Da farko tayi tunanin bugun da take ji cikin kanta kwakwalwar tace take kokarin yaki don samun hanyar fita daga kokon kanta bayan shafe tsayin daren da littafi rike a hannun ta, ba karamin mamaki tayi najin kiran assalatu a kunnen ta ba. Da kyar ta karasa azkar tana zuwa ta gaishe da Daada da fada mata kan ta na ciwo zata kwanta, ta kai wasu dakika kafin ta fahimci hayaniyar ba daga cikin kanta bane ba, bugun kofa ne da yake fitowa daga wajen dakin.
“Ughhh.”
Ta fitar da wani sauti daya fito daga makoshin ta, me yasa yanzun? Duk ranaku me yasa yau? Me yasa sanda take matukar bukatar jin shiru don samun rama ko kadanne daga cikin baccin da tayi sakacin rasawa a daren jiya? Hannu ta kai gefen gadon ta in da tasan gilashinta yana nan ta dauka ta saka a fuskarta ta batare da ta bude idanuwanta ba, dakyar ta iya sauko da kafafuwanta daga kan gadon tana jin kanta kamar an dora jakar kaya saboda nauyi.
Ba karamin yaki tayi da jikin ta kafin ya yarda ta rabashi da gadon ba, tana samu ta bude idanuwanta ta nufi hanyar kofar da bugunta yake ta karuwa. Sai da tayi wata hamma kamar da bakinta zata bude kofar sannan ta mika hannu tana murza hannun kofar tunda ba mukulli bane a jiki. Kafafuwan shi ta fara gani, babu takalma, sai alamar wandon farin yadin da yake sanye da shi, ta kasan gilashin tasa hannu tana murza idanuwanta, ta san mai kafafuwan, tana son dai tabbatar da ba bacci bane yake sakata gane-gane.
“Hamma kafar ka kamar ta mata, zatayi kyau da kunshi.”
Maganar da ta taba fada mishi na dawo mata, tana sakata daga kanta ta sauke shi kan fuskar Nawfal da yake tsaye ya harde hannayen shi a kirjin shi yana kallon ta da murmushi a fuskar shi.
“Hamma…”
Ta kira kamar wadda tayi gudu saboda mamakin ganin shi.
“Daada tace kanki na ciwo, nace karya kike, bacci ne bakiyi ba kin tsaya karatu.”
Dariya tayi, kafin tayi murmushi mai sauti, tana sake wata dariyar saboda ba zatace ga abinda take ji ba, cikin su dai harda sautin bugun zuciyarta da take jin ya karu, da yakan karu ko da tunanin shi tayi, ko kuma taci karo da sakon shi a wayarta kamar yanda sukan yi magana ko da ba kullum bane tunda tayi tata wayar.
“Hamma…”
Ta sake kira a karo na biyu sauran kalaman na makale mata, ko jiya ya tambayi ya take ita da Daada, amman baice mata zaizo ba.
“Ki koma baccin ki, zan ganki ne kafin in wuce.”
Yanda ta zare mishi idanuwa yasa shi girgiza kai yana dariya.
“Gida zanje in huta, daga airport nan nayo… Zan dawo sai anjima…”
Nata kan ta jinjina mishi da murmushin da yaki barin fuskarta har lokacin. Tana kallon shi har ya juya, tana jin tarin maganganun da take son fada mishi, amman ta rasa ta inda zata fara.
“Hamma!”
Juyowa ya yi.
“Sannu da zuwa.”
Dariyar shi ya sake yi, sai ta ga kamar ya kara canzawa, kamar shekaru sun nuna a jikin shi, ya kara yi mata girma. Ba kuma gashin daya bari a fuskar shi bane kawai, harda wata kamala da take tare da shi ko a yanayin takun shi ba wai iya fuskar kawai ba. Har ya fita daga falon tana kallon shi ta kasa komawa cikin daki, sai ma kofar da ta rike tana lilo a jikinta batare da ta sani ba. Lokacin da ta raba jikinta da kofar dakin Daada ta nufa tana samun ta a zaune rike da Qur’anin ta da Hizb biyu ne.
“Daada Am.”
Ta furta cike da farin cikin da take ji ya cika zuciyar ta taf, ta karasa cikin dakin tana zama gefen Daada hadi da dora kanta a kafadarta kafin ta zame gabaki daya tana kwanciya a jikin Daadar.
“Hamma ya zo.”
Cewar Madina tana rufe idanuwanta, dayan hannunta Daada takai tana zare ma Madina gilashin da yake fuskarta.
“Dagani ki koma kan gado.”
Batayi musu ba ta tashi tana jan jikinta zuwa inda tasan gadon yake badan tana ganin komai yanda ya kamata ba, tunda babu gilashinta. Numfashi ta shaka, hancin ta na cika da kamshin da dakin Daada ne kawai yake yin irin shi, wani dan turare ne madara da tun tashin ta tasan Daada na amfani da shi, in ta diba ta shafa sai taji kamshin bai mata a jikin ta ba, ta daifi son ta shigo dakin Daada ta kwanta ta shaki kamshin anan, ko ta kwanta a jikinta, sai taji shi ya bambanta, har tunani take ko wasu mutanen na da nasu kamshin ne.
Dan in dai hakane to da Salim da Daada suna da wannan kamshin nasu na daban, ita bata da tarar turare, kowanne iri ya sha gabanta amfani takeyi da shi in dai taji yayi mata dadi, tana da su kala-kala, Adee ma in dai zataje tayi mata kunshi bayan kudin da sai sun kai ruwa rana take karba sai ta hada mata da turaruka, Julde kan siyo mata shima, haka Daada, Salim kan shi ba zata kirga adadin lokuttan da ya bata kyautar turare ba, duk kuwa da ta littafai ta shallake kowacce kyauta da take giftawa a tsakanin su.
Ita kam tasan bata da wani tsayayyen kamshi, zata iya jera sati kowacce rana da kalar turaren da zata fesa, amman banda Daada da Salim, kamshi daya sukeyi ko da yaushe, in dai bana jikin su bane ba, to ba karamin kokarin su take gani wajen yin amfani da kalar turaren da har ya zame musu jiki haka ba. Nawfal ba zata tantance yana kamshi ko bayayi ba, saboda kamshin shine karshen abinda yake zuwa mata duk in zata gan shi, takan samu bugun zuciyar ta daya kan karu ya koma mata dai-dai ne, zuwa lokacin kuma sun shiga wata hirar da take saka mata manta duk wani abu da yake wakana a wajen abinda suke tattaunawa.
“Me kika ci?”
Madina tayi tambayar a tsakanin hammar da ta subuce mata.
“Kwai na soya na sha shayi.”
Sake gyara kwanciya tayi, tasan akwai ruwan zafi a flask tunda ita ta dafa da daddare, kuma Julde da yazo ya kawo musu biredin da tafi so mai kwakwa, shisa ma ta koma baccin ta bayan tayi sallah dan tasan Daada zata sha shayi babu wani abu da zatayi banda share-share in ta gama baccin. Lumshe idanuwan ta tayi, Daada na kallon ta, ko ba bacci takeyi ba yanzun da babu makaranta sai takai karfe tara na safe bata karya ba, yau gashi goma na neman yi. Baccin kuwa Madina ta koma dan shine a idanuwanta.
*****
A gidan Daada yabar akwatin shi saboda ba zai iya daukar kayan ba a yanda yake jin shi. Jakar ratayawar kawai ya dauka. Kudin da ya sallami mai mashin din daya kaishi gidan daga airport ma a wajen Daada ya karba, haka wanda zai kaishi Hotoro. Murmushin da yayi ma maigadi ma yanajin yanda ya bayyana kan fuskar shi da duk gajiyar da yake tare da ita kafin ya wuce shi yana kara ma takun shi sauri. Harya daga hannu zai kwankwasa kofar yaji muryar Salim cikin kan shi.
“Dole sai kun kwankwasa zaku shigo?”
Murmushi yayi yana kama hannun kofar da tunanin watakila Salim din ma yana falon. Tunanin shi baiyi karya ba kuwa, zaune Salim din yake ya jingina bayan shi da kujerar, hannun shi na rike da remote, yanda idanuwan shi suke a lumshe yasa Nawfal tura kofar a hankali dan yaga kamar bacci yake. A hankali ya karasa shiga cikin dakin, farar rigar da take kan hannun kujera ta tabbatar ma da Nawfal din Salim daga wajen aiki yake.
“Ina jin idanuwan ka a fuskata.”
Salim yai maganar yana sa Nawfal ja da baya saboda ya dan tsorata shi.
“Hamma mana…”
Ya furta yana saka Salim din bude idanuwan shi daya sauke su kan Nawfal.
“Sai ka gama kare mun kallo zaka wuce? Me yasa mutum ba zaiyi bacci a nutse a falon nan ba?”
Kallon shi Nawfal yake yana murmushi kafin ya bude hannayen shi yana nufar inda Salim yake zaune hadi da fadin.
“Na dawo lafiya, kuma nima nayi kewar ka Hamma.”
Yanda Salim din ya zaro idanuwa yana kaucewa ganin da gaske Nawfal rungumar shi zaiyi yasa Nawfal din sauke hannayen shi yana kwashewa da dariya, har kirji Salim ya dafe kamar yaga wani babban abin tashin hankali, wucewa ciki Nawfal yayi ya karasa dakin su, komai a hargitse yake, babu datti dai, amman ko ya rantse bayajin zaiyi kaffara, anfi wata rabon da a gyara gadon. Kwanciya kawai akeyi ana tashi, da zanin gadon da bargon duk sun hade sun cakude waje daya. Numfashi ya sauke yana zame hannun jakar shi daga kafada ya sauke ta kasa.
Sai da ya fara rage kayan jikin shi tunda farin yadi ne manyan kaya. Yabar singileti da gajeran wando tukunna ya hau gyaran dakin, ya dauko wankakken zanin gado ya shimfida, wannan din dama wasu kayan Khalid din da yayi tunanin masu dattine ya tattara yana saka su cikin kwandon da ya ajiye a dakin don zuba kayan dauda da Khalid baya amfani da shi. Har shara ya sake ya dauki turaruka kala biyu ya fesa. Wanka ya shiga ya fito, wata singiletin ya samu cikin jakar shi da gajeran wando ya saka, da yake babu kaya suna gidan Daada cikin kayan Khalid ya samu wata bakar riga marar nauyi ya saka a jikin shi, bai wani bi takan wando ba dan bayajin Khalid na da wandon da zai mishi.
Yanayin jikin su ba daya bane ba, yafi Khalid tsayi, kuma ya fishi jiki. Kafafuwan Khalid sosai suke mishi kama da sandar snooker, amman bai fada ba saboda Khalid zai zage shi. Kitchen ya nufa saboda yunwar da yake ji, banda shayi baiga wani abu da zai iya ci ba, yunwar da yake tare da ita tafi karfin shayi. Shisa ya fito falon wajen Salim da yanzun ya kwanta kan doguwar kujerar yana fadin.
“Hamma ka bani mukullin motar ka da kudi in fita in siyo wani abu, yunwa nake ji.”
Hannu Salim yakai ya laluba kujerar da yake kwance a kai yana mika ma Nawfal din mukullin.
“Wallet dina na cikin motar, akwai kudi a ciki.”
Karba Nawfal yayi.
“Zan taho maka da wani abu?”
Numfashi Salim ya sauke.
“Ka kyaleni Bajjo.”
Juyawa Nawfal yayi yana komawa dakinsu, da kyar ya iya samun wani 3 quarter da yake tunanin na shine ya saka ya fita. Cikin abokan da yayi yan Najeriya acan sai yaji suna maganar yanda suka ga komai ya canza da sukaje gida, har wasu na nuna kamar aiwatar da hidimar yau da gobe a kasar Najeriya tana musu wahala. Da idanuwa Nawfal yakan bi su kawai. Saboda in yai magana tashi zata iyayin zafi, duka shekarar su nawa a kasar wajen? Shekarun da sukayi a Najeriya ya ninka wanda sukayi a can.
Karatu ya kai shi, yanzun kuma daya kammala ya dawo, yana da tarin burukan da yake son fitowa da su daga cikin kan shi, shisa ya dawo, shisa bai bata lokaci ba duk kuwa da yanda yake ganin son hakan a idanuwa Murjanatu. Zaman su basu fara shi da boye-boye ba, ta sani, tun farko ya fada mata zaman kasar waje ba nashi bane ba, ta yarda, ta aminta da inda duk ya saka kafafuwan shi zata bishi.
“Turai na tana tare da kai Gidado, in da duk zan saka kafa idan taka bata biye ba zanji dadi ba, zan fi so ace ka cire kafar ka ne a wajen kafin in dora tawa”
Ba zai manta yanda ya riketa a jikin shi ba, kamar yanda kalaman ta suka samu wajen zama a zuciyar shi. Bai bata lokaci ba, duk da yana jin shi kamar dan koyo saboda yanayin tukin nan da can ba daya bane ba, taka manyan dokokin tuki ba wani abu bane a wajen mutane da yawa a Najeriya balle kuma wasu kananu, ya sha zagi yafi a kirga daga fitar shi zuwa dawowar shi, dariya kawai suka dinga bashi. Sai da ma ya tsaya inda yaga alamar ana saida kati ya siyi sabon sim din MTN ya kuma siyi katin da zai saka a ciki.
A hankali ya tura kofar dakin ya shiga, sai dai Salim baya falon, shisa ya wuce dakin su. Zagi zai sha idan yace yaje ya kai mishi mukullin mota ko da kuwa ba bacci yakeyi ba. Dankali ya siyo soyayye da gasasshen kifi sai ice cream roba biyu, canjin da ya rage ma Salim a wallet din gabaki daya dari takwas ne. Ba magana zaiyi ba ya sani, ko da kudin sun fi haka, Salim din ya koya musu kashe kudin shi kamar suna kashe na su. Ko motar shi ka shiga, ko dakin shi, abinda duk yai maka in kasa hannu ka dauka Salim ba zai kalle ka ba.
Sosai yaci ya koshi, ya dauki dayar robar ice cream din shi ya kai cikin fridge yana komawa daki. Wayar shi ya dauka ya ciro sim din shi yana saka MTN din, ya kumayi loading din katin, data ya siya saboda zaifi mishi sauki yayi ma Murjanatu magana ta whatsapp, in yaso ita sai ta kira shi daga nata bangaren. Yana budewa kuwa sakkoninta suka fara shigo mishi, sunfi goma, biyu daga cikine na tambayar lafiya da ko ya sauka lafiya, sauran na yanda take kewar shi ne. Murmushi yayi, yana amsa kowanne a ciki.
In tana haka wani sai ya dauka ita kadai take kewar shi, idan yace mata yanda duk take ji bai koyi rabin abinda yake ji ba sai tace zatayi mishi gardama. Sake tura mata wani sakon yayi yana fada mata zai kwanta, zai kuma saka wayar a silent. Dan karta kira ta ga bai dauka ba. Dan kan shi ya fara nauyi, kan gadon ya hau yaja bargo yana rufe kafafuwan shi hadi da lumshe idanuwan shi kafin bacci mai nauyi ya dauke shi.
*****
Ba sai wani ya fada mishi ba, yanayin yanda yaga dakin tsaf ya san aikin Nawfal ne.
“Cikin satin nan fa nake son dawowa.”
Nawfal din ya fada mishi.
“Allah ya bamu aron lokacin.”
Shine amsar da ya bashi, idan ya tambaye shi cikin satin wace rana zai iya cewa shima bai sani ba. Kawai abinda ya sani shine cikin satin zai dawo. Da wahala Nawfal ya tsayar maka da lokaci, ko ya sakama abu lokaci, zai dai fadi abinda yake hasashen zai iya faruwa. Basu kuma sake maganar ba dan lokacin duk da zasuyi waya ko suyi chatting sai yayi musu karanci, zantukan su ba masu karewa bane ba. Da shi ya wuni a wajen aiki yau, duk wani abu da za’ace maka alfarma da kudi basa yin shi a Najeriya zai iya karyatawa.
Dan yagani akan bautar kasar shi, Julde kawai ya sanarwa baya son barin garin Kano, camp din ma da ake zama shi bai zauna ba, a ASAD pharmaceuticals ltd da yake nan Kano yayi bautar kasar shi da bai shige watanni da kammalawa ba, kuma sai yayi sa’ar samun gurbin aiki tare da su, ya karba tunda albashin babu laifi yana da kyau. Ba nan yake hari ba, asibitin Aminu Kano yake so, zai kuma nema da zarar ya kammala digiri din shi ta biyu da yake jiran a fara siyar da form ya nema.
Tunda yana hangen kacokan abincin shi a bokon yake gara ya zage dantse ya nema da kyau, kafin ya sauke numfashin da ya shaka an kwankwasa kofar.
“Shigo”
Ya furta yana kwance agogon da yake daure a tsintsiyar hannun shi.
“Kabani charger din ka Khalid, na bar tawa a asibiti.”
Jikin bango inda socket yake Khalid ya karasa yana ciro cajar, shisa yake da guda uku, daya a mota, daya a gida dayar kuma a office din shi dan gudun samun irin wannan matsalar tunda ya san halin shi da mantuwa. Abu muhimmi ma mantawa yake balle kuma wata cajar wayar da in ba kiran shi akayi ba saiya wuni baibi takanta ba.
“Dole sai kayi zanzaro?”
Salim ya tambaya da murmushi a idanuwan shi duk da yanata kokarin ganin bai karasa kan labban shi ba, kugun shi Khalid ya kalla kafin ya daga kai ya kalli Salim.
“Me zanzaro na yayi?”
Kai Salim ya girgiza, idan yayi magana dariya zaiyi, kwanaki yaga Lukman na kallon wani cartoon a bangaren Saratu, ta gefen ido yaga giccin wani a ciki sai da ya dawo baya ya kara kallo da kyau, ya kwana biyu ko shi kadai yake zaune sai yayi dariya saboda kamar sun kalli kugu da kafafuwan Khalid ne kafin suyi zanen. Har yanayin belt din da yake da yakinin sai da Khalid ya kara huda a jiki sannan ya zauna. Duk gidan babu siriri irin Khalid, ya gama makarantar amman yaki yin kumari.
Cajar ya karba yana share kallon rashin fahimtar da Khalid yake mishi, har ya juya ya dawo.
“Randa duk ka zo asibitin mu, in dai da wannan zanzaron ne, kar ka cewa kowa gidan mu daya Khalid, dan Allah kace kawai kana nemana”
Bude baki Khalid yayi, kafin yace wani abu Salim yaja kofar, numfashi yaja ya fitar yana jinjina kai
“Bakomai, Allah na ganin ka Hamma.”
Ya furta a hankali yana kwance belt din ya cire shi hadi da zaro rigarshi waje. Salim baya bude bakin shi ya fadi maganar da zaka so kaji, yanzun da hirar arziki ce da wahala in ba zai zage shi ba yace ya saka shi magana. Amman da yake ci masa mutunci yayi niyyar yi ya bude baki ya fadi abinda babu wanda ya tambaye shi. Har yayi wanka ya fito yana tunanin yanda duk shekarar babu wanda yayi mishi irin zagin da Salim yayi mishi. Masallaci ya fita yayo sallar Magriba ya dawo.
Inda Nawfal yaje yake tunani, ko gidan Daada zai kwana ne? Ya tambayi kan shi kafin ya dauki wayar shi da nufin kiran Madina yaji ko Nawfal din yana can sai gashi ya turo kofar da sallama, kafa ma ya saka, hannuwan shi rike suke da ledoji
“Madina zan kira yanzun inji ko kana gidan Daada.”
Kai Nawfal ya girgiza mishi yana zare takalman shi a gefe ya sake amfani da kafar shi ya tura kofar. Kasa ya zauna kan kafet yana ajiye ledojin da Khalid ya kawo hannu da nufin dauka Nawfal din ya janye gefe da sauri.
“Ba hali me kyau bane wannan Hamma… Daga ajiye abu.”
Kafar shi Khalid din ya saka yana harbin Nawfal a baya kafin ya sake kai hannu ya ja ledar.
“Hamma mana!”
Ko inda yake Khalid bai kalla ba.
“Ka aike ni ne?”
Robobine na take away da zafin su rau na kuwa, fito da su Khalid ya shiga yi.
“Gidan Adee kaje.”
Ya fadi yana saka Nawfal din kallon shi.
“Robobin gidan ta ne wannan, dan ita kadai naga tana amfani da irin su.”
Kai kawai Nawfal ya jinjina.
“Allah ya yafe maka halin nan da ka kwaso.”
Jin Khalid din bai kula shi ba sai ma roba daya daya bude yasa shi dorawa da.
“Bakin halin da ka koya nake nufi.”
Kafar dai Khalid ya sake sawa yana kai mishi harbin daya kauce wannan karin yana dariya. Yayi kewar su, yayi kewar gida da dukkan zuciyar shi. Zama haka a daki daya da Khalid kawai na kara tuna mishi da duk wani dalili da yake da shi na dawowa gida, duk wani dalili da babu inda zaije ya kira gida sai Najeriya. Yana gama baccin shi Adee ya fara kira, ita kadai ya fadama yana airport, dan sunyi hira ma har sai da ya shiga jirgi. Mashin tace yahau suka hadu a hanya dan ta fito karbar ma mijinta wani sako da aka aika mishi daga Abuja.
Har miyar da zata mishi wajen kwana hudu Adee tayi mishi, da farfesun kifi mai yawa. Takarcen da ta hado mishi tsayawa yayi kawai yana kallonta.
“Kafin matar ka ta dawo ne…”
Ta fadi tana dariya, murmushi kawai ya iya yi mata, kuma ta dawo da shi, danma sai da ta tsaya a hanya yayi sallah a wani masallaci tunda ta san yanda baya son rasa sallar a cikin jam’i in ba da wani babban dalili ba. Adee bata shiga gida ba, saboda shine kuma, tare da Adee ba saiya furta abubuwa da yawa ba, ba sai yace mata bai shiga bangaren Saratu ba, ta sani. Idan suka shiga tare dole zaiji kamar bai kyauta ba, shisa taki shiga dan ta kara mishi lokacin da yake bukata.
“Kai ba zaka ci bane ba?”
Khalid ya bukata yana katse ma Nawfal tunanin da yake yi.
“Bangane bana ci ba? In zo da abu kana mun wannan tambayar?”
Zaman shi Khalid ya gyara yana jinjina kai hadi da tsoma hannu cikin robar farfesun kifin daya bude yana fadin,
“Okay…”
Ganin da gaske yake yasa Nawfal din mikewa. Gudun kar suyi bari yasa Khalid sauke robar kasa suka ci tare kafin su fita sallar isha’i su dawo.
“Bari inga me aka dafa.”
Cewar Khalid, har Nawfal ya jinjina mishi kai zai wuce bangaren su sai kuma ya fasa.
“Muje nima ban shiga ba.”
Sai da Khalid yayi mishi kallon da yake fassara ka tabbata yaga ya da dan daga mishi kai tukunna ya shiga gaba shikuma Nawfal na biye da shi har bangaren Saratu da suka shiga tare da yin sallamar da ta amsa, yanayin fuskarta na sauyawa lokacin da ta dora idanuwanta kan Nawfal. Zaune take kan kujera da dan karamin kwano a hannun ta da farfesun naman rago ne ta zubo, tama tsame duk naman, romon ne take dan diba da cokali tana sha.
“Nanna…”
Nawfal ya furta, Khalid na karbewa da.
“Sannu da gida.”
Ya wuce hanyar kitchen da sauri, idon dai Saratu ta kafa mishi cike da tambayoyin da ya rasa wanne zai fara amsawa duk da bata furta su ba.
“Da zun na zo, ina wuni.”
Ya ce cikin sanyin murya.
“Lafiya lau.”
Ta amsa a takaici tana dauke idanuwan ta daga kan shi alamar ta gama bashi iya lokacin da take tunanin zata iya. Juyawa yayi da nufin barin dakin, zuciyar shi yake jin babu dadi, ita kadai ta tsane shi, duk duniya ita kadai ta tsane shi kuma bai san dalili ba, tunanin duniya yayi ko zai tuna wani abu daya taba yi mata banda zama karkashin kulawar mijin ta da Kawun shi ne, yana da hakkin da zai rike shi ko da ba ita yake aure ba. Me yayi mata da zafi haka?
Numfashin kirki ma bayajin yana shaka in tana waje saboda gudun kar sautin shi ya takura mata, yana da rai amman idan Saratu na nan kokarin gani yake ya zama gawar da ba zata iya gani ba, duk dan ya gujema bacin ranta. Ya gaji, bai san yanda ya gaji ba sai yau din nan. Shisa ya koma yana takawa yaje har kan kujerar da take zaune mai daukar mutum uku ya zauna a gefe yana dora murmushin da bayaji a zuciyar shi kan fuskar shi.
“Na dawo ne gabaki daya Nanna, ba nida nufin zama a garin Kano saboda dalilai da yawa, zaki cigaba da gaba da gani na lokaci zuwa lokaci saboda banda yan uwan da suka wuce su Hamma, ban san me nayi miki ba, koma mene ne ba zai taba zama dalilin da zanyi nisa da yan uwa na ba, yaran kine duka, kiyi hakuri zaki cigaba da raba su tare dani…”
Ya karasa maganar yana mikewa ya nufi hanyar kitchen din, yanajin yanda take bin shi da kallo, nauyin da yake ji a kirjin shi duk idan yagan ta yaji ya daga mishi, tsanar da tayi mishi zabinta ne, ya gaji da raba nauyin tare da ita. Taje ta dauka ita kadai, ko babu wani abu ta bashi su Khalid, shisa take kasancewa cikin addu’o’in shi. Tana da wannan darajar a idanuwan shi, fridge ya bude yana daukar ruwa roba daya.
“Zuba abinci ne kamar zaka dafa sabo.”
Ya ce ma Khalid da yake rike da filet a hannu
“Ina ruwanka?”
Khalid din yace, Nawfal ya amsa da,
“Babu”
Yana ficewa daga kitchen din, murmushi Khalid yayi, ranar farko da yaji dadin karfin halin da Nawfal yayi. Sai dai yana juya maganar Nawfal din da yace bashi da nufin zama a garin Kano, ina yake nufin zai zauna? Shi bai fada mishi ba, watakila sai sun samu zama tukunna. Koma ina ne in dai yana kasar komai zaiyi dai-dai. Tuwon shinkafa ne, zubawa yayi yana dibar malmala biyu dan shi bai cika rike mishi ciki ba, yana iya kai sha biyu a zaune yaji yunwa.