Bai san ko ya kamata ace yana jin shi wani iri tun safiyar ranar ba, da Julde ya kira shi yace an daura ma baiji wani abu ba. Wasu kance sunji su kamar suna yawo kan gajimare saboda farin cikin an daura musu aure. Shi baiji duk wannan ba, farin ciki, yana cikin shi tunda ya samu goyon bayan su Julde akan auren, na rana daya bai taba jin ba zai samu Murjanatu ba, sai dai in rashin tabbas na rayuwa, mutuwa ta raba tsakanin su. Shi da ita din basu fara soyayya lokaci daya ba, daya ganta in da ance zaiji wani abu a kanta, ko zai kirata matar shi wata rana zaiyi mamaki.
“Ka zauna mun a waje”
Shine maganar farko da tayi mishi a coffee shop din daya shiga cikin harshen turanci , an kuma hado mishi irin yanda yake so da kankaru a ciki. Ya zabi teburin ne saboda yana can lungu, kuma mai kujera biyu ne da ba lallai inka zauna kaga wani ya zo ya zauna kusa da kai ba. Harya hango yanda Coffee shop din zai zamana wajen zuwan shi duk rana. Yanda take kallon shi haka shima ya daga kai ya saka nashi idanuwan cikin nata, da yake lokaci ne na sanyi, shigar sanyi ce a jikinta, iya abinda yake gani na daga fuskarta ya gane ita din me kyau ce, kyau irin wanda zaka gani a kallo daya.
“Banga sunan kowa a wajen ba kafin in zauna.”
Hannuwanta da babu safa ta murza kamar sun daskare mata.
“I’m a regular a wajen nan. Kowa zai fada maka corner dina ce nan.”
Ta karashe maganar da Hausa wannan karin dan yayi mata kama da bahaushe.
“Kaga karfin hali.”
Ya fadi da fulatanci a muryar da yayi tunanin dai-dai kunnen shi ta tsaya.
“Ba karfin hali bane ba, gaskiya ce.”
Ta amsa shi da fulatancin tana ganin mamakin daya bayyana akan fuskar shi, dayar kujerar taja ta zauna.
“Bafullatana ce ni, tunda kaji nayi Hausa bai kamata kayi mamaki dan nayi yare na ba.”
Dariya yayi, ba dan akwai abin nishadi a muryar ta ba, sai kwarin gwiwar ta da yanda take mishi magana kamar ta dade da sanin shi. Kamar ta san cewa ita da shi din ranar ne labarin su ya fara, sai da aka kawo mata abinda tayi order harda cookies ya gani sannan ta sake ce mishi.
“Murjanatu Faruk”
Kai ya jinjina mata.
“Nawfal Bukar”
Ba zaice sunyi hira ba, ta dai riga shi tashi daga wajen dan lokaci zuwa lokaci tana duba agogon da yake wajen, yanayin ta ya nuna cikin sauri take.
“Next time ka nemi wajen ka, this is my spot.”
Dariya kawai yayi, kafin ma ya amsata tabar wajen. Ko da ya tafi ba zaice yayi tunanin ta ba, daga ranar ma zuwa safiya ko sau daya bata fado a ran shi ba. Watakila duk littafine da fina-finai ke zuzuta wannan kalar soyayyar. Sai ace idanuwa sun sarke cikin na juna shikenan har soyayya ta kullu, ko an gogi juna jiki da ruhi sun girgiza. Watakila kuma kaddara ta hada hanyar shi da Murjanatu ne dan su kafa tarihin da zai karyata wannan kalar soyayyar. Sunyi haduwa wajen goma bayan nan, ta shigo Coffee house din shi zai fita, ya shigo ita zata fita, banda gaisuwa babu wani abu da yake hada su.
Maganar su ta fara tsayine randa ta same shi zaune da sketch book dinshi yana nazarin wasu zanunnuka.
“Kai Artist ne?”
Ta tambaya, zai tuna ya girgiza mata kai, kamar ba zai ce mata komai ba kafin ya amsa,
“I’m a furniture designer, ko ince abinda nake karanta kenan.”
Gabaki daya hirar su akan abinda yake karantawa ne har suka rabu. Zaice ita ta fara neman shakuwa da shi, ta fara neman alakar su ta wuce haduwa a Coffee Shop din bayan ta gayyace shi wani furniture showcase da za’ayi a cewarta baban dan ajin su ne a wajen ko wani bayani da ba zaice ya fahimta ba gabaki daya, an gayyace ta, ita kuma ta gayyace shi. Ya amsa ta da cewar zaije ta rubuta mishi lambar ta a takarda tana ajiye mishi sukai sallama.
Ranar ta bude musu sabon shafi, dan duk wani yunkuri da zaiyi sai ya gan su a tare a wani wajen, sai yaji kamar dama can ya santa ne, babu wata bakuntar juna a tare da su. Kamar yanda a cikin duk wata dariya da zasuyi ya fara jin ba ita bace ta karshe. A cikin shekara daya sunyi wani irin sabo da kalamai zasuyi karanci wajen fassara shi, dan a gidan su Murjanatu babu wanda bai san shi ba, har idan an nemeta ba’a samu ba, yana cikin jerin abokanta da Mamanta ko babanta zasu fara kira suji ko suna tare ko kuma ta fada mishi inda taje.
Rana daya ya tashi da safe yaji baya son hango tana da kayadadden lokaci a rayuwar shi, baya son hango wasu ranaku a cikin rayuwar shi da babu ita a cikin su
“Ina son kasancewa da ke, fiye da abokanta.”
Ya fada mata batare da shakku ba, ta dauki mintina biyar, har saida shirunta ya fara tsoro ta shi kafin ta dago tana saka hannuwa ta dauke kwallar dake cikin idanuwanta.
“Na dauka ba zaka taba tambaya ta ba.”
Tayi maganar muryarta na rawa.
“Ka san tun yaushe nake son ka.”
Kai ya girgiza mata, jin tayi shiru na sa shi fadin,
“Wannan na da muhimmanci ne yanzun?”
Dariya tayi mai sauti.
“Babu, kana jin yanda nake ji, shine a saman komai.”
Daga nan suka fara, bai san a inda zasu tsaya ba. Ya dai san zai karasa sauran rayuwar shi tare da ita yana mata godiyar yanda ta yarda da shi da zuciyarta, da farin cikinta harda abubuwan da tasan shi kan shi bashida tabbaci akan su.
“Zan sauke ka gidan Daada ko in wuce?”
Khalid daya turo dakin ya fadi yana katse mishi tunanin da yake yi.
“Hamma mana, ba zaka dinga kwankwasa daki ba zaka shigo.”
Dan karamin tsaki Khalid ya ja.
“Har wanka na maka Bajjo.”
Dafe kai Nawfal yayi yana fadin,
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”
Kafin ya dago ya kalli Khalid din,
“Zan wuce wallahi ina da abinyi…”
Mikewa Nawfal yayi.
“Da zan kara watsa ruwa ne.”
Ganin yanda Khalid yaja kofar ya rufe yasa shi karasawa wajen kofar da gudu yana budewa.
“Yi hakuri ka jirani in dauko jakata.”
Dariya yayi ganin hararar da Khalid ya watsa mishi. Anan cikin falon Khalid yake tsaye yana jiran shi dan baiji shigowar Salim ba sai ture shin da yayi yana furta,
“Tashi dalla.”
Sake matsawa Khalid din yayi, dan Salim ya tsani ka tsaya akan hanya, ya dan fara rage saurin hannu da ya mare shi, ko kuma sun fara girma ne a idanuwan shi, Khalid din ba zaice wanne bane a cikin biyun, dakin shi Salim ya wuce yana rufo kofar, dai-dai lokacin da Nawfal ya fito yana janyo tasu kofar dakin.
“Uban me yasa zaku dinga jan kofa kamar zaku rabata da mazaunin ta? Me yasa ba zaku rufe a hankali ba?”
Salim ya leko yana fadi a masife, har kanshi saida ya sara da yanda yaji karar rufe kofar da Nawfal yayi. Ko inda Salim din yake babu wanda ya kalla a cikin su, sauri ma sukayi suna fita daga dakin, Khalid ne karshe, yana sane ya buga kofar da zai rufe.
“Khalid!”
Yaji muryar Salim din, sauri suka kara suna dariya, yasan koya dawo ba zai mishi magana ba tunda ba son surutu yake ba. Zai dinga binshi da harara ne, ba ma zai zauna a falon ba sam, dakin shi zai shige yana dawowa, Nafwal zai kwana gidan Daada.
*****
Gabaki daya hankalin ta yana kan littafin da take karantawa, novel ne na James Hadley Chase mai suna (A coffin from hong kong). Abincin da ta zuba har yayi sanyi saboda gabaki daya bata san abinda yake faruwa a wajen duniyarta ba. Tana son litattafan mutumin, har mamakin irin fasahar da yake da shi takeyi. Guda goma Salim ya kawo mata a lokaci daya, kamar tayi me dan murna ranar. Cancana su takeyi, bata karantawa sai ranakun karshen mako, ta dauki guda daya ta karanta a ranaku biyun.
Yanzun ma Daada ta daina mata magana kan karatu, a cewar ta,
“Bakina ya gaji da surutu Madina, in shaa Allah ba zan kuma ba, in dai akan wannan litattafan ne, ace abinci ma ba zaka natsu kaci shi ba.”
Tana kuma kokarin kyautata maganar tata, idan Madina ta kula da ita ne, sai ta ajiye ta dan kara tsakurar abincin ta mayar ta ajiye. To yau tunda Salim ya dawo da ita daga restaurant din can, sallah ce kawai abinda yake tashin ta daga inda take. Littafin saiya rage mata yanayin da ta shigo gidan da shi, yanzun ma isha’i take jira a kira tana da alwala in tayi ta shige dakinta. Shisa sam bata ji shigowar Nawfal ba, balle sallamar shi. Sai hannun shi da ya sa yana yin kasa da littafin nata ta gani, a hankali ta dago suna hada idanuwa ta cikin gilashin ta.
“Hamma…”
Ta kira da sanyin muryar da Nawfal yaji yayi mishi tsaye, littafin ya zare daga hannunta, babu gardama ta sakar mishi, duba sunan yayi.
“Da dadi?”
Ya tambaya, ta jinjina mishi kai.
“Sosai ma… Bansan zaka zo ba. Me zaka ci?”
Dan jim yayi.
“Ki bani shayi kawai, bana jin yunwa.”
Mikewa Madina tayi tana shiga kitchen din, ta san yanda yake son shayin shi, babu bata lokaci ta hado mishi, kafin ta gama tana jin muryoyin su shida Daada data fito daga daki, tana fitowa ta mika mishi.
“Ka sha ko sikarin yayi maka kadan.”
Karba yayi yana sake juyawa da cokalin da yake cikin kofin kafin ya kurba.
“Ki karamun Milo kawai ko cokali daya.”
Cewar Nawfal yana mika mata kofin shayin. Karo mishi tayi ta dawo tana bashi, ta dauki plate din abincin da tasan ba ci zatayi ba ta mayar da shi kitchen, sanda ta dawo ana kiran sallar isha’i, shisa bata zauna ba ta nufi dakin ta. Nawfal ma mikewar yayi, ya shiga kitchen ya bude fridge ya saka kofin shayin yana fita masallaci. Sanda ya dawo babu kowa a dakin, kan kujerar da land-line din Daada take gefe a ajiye ya zauna yana janyowa, lambar Murjanatu ya kira tana dagawa yace ta kira shi, saboda yasan zaifi sauki daga can akan ya kirata daga nan din.
“Jaan…”
Ya kira yana jin yanda yayi kewar ta.
“Ina missing din ka sosai.”
Murmushi ya yi.
“Kan ki kawai kika sani.”
Yana jin dariyar ta cikin kunnen shi, sautin na nutsar mishi da zuciya yana saka shi sake shigewa cikin kujerar.
“Na kira Hamma yace mun kana gidan Daada, nace ba kai nake nema ba na kira ne in gaishe shi…”
Wannan karin shi yayi dariyar.
“Bai yarda ba ai, yace yaji dadi dana kira saboda yana so yayi magana da ni daman. Yan uwan suna son ka Gidado.”
Ta karasa da sunan da takan kira shi a lokaci irin wannan, idan tana jin tsokana zata kira shi da Bajjo tun ranar da taji Khalid ya kira shi da hakan.
“Na sani, na san hakan Jaan.”
Nawfal yayi maganar batare da shakkun komai ba, yana da cikakkiyar yarda akan soyayyar da take tsakanin shi da yan uwan shi.
“Hamma yace in kula da kai, yace kar in cutar da kai, zai bada shaida ba zaka taba yin abinda zai basu kunya ba…”
Wani abu Nawfal yaji ya tsaya mishi a kirji, Khalid, Khalid daban ne a wajen shi.
“Zan so ace nayi recording din kiran kaji kalaman shi idan ka dawo, ban rike gabaki daya ba saboda ina ta share hawaye, ya karya mun zuciya da yawa.”
Dariya Nawfal yayi, shima tashi zuciyar rawa yaji tana yi.
“Ke komai abin kuka ne ai.”
Yanayin yanda yayi maganar yasa Madina da ta fito juyawa zata koma dan tasan dawa yake magana, ta kuma san yana bukatar kasancewa shi kadai dan ya sake da matar shi, amman sai taga yana daga mata hannu cikin nuni da ta karasa inda yake din.
“Jaan ga Madina zaku gaisa.”
Ya fadi yana kallon Madina da take kokarin ware mishi kananun idanuwan ta, nunin dai ya sake mata da hannu yana kiranta, da kyar ta karasa ta karbi wayar tana furta.
“Hello…”
Cikin yar karamar murya.
“Madina, ya kike?”
Murjanatu ta fadi ta dayan bangaren, yanayin hausarta kawai ya isa bama Madina tabbacin yar gayu ce, dan yanda ta ajiye kowacce kalma harda sunan Madina din cikin ba kowanne harafi hakkin shi zai tabbatar maka da hakan, ga muryarta ma,
“Alhamdulillah, ya kike kema? Ya aiki?”
Dariya Murjanatu tayi.
“Lafiya kalau, aiki da karatu duka. Ya naki?”
Saida Madina ta gyara gilashin ta sannan ta amsa tana sauke numfashi.
“Ban sanki ba, amman na san Hamma, in ya yarda kin zama matar shi, muma mun yarda da kasancewar ki a cikin mu. Dan Allah ki kula da shi.”
Maganganun suka kubcewa Madina batare da tayi wani tunani ba.
“In shaa Allah, shima kice ya kula dani, ku daina son kai haka.”
Kai Madina ta jinjina tana murmushin da batasan me yasa yake bude wani abu a kirjinta ba.
“Zan fada mishi shima… Mun gode sosai.”
Ta amsa tana mika ma Nawfal wayar batare da ta jira amsar Murjanatu ba, shima bata bari sun hada ido ba, dan haka kawai take jin idanuwan shi na shiga cikin nata zata iyayin kuka. Gashi suna daki daya amman tana jin yayi mata wani irin nisa. Karasawa tayi kan kujera ta dauki littafin ta sannan ta wuce daki tana maido kofar ta rufe a hankali.
*****
Wannan karin jirgin shi na karfe hudu ne, tunda safe yaje gidan Daada sukayi sallama, abinda yake gudun saida ya faru, tana ta kuka kamar wanda zaiki dawowa, dan wannan karin duk yanda yace mata zai dawo yana ganin rashin yarda shimfide akan fuskarta. Haka ya dawo duk ta kashe mishi jiki, bacci yayi zuwa azahar, yana tashi ya fara shisshirya kayan shi ya watsa ruwa, ya sake kaya kenan yana taje sumar kan shi aka kwankwasa dakin.
“Shigo.”
Ya fadi dan a tunanin shi ma Lukman ne, sai yaga Salim daya shigo dakin gabaki daya yana mayar da kofar ya rufe. Lokacin Nawfal yaga yar jakar da take hannun Salim din, mika mishi yayi, da mamaki yasa hannu ya karba.
“Na matar ka ne, ka kira mun ita.”
Murmushi Nawfal yayi yana kallon Salim din, kafin ya ajiye jakar a gefen shi, wayar Khalid na wajen shi, dan haka ya mike yana duddubata akan gadon ya dauko. Babu bata lokaci ya kira Murjanatu da yasan tana tare da wayar dan yace zai kirata kafin ya fita daga gidan.
“Harka gama shiryawa?”
Ta fadi bayan ta daga.
“Zaku gaisa da Hamma Salim ne, ina kanyi.”
Nawfal ya fadi yanajin yanda harshen shi yayi nauyi a gaban Salim din, wani abu kamar kunya na son lullube shi, mika mishi wayar yayi ya koma ya zauna, yana jin suka gaisa kafin Salim din ya dora da,
“Bajjo yace miki bana magana da yawa ko?”
Baisan me Murjanatu tace ma Salim din ba, amman yasa yayi dan murmushi.
“Nasiha ya kamata in miki, amman banda wasu kalamai masu yawa. Bajjo bashi da matsala, shine mutum daya marar matsala dana sani, ba don yana kanina ba. Yana da karancin shekaru amman ba yaro bane ba, yana da hankalin da zai rike ki da kyau. Karki cutar da shi, shine kawai abinda zan fada miki, ba kashe di bane ba, roko ne, kece zaki zama mutum ta farko dana roka alfarma, ki rike mun kanina da kyau.”
Salim ya karasa cikin sauke muryar da Nawfal bai taba ji a tare da shi ba.
“Allah ya sa muku albarka a zaman ku ya tabbatar muku da alkhairi.”
Saida ta amsa tukunna ya mika ma Nawfal wayar yana ficewa daga dakin. Da dukkan zuciyar shi yake addu’a tun da aka fara maganar auren, addu’ar da rabon daya zauna yayi irinta harya manta. Saboda hayaniyar dayake gani a cikin auren Julde da Saratu baya son ta kasance a tare da Nawfal, rayuwa da tayi kason tashin hankali a faranti Nawfal baiyi hankalin da zai dauka ba, miko mishi kason shi tayi da kanta ya karba saboda bashi da wani zabi. Baisan duka labarin Nawfal ba, amman yasan me yake faruwa da shi a zaman da yake a cikin gidan su, idan shine bashi da yakinin zuciyar shi zata dauka.
Shisa ya roki Murjanatu, idan bata samar mishi da nutsuwa ba baisan me zai faru da yaron ba. Yanata tunanin kyautar da zai basu, sai shekaranjiya yaga wani bracelet na azurfa a hannun wata yarinya a makaranta, yayi mishi kyau shisa ya tambayeta inda ta siya, tace mishi yayanta ne yake siyarwa, basu rabu ba saida ta kira masa shi sukayi magana ya fadi abinda yake so a rubuta a jiki, da yake aikin cikin saurine sai da ya kara mishi kudi, an kuma yi masa shi yanda yake so. Dakin shi ya wuce yana daura alwalar la’asar, raka Nawfal airport ne abinda ya dawo da shi daga gidan.
Nawfal kuwa inda Salim yabar shi nan ya zauna, ya rasa inda zai sa zuciyar shi ya rage emotions din da yake ji. Dakyar ya iya yin alwala ya fita masallaci. A sujjadar shi, a karo na farko ya roki Allah da karya ba Saratu nasarar raba shi da yan uwan shi, yaranta ne ya sani, amman Allah yake roko daya saka mata salama a zuciyarta ta taimaka mishi ta raba su tare da shi, karta raba su, kome take mishi yana yafe mata, in tayi wannan ba zai iya ba, ba zai taba yafe mata ba saboda suna da muhimmanci na gaske a rayuwar shi.
Har kasan ran shi yaji sanyi daya ga bangaren Saratu a kulle, da alama bata nan, har sauri yake wajen dauko jakar shi dan subar gidan kafin ta dawo, duka haduwa biyu sukayi tunda ya dawo kasar, bayason suyi ta uku, baya son ya tafi da wasu cikin maganganun da yasan dole saita fada masa su. Ai kuwa har Khalid ya zo ya shigo motar, Salim ma ya fito bata dawo ba, ajiyar zuciya ya sauke har Khalid na kallon shi.
Da yake babu wani isasshen lokaci kusan a gaggauce suke sallamar.
“Baka dai manta komai ba ko?”
Julde yake tambaya.
“Babu abinda na manta Daddy, kayan babu yawa ai”
Kai Julde yake jinjinawa.
“Na kara maka kudi, in dai kana bukatar wani abin ka kirani kana ji ko?”
Sau hudu yana kara mishi kudi kenan, saboda gani yake kamar zasuyi mishi kadan, baya so yaje yana manejin komai ga yarinyar mutane, yanda danginta suka karamma shi a Abuja ba zai so ace Nawfal baya rike musu yarinya da kyau ba, babanta ma kusan sau hudu suna gaisawa, uku daga ciki duk shi ya kira Julden, basu da matsala ko kadan ya kula, mutane ne su masu karamci da saukin kai, duk kuwa da tarin arzikin da yaga Allah ya wadata su da shi, bai saka musu girman kyau da kyamar mutane ba, ko Kawun Murjanatun yaga yanda yake faran faran da ma’aikatan gidan na shi kamar wasu abokan shi.
“Daddy kudin ai yayi yawa, da gaske ba wani abu nake siye ba, kuma nace maka ina aiki.”
Kallon shi Julde yayi.
“Ka tsayar da hankalin ka kan karatun ka, da zaka ajiye wannan aikin ma zaifi.”
Dariya kawai Nawfal yayi, yanda duk zai ma Julden bayani yasan ba zai yarda ba, tsadar rayuwa acan kawai in baka da lafiya ne, ganin likita da magungunan su akwai tsada sai kuma kudin haya, amman abinci kowanne mazaunin New York ko wanda ya taba kai ziyara zai fada maka babu tsadar kayan ciye-ciye. Karasawa yayi kawai yana hugging din Khalid da Julde, bai ma fara nufar Salim ba. Shi din dai ya kara so ya karbi akwatin Nawfal din yana dan yin gaba, sallama ya sake yi wa su Khalid ya karasa inda Salim din yake.
“Ka kula musu da yarinya Bajjo, kai kace zaka aure ta. Karka bani kunya.”
Murmushi Nawfal yayi.
“Ita rokonta naji kayi Hamma.”
Babu wasa a fuskar Salim yace, “Kai kashedi ne nake maka.”
Hannu Nawfal ya daga cikin alamar salute yana saka Salim din girgiza kai kawai ya mika mishi akwatin shi ya juya.
“‘Hamma…”
Ya kira, juyawa Salim yayi, hannu Nawfal yasa akan kirjin shi inda yake tunanin zuciyar shi take yana ganin Salim din ya sake bata rai.
“Na gode.”
Ya fadi a hankali, yasan baiji sautin muryar shi ba, amman ya karanci godiyar akan labban shi. Bai daiyi magana ba kamar yanda yayi tsammani ya sake juyawa. Salim yana da wahalar fahimta, kullum nuna musu yake rayuwar shi yasa a gaba, bai damu da harkar kowa ba, amman a cikin kananun shiga harkokin su da yakeyi yana nuna musu cewa yana tare da su duk runtsi, zasu kuma iya jingina da shi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, amman su tsaya da nasu kafafuwan shine abinda zaifi son gani.
“Allah ya kula da kai Hamma Am.”
Nawfal yayi addu’ar cikin zuciyar shi, yana sauke numfashi, inda wani zaigani zaiyi tunanin Nawfal ya leka wasu a cikin shafukan da kaddara ta tanadarwa Salim.
Kamar yaga yanda yake bukatar addu’ar.
Kamar yasan kurar da take tunkaro rayuwar shi bata wasa bace ba.