Sake runtsa idanuwan ta tayi a karo na babu adadi, saboda duk lokacin da zata bude idanuwan sai ta dinga jinta a wata duniya tsakanin rayuwa da wani abu da ba zata iya kira da mutuwa ba tunda bata san yanda take ba. Ko wacce gaba ta jikinta ciwo takeyi, ga kirjin ta da yayi nauyi tamkar an dora wani irin dutse a saman shi.
“Daga jikin wa ka baro ka taho?”
Kunnuwan ta sun jiye mata wannan kalaman, idan ba karya suka isarwa kwakwalwar ta ba tabbas muryarta Saratu ce, a tsayin shekarun nan duk wasu kalamanta na rashin kirki ta koyi takaita su ne akan Julde kawai, shisa zuciyar Daada take hasasa mata cewa wannan karin ma da Julden take, wani irin hijabi taji ya gifta tsakanin ta da zantukan su Saratun shisa ta hakura tana barin duhun da ya janyeta yin nasara.
“Daada ga Hamma can ana dukan shi a gonar mai saje, kiyi sauri kizo, kiyi sauri kar su illata shi.”
Yelwa ta sauke kowacce kalma a tsakanin numfashin da take kokawa da shi cikin alamun gudu tayi, a cikin harshen fulatanci, murfin tukunyar tuwon da Daada ta gama tukawa ta dauka tana rufewa, kafin ta daga idanuwanta tana sauke su kan Yelwa cike da nutsuwar da zakayi mamakin ta a tattare da mahaifiyar da aka zo ma da sakon ana dukan danta. Sai dai bashi bane karo na farko, ba kuma na biyu bane ba, idan Daada zata runtsa idanuwan ta, lokutta irin wannan zasu bace a tunanin ta, ba zata iya lissafa adadin su ba saboda yawaitar faruwar su.
“Daada ki ta so.”
Yelwa ta sake fadi a kagauce, murmushi Daada tayi, murmushin da taji ya fito daga tsakankanin zuciyar ta inda yake yawaita yi mata ciwo da labarai irin wa’annan.
“Me zan musu Yelwa? Zan iya hana su dukan shi ne?”
Kai Yelwa ta girgiza cikin alamar rashin yarda, daga inda Daada take zaune tana ganin kyallin hawayen da yake cike da idanuwan Yelwar, kafin ta kai hannu tana daukar muciyar da take a jingine da bango, ko gama bushewa daga wankin da Daada tayi mata ba tayi ba.
“Ba zasu kashe shi ba, ba zan bari su kashe shi ba Daada.”
Yelwa ta karashe maganar tana kai dayan hannunta ta dauke hawayen da take jin alamun zubowar shi tana juyawa.
“Allah ya tsine miki albarka idan kika saka kafa kika fita daga cikin gidan nan.”
Ta tsinkayo muryar Datti a masife da ta saka kafafuwanta tsayawa cak.
“Kin jini ko Yelwa? Allah ya tsine miki albarka idan kika fita daga gidan nan.”
Juyawa tayi tana fara sauke idanuwan ta kan butar da take hannun shi, daga bandaki ya fito. Yana gidan kenan? Dariya Yelwa tayi me sauti,
“Ki bari su kashe shi, Allah ya basu sa’a su kashe shi.”
Wannan karin hawayen Yelwa zubowa su kayi.
“Asarar tawa ce ni kadai idan sun kashe shi na sani…”
Ta ce tana sake kai hannu ta share kuncin ta, tana kara ba wasu hawayen damar zubowa, kafin ta janye idanuwan ta daga na Datti tana sauke su cikin na Daada.
“Muna da junanmu, ni da shi, ki fada mishi Daada, ya kara tsinuwar shi akan jerin na baya…”
Yelwa ta karashe tana juyawa ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga cikin gidan, sautin tsinuwar da Datti yake jera mata nayi mata rakiya.
“Daada…”
Ta tsinkayi muryar Yelwa na mata kutse cikin duhun da ya janyeta.
“Daada!”
Ta sake jin muryar.
“Ki barta tayi baccin ta.”
Ta tsinkayi wata murya da take son gane madaukinta.
“Idan naga ta bude idanuwan ta ko kadan ne zan samu natsuwa Hamma…Daada!”
Sai dai a karo na farko ta raina karfin ta, saboda yanda take kokawa da fatar da take lullube da idanuwan ta cikin kokarin bude su. Hannun da taji kan nata ya kara mata karfin gwiwa, da kyar ta iya bude rabi tana ganin dishi-dishi, ta mayar ta rufe, tana sake kokartawa wannan karin dan gabaki dayan shi ta bude shi.
“Madina”
Ta fadi cikin zuciyar ta, ganin gilashin da yake fuskar ta, ba Yelwa bace ba, Madina ce, tunani ne ya dibeta zuwa baya, babu wani abu. Tabaro wannan rayuwar, tayi nisa da ita. Inda take yanzun ba can bane ba, tana tare da Madina, tana tare da sanyin idaniyar ta, tana tare da yarinyar da ta saukaka ciwon da yake cikin kirjinta.
“Daada…”
Madina ta fadi da murmushin nan nata da yake sanyaya wajaje da dama a tare da Daadar.
“An mata allurar bacci ne fa, me yasa ba kya jin magana ne?”
Salim yace yana jin muryar shi ta fito da wani irin sanyi da baiyi tsammani ba, fada yaso yayi mata, a fadace ya jera kalaman cikin kan shi, a tsakanin ratsowa ta cikin kan zuwa makoshin shi suka sanyaya haka, tafi minti sha biyar tana son tashin Daadar yana hanata, har bakin shi ya fara nauyi da yanda take ta saka shi yawan magana. Rigar ta da shi kan shi ta mishi yawa ya kama ta baya yana janyo ta baya kamar ya jawo ledar da babu komai, kafin tayi wata garda ya sa kafar shi ya jayo kujera yana fisgarta ya zaunar a kai.
Bayan yatsun shi biyu da manuniyar da na tsakiyar ya hade waje daya yayi amfani da su yana kai mata duka a goshin ta har saida ta runtsa idanuwan ta dan taji zafi sosai tana fadin,
“Ouchhh Hamma…”
Hadi da murza wajen tana turo labba.
“Ki zauna nan, nagaji da Magana.”
Bakin dai ta sake turowa har lokacin tana murza goshin ta, Daada ta kalla, ta sake mayar da idanuwan ta rufe, yanayin yanda take numfashi na nuna alamar bacci ya sake dauke ta, agogon da yake daure a hannun shi Salim ya duba, sam bai san lokaci ya ja haka ba, shisa yaji kan shi yayi nauyi. Bacci ne sosai a idanuwan shi, gashi aikin dare yake da shi yau ma, mikewa ya yi.
“Zanje gida in watsa ruwa in dan kwanta, ki kirani idan akwai wani abu, anjima zan dawo.”
Kai Madina ta jinjina mishi, tun dazun yake ta hamma, da tace yaje yayi bacci kai ya girgiza mata, itama bata son zama ita kadai, taji dadi da Adee ta zo, amman bata wuce awa biyu ba tace zata koma dan ta dake dora musu abincin da zata kawo da daddare, zasu sake dawowa da mijinta. Julde ma kiran da ake ta mishi a waya yasa Salim ya lallaba shi ya tafi bayan ya tabbatar mishi da cewa babu komai, bacci Daadar takeyi saboda ana so ta huta sosai.
“Ka siyo mun awara idan zaka dawo.”
Numfashi Salim ya fitar.
“Ina zan ga awara?”
Shagwabe fuska tayi.
“Akan titi fa, ko ina zaka ga ana soyawa, ba mun taba siya ba rannan?”
Kai Salim ya girgiza.
“Rannan din kinsan wacce hanya ce? Kibari idan muka fita tare.”
Yanda tayi da fuska tana kai hannu ta sake tura gilashin ta sai yaji gwiwoyin shi sun yi sanyi, kananun abubuwa haka zatayi duk sai yaji ta kashe mishi jiki.
“Fine, idan nagani.”
Murmushin nan ya samu da takanyi da dukkan hakoranta, tana saka shi mayar mata da martini.
“Ina kudin da Daddy ya baki?”
Hannu ta fara kaiwa aljihun wandon da yake jikinta, tana saka shi girgiza mata kai.
“Ba sai kin dauko ba, idan kina son wani abu ki fita ki siya, inda muka siyo ruwa dazun, zaki gane ko?”
Kai Madina ta daga mishi kafin ya sake numfasawa.
“Ki kula kina ji? Ba zan dade ba.”
Kan dai ta sake daga mishi, ji yake kamar karya tafi ya barta, amman ko baya bukatar hutu yana son watsa ruwa ya sako kaya. Dakyar ya iya jan kafafuwan shi yana fita daga dakin. Gyara zamanta Madina ta karayi akan kujerar tana jingina sosai, ita ma baccin ne a idanuwanta. Ta kusan mintina biyar a haka kafin ta ja kujerar har kusa da gadon Daada, kanta ta dora akan gadon daga gefe tana runtsa idanuwanta.
“Allah ya baki lafiya Daada… Allah ya baki lafiya.”
Ta furta cikin ranta, addu’a ce da tun da suka shigo asibitin ta dan samu nutsuwa take ta furtawa cikin zuciyar ta. Sanin ba bangaren hannun da ake karawa Daada ruwa bane ya sa ta lalubo shi tana dumtsawa cikin nata, akwai wajaje da dama da ko da wasa ba zata bari tunani ya dauketa ya kaita ba, cikin su har da rasa Daada. Shisa ta sauke numfashi mai nauyin gaske tana sake runtsa idanuwan ta cike da neman baccin da yake cike da su.
*****
Yau kwanaki biyu kenan da sallamar Daada daga asibiti, ta ji sauki sosai, sai yawan baccin da takeyi da kuma rashin karfin jiki da ba za’a rasa wanda ya warke ciwo da shi ba, tunda lafiya ce kadai abinda yake kwace maka a yan mintina, amman dawowar ta sai ta dauki lokacin da baka ma yi tunani ba. Madina ta ji dadin kasancewar lokacin cikin hutun da suka samu na tsakanin Waec da Neco. Ko da ace babu hutu ba zata iya tafiya ko ina tabar Daada ba, shisa duk nacin ta da makaranta ta hakura da islamiyya sai ta ga Daada na hidimarta kamar ko da yaushe.
Da wuri ta gama miyar ta da ta sha naman kaza, Julde ya zo ya kawo musu cefane jiya. Ya karo musu kajin da suna da saura a fridge tun wancen karin, farar shinkafa ta dafa, ta fita da kanta tana samun yaro ta aika ya siyo mata salak da tumatir ta yayyanka, kafin sha biyu harta gama gyara ko ina tsaf. Ko da ta idar da sallar azahar ma ta tashi Daada tayi itama, ta samu ta bata abincin da ta dan ci kadan, magungunan rana ta bata sannan ta sake komawa bacci.
Matar da tayi wa alkawarin kunshi tun satin daya fita ce ta zo, ko da tayi mata ya mai jiki Madina batayi mamaki ba sam. Ta san matar ta shiga makota ne ake fada mata, Daada mai mutane, yanda aka dinga zuwa asibitin dubata har mamaki ya dinga bawa Madina, wasu ma ita bata san su ba, duk yawanci basu zo hannu biyu ba, wata mata da kallo daya zakayi mata ka fahimci halin rashin da take ciki dan rake ne ta zo da shi a bakar leda irin wanda ake siyarwa a datse, yanayin karfin halin ta sai da ya taba Madina ba kadan ba.
Kirki abune da ba sai mai hali ba, kowa ma zai iya kamantawa in dai akwai shi a zuciya. Matar ma da ta zo kunshin harda lemon zaki da ayaba ta riko
“Munyi waya da Maman Anisa take fadamun an sallame ku.”
Godiya sosai Madina tayi mata, kunyar matar ta sata hada lallen tunda baki ne take so, ta zana mata a bayan hannu da tafuka, basu wani dauki lokaci ba, yana shan iska tace zata tafi gidan Maman Anisan ya karasa bushewa acan sai ta wanke. Yanda duk tayi da Madina kin karbar kudin kunshin tayi, ko dan alkawarin da tayi ma matar ta saba mata ba zata karba ba. Haka sukayi sallama suna ma juna godiyar karamcin daya gifta tsakanin su, Madina ta tattara kayan kunshin ta tana nade tabarmar ta koma cikin daki. Ganin hudu harda minti biyu ya sa ta nufi dakin ta ta shiga bandaki dan gabatar da uzurinta ta fito bayan ta dauro alwala. Sanda ta shiga dakin Daada ta sameta harta tashi tana sallah.
A gefe ta raba itama tana fara gabatar da tata sallar, ta idar tana dorawa da azkar din yammaci kafin ta jero tarin bukatunta.
“Ya jikin Daada? Ko kina marmarin cin wani abin in dafa miki?”
Kai Daada ta girgiza mata.
“Alhamdulillah, da sauki sosai.”
Hannu Madina ta kai tana taba kuncin Daada.
“Babu zazzabin fa, na ce miki yayi sauki.”
Daada ta fadi da dan murmushi.
“Allah ya karo miki lafiya Daada Am… Kinga wata tazo kunshi ta kawo miki lemo da ayaba da yawa, yar uwar Maman Anisa ce…”
Kai Daada ta jinjina.
“Allah ya saka mata da alkhairi, nagode sosai kuwa.”
Suna da sauran fruits da Julde ya kawo, wannan dinma duk a fridge ta hada ta samar musu wajen zama.
“Ko in kara kawo miki ruwa?”
Kai Daada ta girgiza, babu wani abu da take bukata, matsawa kusa da ita Madina tayi yanda zata iya dora kanta a jikin damtsen hannun Daadar tana jingina da ita sosai.
“Karasa ni zakiyi daga farfadowa ta?”
Dariya Madina tayi saboda tana jin zolayar da take cikin muryar Daadar.
“Idan na karasa ki in zauna da wa? Hutawa kawai nake danyi, kwana biyu banji dumin ki haka ba.”
Dan kallon ta Daada tayi
“Kaji karya fa, ina ce ko a asibiti a bayana kike kwanciya.”
Dariya Madina tayi, jiyama a bayan Daadar tayi bacci, lokutta da dama tafi son jinta makale a jikin Daada, ta zagaya hannunta a cikinta tana saka nata hannun cikin na Daada ta hada yatsun su waje daya. Wasu ranakun ma ko baccin rana a jikin Daada takeyi. Karar wayarta da ta bari a falo ya sata raba jikin ta da na Daada, saboda tasan babu wanda zai kirata in ba Salim ba, har yanzun babu wanda ya san tana da waya, bata samu nutsuwar da zata kikkira mutane da ita ba.
“Hamma…”
Ta furta bayan ta daga wayar ta kai kunnen ta.
“Ina kofar gida, yunwa nake ji, me kika dafa?”
Murmushi tayi, yana tuna mata da ita ma bata ci abincin ba.
“Ka shigo sai muci, nima banci abinci ba.”
Bai amsata ba ya kashe wayar, ta sauke ta daga kunnenta tana ajiyewa akan kujera, dakin Daada ta koma.
“Hamma ne ya zo…”
Kai kawai Daada ta daga mata batare da tace komai ba, Madinar ma juyawa tayi, tana shiga kitchen taji sallamar da Salim yayi, daga kitchen din ta amsa shi. Tana zubo abincin a plates guda biyu ta fara kawowa sannan ta hado musu miyar a kwano daya tana sake kawowa, ta samu wani waje ta zubo salak din da kayan hadi. Kafin ma ta dauko ruwa ta dawo Salim harya sakko kasa yaja na shi plate din ya fara ci, tun safe rabon cikin shi da wani abu, shima shayi ne ya sha dan Saratu na mishi fadan cewa ba inda zai fita bai saka wani abu a cikin shi ba.
“Baka zama kaci abinci ko Hamma?”
Madina ta fadi tana kallon yanda idanuwan shi sukayi zuru-zuru, ya wuce ace yunwar yini daya ce,
“Gashi ina ci yanzun.”
Ya amsa, kai kawai ta girgiza, in dai akan abinci ne Salim din kamar karamin yaro haka yake, wata rana idan ya zo sai ta zuba mishi ya tafi da shi, ko ta tsare shi ya ci, sai yace mata aiki ya mishi yawa, ko yunwar ma baiji ba. Ya rigata cinye abincin shi, harya koma plate din ta suka cinye tare.
“Ina karo maka?”
Kai ya girgiza mata, ita ce ma ya kamata ta kara, ya san Madina kamar yanda ta san shi, idan tana so ta karo ba zata jira ya fada mata ba. Cikin ta na daya daga cikin abinda bata wasa da shi ko kadan. Kwanonin ta tattara tana mayarwa kitchen ta dawo ta zauna, yatsun ta ya bi da kallo.
“Kunshi kikayi ko?”
Ya furta yana jan jikin shi kusa da ita ya kamo hannun ta, bakin da yatsun ukku sukayi har ya fara ragewa dan zaman asibitin da sukayi.
“Wata mata nayi wa dazun…”
Kai kawai ya girgiza.
“Kina bata hannun ki, na ce ki dinga saka safar hannu.”
Dakuna fuska tayi.
“Ni wani iri fa, bayamun dadi shisa.”
Jujjuya hannun nata yakeyi cikin na shi.
“Jibu farcen ki.”
Dayan hannun ya dago tana dubawa, shima duk ya taru.
“Daada ce take yanke mun, ban iya ba da reza.”
Kai kawai Salim ya girgiza yana mikewa. Yana jinta tana binshi da idanuwa, baifi mintina hudu ba ya dawo yana zama in da ya tashi. Hannun ta na dama ya kamo.
“Waye yace da reza zaki yanke?”
Karamin yatsanta ya fara kamawa sannan ta kula da nail cutter din da yake rike da shi. Tunda yake mutum daya ya taba yankewa farce, sam baya son yaga kumba ta taru a hannun mutum, yana mishi kazanta ba kadan ba.
“Kalli farcen ka Bajjo.”
Ya fadi bayan Nawfal din ya mika mishi remote din daya bukata.
“Ni banga mai gyaran farce ba, ni kuma ban iya yankewa ba.”
Zai tuna yanda yaja karamin tsaki, yana mamakin yanda kato kamar Nawfal zaice bai iya yanke farcen shi ba, menene a ciki? Ka sa nail cutter din ka datse? Shi kusan duk kayan shi zaka samu nail cutter a ciki, in dai ya gani saiya siya, ko a mota yana da sunfi biyar, baya so ma ya zo ya nema ya rasa. Nawfal din ya sa yaje daki ya dauko ya dawo.
“Kai dai katon banza ne Bajjo.”
Ya furta yana kama yatsan Nawfal din da yayi dariya kawai. Ya dauka ranar ce ta farko kuma ta karshe, sai yanzun da yake rike da na Madina, daya bayan daya haka ya kama yana yanke mata harya gama tsaf.
“Kafar fa?”
Batayi musu ba ta zare safarta guda daya tana mika mishi kafar.
“Me yasa kike rufewa?”
Ya tambaya ganin kafar tas, ga kunshin jan lalle da tayi. Ba zai yiwu ace idanuwa shi bane kawai suka ga kyawun kafarta, idan yana da irin wannan kafar baiga dalilin da zaisa ya dinga kunsheta cikin safa ba.
“Bana so tayi kura ne fa, iska yana shigar mun kuma.”
Numfashi Salim ya sauke, farcen kafar bai wani taru ba, idan na shi ko bai kai haka ba zai yanke, amman kafar ta Madina ce, bai yarda da kanshi cewa zai tsaya a riketa ba kawai.
“Na kafar bai taru ba ai…”
Kai ta jinjina mishi tana janye kafarta ta mayar da safar, dan yaji yana wani abu da hannun shi da yake kaikayin son taba kafarta yaji ko laushin da yake gani a idanuwan shi zaiji shi har a tafin shine ya sa yabi duka farcen daya yanke mata yana tattara shi ya saka a hannun shi guda daya ya mike ya nufi kitchen, ya kuwa yi sa’a akwai kwandon shara a ciki, ya zuba ya karasa sink ya wanke hannun shi, sai da ya bude fridge ya sake shan ruwa ya dan tsaya ya mayar da numfashi tukunna ya fito. Yanayin da yake ji ma ba zai iya zama ba.
“Tafiya zanyi.”
Ya fadi da wani sanyin murya da ya sa Madina kallon shi.
“Tun yanzun?”
Ta furta, kai ya daga mata.
“Baku gaisa da Daada ba.”
Sai daya lumshe mata idanuwan shi yana sake bude su, tukunna ya girgiza kai.
“Ki ce ina gaishe ta.”
Mikewa Madina tayi, daman tace mishi ne ba dan ta sa rai zai amince ba, jiya ma sa’a taci bai musa ba ya shigo suka gaisa da Daadar, tama fi alakanta yardar shi da son sake duba jikin Daadar tunda taji ya mata wasu yan tambayoyi kan yanda take jin jikin. Shi ba ko yaushe yake son gaisawa da kowa ba, ko su Julde ma yana iya sati banda.
“Daddy…”
Ko
“Nanna”
Da zai furta cikin sigar gaisuwa ya wuce, wata gaisuwa mai tsayi bata hada su ba, Khalid ma da suke bangare daya, yana iya gaishe da shi ya wuce batare daya amsa ba, ranakun daya amsa din kuma idan sun sake haduwa da yamma sai Khalid din yace zai kara gaishe da shi.
“Wai ba ka gaisheni dazun ba?”
Ya kan fadi a zafafe, amman ko a jikin Khalid, da dare ma in ba ya watsa mishi zagi ba saiya kara gaishe da shi, baya so, ko kadan, tunda sun ga juna ai ya wadatar, kowa ya ga lafiyar kowa, meye na wahalar motsa labba in ba neman surutu da sassafe ba.
“Sai munyi waya ko?”
Madina ta bukata ganin ya shiga motar shi baice mata komai ba, yau yan rashin surutun sun motsa mishi, kai kawai ya daga mata yana jan motar shi, tsaye tayi da murmushi a fuskarta harya bace ma ganin ta. Hamman ta kenan, kamar mai aljanu, lokaci daya suna cikin hira zaiyi dif kamar bai taba surutu da ita ba, duk abinda zatace da kai zai ta amsa ta, karshe ma yace mata shi tafiya zaiyi, ko da wasa ranta bai taba baci ba tunda ta san haka yake, shisa yanzun ma ta koma cikin gida abinta, idan bai kirata ba, ita zata kira shi.
Masha Allah