Skip to content
Part 18 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Da idanuwa Saratu take bin shi ba tun safiyar ranar ba, tun sati biyu da suka wuce saboda tambaya babu irin wadda batayi mishi ba akan me yake damun shi yana amfani da damar wajen nuna mata cewa da gaske bata da wani muhimmanci a wajen shi. A tsayin shekarun auren su zata kirga adadin lokuttan da yayi rashin lafiya har ya kwanta, a cikin adadin zatace sau daya ya taba wadda ta kai shi da kwanaki a kwance, wannan kuma rashin lafiya ce da take son shafewa a kundin tarihi idan har tana da halin haka.

Sai kuma satikan nan da suka wuce da alamu duka suka nuna cewa ba ciwo yake ba, ya dai koma kamar wani gunki-gunki ne, abinci haka zai ta wasa da cokali a ciki, a yinin rana baifi ya saka ruwan shayi da yar wainar kwai a cikin shi ba, satin farko ya jera kwanaki hudu yana fita tunda sassafe sai yammaci liqis zai dawo, kafin daga baya ya koma rabuwa da kan gadon dakin shi ma sai yaji su Khalid a falon ne zata ga yayi ta. Suna kuma fita zai koma ya sake bin gadon ya kwanta. Har daki take bin shi da abincin safe, rana da na dare. Yau na safen da na ranar duka haka ta zo ta dauke ta sake fita da su, babu alamar da ta nuna ya ko bude balle ya ci.

Rashin muhimmanci da take da shi a wajen Julde ba sabon abu bane, abune da lokaci bai sa ta daina jin ciwon shi ba, wannan karin dai tunanin halin da yake ciki shiya danne mata ciwon da take ji. Ta na son shi, ta na son Julde fiye da yanda kalamai zasuyi mata adalci wajen misaltawa, saboda ko wulakancin shi na yau da kullum bai dakushe tasirin soyayyar shi a zuciyar ta ba. Na dole sun dawo wuni cikin dakin kamar marassa gaskiya, bai kore ta ba, yanda yake nunawa ma kamar bai san tana cikin dakin ba tunda ko inda take baya kallo.

Ta kai zuciyar ta nesa dai wajen ganin bata yi komai daya wuce taya shi zama a cikin dakin ba. Tana kallon shi bayan la’asar ya shiga bayi, tana nan zaune ya fito, idanuwan ta suka fara sauka kan fuskar shi da ta manta rabon da ta ganta babu gashi, a kwanakin nan ma ta cika sosai saboda bai damu da yunwar cikin shi ba balle wata sumar fuska, yanzun ya kwashe komai, ko fuskar Lukman akwai gashin baki daya fara fitowa luf da shi, har tana tsokanar shi a kai ma. Fuskar Julde da bayan kwai basu da bambanci. Haka kawai sai yanayin ya hasko mata wani hoto da yasa zuciyar ta bugawa kamar tana neman hanyar fita daga cikin kirjin ta.

Tabbas shekaru ba karya bane ba, don sun nuna kan su a tare da Julden, bata san ko idanuwanta bane suka rage wannan shekarun akan fuskar shi suna dai-daita mata fuskar da hoton da take da shi a cikin kanta. Bambancin ba a zanen fuskar yake ba, a sarkar da babu ita yanzun a wuyan shi ce, kayan fulanin da yake sakawa a wancen lokacin, sai kuma askin kan shi da yake kasa sosai, sabanin wancen lokacin da ya tara gashin, bayan kadai ake ragewa an tado gaban yayi tozo irin na samarin fulani da suke ji da kan su a wancen lokacin. Julden ta, Julden da zuciyarta ta zaba tun kafin ma tayi wayon sanin haka.

Mata da yawa na son maza masu kasumba, maza da yawa sukan ce cikar kamala ta da namiji kenan, musamman magidanci kamar Julde, in ba dalili na aikin kaki da kan hana ma wasu mazan yin hakan ba, banda Saratu, a yau, a yanzun kuma ban da ita.

“Kayi kyau,”

Kalmomin biyu da tayi nufin furtawa a zuciyarta suka kubce mata suna kuma saka Julde sauke idanuwan shi da yanayin da yake ciki bai sa farin su canzawa ba, kyallin na shigar mata wani waje da bata san da shi a zuciyar ta ba, har yana sata gasgata maganar cewa so baya tsufa da masu azancin magana suke yawan fada,

“Da ka aske sumar sai kayi kyau,”

Ta furta muryarta na sauke kasa tunda kalaman farko suka subuce sai suka bata kwarin gwiwar furta sauran. Har lokacin dai kallon ta yake yi, tun kafin ya san menene soyayya, tun kafin Mero yake ganin soyayyar shi a idanuwan Saratu, a irin wannan lokacin a baya da take fito mishi da asalin kaunar da take mishi ya sha tambayar kan shi dalilin da yasa ya kasa mayar mata ko da kadan ne daga cikin tarin soyayyar da ya gani, kuma ya san tana mishi. Watakila da ta rage mishi radadin rashin Mero da yake fama da shi.

Da bai gan ta ba, da bai sake ganin ta ba da bata fama mishi tsohon ciwon da yake riritawa ba, kamar mahaukaci haka ya dinga zagaye unguwar da ya ganta yana tambayar duk wani wanda zai tsaya ya saurare shi ko ya ganta ta hanyar zayyana mishi kamannin ta, a idanuwan mutane mabanbanta yaga mamakin da suke da ya kasance cikin shiga ta kamala, ko kadan alamu basu nuna cewa yana dauke da cutar rangwamen hankali ba, amman daga ya bude  bakin shi sai kalaman shi su sha bamban da kamammin shi. Ziyara ta zo, ya san iya wannan in ba kuma dalili ya raba auren da tayi a Kaduna ba kamar yanda yake fata.

Har yanzun, yana kuma jin har abada Mero zata kasance rike da kaso mafi girma na zuciyar shi da duka walwalar shi. Baiyi karya ba da ya taba ce mata.

“Ina jin kamar ban san farin ciki ba sai da kika shigo rayuwa ta Mero.”

Akan ta ya fara sanin menene asalin farin ciki kafin ya samu su Salim da suka karasa cika mishi abinda ya rage na daga cikin farin cikin. A yanzun kuma duk wata yar walwala da yake yi a duniya su ne sanadi, su kadai yake kallo ya samu nutsuwa. Ko sauran matan da yake bibiya baya samun nutsuwar da yake nema a tare da su, kamar akwai wani duhu da yake mamaye da shi ya hana mishi sukuni.

“Ko kana sha’awar cin wani abu?”

Maganar Saratu ta kutsa ta cikin tunanin shi.

“Idan anyi sallah ki kira su Khalid sai muci gabaki daya,”

Yana kallon murmushin da tayi tana daga kai hadi da mikewa ta fice daga dakin, da zai iya da ya so ta, ko kadan da ya so matar nan. Amman ba zai iya ba, lokaci dai ya koya mishi sabo da ita, amman babu soyayyar ta ko daya a cikin zuciyar shi, akwai dai jin ko na rana daya ya kamata yayi mata godiya, da ta bashi su Salim, da ta ke tare da shi tana kula da gidan shi duk fitowar rana da faduwar ta. Ta cancanci ko da iya wannan jinjinawar ne.

Komai da sanyi-sanyi yake tayin shi, sanda ya gama shiryawa cikin wani farin yadi da ya karbi jikin shi har ana kiran magriba, fita masallaci yayi, bai hadu da kowa ba wajen dawowa sai Khalid da suka taho tare, Nawfal daman ya saba ya zauna masallaci bayan Magriba wasu ranakun ma har sai anyi isha’i yake dawowa. In kuma bai tsaya ba to sai ya gama duka azkar din shi, Khalid ya sha zama tare da shi sai yaga ya samu waje ya jingina bayan shi da bangon masallacin, kamar akwai wata nutsuwa ta daban da sai a cikin masallacin ya ke samun ta.

“Ku zo muci abinci, ka fada ma su Bajjo.”

Julde ya cewa Khalid daya daga mishi kai.

“Yanzun kuwa… Me Nanna ta dafa?”

Kai Julde ya girgiza mishi.

“Ni ma ban sani ba fa…”

Yana ba Khalid din dariya kafin su rabu kowa ya wuce bangaren shi. Sanda Julde ya shiga har Saratu ta shirya teburin cin abincin mai mazaunin mutum takwas. Kujera yaja ya zauna. Ya kusan mintina goma kafin Khalid da Nawfal su shigo da sallamar da ko amsa musu Julde baiyi ba suka cigaba da maganar da sukeyi.

“Ni fa bana son wannan tattare-tattaren da kake mun… Jiya ba akan gado na ajiye takardar ba? Saboda idan na zo in dauka, yanzun duk ka hade su waje daya…”

Kallon shi Nawfal yakeyi.

“Kan gado wajen ajiye takarda ne Hamma? Kan gado fa? Meye amfanin teburin dakin?”

Kafin Khalid daya daga ido a zafafe ya amsa, Salim ya rike wuyan kowannen su da hannun shi, yana saka su fadin.

“Hamma mana…”

A tare.

“Tun kafin in shigo nake jin hayaniyar ku…sai kace kaji.”

Nawfal ya fara zamewa sannan Khalid, babu shiri kowa ya samu kujera ya zauna, Khalid na sa kafa cikin kokarin ture kujerar Nawfal daya zauna kusa da shi.

“Daddy kai ma Hamma Magana.”

Kallon su Julde yakeyi fuskar shi dauke da murmushi, yanajin wani abu daya kulle mishi kirji yana sassautawa.

“Kai da baka ma jin yunwa? Me ka zo yi?”

Khalid din ya amsa.

“Idan banzo ba waye zai takura maka?”

Wannan karin Khalid din ne ya kalli Julde.

“Kana jin shi ko Daddy? Kana jin me yake cewa.”

Khalid ya karasa yana kaima Nawfal dukan daya kauce yana dariya.

“Har yanzun kun kasa wuce shekara sha biyu.”

Lukman daya karaso wajen ya fadi cikin harshen fulatanci yana tsayawa kan kujerar da Nawfal yake hadi da fadin.

“Ka koma can Hamma.”

Akwai wani yanayi tattare da Lukman da yake saka kowa yi mishi abinda yake so, ko sanyin halin shine ko kuma kwarjini ne daya ke yalwace saman fuskar shi duk da karancin shekarun shi. Tashin Nawfal yayi, Lukman ya ja kujerar yana zama a tsakiyar Khalid din da Nawfal kafin ya gaishe da Salim da Daddy.

“Lukman ba’a ganin ka sam.”

Nawfal ya fadi, har mantawa yake Lukman yana gidan, sai ya ga giccin shi.

“Ina nan Hamma.”

Ya amsa a takaice yana mikewa dan yaga alamar kamar ba yunwa suke ji ba, shi ko abincin rana baici ba, cake ne kwara daya yaci a makaranta. Bubbude warmers din yayi, shinkafa ce da miyar kaji, sai kamshi yake tashi, in dai girki ne Allah ya hore ma Saratu, gashi tana son yin shi, ko wani gidan taje aka bata abinda bata sani ba bata girman kai take tambayar sunan shi da kuma yanda akeyi, hakan ne ya sa ta kara gogewa da abincin gayu kala-kala. Lukman ya zuba ma kowa yana kallon Nawfal daya girgiza mishi kai a hankali. Zai so yaci abinci a cikin su, sai dai ko kifi aka saka ba nama ba a abincin haramiyar shine tunda ya san akwai yaji.

Numfashin da ya shaka yaji yaki kaiwa in da ya kamata da zuwan Saratu wajen, yana kuma jin illar hakan a muryar shi lokacin daya furta.

“Nanna…”

Cikin sigar gaisuwa. Bata kalle shi ba, amman ta amsa da,

“Bajjo”

Salim da yake kusa da Julde ya mike ta zauna a kujerar shikuma ya zauna a ta kusa da ita.

“Na bar wayata a daki, za’a iya kirana.”

Yace yana mikewa batare daya kalli kowa ba balle yaga yanda suka san karya yake, suka san uzuri ne dan kawai ya bar wajen tunda Saratu ta zo, babu kuma wanda yayi yunkurin hana shi, akwai abubuwa da yawa da lokaci yake koya maka ciki kuwa harda kiyaye halayen makusancin ka. Yanda duk Saratu da Nawfal zasuyi kokarin boye rashin kaunar da yake tsakanin su idan wani yana nan, duk su Khalid din na fahimta, kamar yanda suka san daga Saratun har Nawfal sun san biye musu kawai sukeyi. Fitar Nawfal tayi dai-dai da dagowar kan Salim yana sauke idanuwan shi cikin na Khalid da suke shimfide da tuhuma, shakku da alamar tarin tambayoyi.

Baya so, tun shekaranjiya Khalid yake bin shi da idanuwa haka, har yau ya so kauce ma dawowa gidan ya kwana. Ocean Palace guest Inn ne karshen in da yai tsammanin wani wanda ya san shi zai gan shi balle kuma Khalid.

“Nagan ka Hamma… Na ganka yau.”

Khalid din ya fadi, ba shi bane karo na farko da wani a cikin shi ko Nawfal suka ce sun ganshi, sai dai a shekaranjiyan kawai sai yaji zuciyar shi tayo tsalle zuwa makoshin shi da ya bushe lokaci daya yana kuma neman yawun da zai samu ya jiqa shi ya rasa.

“Nagan ka.”

Khalid din ya sake maimaitawa muryar shi dauke da wani abu da Salim bai taba tunanin zai gifta a tsakanin su ba.

“Kila ya kamata in nuna kamar ban gan ka ba, kamar banga yarinyar da ka hada da jikin ka ba Hamma, amman ba zan iya ba, ban san ya zanki maka magana ba. Kace mun iya abinda nagani ne kawai…dan Allah kace mun iya abinda nagani ne kawai bai kai inda tunani ya nufa ba…”

Duk kalma daya da Khalid din zai furta wani irin abune yake lullube Salim, ko dai haka kunyar da yaji mutane na fada take shisa ya kasa daga idanuwa ya kalli Khalid, a karo na farko a rayuwar shi da yake son kasa ta bude ya shige ciki akan ya fuskanci Khalid a yanzun. Rabon da yaji kamar abinda yake bashi da kyau har ya manta sai a lokacin. Yana jin numfashin da Khalid ya ja ya fitar

“Hamma…”

Ya kira zuciyar shi a shimfide cikin yanayin yanda ya kira sunan Salim din, bai daga kai ba, kasa yake kallo, haka Khalid din bai sake furta komai ba ya juya kawai. Amman tun shekaranjiya din yake bin shi da irin wannan kallon tuhumar duk haduwar da zasuyi, banda gaisuwa wata kalma bata gifta a tsakanin su ba sai yau din nan, shima ya san saboda su Nawfal suna wajen ne. Ya sa shi yanajin babu dadi tun shekaranjiya, abinci ma ya daina gane dandanon shi saboda taraddadin da ya kasa fassara kona menene takamaimai.

Yanda Salim baiyi tsammanin ganin Khalid din ba haka shima. Dan dakyar ma ya gane wajen da kwatance da komai. Wani abokin aikin shine kirista dan kabilar Igala yake aure a cikin satin, to abokan shi da suka zo daga garin su sai suka sauka a wannan Guest Inn din. Akwai takardun daya manta bai bari ba a wajen aiki kafin ya dauki gajeran hutun, sune ya roki Khalid da zaije dasu hotel din da yaje ya karba. Saboda nisan wajen ma yana tafiya yana jan karamin tsaki harya karasa, kawai dan dai Michael din yana da kirki, bashi da matsala sam, amman Khalid na daya daga cikin mutanen da kunya bata cika saka su yin abinda zasu takura ba.

Ya kira Micheal din kuma yace mishi baima karaso wajen ba, shine abinda ya saka shi zama cikin mota in da yayi parking yana jira, kalle-kalle yake yanda ake shige da fice, mata da maza a hade. Waje irin haka ya kamata ace ya zama wajen da uzuri zai iya kawo kowa, amman ya kasa kauda zargin da yake ma matan da yake ta gani suna shige da fice daga cikin hotel din, watakila tare da mazajen su suke, watakila sako suka zo karba kamar yanda yayi, ko wani uzurin mai tsafta, amman bata gari sun riga sun fesa ma waje irin wannan ruwan da har abada jirwayen shi ba zai taba wankewa ba.

Idanuwan shi da yake ta yawata wa yana kalle-kalle ya sauke kan wata jar mota da baiga lambar ba, amman sak irin ta Salim, sai dai baya tunanin akwai abinda zai kawo Salim wajen nan, watakila ma yana asibiti ko gida a wannan lokacin. Kafin Salim din ya fito yana karyata tunanin Khalid da ya kama murfin mota zai bude da nufin fita ya karasa wajen Salim din, yarinyar da yaga ta sakala hannunta a kugun Salim na saka duk wani abu da yake kirjin shi amsawa cikin yanayi marar dadin misaltawa. Dakyar ya iya runtsa idanuwan shi yana sake bude su dai-dai lokacin da Salim ya juyo da yarinyar da duka alamu suka nuna bambancin addini da yare a tsakanin su,Khalid na sake runtsa idanuwan shi babu shiri

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ya iya furtawa saboda ba zaiga hoton da baisan yanda zai fara goge shi daga cikin kan shi ba, jikin shi ko ina bari yake saboda tashin hankali. Wacce irin bakar rana ce wannan yaci karo da ita? Me zai gani? Salim? Hamman shi? Hamman shi da kimar shi take kamar jirgin sama a wajen shi har sai ya daga kai yake iya hango nisanta, me yasa ya zo wajen nan? Me yasa kimar nan zata ruguzo a saman kan shi kamar daman bata da nauyin rike kanta a saman shi? Me yasa Salim ma zai karya mishi zuciya haka?

“Kar kayi saurin yanke hukunci”

Wata murya da bata da kuzari ta karfafe shi, bayajin wani lokaci mai tsayi ya wuce, amman ji yayi kamar zamani ne ya zo ya wuce yana nan zaune saboda tashin hankali, sanda ya daga kai baiga yarinyar ba, baiga Salim ba sai motar shi da yake ja yana fita daga wajen. Ko ringing din wayar shi Khalid baiji ba, Allah ne ya taimaka Micheal din ya hango shi zaune cikin mota, idan yace ga yaren da suka gaisa ciki zaiyi karya, ya karbi file din dai, ko sallamar kirki baya tunanin yayi da Micheal balle ya tambaye shi ya shirye-shiryen bikin shi suke tafiya. Duka wannan abubuwane da muhimmanci yayi baya yana tazara mai nisa da abinda Khalid din yake ji.

Da sanyin da jikin shi yayi yake tuki har gida. So kawai yake ya shiga ya tambayi Salim dan ya karyata mishi abinda ya gani, dan ya tabbatar ma da tunanin shi abinda ya gani a wajen Guest Inn din ne kawai. Amman sai shirun Khalid din ya karfafa tunanin shi yana ruguza wani bangare na zuciyar shi. Saura wa kuma ya rage yayi disappointing din shi haka? Sosai zuciyar shi ta sosu, ba farin cikin duniya kawai Salim yake wasa da shi ba, har lahirar shi ma lilo takeyi amman yake rayuwa kullum kamar babu mala’iku har biyu a kowanne gefen shi, kamar baisan suna rubuta duk wani motsin shi ba.

Rashin tsoro irin na dan adam abune mai ban al’ajabi, ko wani abin Khalid yayi da yasan babu kyau sai yazo kwanciya yaji kirjin shi na bugawa cike da taraddadi, kan shi na wankewa yana barin tunani kwara daya tak, zai iya runtae idanuwan shi na har abada, baccin da zaiyi da nufin ya wayi gari zai iya bude idanuwan shi a cikin kabari. Ta ya mutane masu tarin zunnubai suke rayuwar yau da kullum kamar ba zasu hadu da Allah ba? Abin da al’ajabi, ba kadan ba. Laifin na Salim ne amman shi ya kasa bacci duk tsayin daren, ga zuciyar shi da take zafi.

Kwanakin nan biyu haka yake yin su a daddafe kawai, ko da sukai waya da Nawfal shekaranjiyan wajen tara sai da ya tambaye shi me yake damun shi

“Gajiya ce kawai”

Amman ya san Nawfal bai yarda ba shisa ya dawo garin jiya. Yanayin yanda yake ta tsokanar shi yana sanar mishi da cewa ko meye yake damun shi in dai yana son su tattauna Nawfal din a shirye yake da ya saurare shi, in kuma yana ganin zai iya shawo kan abin shi kadai ma Nawfal din ba zai matsa ba. Tsintar kan shi yayi da godewa Allah da Nawfal ya kasance jinin shi, mutum daya kuma da yake da yakini mai karfi akan cewa ba zai taba karya mishi zuciya kamar yanda kowa yake ta zabar yi ba.

Ganin Salim din na ta wasa da cokalin shi cikin abinci yasa Khalid ture na shi plate din, daman ba wai yana jin wata yunwa bane ba.

“Har kayi me? Shisa kake ta kara ramewa kullum.”

Julde ya fadi, murmushin karfin hali Khalid yayi, kafin ya amsa Lukman ya riga shi da fadin.

“Meye babu a fuskar ka Daddy?”

Saboda tun dazun yake ganin kamar akwai abinda ya kamata ace akwai a fuskar Julden, hakan yasa daga Khalid har Salim kallon Julde kafin Khalid ya kwashe da dariya.

“Inalillahi… Daddy waye yai maka wannan yankar kaunar?”

Murmushi Julde yayi, bai san dalili ba, amman ji yayi kamar idan ya aske gashin fuskar zai rage nauyin da kirjin shi yayi, kamar ita kanta sumar na da wani nauyi na daban da bai taba sani ba, banda iska da yake ji tana shigar mishi fuska ta ko ina babu abinda cire gashin yayi mishi.

“Ni na aske abu na, furfura ta fara cika shi, shine na aske sai baki ya fito.”

Wannan karin har Salim sai da yayi dariya.

“Nanna kina ganin shi ya aske?”

Khalid ya tambaya, murmushi Saratu tayi, bata cika saka musu baki a irin wannan lokacin ba, saboda a cikin shine take samun ganin dariyar Julde, ta kuma ji zolayar shi da bai taba gwadawa a kanta ba, sai taga kamar wani ne daban ba mijin da ta aura ba, ba mijin da take zaune da shi ba kuma. Ko dan wannan ba mijin ta bane ba, mahaifi ne tare da yaran shi, ubane da kaunar yayan shi take a bayyane.

“Ko da ya aske din dai babu wanda zai nuna mishi kyau a cikin ku.”

Lukman ne ya fitar da wani sauti a kasan makoshin shi da ya sake saka Khalid fashewa da dariya.

“Son kai dai Nanna.

Cewar Salim.

“Son Daddy dai zaka ce.”

Khalid ya amsa suna hada ido, yanayin da yake tsakanin su na sake giftawa kamar labulen da su kadai suke ganin shi. Kamar yanayin ya ba Khalid damar mikewa dai-dai lokacin da suka fara jiyo kiran sallar isha’i.

“A gajiye nake ni kam, ina dawowa sallah zan kwanta. Sai da safen ku.”

Cewar Khalid din yana dan amsa tambayar Nanna da take mishi na ko karfe nawa zai fita da safe kafin ya juya yana barin dakin. Sai dai bai koyi minti biyu ba yaji takun tafiya a bayan shi da yasa shi juyawa.

“Khalid…”

Salim ya furta sauran kalaman da bai gama hadawa a cikin kan shi ba suna makalewa, wani abu ya kamata yace, amman shi din ba mai yawan magana bane tun da can, balle kuma magana irin wannan da bai taba tunanin zata hadasu da Khalid ba. Murmushin da bai kai cikin idanuwan shi ba Khalid yayi.

“Bani zaka yiwa bayani ba Hamma, ba fahimta ko yafiya ta zaka nema ba, bani da iko akan anjiman ka balle har a tsallaka lahirar ka. Kawai kabari, ko menene dalilin ka bashi da tushe, ka daina, ka roki Allah ya yafe maka kafin lokaci yayi maka karanci…”

Idan ya fito da sanyin jiki, kalaman Khalid sun sa yaji kamar kashin gwiwar shi ya sulale zuwa wani waje da bai sani ba.

“Zanje sallah…”

Khalid din ya furta yana sake juyawa yabar Salim a tsaye. Ya so ya shiga bangaren su ya sake daura alwala, amman yana gudun kar Salim din ya sake bin shi, shisa ya fice daga gidan. A masallaci yayi alwalar, ana idarwa ya gama lazumin bayan sallah ya daga hannuwan shi sama sai kanshi yayi wani irin wayam, ga tarin bukatu a zuciyar shi amman kwakwalwar shi taki bashi hadin kai. Ya dauki lokaci da hannayen shi a sama, zuciyar shi a bude cike da yakini da kuma sallamawa har sai da yaji wani sanyi da tsoron Allah ya ratsa sassan jikin shi tukunna ya mike.

Da ya koma gida kai tsaye dakin su ya wuce, ya samu Nawfal zaune kan kujerar teburin daya dora hannayen shi yana latsa waya da kofin da Khalid ya san shayi ne a ciki. In zai farkawa biyar zai iya ganin Nawfal din a zaune kamar ba dare ba.

“Wai kai ba zakayi bacci bane ka huta ma ran ka?”

Ya tambaye shi kwanaki hudu bayan ya zo.

“Bana ji ne Hamma, bambanci lokacin nan yana ta bani wahala… Gara in dan rage wani abin da safe na rama In shaa Allah,”

Amman hakan baya hana shi yi mishi magana idan ya farka ya ga dare ya raba. Ko ba zai bacci ba dai ya kwanta kwakwalwar shi ta dan samu hutu. Zai so ya watsa ruwa amman kasala yake ji, shisa ya rage kayan jikin shi yana samun T-shirt marar nauyi ya dora akan singlet din shi, sai gajeran wando yabi lafiyar gadon da ya sha gyara sai kamshi ke tashi. Shi kanshi dakin yafi mishi dadi idan Nawfal yana nan, matar shi dai ta huta, Khalid din ya sani. Tsantsainin Nawfal ba zai barshi ya jira sai tayi gyaran gida ba, tana ma iyayi ya sake maimaitawa, dan duk yanda zakayi shara sai kaga ya kara yin wata.

Addu’ar bacci yayi, yana runtsa idanuwan shi, a hankali yake motsa labban shi yana fara karanta ayoyin da suke cikin Suratul-Mulk dan neman saukin kwanciyar kabari, baya taba mantawa tunda ya mallaki hankalin shi ya kuma ci karo da muhimmancin hakan, jarabawar duniya ma neman hanyoyin samun saukin ta yake, balle kuma samun lahira da komai ya zo mana a bayyane. Daya dire cikon ayar karshe harya juya baya sai kuma ya sake juyowa yana bude idanuwan shi akan Nawfal da yake zaune yana danna wayar shi har lokacin.

“Bajjo…”

Ya kira da sanyin murya, yana kasa tsayawa ma Nawfal din ya amsa shi dan harya dan juyo da kai.

“Dole ne sai yara sun biya zunuban iyayen su? Kana ganin Allah zai iya duba zuciyar yaran yaki jarabtar su?”

Girar Nawfal ta hade waje daya cike da mamaki da kuma son fahimtar in da tambayar Khalid din ta dosa.

“Kamar zina da akace maiko take da shi, kana tunanin yara zasu iya kubuce ma wannan maikon kuwa?”

Wannan karin akwai bayanannen tsoro a muryar Khalid da yasa Nawfal mika mishi hankalin shi duka, a iya sanin shi Khalid bashi da wani hali marar kyau, ko a mugun mafarki kuwa ba zai hada shi da aikata laifi mai munin zina ba. Shisa yake neman dalilin da tunanin Khalid din zai dibe shi zuwa inda yake yanzun har ma wannan tambayoyin su hade mishi.

“Banajin na fahimci tambayar ka Hamma…”

Nawfal ya fadi da dukkanin gaskiyar shi, numfashi mai nauyi Khalid ya sauke, idanuwan shi cike da wani firgici da Nawfal ya rasa dalilin shi hadi da furta.

“Hmmm…”

Sosai Nawfal ya juya dan saida ya motsa kujerar da yake da kai.

“Banda amsar tambayar ka, abu daya na sani, kaima kuma ka sani, babu wani abu da yafi karfin Allah, wanda Ya so a cikin kowanne hali zai iya kubutar da shi.”

Kai Khalid ya jinjina ma Nawfal yana juyawa da alamar da take nuna ya gama maganar. Mikewa Nawfal din yayi ya karasa wajen kwan fitilar dakin ya kashe ma Khalid din, ba zai daice ya kashe ba, amman yasan hasken zai iya takura mishi. Ya bada wajen mintina sha biyar a tsakani, baiji Khalid din ya motsa ba, cikin sanda ya karasa ya leqa fuskar Khalid, idanuwan shi a rufe suke, da alama bacci ya dauke shi. Abin rufa Nawfal yaja ya rufe shi yana tsaye akan shi, duk wata addu’a ta tsari da neman sauki sai da yayi yana tofa mishi, baisan me ya same shi ba, amman baya son tsoron da ya gani a cikin idanuwan shi.

“Allah zai kare mun kai Hamma, daga dukkan abin ki.”

Ya furta a kasan numfashin shi yana komawa ya zauna, Khalid na jin shi, yana ji yaja mayafi ya rufa mishi, yana jin addu’ar daya tofa mishi, haka kuma kalaman shi da suka rufe Khalid din ruf, fiye da mayafin da Nawfal ya rufa mishi, kirjin shi yanayin nauyi da sirrin da yake tunanin shi kadai ya san da shi.

<< Rai Da Kaddara 17Rai Da Kaddara 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×