Da kyar yake iya daga idanuwan shi, ya san Allah ne kawai ya tsare mishi hanya daga asibiti zuwa gida.
"Idan ka gaji haka ka dinga kwanciya a asibiti ko baccin awa biyu ne kayi tukunna ka hau titi, ko ka kira Hamma Khalid ya zo ya dauke ka."
Rokon da Madina tayi mishi kenan kwanaki tana dorawa da.
"Kaji Hamma, dan Allah, kaji."
Bai amsa ta ba, saboda inya amsa zai zama kamar yayi mata alkawari ne. Bacci a asibiti ba zai iya shi ba kamar yanda yaga sauran abokan aikin shi sunayi, saboda akwai hayaniya, duk da ofishin. . .