tafiyar da batayi mun dadi ba, naji tafiya da dalili da tafiya babu dalili, duka basuyi mun dadi ba…”

Kai yake girgizawa tunda ta fara magana, ga wani abu daya taso daga zuciyar shi yana tokare mishi makoshi.

“Karki hada mu, ko a tunanin ki karki hada mu, ba zan sake cewa daga jikin shi na fito ba. Amman ni daban ne, ni bashi bane ba, ba zan watsar da ku kamar baku da muhimmanci a rayuwata ba, karatu zan tafi, karatu zanyi in dawo Daada… Zan dawo.”

Ya karasa cikin dishewar murya, ba zai ce ga ranar karshe da yayi kuka ba, amman yanzun alamun shi yake ji. Ya san zafin da Daada take ji, amman baya son inda tunaninta yake son daukarta ya kaita balle ta ja shi su tafi tare. Shafine daya dade da rufewa. Abinda ya wuce ko kayi tunani a kai ba zai canza komai ba, shisa yake zabar barin shi inda yake, a matsayin abinda ya wuce.

“Zan dawo Daada… Ni bashi bane.”

Ya sake fadi, murmushi tayi mai sauti duk da kukan da take ta kokarin tsayarwa. Yanda Nawfal yake jaddada bambanci da yake tsakanin su da Bukar na karya mata zuciya. Kila tsayin shekaru yasa shi manta muryar Bukar da take ji a cikin tashi muryar, duk idan zai shigo gidan da sallama sai zuciyarta ta doka a cikin kirjinta, ko shigowa yayi fuskar Bukar take gani, ko a dabi’a bambanci da yake tsakanin su ba mai yawa bane ba. Ba ta da karfin fada mishi haka, ko tana da shi ma ta ina zata fara?

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.”

Ta furta tana saka Nawfal sauke numfashin da yake rike da shi

“Duk karshen shekara fa anan zanyi shi In shaa Allah…”

Kai Daada ta jinjina, zuciyarta taki natsuwa da tafiyar, in da zai hakura zata fi son haka. Da tana jin ta isa ta hana shi tafiyar zata hana ko dan gudun da takeyi na kar tarihi ya maimaita kan shi.

“Daada”

Nawfal ya kira, baya son yanayin da yake cikin idanuwan ta da kan fuskarta

“Ina Madina? Ba tace anyi hutun islamiyya ba? Ina taje?”

Ya tambaya cikin son sauya maganar gabaki dayan ta, fuskarta Daada ta goge sosai, dan har gefen zaninta ta kama tayi amfani da shi. Sai da tayi gyaran murya sannan ta amsa Nawfal din.

“Nan bayan gida suke taron suna gobe idan Allah ya kaimu, shine taje tayi musu kunshi, tun jiya ma take tayi.”

Dan dakuna fuska yayi

“Kin sansu ne Daada, kince jiya ma taje fa.”

Kai ta jinjina mishi

“Bata nisa ai, suma dan ana mutunci da sai dai su same ta a gida….baki ma nake gudu, kowa zancen kunshin ta da kuma karancin shekaru yakeyi.”

Numfashi Nawfal ya sauke, dole za’ayi magana, idan har kalar zanukan da yake gani tanayi ne a littafi, tun ba yanzun bama idan yazo ya same ta tana aikin da aka basu a makaranta, littafin duk da zai dauka ba zaka rasa yar flower da ta zana a jiki ba. Idan yace,

“Madina ana ina kika ga wannan zanen?”

Zata amsa shi da

“Ba ko ina fa, kawai na zana ne.”

Yanzun da ta dan fara hankali ne take ware litattafan da take zanen a ciki daban dana makaranta. Yanzun gashi alamu sun nuna kunshi zai iya zame mata sana’a. Kawai baya son ta da zuwa wani waje da sunan kunshi ne, kowa yazo gida ya same ta. Kasa hakuri yayi sai da yayi wa Daada mitar.

“Bajjo nace maka dan makota ne kawai shisa taje, karka isheni dan Allah… Ka fita ka tambaya gidan su Salaha, ka kirata ka rabu dani.”

Shiru yayi yana gyara zaman shi a kujera, zai dai jira tazo ya ganta sai ya tafi. Alawoyin daya siyo da hannun shi yake son ya bata, ba kwana zaiyi ba, yanda yake lallaba Julde ba zai sake tambayar shi wani abu ba har yabar kasar, ciki kuwa harda kwana gidan Daada.

“Rochester Institute of Technology”

Sunan makarantar ya fado mishi a rai yana saka shi sake sauke numfashi a karo na ba adadi tun wayewar garin. Wani yanayi yake ji tunda ya ga hotunan makarantar a Café din da yaje domin yin binciken makarantar da zatayi dai-dai da ra’ayin shi, daga hotunan yake jin kamar wani abu mai girma da ya wuce karatu zai faru da shi a kasar New York da take yankin amurka, a cikin makarantar da sunan ta kawai ya sa murmushi kwace mishi.

*****

“Sai yanzun kake dawowo Julde? Karfe biyu uku saura? Ka kasa yima kanka fada, idan anyi maka ba zaka saurara ba.”

Muryar Saratu ta daki kunnuwan shi, da alama a hanyar da zata hadaka da dakin baccin su take tsaye, sake rakubewa yayi jikin bangon kitchen din yana dana sanin shigowar da yayi. Wani irin kunnuwa gare shi da komin baccin da yakeyi takun tafiya idan akayi kusa da kofar dakin shi saiya bude ido. Ko dakin da yake kusa da nashi da Lukman ne a ciki yasha shiga da dare ya watsa mishi zagi saboda yana buga kofar bandakin da yake cikin dakin idan ya farka zai shiga.

Fadan su Julde da tun bashi da hankalin gane inda ya dosa ya sha tashin shi cikin dare. Daya fara hankalin gane yawancin maganganun su saiya ke tsintar kan shi da kallon Julde da wasu irin idanuwa na daban, yana kuma cika da mamaki ko da yaushe na yanda yake Daddyn su a gaban su, yake cikin rigar mutunci da kamala idan yana gaban su, amman sai ya cire ta ya yarda daga yayi tunanin sun dauke idanuwan su daga kan shi. Mutuncin da suke tunanin yana da shi, mutuncin da suke ganin zasu daki kirji a kai a waje shine yake zubarwa da duk rana.

“Meye a jikin matan nan da kake bi da ni na rasa?”

Maganganun Saratu kenan da suka kasa gogewa daga cikin kunnuwan Salim

“Idan na miki bayani ba zaki gane ba, idan ba kafafuwan ki kika saka a takalmana ba…”

Shine amsar da Julde ya bata wani dare da ba zai tuna a cikin wacce shekara ko wata yake ba, amman dare ne a cikin dubban darare da ba zai taba mantawa da shi ba. Saboda dare ne da wayewar garin shi ta zo mishi da wani sabon al’amari. Yana son Daddy, soyayya da ba zai taba iya kwatanta yawanta ba, shisa yake so ya fahimce shi, fahimtar da yake kiran Saratu ta kasa mishi ita, tabbas ba zata iya saka kafafuwanta a takalman Julde ba, amman shi zai iya. Ba shi da kyawun sauran yaran gidan, akan ce Khalid duk yafi su kyau. Shima ya yarda, amman ya fi kowa hasken fata, sannan kuma dogo ne, irin dogayen da ko a cikin masu tsayi sai ka dade baka gan su ba.

Kuma da yake da tsayi shi din ba siriri bane, dirarren namiji ne da tun yana sakandire yake kula da yanda yan mata suke son magana da shi, hayaniyar da baya so take saka shi share su. Amman tunda ya samu gurbin karatu a jami’ar Bayaro bangaren likitanci sai hakan ya kara haska shi a idanuwan mutane da yawa, baya mu’amala da kowa a ajin, sallama ce take rabasu, amman tun sakamon jarabawar su ta farko da aka kafe ya zamana shine a saman kowa wajen samun maki yasa mutane suka kara sanin shi.

Yanda duk yakan so zamewa sai sun saka shi yayi musu bitar wasu cikin darussan da sukan yi, musamman ma wa’anda suka hada da lissafi. Mata bashi yake kula su ba, sune suke kula shi. Ranar farko da yayi watsi da duk wani gargadi da zuciyar shi take mishi akan abinda ya kudurci yi tun safiyar da zai fita bayan yace wa Saratu.

“Zan kwana a makaranta yau Nanna, akwai abubuwan da zanyi.”

Bai san ya akayi bata ji muryar shi na rawa ba, da kuma tsoron da yake shimfide a cikin idanuwan shi, watakila da ta tambaye shi menene abinda zaiyi a makaranta a ranar daya canza komai, amman bata tambaya ba.

“Allah ya tsare, kar dai ka zauna da yunwa.”

Shine amsar daya samu, daya hadu da Khalid ma a hanyar fitar shi, gefe Khalid din ya rabe ko magana baiyi mishi ba. Shidin ba ma’abocin ciye-ciye a waje bane ba, ko zai yini a makaranta ruwane zai siya yayi ta sha. Ko yana gida idan zaiyi kyakkyawan karin safe zai iya kaiwa dare bai sake saka komai a cikin shi ba.

“Dogaye da cikin zani aka sansu, amman kalli dan abincin da ka zubo.”

Julde kan tsokane shi, wani lokacin har Saratu na shiga.

“Kuma fa tun abincin safe banga ya kara cin komai ba, da abinci ke saka jiki yaron nan tsayin nan ma ba zaiyi ba.”

Murmushi yakan yi ya wuce su, tunda da wahalar gaske kaga ya zauna anci abinci dashi gabaki daya, baya son yin zagi a gaban su Julde, to kuma ko Lukman saiya saka shi yayi magana saboda yanda yake tauna abinci kamar yana cin karfe. Duk kudin da Julde zai bashi na kashewa da kuma na hidimar makaranta bai cika amfani da su ba. Idan Adee tazo gidan yafi kashe kudin shi, tunda in taga zai fita ba zata rasa cewa ya siyo mata wani abin ba.

Wata yarinya yar asalin garin Kaduna, kabilar Bajju ce ta manne mishi, yana aji biyu tana aji hudu ko a lokacin, ta sha kai tsaye ta fito mishi da asalin abinda take so daga wajen shi, tunda tasan ko hauka take soyayya a tsakanin su ba zata yiwuwa ba, idan nashi addinin ya amince mishi auren mabiyiya wani addinin, ita nata ba zasu amince ba, kuma ga bambanci shekaru a tsakanin su. Shisa itace zabin farko da yake da shi. Harya gama darasin shi karfe shidda na yamma yana jin shi kamar akan allurai, karfe tara na dare suka yi da ita.

A masallacin makaranta yayi sallar isha’i, da suka hada idanuwa da dalibin da yayi musu limancin da sauri ya sauke nashi, saboda ya tsargu, sai yaga kamar yana mai kallon “Nasan abinda kake shirin aikatawa”. Tun daga lokacin da suka fita daga cikin makarantar da Victoria ta saka hannunta cikin nashi tana dumtsewa yake jin kuskuren da yake a cikin duk wani taku da zasuyi. Shiya bata kudin da ta kama musu hotel na kwana daya, sai dai suna shiga cikin dakin ta mayar ta rufe yaji ta rufe da wani abu daya bari a wajen dakin.

Bayan sun fito da safe, kowa yayi wajen shi daban yaji canjin da yayiwa gabaki dayan rayuwar shi. Dararen da kuma ranakun da suka biyo bayan wannan daren na biyu daya hadu dana farko wajen yin jagorar canza gabaki daya rayuwar Salim zuwa sukeyi suna wuce mishi da wani irin yanayi da yake kara dishe wani haske da baisan dashi a kirjin shi ba saida ya fara dakushewa. Dan ya fahimci Julde ya fara, sai ya budema kan shi wata irin duniya da bai taba sanin akwaita ba.

Ruwa ya kare a bangaren su, na famfon gidan kuma burtsatse ne ba dadi gare shi ba, shisa ya shigo bangaren su Julde da fadan su yasa shi tattara komai nashi yabar musu. Da badan karatun jarabawar da yake yi ba sam ba zai shigo ba, zai hakura da ruwan. Duk maganganun da suke fadama juna a cikin kunnuwan shi suke direwa suna karasawa zuciyar shi da yanayin da yake nisantata da son kusantar aure da duk wani rikici da zai biyo bayan shi. Rayuwar hayaniya ce sam ba zai iya ba, aure kuma cike yake da hayaniya, nashi iyayen babban misali ne.

Sai da ya sauke numfashi da yaji karar rufe kofa, tsaya yayi sai da ya sake jin budewa da rufewar kofa a karo na biyu tukunna ya fito daga kitchen din da robar ruwan daya rike kamar ya sato. A hankali yaja kofar gidan bayan ya fita, iska yake shaka yana fitarwa kamar mai son raba huhun shi da iskar daya shaka a cikin gidan. Yau ya kara fahimtar Julde, akwai shirun da yake tattare da dayar rigar dayake sakawa a wajen gidan aure, ba mai tsayi bane shirun, na kankanin lokaci ne, amman shiru ne, shi da baya tare da hayaniyar aure yakan bukaci wannan shirun. Balle kuma Julde, shisa yanzun da yake komawa bangaren su yake kara hango tazarar da take tsakanin shi da kusantar duk wani abu daya danganci aure.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×