Kamshin turaren shi ya fara cika mata hanci ta zo juya kwanciya, dan tana daya daga cikin mutanen da in har zasuyi juyi komin baccin da suke sai sun farka. Wani lokacin ma sai ta tashi zaune, kamar yanzun dinma haka ta faru da Saratu. Idanuwanta ta sauke akan Julde cikin shaddar shi ruwan toka da tayi matukar amsar farar fatar shi, agogon da yake manne jikin bango ta kalla tana ganin karfe sha daya harda wani abu na dare.
"Ina zaka cikin daren nan?"
Ta bukata tana jin wani abu da ya tokare mata makoshi. Sai da tayi tunanin. . .
Wow