Skip to content
Part 13 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Kan wayar Madina ta maida mazaunin shi tana mikewa, dakinta ta wuce tana sauko karamar hijab, riga da wando ne a jikinta, rigar sai a saka irinta su hudu kafin su cikata, takalman kafarta wasu manya ne da Daada bata san inda ita da Julde suka nemo su ba, amman masu gashine, kamar ma kan kaza-kaza take gani daga karshen takalman dan harda yan idanuwa daga jiki, da tayi magana randa ta fara ganin Madina na yawo da su a cikin gida dariya tayi.

“Guda biyu ne, in dauko miki dayan Daada, zaki ji dadin shi, ga laushi, kuma yana da dumi.”

Kai ta girgiza,

“Allah ya tsare ni, ke dai kiyita fama.”

Ai kam kamar ta dauki shawararta, in dai tana cikin daki to da wahala kaga kafafuwanta babu su, ga safa ga wannan takalman.

“Zan ga Hamma a waje.”

Ta fadi tana kama hanya batare ma da ta jira amsar da Daadar zata bata ba. Da ido kawai Daada ta bi Madina harta fice. Bata son kawo komai a ranta akan Madinar da Salim, amman kullum sai yazo, shi yake zuwa ya dauko ta daga makaranta, kuma da yamma idan bai zo ba to dai-dai irin lokacin nan zaka gan shi. Da yawan lokutta takan dawo da ledoji yayo mata siyayya, tayi fata kala-kala a baya da bai kasance ba, ba zatayi wani akan Madina da Salim ba, koma menene yau da gobe zata nuna.

Madina da ta fita motar Salim ta bude ta shiga tana mayar da murfin ta rufe hadi da sauke numfashi, jikinta har bari yakeyi. Bata taba tunanin zata iya boyewa Daada halin da take ciki ba sai yau, saboda wani abu da zaisa tayi hakan bai taba faruwa ba. Asalima bata san ta kwana da wani abu a ranta ba sai bayan auren Nawfal, haka kawai zata nemi bacci a lokacin da ta saba yin shi ta rasa saboda yanda tunanin shi yake damunta, da yawan ranaku takan labe bakin kofa a dai-dai lokacin da yake kiran Daada taji ringing din wayar sannan ta koma ta kwanta.

Zuciyar ta kan raya mata ta fita ta karbi wayar su gaisa, amman sai kafafuwan ta su kasa fitar da ita, tana daukar abin zaiyi sauki lokacin da awanni suka shude a cikin ranaku, amman a hankali wannan ranakun suka dinga tafiya da satikan da suke cikar watanni har shekarar da take ganin kamar ta rufe ido ne ta bude. Yanayin bai barta ba, amman ta saba da shi, ta dai kasa samun amsar dalilin da yasa take jin nisan da yake tsakanin su ya ninka na da. A gefe daya kuma Salim ya zame mata wani bango da take jingine da shi batare da fargabar komai ba.

Duk sanda take da wata bukata sai ta ga Salim tsaye a gabanta yana kallon ta kamar in har yana tare da ita babu wani abu da zatayi kukan rashin shi, tasha tsinto kalmomi biyu a litattafai ‘comfort zone’ tare da Salim take ganin asalin ma’anar kalaman, dan kamar shi din da matsayin shi a rayuwar ta bature ya kalla ya kirki kalaman. Shisa yau da ya zama rana ta farko da tashin hankali ya fara yiwa rayuwarta sallama ya zama mutum na farko da take son rugawa wajen shi.

Safiyar ranar alhamis din tazo mata a birkice tun bayan zuwanta makaranta suka kuma juyo sakamon rasuwar Malami a makarantar, ba bangaren ta yake koyarwa ba, amman mutuwar ta daketa, sai take ta ganin fuskar shi, ta daiji dadi daya kasance musulmi saboda ko bakomai mutanen da zasu roka mishi gafara a wajen Allah kuma addu’ar ta same shi suna da yawa, a cikin su harda ita kuwa. Da yake ta saba tsara ranarta, sai lokacin ya zame mata wani abu da bata san me zatayi da shi ba.

Shisa ta tsiri yin kwalema, share nan, goge can, lokacin da taje dakin Daada ta sameta ta gama shiri wai zataje jaje nan makota in da yaro ya sa kafa cikin tuwon da aka kwashe a kwano ya kone. Bayan ta Madina tabi tana kulle gidan, tasan gidan da Daada take magana, akwai mahaifiyar maigidan da take zaune tare da su, kusan kawaye ne ita da Daada din, Madina tasan in ta shiga zasu zauna ne suna ta hira, gara ta kulle gidan kafin wani ya fado mata.

“Ko da ba zan dade ba kece fa, zan ga yanda zakiyi da tsoron nan in kikayi aure.”

Daada ta fadi cike da zolayar da ta saba yi mata duk sanda zata fita. Dariya kawai tayi, tsoro ai halal ne ko a musulunci babu inda ta ga an haramta shi har yanzun da take zuwa Islamiyya. Bata san ko a gaba ba, in ba nan gidan su ba, batajin akwai gidan da zataje abarta ita kadai a ciki ta zauna. Tunda Allah yayi mata tsoro, sai ta ga kamar wani zai shigo ya yankata kafin tayi ihun da za’a aji har a kawo mata dauki. Ko da ta koma dakin Daada ta nufa tana cigaba da aikinta.

“Yanzun ji tarkacen da yake dakin nan, amman na dakina take gani.”

Madina take tsegumi tana janyo wata tsohuwar butar tangaran mai murfi, bambanci dakin Daada da nata bata ganin yana da wani yawa, kawai ita Daada komai a kammale yake, ita kuma nata a barbaje suke. Zama tayi tana bude butar dan ganin meye Daada ta ajiye a ciki, zazzage butar tayi a kasa tana murmushi ganin harda wasu kudin karfe irin na da, ta dauka ta duba, da wani hoton fasfot, duk da babu kala a jikin shi kuma ya tsufa sosai bai hanata ganin kamannin mutumin da na Julde ba, wata irin kama ta ban mamaki.

Ajiyewa tayi a gefe tana daukar wata takarda da saboda tsufan da tayi har ta fara ja, ga wani maikon ajiya da yake jiki kamar an tsoma cikin mai an fiddo. Zaman gilashin ta da ta gyara baisa ta ganin rubutun da kyau ba bayan ta bude takardar, tashi tayi tana sake kunna dayan kwan dakin dan ta ga haske sosai,

Daada,

Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu’a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba.

Yelwa.

Ta karasa karanta suna da ya zama karshen rubutun da yake jikin takardar, a karo na farko tana tabbatar da yaren hausa bashi bane asalin ta saboda yanda rubutun da akayi a cikin harshen ya birkita mata kwakwalwa yana sa ta kasa fahimtar shi kai tsaye, sake karantawa tayi, wannan karin a zaune, zaman da bata san lokacin da tayi shi ba, kamar yanda har zuwa yanzun ba zata ce ga adadin yanda rubutun da yake jikin takardar da zata zama mafarin budewar abinda aka dade ana boye mata ba ya dawo mata. Ta haddace kowacce kalma, ta dai rasa ma’aunin dora nauyin da sukayi mata.

Da rarrafe ta karasa ta kwashe kayan da ta zazzago tana mayar da su cikin butar banda takardar da ta ninke. Butar ma mayar da ita tayi inda ta dauko, har ta karasa share dakin, ta koma nata ta bude littafi ta saka wasikar ba zata ce ga abinda take ji ba, ko me tunaninta yake so da ita ba, saboda yaki daukarta ya kaita ko ina. Murmushi take tana jin kamar ba fuskarta ba, amsa hirar Daada take tana rasa daga inda kalaman suke fito mata, duk idan sautin muryarta ya koma cikin kunnuwan ta sai tayi mamakin yanda bai fito da alamar tambayar da tafi kowacce yi mata yawo cikin kai ba.

“Wace ce Yelwa?”

Kusan har ihun wata murya take ji cikin kanta da wannan tambayar, amman yanda akayi bata sakko daga kan nata zuwa makoshinta ba abin mamaki ne. Har girki tayi, duk wani abu daya kamata ace tayi saida ta gudanar yau, wajen karfe biyu da rabi wayar dakin Daadar ta hau ruri, da yake Daada ce a kusa ita ta amsa tana yin jim hadi da fadin.

“Lafiya kalau Salim, gata nan a kusa ma.”

Ta karasa tana mika ma Madina kan telfon din.

“Mug…”

Salim ya kira ta dayan bangaren, muryar shi da taji, da yanda ya kira sunan daya makala mata kamar yasan tana boye wani abu yasa taji gwiwoyin ta sunyi sanyi, zuciyarta ta karye.

“Hamma”

Ta amsa tana yin gyaran murya jin maganar ta fito daga kasan makoshin ta

“Kana makarantar mu ko? Banyi tunanin kiran ka ba sam, kayi hakuri.”

Tana jin yanda ya sauke numfashi a kunnen ta.

“Zanyi abu yanzun, ban san lokacin da zan gama ba, amman zan zo in ganki.”

Kai ta jinjina kamar yana ganin ta.

“Allah ya taimaka, sai kazo.”

Ta san ba wani abu zai sake cewa ba shisa ta mika ma Daada kan telfon din da ta mayar mazaunin shi. Yanda zuciyarta ke karyewa ne yasa ta mikewa tabar falon. Kwanciya tayi har la’asar. Da ta fito taji ko Daada na marmarin wani abin ta dafa mata tace mata a’a daki ta sake komawa. Ba zatace ga abinda take ji ba, lokacine dai yaki yi mata sauri har zuwa yanzun da take cikin motar Salim inda ta hada kanta da gaban motar tana sauke numfashi. Wasu abubuwa da bata san suna daure a jikinta ba take jin suna kwancewa a hankali yanzun.

“Madina…”

Salim ya kira ganin yanayin ta. Ta kasa dagowa, numfashin ta da take jin daidaton shi ya kwace mata take son nutsarwa.

“Madina”

Salim ya sake kira yana jin zuciyar shi na dokawa, bai taba ganin ta yanda yake ganin ta yanzun ba, tunda rana da ya kira yaji kamar yanayin muryata ya canza, baisan yanda zai tambayeta ba shisa yayi shiru, amman tana rashin tun lokacin, kawai akwai abinda yake dubawa ne saboda jarabawar shi ta karshe da take gabatowa. Danma yajin aikin da akayi ta fama da shi, da sun manta da gama wannan wahalar. Hannun shi ya kai yana dan bubbuga kafadar ta.

“Hey Mug.”

Ya fadi cikin wani irin sauke murya da baisan ya iya ba, lallashi ba sabon shi bane ba, ko su Khalid idan yaga alamar wani abu na damun su, karshen abinda yakeyi shine ya fita ya siyo musu wani abu da yake tunanin suna so yazo ya basu, in a falo suke ya zauna da su har sai sun tashi sun bashi waje, idan a dakin sune zai ta tsayuwa har saiya tabbatar idan ya tafin babu abinda zai same su, ko a fuskar su yaga alamar suna son ya tafin. Ko Saratu da ya sha shiga bangaren su ya jiyo sautin kukanta duk da kofa a kulle take bai taba kwatanta shiga ba.

Zai tsaya daga inda yake zuciyar shi na wani irin ciwo da ba zai fassaru ba har saiya daina jiyo sautin kukan nata sannan zai tafi. Shisa yanzun yake addu’a ba kuka Madina zatayi ba, tunda baisan yanda zaiyi da ita ba, zai sake magana ta dago tana gyara zamanta, da yake ya kunna fitilar cikin motar yana ganin fuskarta fayau, babu alamar kuka tayi, yana dai so yaga idanuwanta ne yau, shisa ya mika hannu yana zare gilashin dake fuskarta, sai idanuwan nata suka kankance mishi, kamar ta cikin gilashin sun fi haka girma.

“Idanuwa ne haka Madina?”

Sai da murmushi ya kwace mata duk kuwa yanda take jin zuciyar ta, Salim na da wannan tasirin a tare da ita, hannu ta mika tana karbar gilashin ta.

“Bana gani da kyau Hamma.”

Ta fadi tana mayarwa ta gyara mishi zama, takardar da take hannunta ta mika mishi, da mamaki ya karba yana warware wa, kallon Madina yayi ta dan daga mishi kai cikin alamar ya karanta, bai kuwa yi musu ba ya karanta din kafin ya raba idon shi da takardar yana kallon Madina da ta dan daga mishi kafadu.

“Mama na ce ko?”

Tayi tambayar da taji tsoron furtawa har a cikin kanta tun safe, Salim na ganin firgicin da yake cikin idanuwan ta.

“Madina…”

Ya kira da wani yanayi da yasa ta kai hannuwa tana rufe fuskarta hadi da furta.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Shi kan shi kalaman cikin wasikar ne suke mishi yawo, yana harhada ma’anar su. Baije islamiyya kamar yanda su Khalid suka ba, tunda har yanzun yaga Khalid na zuwa, amman yayi zuwan da ya fahimci kalaman Yelwa a cikin wasikar ‘…Yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi.’

“Madina”

Kawai ya iya sake furtawa a karo na biyu yana son ya rungumeta a jikin shi, dan hakan ne hanyar lallashin da ya fara zuwa kan shi, sai dai kafin yayi wani yunkuri ta bude fuskarta tana kallon shi.

“Ya zan koma baya Hamma? Ya zan koma lokacin da banga takardar nan ba? Ya zan koma in mayar da ita in jira sai lokacin da Daada ta ga ya kamata in sani ta fada mun da kan ta?”

Sosai take kallon shi tana son ya taimaka mata ko zata daina jin wani abu na budewa a cikin kirjinta, ko tarin tambayoyin da suke mata yawo zasu daina, idan tace bata tunanin su waye iyayen ta zatayi karya, a duk wani PTA meeting na makaranta sukan fado mata, a lokuttan da za’a bayar da wata takarda da sunan iyaye su saka hannu sai Julde ne zai saka mata tunanin me ya faru da su kan zo mata. Bata tambaya bane saboda tasan idan lokacin ta sani yayi za’a sanar da ita.

Ko da wasa bata hango sanin zai iya zo mata da hargitsi irin wannan ba, idan Yelwa mahaifiyar ta ce tana ina? Ba rasuwa tayi ba kenan? Kamar yanda tunanin ta ya sha ba ta, shisa Daada bata maganar ta, zafin rashin ne yake taba ta har zuwa yanzun. Wanne son kaine tayi a karo na farko idan tsallakewa ta barta ne na biyu? Da sauri ta fisge takardar dake hannun Salim tana sake duba wani layi da sai yanzun ma’anar shi take bude mata, yanda ta dago ta kalli Salim ne ya tabbatar mishi da sai yanzun ta gane, ta gani amman sai yanzun ta gane, takardar ya karba ya ninke yana kamo hannunta ya saka a ciki

“Koma mene ne, ina nan, kina jina, ina nan tare dake.”

Kai take daga mishi tana jin hawayen da suka cika idanuwanta suna zubowa.

“Kin gani, babu yanda zaki goge ganin da kikayi, idan nace miki komai ba zai canza ba zanyi miki karya.”

Kamar yanda baima san me yake ce mata ba, kalamai yake nema, kalaman da zasu tausasa abinda yake tunanin tana ji a zuciyar ta, shisa ya kama dayan hannun nata yana rike shi da nashi, kamar hakan zaisa damuwarta ta koma jikin shi, zuwa lokacin kuka takeyi marar sauti, amman duka jikinta bari yake saboda tashin hankali, bata da gadon babanta, idan bata da gadon shi hakan na nufin ita din ba ta hanyar daya kamata aka same ta ba.

“Kana jinta… Ban.. Banda gadon Baba na, kaji me tace Hamma.”

Ta san sunan shi Kabir, tunda da shi take amfani a makaranta, hakan ne ma ya sa ta gane ba Julde bane baban ta, ita da Nawfal ta san bashi ya haife su ba, shi yana amfani da Bukar ita tana amfani da Kabir. Kwance seatbelt din shi Salim yayi yana gyara zaman shi yanda zai rike hannuwan ta sosai, so yake ya hadata da jikin shi

“Madina ce.”

Zuciyar shi ta fada mishi kamar harda gargadi a cikin yanda tayi maganar.

“Lallashin ta zanyi.”

Ya amsa zuciyar tashi a hankali, sai dai anya zai tsaya iya lallashi? Ba tun yau yake son jinta a jikin shi ba, ba tun yau suke zama a mota yake duk wani kokari da zai iya na ganin ko da hannunta ne bai rike ba. Ko mace ya raba da kirjin shi zai fara tunanin yanda zai kasance idan Madina ce, ya rasa lokacin da hakan ya fara, kawai tsintar kan shi yayi a tsakiya, ya kuma rasa yanda zai ya fita. Yanzun ma da hannun ta yake cikin na shi yana jin dumin shi har kasan ran shi. Idan ya rike ta a jikin shi ba zai taba tsayawa a lallashi ba ya sani.

“Baki sani ba Madina, karki fassara duk abinda kika gani a cikin rubutun nan, zai iya nufin komai, kar mu ce zamu bashi fassara daya, umm?”

Ya karasa yana dan jan hannun ta da take kokarin zamewa, bai kokarin hanata ba, hawayenta ta goge tana jinjina mishi kai, so take ta yarda da shi, kalaman shi su zame mata igiyar da zata kama dan jinta take cikin wani irin rami, ko bata fito ba, ya zamana tana rike da igiyar, hakan zaisa taji kamar tana da zabi a fitowa daga ramin.

“Ki mayar da takardar nan inda kika dauka, ki jira Daada, ki jira ta fada miki da kanta.”

Kai take jinjina mishi, yana ganin yanda kalaman shi suke zauna mata.

“Kirjina yana mun ciwo.”

Ta fadi wasu sababbin hawayen na zubo mata, sosai yarintar da take tare da Madinar ta bayyana a yanayin yanda tayi maganar da kukan daya kwace mata bayan hakan, lumshe idanuwan shi Salim yayi yana sake bude su a kanta

“Kukan ne bana so ai, zai bari idan kika daina…”

Hannu tasa ta goge hawayen ta, kara matsawa Salim yayi yana kama hannun nata yayi amfani da shi wajen kara goge mata fuskarta, tsoron ya kai nashi jikin kuncinta kai tsaye yakeyi

“Idon zai kara kankancewa, ki rufa mana asiri Madina”

Dariya tayi mai sauti, duk da ta sake hadowa da wani kukan, shima dariyar karfin hali yayi, gabaki daya wani iri yake jin shi

“Kin ci abinci?”

Ya tambaya bayan ya koma ya gyara zaman shi akan kujerar, kai ta daga mishi

“Tun dazun.”

Duk da bata gane kan abincin ba taci, saboda bata so Daada tayi mata magana, ko ta tambayeta mai yasa bata ci abinci ba. Yanda Madina take kallon shi yasa shi fadin,

“Kina son wani abin muje mu siyo?”

Kai ta girgiza mishi.

“Littafi?”

Dariya tayi.

“Da gaske nake yi.”

Kai ta girgiza mishi.

“I will be fine…”

Ta fadi da wani irin sanyin murya duk da bata jin zatayi dai-dai din.

“Karki yi mun karya, bana so, kar ki fara boye mun kina jina?”

Da sauri ta daga mishi kai,

“Dare yana yi, ki koma gida, da safe zan zo in kaiki makaranta In shaa Allah…”

Murfin motar ta bude ta sauke kafafuwan ta a waje.

“Mug.”

Ya kira, juyawa tayi da murmushi a fuskar ta, haka yake son gani, murmushin nan, ko kadan bayason yaga fuskarta babu shi.

“Komai zaiyi dai-dai, kina jina, ko babu su, kina da mu, mu kadai ne daman, tuntuni mu kadai ne, kar tunanin su ya dame ki da yawa.”

Numfashi ta sauke.

“Mu kadai ne daman, tuntuni mu kadai ne.”

Ta maimaita cikin kanta, kalaman na zauna mata, tunda ta bude ido su kadai din ta gani, ita da Daada, kafin ta ga su Daddy, su kadai ne kamar yanda Salim ya fada, daga Yelwa har Kabir basa nan, basa tare da ita tun daga farko, ganin takardar nan ba zai kawo su ba in har suna raye, shekaru sha shida suke da shi su zo inda take, duk basu zo ba. Ba zasu dame ta da yawa ba, ba zata basu wannan muhimmanci ba, watakila a gaba, amman yanzun bata jin zasu same shi. Kamar Salim yaji tunanin da take yi.

“I love you.”

Kalaman suka subuce suna komawa cikin kunnen shi da wani yanayi da ba zai misaltu ba, tunda yake, ko da wasa, ko a mafarki bai taba furta su ba, babu wanda ya taba furtawa, duk da su Adee na yawan fada mishi, amman bai taba mayar musu ba, idan basu gane yana son su a kananun abubuwan da yake musu ba, to baya jin dan ya fada zai canza wani abu, sai gasu yau kalaman sun subuce mishi kamar bashi da iko da su. Dariya Madina tayi tana kallon fuskar shi.

“Nawa yafi yawa, na gode Hamma.”

Ya kasa ko motsin kirki sai ta fita harta rufe mishi murfin motar, ba shiri ya zare seatbelt din yana fitowa, harta shiga gida, da kusan gudu ya bita yana kiran sunan ta, da mamaki ta juyo, numfashi ya sauke yana kai hannu ya yamutsa sumar da yake askewa kasa sosai, amman yanda take a nannade duk da bamai yawa bace zai sa kagane ya hada jini da fulani.

“Ki fada in ji.”

Ya tsinci kan shi da fadi, yana so yaji ta furta kalaman ko zai samu saukin cewa shi sun kubce mishi, yana so yaji ta furta dan ta nuna mishi itama a wajen ta suna da saukin fita kamar a wajen su Khalid, kalaman basu da nauyin da yake jin sun mishi.

“I need to hear you say them, Mug.”

Ya fadi yana saka idanuwan shi cikin nata, ita kuma da mamaki take kallon shi, saboda tana tunanin meye yake so ta fada din.

“Mug…”

Ya kira wannan karin muryar shi na fitowa a kagauce, numfashi ta ja

“Oh…”

Tana tuna me ya fada a karshe.

“Mi yedi ma Hamma Am, ina son ka.”

Numfashin da bai san yana rike da shi ba ya saki yana jinjina kai, kafin ta sake fadin wani abu harya juya. Motar shi ya koma ya kunna yana janta ya fita daga unguwar, yakan ja gilasan ne ya rufe saiya kunna AC din ciki saboda ya rage ma kan shi hayaniyar kan hanyar. Amman yau iskar da take cikin motar yake jin tayi mishi kadan, shisa ya sauke gilasan gabaki dayan su, yana shakar iskar da ta shigo, tana fifita mishi wajajen da baima san yayi zufa ba.

Ba gida yayi niyyar nufa ba, shisa da ya gan shi bakin gate, yaga an bude mishi yasan Allah ne kawai ya kawo shi lafiya, hankalin shi gabaki daya baya jikin shi, shiga yayi da motar ciki, kila idan ya watsa ruwa ya dawo dai-dai. Sai dai yana fitowa daga motar yana cin karo da Julde cikin wata shadda mai maiko da ta karbi jikin shi. Shisa duk yanda za’ace yana da kyau baya mamaki, in har yayi rabin kyawun Julde to tabbas za’a kira shi me kyau, ko shi da kan shi ma zai ga kyawun na shi.

Har yanzun hasken fitilar kyawun Julde zai dishe na shi duk da bambancin shekarun da yake tsakanin su.

“Daddy…”

Salim ya kira yana dorawa da gaisuwar da Julde ya amsa fuskar shi dauke da murmushi

“Ya makarantar? Har an dawo?”

Kai Salim ya jinjina.

“Zan sake fita, ina so in dan watsa ruwa ne.”

Da murmushi a fuskar Julde har lokacin ya ce.

“Allah ya taimaka yayi jagora. A dinga kula dai.”

A cikin zuciya Salim ya amsa addu’ar Julden yana wucewa, har yayi gaba ya juyo.

“Daddy”

Ya kira yana sa Julde juyowa shima ya kalle shi, dan har ya bude murfin mota

“Wace ce Yelwa?”

Ya jefi Julde da tambayar da yaji kamar fadowar gini, babu shiri ya nemi majingini da motar da yake tsaye a jiki, saida ya tabbata muryar shi ba zatayi rawa ba tukunna ya amsa da

“Kanwata ce.”

Kai Salim din ya jinjina, haka kawai ya tsinci kan shi da son sani, ko iya hakane, alakar da take tsakanin shi da Madina, ya san yar uwar shi ce, amman yau yana son sanin me suka hada. Juyawa yayi, Julde na bin bayan shi da kallo har ya bace mishi, tambayar ta dake shi, a ina yaji sunan Yelwa? A ina Salim yaji sunan da yake da tabbacin ko Saratu ba zatayi kuskuren furtawa a gaban yaran ba. Ba zama sukayi sukai shawara ba, basa bukatar sanin ya kamata su kare yaran daga abinda ya rabo su da asalin su.

Sai dai wasu sirrikan basa binnuwa

Wasu sirri kan ko ba’a tono su ba sai sun bayyana kan su.

<< Rai Da Kaddara 12Rai Da Kaddara 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.