Mutane zasu tsammaci ganin kunshi a hannuwanta ko da yaushe kasancewar ta wadda ta iya. Amman tana daya daga cikin mutanen da lalle bai dame su ba sam. Asalima sai ta dade ko a farcenta bata saka ba, baifi kagani a jikin babban yatsan ta da kuma mabiyin shi, shima baka raba kowacce mai kunshi da shi, sai dai wanda suke saka safar hannu. Tana da su da yawa, irin na asibiti ma, kwali daya Salim ya bata, rashin sabo yasa duk sai taji ta takura, kwarkwaron kunshin ma yana zamewa daga hannunta idan ta saka. Tun yana mitar baya son ganin tana bata hannun ta harya gaji.
Yau din ma sauran wanda ya rage a kwarkwaron da tayiwa wata yar islamiyyar su ne kawai ta zauna tana zanawa a jikin hannun ta, ba wani mai yawa bane ba, amman ko ita da tayi sai taga yayi mata kyau bayan ta gama tun ma bai bushe ba, hannun harya zama na mace, tana tunanin yanda in ta wanke lallen har wasu zobuna masu yawa da Adee ta bata zata dauko ta bude kwalin ta gwada ko da kwara biyune a yatsun taga yanda zasuyi. Adee akwai son kwalliya, kuma kyau takeyi ma Madinar, zobe zaka gani a kasa da saman yatsun ta, in gidanta kaje yanzun da tayi aure ma har a yatsunta biyu na kafar dama zaka sameta da su ta saka.
Daki ta koma ta dauki remote sannan ta samu kujera ta zauna duk da la’asar ake kira tunda Allah ya hutar da ita, shisa ma ta zana kunshin ta hankali a kwance. Tashar India ta kai ana tsakiyar yin film din Kabhi Khushi Kabhie Gham, labarin film din take ji ana yawan yi, tana kuma sakawa a ranta da zata nema ta kalla, sai dai ba littafi bane ba, film ne. Kallo na karshen abubuwan da ta damu da su, idan tana zaune kamar yanzun ma tana iya taita wasa da remote din tana rasa inda zata tsaya ta kalla, karshe tashar labarai ko documentary ne abinda zaiyi nasarar rike hankalin ta. Da yake ana rubuta fassarar da turanci sai ta bama tv din dukkan nutsuwar ta.
Tana iya juyo sautin bugun zuciyarta da ya zarta har cikin kunnuwan ta da wani yanayi da ba zai misaltu ba, bakinta na gaurayewa da dandanon gishirin da bata san inda ta samo shi ba, ko dandanon hawayen da take jine cike taf da idanuwan ta da take kokarin hanawa su zubo suka koma suka gangara cikin bakinta, shakuwar da take tsakanin jarumin film din da mahaifiyar shi na jijjiga duniyar da take zaune tana sa hanjinta yamutsawa kamar suna son sake mazauni saboda hargitsin da take ji har su ya tarar a cikin nata. Idan tace Yelwa bata fado mata lokaci zuwa lokaci tun kafin ta karanta wasikar nan zai zamana karya, duk lokacin da idanuwanta zasu sauka akan wani shafin littafi da yake magana kan mahaifiya sai tunanin tata ya kutsa mata.
Haka idan taji wasu suna labarin ta su, ba zatace ta rasa nagartacciyar soyayya da kulawa a wajen Daada ba, amman akwai ramin da take ji a zuciyar ta kamar wajen an halicce shi domin Yelwa ne, kasancewar ta a rayuwar ta ko akasin hakan baya nufin wani zai taba iya zama a gurin. Sai take jin da za’a bata dama guda daya zata koma ta goge ranar da taga wasikar nan, yanda duk ta so ta koma dai-dai, ta koma kamar kafin ta ga wasikar nan sai ta kasa. Abu kadan daya danganci mahaifiya take jin yanda yake samun tasirin raunana mata zuciya.
Ko jiya taga kallon da Daada take yiwa Julde, batasan ko raunin zuciyarta bane ya sa ta ganin zuciyar Daada a cikin idanuwanta duk idan tana kallon Julde, kaman in dai yana karkashin kulawarta zata kareshi daga dukkan wani abu da yake ikon ta, kamar rayuwar ta na da muhimmanci ne tare da dan nata. Da bata gani, amman yanzun tana ganin wannan kaunar, murmushin Daada ma akwai banbanci a cikin shi idan Julden yana kusa. Tsakanin mahaifiya da yaranta wata sirrantacciyar kauna ce da Allah daya halitta musu ne kawai Ya san girman ta.
Sai take tunanin meye bambancin sauran iyaye da tata mahaifiyar? Me yasa tabar ta? Ko dan rashin tabbacin da yake cikin halarcin haihuwar ta? Idan ta duba wannan kawai ya isa ya zama babban dalili a wajen Yelwa, takan ji kamar tana neman wani uzuri ne da zai saukaka mata abinda takeji. Salim yace ta jira Daada idan ta shirya zata fada mata komai a lokacin da take tunanin ya dace, tana kuma kokarin ganin tayi hakan, sai dai da duk wata rana da zata wuce da yanda tarin tambayoyin ta suke kara ninkuwa. Har mamaki takeyi yanda Daada ta kasa karantar tambayoyin a cikin idanuwanta.
Wanne lokaci ne ya dace? Yaushe ne Daada zata fada mata komai? Ko ma tana da niyyar fada mata din? Duka amsoshin tambayoyin nata na wajen Daada. Zuciyarta da nauyi kamar an dora mata dutse ta kai hannu ta dauki remote din tana canza tashar. Mikewa ma tayi tana komawa daki, bayi ta wuce ta wanke kunshin da yanzun ya fita daga kanta saboda zuciyar ta da take ji cunkushe. Sai kewar Salim ta danneta har tana sakata karasawa kan gadon dakin nata ta dauki wayarta ta duba taga bai kirata ba, bai kuma tura mata ko da text bane ba. Sun yi waya da safe, amman gaisawa kawai sukayi, tun shekaranjiya rabon da ta saka shi a idanuwanta.
Jikin ta yana bata akwai abinda yake damun shi, amman shi din ba mai yawan magana bane ba, bai taba bude baki yace mata ga damuwar shi ba, sai dai ta karanci yanayin shu taita jan shi da hirarrakin da take tunanin zasu saka shi murmushi ko kadan ne, ta kuma dinga tuna mishi yaci wani abu, dan in yana cikin yanayi irin wannan sai kaga idanuwan shi duk sunyi zuru-zuru ko idan aiki ya sha mishi kai, in tace ya rame baya cin abinci yanda ya kamata sai yace mata.
“Mantawa nake yi Mug, bakya tuna mun, mantawa nakeyi idan abubuwa sun mun yawa.”
Yanzun idan ta ganshi haka sai taita jin kamar harda lefinta, kamar in shi ya manta bai kamata ita ta manta ba. Ko ba komai Salim ne, komai nata damuwar shine, shirme da hankali zai bata nutsuwar shi kamar duk duniya babu wani abu mai muhimmanci kamar sauraren ta da abinda yake damunta. Ya kamata shima tashi damuwar ta zama tata, ta kamanta mishi kalar karamcin da yake nuna mata. Tun dazun ta manta basu yi magana ba, bata ma tuna da shi ba sai yanzun da damuwar da take neman ya taimaka ya saukaka mata ta taso.
Tsintar kanta tayi da jin kunya har tana kasa kiran shi, ta dai dauki wayar ta sake komawa falon ko da shi zai kirata. Daada ta samu a zaune ta fito itama, yanzun tafi zama cikin dakinta fiye da yanda take zama a falon. Canjine Madina take gani bayyane a tare da Daadar da ya girmi tsufa kamar yanda take yawan fada, kullum gani Madina takeyi tana kara ramewa kamar bata cin abinci, da ba gida daya suke ba kuma ba ita take kula da cin safe, rana harma na daren Daadar ba zatace ba’a kula da ita yanda ya kamata.
“Assalamu alaikum”
Muryar Nawfal ta daki kunnuwan Madina tana sakata saurin daga idanuwanta da zuciyarta da tayi tsalle zuwa cikin su tana kallon Nawfal da ya sakko kafar shi cikin dakin fuskar shi dauke da murmushi, manyan kayane a jikin shi, yadi kalar sararin samaniya sai hula mai kalar amman mai duhu, kayan sun karbi jikin shi, rigar na nuna fadin kafadun shi da cikar halittar shi duk da bata matse shi ba. Sai dai akwai banbanci a yanayin yanda muryar Nawfal ta sauka a kunnuwan Madina da kuma na Daada. Muryar Bukar taji, muryar dan ta da rayuwa ta zabi ta rabata da shi a karo daban-daban.
Da ta daga ido ma ta sauke akan Nawfal fuskar Bukar ta gani, murmushin shi mai sanyi kamar halayen shi take gani, duk da ko kusa da sanyin halin Bukar din Nawfal bai kai ba, ita kam yau Bukar take gani kamar yanda yanzun da karfin alaka ta jini tasa take ganin Yelwa a tattare da Madina duk da kowa yasan Yelwa zaice bata kama da Madina, amman jini yafi karfin wasa. Da duk wayewar gari da yanda nauyin kirjinta yake karuwa a tsayin shekarun nan, yanzun ya kai inda take jin anya bashi zaiyi ajalin ta ba kuwa? Idan ta kwanta bata tunanin komai sai yanda zata sauka daga gado da safe, yanda za tayi rayuwa a yinin ranar batare da ta kara ma Madina damuwar da take gani cikin idanuwan ta ba.
A satikan nan tana bude bakin ta yafi a kirga sai ta kasa furta komai, me zata ce? Me zata fadama Madina? Ta ina ma zata fara? Yarinyar bata taba tambayar ta komai ba, kamar sun zauna sun hada baki da Nawfal suka zabi shirun da ya saukaka mata komai saboda bata da kwarin gwiwar fuskantar su da labarin da ba zai amfane su da komai ba, bata son ko na minti daya su raba nauyin da take ji tare, duk da tasan nauyin ba nata bane ita kadai, wata rana dole ta raba shi tare da su, yanzun tana jin kusancin ranar fiye da kowanne lokaci. Girma sukeyi su duka, shekaru na riskar su, rashin tabbas din yau da kullum na kara lullube Daadar.
Tana jin ina ma ace ta san sauran kwanakin da suka rage mata, da tafi tsara yanda komai zai kasance.
“Daada Am”
Muryar Nawfal ta kutsa cikin tunanin ta,
“Soyayyar tawa ce ta motsa haka kike ta kallo na harma bakyajin me nake cewa?”
Murmushi tayi tana jin wani abu ya rabe a cikin kirjinta.
“Ko bata bakina ma ba zanyi ba.”
Dariya yayi yana karasawa ya tsugunna a gabanta.
“Bana son ramar nan dake cikin idanuwan ki Daada… Duka kwana nawa ne ban ganki ba yau amman kin kara ramewa”
Kai Daada ta girgiza tana sauke idanuwan ta daga cikin na shi saboda bata son yanda yake kallon ta kamar yana neman tono dukkan sirrikan da take boyewa
“Wai ba zaku kyaleni ba ne? Idan ma bana ramewa yanzun surutun da kuke mun zai sa in fara.”
Ta karasa maganar tana kokarin mikewa, Nawfal na tayata cikin hanzari, yana tuna mata lokuttan da ta taimaka mishi ya mike haka, ta ma daga shi gabaki daya tana mikarwa. Sai da ya tabbatar ta tsaya da kafafuwan ta tukunna ya saketa a hankali yana nazarin ta bayan ta juya, yanda take cira kafafuwan ta dakyar yasa zuciyar shi yin nauyi. Ko lafiyar ta kalau akwai abinda ta saka a ranta, shisa take boye mishi haka, daya shigo gidan suka gaisa take tashi tabar falon, idan dakin ta ya bita sai ta kwanta kamar bacci ya dauketa, wata rana ya dauki filo ya kwanta anan kasa, ko ya dora kan shi akan gadon har saiya gaji da zama.
Yanzun da yake kallon ta babu komai cikin kanshi sai rokon da yake ma Allah na ya ara mishi lokaci mai tsayi tare da Daada saboda itace cikon komai na rayuwar shi, ko Murjanatu bata gani ba sai dai a waya, akwai tarin abubuwan da yake bukatar aron lokaci ya gudanar da su tare da Daada a cikin rayuwar shi. Itama tana jin idanuwan Nawfal din, tasan kallon ta yakeyi, kanta take ji yayi nauyi fiye da misali, kamar babu iska a cikin shi duk da bata san ko akwai yiwuwar cewa iska zata kasance cikin kai ba, kawai hakan zata iya amfani da shi wajen misalta yanayin da take ji.
Hasken daya gilma cikin idanuwan ta na sakata runtsa su ta bude, sai taga duhu, ba duhu irin na gabatowar magriba ba, duhu fiye da na tsakar dare saboda bata iya ganin kyallin komai, sake runtsa idanuwan nata tayi wannan karin duhun na karasawa har cikin kanta.
“Daada…”
Taji an kirata kamar daga wata duniya saboda nisan da kwakwalwar ta tayi da kanta duk kuwa da suna hade waje daya, hakan na sa wani abu cikewa a kirjinta kafin komai ya tsaya mata cak.
*****
Kamar shirin film haka komai yake dawo ma Madina da Nawfal, da murmushi a fuskokin su, komai na tafiya lafiya kafin ya birkice a kasa da minti daya. Kowa ka tambaya zaice shi ya fara ganin alamar Daada zata fadi, amman babu lokacin wannan musun tunda babu wanda ya iya karasawa ya tare ta a cikin su sai bayan da ta kai kasa tana faduwa tare da wani bamgare na zuciyoyin su. Sai sakanni suka dinga wuce ma Nawfal da nisan awanni, komai baya sauri har shi kan shi, haka yaji daga daukar Daada daga cikin gidan zuwa motar shi haka shigowar su asibiti, haka dorata akan gadon da ya kama aka gungura har zuwa dakin da wani likita ya kai hannu yana turo shi baya kafin su maido kofar su rufe.
Tsaye yake amman ya rasa inda zai sa kan shi yaji sanyi, numfashi ma kokawa yake da shi a wannan lokacin.
“Ka zauna Hamma…”
Madina ta fadi cikin sanyin murya tana saka shi juyawa ya kalleta, nutsuwar ta na bashi mamaki, akwai damuwa shimfide saman fuskarta amman a nutse take.
“Tashin hankali baya taimakon marar lafiya, nutsuwa yake bukata fiye da komai. Nutsuwar ki ita ce taimakon farko, ki rufe idanuwan ki kiyi numfashi mai nauyi ki fitar har sai kin tabbata kin samu nutsuwar da kike bukata…”
Shine abinda Salim ya fada mata, ya maimaita mata har saida ya tabbatar ta fahimta bayan ta haddace kowacce kalma. Shisa yanzun ita ta fada ma likitan sunan Daada, shekarun ta da kuma lambar katinta da ta haddace ko da zasu taho asibiti a hargitse bata dauko ba za’a iya amfani da lambobin a binciko file din ta kamar yanda tasan anyi yanzun din, ko ana kanyi.
“Ina wayar ka?”
Ta bukata ganin gardamar da take cike da idanuwan Nawfal din akan tayin zaman da tayi mishi, ta masa uzuri, wannan ne rashin lafiyar farko da Daada tayi yana nan. Aljihun shi Nawfal ya laluba yana dauko karamar wayar da yaji a jikin shi ya mika mata. Lambar Salim da ta haddace ta saka tana kiran shi, sai da ta kira sau uku ana hudun ya daga da fadin.
“Yanzun na shigo na dauki wayar Bajjo, mene ne?”
Numfashi taja tana fitarwa.
“Hamma ni ce.”
Da mamaki a muryar Salim ya ce,
“Madina?”
Cike da alamar tambaya kafin ya dora da.
“Lafiya? Me ya faru? Ina Bajjon?”
Sai da ta kalli Nawfal sannan ta amsa
“Gashi nan, yana lafiya. Muna asibitinku… Daada ce ta fadi.”
Ta karasa tana jin yanda bugun zuciyar ta yake karuwa cike da tsoro, girman abin da ya faru a gabanta yana danne ta.
“Ki tashi ki duba saiki fadamun inda kuke?”
Mikewar tayi kuwa, ya nuna mata yanda zata karanta sunan kowanne ward a asibitin ta kuma gane in da take, dubawar tayi tana fada mishi.
“Gani nan zuwa yanzun…Daddy ya sani?”
Kai Madina ta girgiza.
“Kai na fara kira…”
Ta fadi cikin sanyin murya.
“Karki kira kowa tukunna, gani nan.”
Wayar ta sauke daga kunnenta tana kashe kiran. Riga da wando ne a jikinta, ta dora ta sanyi doguwa akan tshirt din da takai mata har gwiwar ta, akwai maballai a jikin rigar daga farko har karshe, an yi kwalliya da wasu har a gefe, sai hula da ta dan tura baya batare da gashin ta ya bayyana ba, haka take zaune sanda Nawfal ya zo, haka kuma ta fito batare da ta saka komai ba sai takalmin da daman akwai shi a kafarta na yawo cikin daki. Tsaye take har Salim ya karaso yana kai hannu ya tura mata gilashin dake fuskarta ganin ya dan sakko ita kuma bata mayar da shi ba.
Tayi mishi kyau kamar ya dauketa ya boye, zuciyar shi ta yamutsa lokacin da ya yawata da idanuwan shi akan fuskarta.
“Wanne daki suka shiga da ita?”
Da hannu ta nuna mishi saboda idanuwanta da taji sun cika da hawaye, tana yin magana zubowa zasuyi, kai ya jinjina yana kama hannun nata ya jata ya karasa da ita inda ta tashi a waiting area din yana zaunar da ita. Nawfal ya kalla da yake tsaye
“Bajjo…”
Ya kira a hankali, tun yarinta zaka iya cewa Nawfal na da juriya, tunda kafin kaji kukan shi zai wahala komin dukan da Saratu zatayi mishi kuwa, sai ta mare shi ya fadi ya tashi yayi tsaye kamar yana son ganin iya abinda zata iya yi. Kowa zai ce yana da karfin hali, abinda zai taba shi mai girma ne. Shi ne zai karyata, Nawfal ne yaro mafi rauni daya taba cin karo da shi, ko idanuwan shi ka kalla zaka ga wannan raunin, yana da babbar zuciyar da yake yawo da ita rike cikin hannuwan shi yana jiran mai rabo ya gifta dan ya karbe shi cike da karamci.
Akwai vulnerability a tare da Nawfal din da baisan yanda zai misalta ba. Kullum ya gan shi sai yaga kamar akwai abinda yake bukata da su duka suka kasa ba shi, ya dauka zai ga abin ya kau bayan yayi aure, yana nan, matar shi ma bata bashi wannan abin da yake nema ba, har yanzun bai cika ba, akwai rami mai girma a tare da shi. Wannan raunin kuwa shine a bayyane yanzun, karasawa Salim yayi yana kamo hannun Nawfal din da yake kokarin kwacewa, sai dai ba girman su bane kadai bambancin, harma da karfin su, jan shi yayi yana amfani da karfi wajen zaunar da shi gefen Madina.
“Har yanzun ba su fito ba Hamma? Bata numfashi sanda muka zo…bata numfashi… Daada bata numfashi Hamma…”
Kai Salim ya daga mishi kamar a gaban shi akayi, saboda fahimta Nawfal yake bukata, so yake wani ya fahimci abinda yake ji ko zai samu sauki. Kirjin shi kamar zai tsage gida biyu, da gaske labarin tashin hankali yake ji, bai taba fahimtar ya yake ba sai yau, wancen karin abinda yaji wasan yara ne, ya dauka idan yazo yaga Daada, ana komai a gaban idanuwan shi sai yafi samun sauki. Ashe ba haka abin yake ba, ashe nisan da yayi sauki ne, bai ganta ba, bai ga kamar ya rasa ta ba.
Tare da wani bangare a zuciyar shi suka fadi, ko Daada ta tashi bayajin wannan bangaren zai mike, faduwar da yayi ba wadda zai mike bace ba.
“Breath…”
Salim ya furta cikin umarni.
“Yanzun Bajjo, in… Out… In… Out”
Numfashin kuwa yake ja, yana fitarwa, muryar Salim na mishi jagora, har sai da ya dan fara samun nutsuwa tukunna.
“Ka zauna nan, ku duka ku zauna nan.”
Ya fadi yana kallon Madina da ta kai hannu tana share hawayen da ya zubo mata. Bayajin ta kamar Nawfal, tana da karfin hali duk da kankantar ta. Idan ta kama ya san zata ture damuwar ta a gefe ta kula da Nawfal din. Yana shirin karasawa dakin likitan na fitowa. Daga inda su Nawfal suke basa iya juyo abinda su Salim din suke fadi, ta gaban su dai suka wuce, sun fi mintina sha biyar kuma kafin Salim ya dawo shi kadai.
“Me yace? Ta tashi? Me yace ya same ta?”
Nawfal ya jera ma Salim tambayoyin da kafin ya zabi wadda zai fara amsawa ya kara da.
“Zamu iya shiga mu ganta? In shiga in gan ta Hamma?”
Kai Salim ya girgiza mishi a hankali
“Sai ta kara hutawa…za’a kara mata wasu tests din tukunna…”
So yake ya basu tabbacin da yaga suna nema akan fuskar shi kamar duk wani wanda zai kawo marar lafiya, amman a yanzun ya ture batun cewa su din na shi ne, likita ne shi a yanzun, su kuma yan uwan mai jinya.
“Zamu san komai idan aka karasa sauran tests din…banda abinda zan fada muku yanzun da ya wuce tana samun dukkan taimakon da take bukata”
Hannuwa Nawfal ya saka yana dafe kan shi da su, likita ne a gaban shi ba Salim ba, ya gani, ya kuma ji a muryar shi, numfashi yake ja yana fitarwa a hankali sannan ya dago ya kalli Salim din
“Hamma…”
Ya kira amman Salim yaki kallon cikin idanuwan shi
“Hamma ka cire rigar nan kayi mun magana, dan Allah kayi mun magana”
Nawfal ya karasa cikin roko, muryar shi na fitowa cike da rauni.
“Ka fadamun… Kaji”
Yayi maganar cikin karfin hali yana son Salim ya fahimci zai iya daukar koma menene akace yana damun Daadar, so yake yaga ba yaro bane shi karami da yake bukatar kariya. Dan murmushi Salim din yayi mishi
“Sai an gama running tests Bajjo…”
Gardama zai karayi Madina ta katse shi
“Zaka zauna damu ko zaka kara dawowa?”
Numfashi Salim ya sauke yana godema Madina, idanuwan shi ya sauke cikin nata yana fatan taga godiyar shi.
“Zan sake dawowa…da sun gama abinda sukeyi zasu sake mata daki, sai ku zauna da ita.”
Madina ce kawai ta iya daga mishi kai.
“Idan kuna bukatar wani abin sai ki kirani.”
Kan dai ta sake daga mishi, ya kalli Nawfal daya kauda na shi kan gefe da alamar fushi yakeyi saboda yaki gaya mishi me ya samu Daada, numfashi kawai ya sauke yana wucewa yabar su a wajen. Office din shi ya koma ya zauna yana sauke wani dogon numfashi hadi da kai hannu ya murza kan shi daya fara alamar ciwo, ya gama round din shi sai kuma nan da awa daya, idan ba an shigo da marar lafiyar da yake bukatar agajin gaggawa ba. Ya kira Julde bayan sun gama magana da likitan yana kuma jira ne ya karaso asibitin.
Da gaske ne da yace ma su Nawfal sai an gama gwaje-gwaje tukunna, amman yana da abinda zai fada musu, zuciyar da zaiyi amfani da ita ya fada musun ne bashi da ita. Da Madina ce ita kadai zai san yanda zai gaya mata yayi mata bayanin da zata fahimta, Madina ce zai ma iya neman wasu takardu akan matsalar ya bata ta karanta, zai sha tarin tambayoyin da yasan ba zai iya amsa mata ba tunda shi ba likitan zuciya bane ba, amman ya san likitan zuciyar, ya kuma san zaiyi farin cikin amsa ma Madina dukkan tambayoyin ta.
Nawfal yake ji, yanda yake a hargitsen nan yana ce mishi akwai yiwuwar sai an ma Daada aiki, akwai yiwuwar ba toshewar jini bane da rashin kai kawon shi yanda ya kamata a tsakanin jijiyoyin ta da kuma zuciyar ta kamar wancen karin, matsala ce da ta girmi a dora ta akan magunguna, zai iya yiwuwa sashe ne kacokan a jikin zuciyar tata ya gaza yake kuma bukatar a sake shi cikin gaggawa kafin ya haifar da wata sabuwar matsalar, duka hasashe ne yanzun, babu abinda aka tabbatar sai likitan da aka kira ya zo. Bashi da karfin halin da zai sake daga ma Nawfal din hankali akan hasashe, sai an tabbatar da komai tukunna.
Ya godema Allah da bai fada ma su Nawfal komai ba ganin yanda Julde ya hargitse bayan ya zo asibitin ya karasa Office din Salim din ya kuma yi mishi bayanin hasashen da likitan yayi.
“Dan Allah Daddy, kar su Bajjo su ganka haka su dauka wani babban abin ne, bafa wata matsala bace da ba za’a iya shawo kanta ba, idan ma surgery dinne bashi da wata matsala…”
Salim yake fadi cikin tausasawa.
“Ko kasar za’a bari da ita, Alhamdulillah akwai halin yin hakan… Dan Allah ka kwantar da hankalin ka.”
Kai kawai Julde yake daga ma Salim din ba dan yasan ta inda zai fara kwantar da hankalin shi ba. Har ruwa ya bashi mai sanyi, da kan shi ya bude mishi robar, kurba daya yayi yana jin ruwan ya wuce dakyar, kan shi ya dora a jikin teburin office din Salim din yana maida numfashi, yaji dadin shirun da Salim yayi yana bashi dama ya nemi nutsuwa da kan shi. Bugun da zuciyar shi takeyi shi dinma in aka auna za’a iya bukatar yi mishi aiki a cikinta.
“Ina jin kamar ba zan sake saka su a idanuwa na ba Julde.”
Muryar Daada a waccen jinyar da tayi ya dawo mishi, shirun da ya biyo bayan maganar tata na biyo shi tun daga wancen lokacin zuwa yanzun da yake zaune a ofishin Salim. Shiru ya zaba, Daada bata matsa mishi ba, bata ambaci sunaye ba, amman yasan me take nufi, bata bukatar ta ambaci sunan kowa. Ya zabi shiru ne ya kuma zabi danna tambayoyin ta can kasa tare da duk wani abu daya danganci Yelwa da Bukar din. Bata sake daga mishi zancen ba, shima bai sake bari ya dawo mishi ba sai yanzun. Saboda ya zabi ya so kan shi, ya dora bukatar shi akan tata. Son kan da sai yanzun yake ganin sh.
Su duka Yelwa ta tsalla ke.
Ba shi ka dai ta bari ba.
Har da Daada.