Skip to content
Part 48 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Ba zaice ga asalin abinda ya faru da Baban shi ba, tun idan ya rufe idanuwanshi yana hada kadan daga cikin alamomin fuskar Bukar har ta bace masa, muryarshi da yake tunawa ma gani yake kamar hasashen zuciyarshi ne. Sauran abubuwan a bakin Saratu yaji.

“Babanka ma tsallakewa yayi ya barka, me yasa ni za’a tilasta mun zama da kai?”

Ranaku babu adadi, ya sha numfasawa da nufin tambayar Daada, saiya kasa, saboda yanda take kallon shi, saboda abinda yake gani a cikin idanuwanta, shine yake tsayar dashi kowanne lokaci, saboda tasha furta.

“Bukar…”

A kasan numfashinta idan yayi sallama, ko kuma taga giccin shi, sai yaga ta runtsa idanuwanta ta sake budewa ta girgiza kanta a hankali, yanayin saiya taba zuciyar shi. Taya zai tambayeta, me zaice mata?

“Daada me ya faru? Ina Babana? Me yasa ya tafi bai sake waiwayen mu ba?”

Bayan yana ganin yanda take da tambayoyi iri daya da nashi, yana kuma ganin yanda rashin dawowar Bukar din yake nukurkusarta fiye dashi. Duka sanin shekara nawa yayi masa? Daada tasan shi tun yana cikin jikinta, ta so shi tun kafin ta dora idanuwanta akan shi. Da wacce zuciyar zai tambayi uwa labarin batan danta? Ya taba tambayar Julde sau daya.

“Kome zan fada maka zanyi karya Bajjo, Bukar ya tafi neman karatu Maiduguri, da farko baya hada shekara yake zuwa ganin gida, daga baya saiya dade baizo ba, sai mu dade bamu saka shi a idanuwanmu ba. Bansan dawowar shi ta karshe ba, saboda ina nan Kano, na koma na samu ya dawo ya barka…”

Shirun da yayi bayan amsar Julde yasa Julden kiran sunan shi a hankali.

“Ba kai kadai yabari ba, mu duka ya bari.”

Shisa ya kasa tambayar Daada, da gaskene su duka ya bari, ko a kalaman Julde yana jin ciwon da yake zuciyarshi na tafiyar Bukar din da rashin sanin abinda ya faru dashi. Sai dai a lokacin ya dauka tafiyar Bukar ta karya wani abu a zuciyarshi, tana kuma karyawa duk ranar da zai wayi gari tunanin ya fado masa. Yanda Julde ya rike shi, yana da yakinin ko a hannun Bukar ya tashi, soyayya ta mahaifi iya wadda zai samu kenan. Duk da tunasarwar da Saratu take yawan yi masa, na cewa Julde ba mahaifinshi bane ba, ya kuma sani, tunda ko a makaranta ba da sunan yake amfani ba, Nawfal Bukar yake sakawa. A zuciyar shi, Julde kawunshi ne daya dauki matsayin mahaifin daya tsallake shi.

Baisan matsayin da yake dashi ya wuce duk wani tunanin shi ba sai jiya, saida yaga abinda a labaran duk da suka taba isa kunnuwanshi bai taba cin karo da kwatankwacin su ba. Ba kamar Khalid da Salim ba, halayen Julde masu kyan kadai ya sani, shisa da yaga wannan bangaren ya girgiza, abinda kuma ya karye a zuciyar shi ba irin wanda ya karye da tafiyar Bukar bane ba, da kuma rashin dawowar shi, ko tunanin Bukar ya mutu bai jefashi kunci irin wanda yake ciki ba. Ko ganin kirki bayayi sanda ya karasa cikin dakinsu. A kasa ya zauna, sai yaji kamar bashi da karfin zaman shisa ya kwanta, da takalma da komai a kafarshi, yaja jikinshi ya dunkule waje daya.

Zuciyarshi ciwo takeyi da yake amsawa a ko ina na jikinshi, da zai iya daya cirota ya ajiyeta a gefe ya dan sarara. Baisan kuka yakeyi ba saida yaja numfashi yaji wata shesheka ta kwace masa kamar karamin yaro, kuka yakeyi da yaji dadi babu kowa a kusa dashi balle ace za’a bashi hakuri ko a lallashe shi. Kuka yakeyi da yake neman zuciyarshi ta samu saukin ciwon da takeyi ko kadanne. Anan kasan wani wahalallen bacci ya dauke shi. Sanda ya tashi yanayin duhun dakin ya sanar dashi Magriba tayi ko kuma tana gab, tunda yake bai taba baccin rana irin wannan ba. Mikewa yayi dakyar, ko ina na jikinshi ciwo yake masa kamar mota ta taka shi.

Karasawa yayi wajen makunni ya kunna kwan dakin, mamaki ya fara cika masa zuciya ganin Khalid kwance akan gadon. Alamu sun nuna ya dawo, ya ganshi kwance a kasa, ya zagaye shi ya hau gado ya kwanta. Bai kuma tashe shi yayi sallah ba, yanda yaga Khalid din kwance luf sai yaji zuciyarshi ta doka, wani tunani da yasa kafafuwan shi motsawa na gifta masa.

“Hamma…”

Ya kira da sauri yana bubbuga shi, a hankali ya motsa yana juyo da jikinshi.

“Yamma tayi sosai, kayi sallah? Ni ko azahar banyi ba.”
Kai Khalid ya daga masa, yayi azahar da la’asar duka, baima dade da shigowa dakin ya kwanta ba.

“To ka tashi ko ba’a kira Magrib ba yanzun za’a kira.”

Ya karasa fadi yana wucewa bandakin, fuskarshi ya fara wankewa sannan ya dauro alwala ya fito, azahar da la’asar ya gabatar, yana idarwa yaji ana kiran Magriba, saiya mike, a hanyarshi ta zuwa masallacin yake neman gafarar Ubangiji ta sallolin da baiyi akan lokaci ba, saboda hade sallah ba sabonshi bane ba, wani iri yakeji. Da aka idar saida ya duba Khalid bai ganshi ba, nan ya zauna cikin masallacin saboda zuciyarshi ta dan samu sarari, sanyin masallacin ya sanyaya masa wajajen da suke masa zafi, yasan yana fita daga ciki komai zai sake danne shi.

Sai yai zamanshi har akayi isha’i sannan, shima dakyar ya tafi, don ji yake kamar ya kwana cikin masallacin, dole gidanshi ko bai gina masallaci ba, zai ware wani waje da sallah kawai za’a dingayi, watalila yayi sanyi da albarka irin wadda masallacine kawai yake da ita, don ya samu wajen kwanciya idan yana cikin damuwa. Zuciyarshi matse a cikin kirjinshi da yaga Khalid a zaune kan darduma, a gida yayi sallah kenan, abinda zaisa shi sallah a gida ba karami bane ba. Baiyi masa magana ba.

“Ina mukullin motarka?”

Ya tambaya, hannu yasa a aljihu ya ciro ya mika masa, nashi aljihun ya duba yaga yana da dubu shidda. Sai ya fita, baiyi wani nisa ba yayo musu takeaway badan yana jin yunwa ko yana cikin yanayin son cin komai ba, jikinshi na bukatar abinci ya sani, haka Khalid, yafi bukatar ganin yaci wani abu ma. Yana komawa ya samu Khalid harya kwanta, a kasa ya ajiye komai.

“Hamma ka taso mu ci abinci.”

Cikin sanyin murya Khalid ya amsa shi da,

“Banajin yunwa Bajjo, ka kyaleni dan Allah.”

Mikewa Nawfal yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito ya sake kaya ya kwanta shima.

“Ka tashi kaci wani abu, ka kashe mana kwan dakin kuma.”

Khalid ya fadi, don yana kallon Nawfal din, ko amsa bai bashi ba.

“Da kai nake magana kana jina kuma.”

Bargo Nawfal yaja ya rufe jikinshi har kai.

“Ka girmi wannan yarintar, har mata kake da Bajjo.”

Baiyi magana ba, yanajin Khalid din sarai, idan ba haka yayi masa ba, ba zaici abincin ba, bashi bane yaro, Khalid ne yarinta bata saki ba, yi masa dabara bashida wahala, yanajin shi yaja tsaki a jere yafi sau hudu kafin ya sauka.

“Saika sauko muci dan ubanka.”

Duk yanayin da yakeji bai hana murmushi kwace masa ba.

“Magana fa nake maka.”
Bude bargon yayi ya fito yana kokarin danne dariyar da take neman subuce masa. Abincin sukaci, shinkafa da dankali ne ya siyowa Khalid, shikuma ya siyowa kanshi kifi da dankali, yayi mamakin yanda sukaci abincin sosai, shiya kwashe kwanonin ya dawo, suka zauna suna dan hirar da ba zasuce ga asalin abinda suke fada ba, hirace da kowa abinda yake son magana akai daban da abinda yake fitowa daga bakin shi. Wani numfashi mai nauyi Khalid yaja yana fitarwa, idanuwanshi kafe jikin bangon wajen kamar mai son gano duka amsoshin tambayoyin da yake dasu akan bangon ya ce.

“Idan abin nan ya taba har yaranmu fa?”

Wani irin shiru ya ratsa dakin kafin Nawfal ya iya bude bakin shi da yakejin yayi masa nauyi.

“Babu abinda ya faru, kaji Daddy ai, yace babu abinda ya faru.”

Kai Khalid ya jinjina, Julde na da halaye da yawa, amman karya bata cikinsu.

“Bai faru ba yau…”

Khalid ya fada yana rasa ta inda zai fara gayawa Nawfal halayen Julde daya sani, da kuma yanda Salim yaga babu halin daya kamaci ya dauka irin wannan, da gaskene kowa yana da labarin bayarwa, kowanne mutum da zaka hadu dashi a hanya yana da labarin da zai baka inda zaka tambaye shi, amman wasu labaran duk da akwaisu ba zasu taba baduwa ba, wasu labarin kokarin binne su akeyi yanda ko kurarsu wani ba zai tarar ba balle kuma yaji su. A cikin wannan labaran akwai wannan, saboda ba labarinshi bane ba, masu labarin idan suna so ya sani zasu bashi da kansu, idan yana da rabon ya sani zai sani kamar yanda shima ya sani.

Numfashi ya sake ja, kirjinshi na tafasa, daya runtsa idanuwa, fuskar Daada ta dawo masa dazun, yanda tayi masa murmushi kamar babu ciwo a kirjinta, kokarin yakice zuciyarshi yakeyi dan karta hasaso masa abinda Daadar take ji amman ya kasa. Ya Daddy zai musu haka? Jin wani abu na toshe masa makoshi, tafukan hannunshi yasa ya tallabi fuskarshi dasu yana sauke numfashi hadi dajin dumin hawayen shi na zubowa, wanne irin abin kunya ne wannan? Ya zai iya sake hada idanuwa da Madina yanzun? Ta sani? Idan bata sani ba ta sani din ya zataji? Rayuwarta zatayi canzawar da ba zata taba komawa dai-dai ba.

Saboda Julde ya tabasu ta fannin da warkewarshi zaiyi wahala, tabon da zai bari kuma zai dauke su har karshen rayuwarsu bai daina ciwo ba, ko motsin kirki Nawfal baiyi ba, numfashin shima bayaso yayi karar da zata katsewa Khalid yanayin da yake ciki. Kuka ne yau anyi musu abinda dole zasuyi shi, zai karya idan yace baiji sauki-sauki ba, hade kanshi da gwiwa Khalid yayi, ya dauki lokaci a haka kafin ya dago, sai Nawfal ya kauda kanshi kawai, ya bashi tazarar da yasan yana bukata harya mike ya shiga bandaki, saiya tashi ya hau gadon ya kwanta.  Daya fito shi ya kashe musu fitilar dakin, sannan shima ya kwanta, ko saida safe ba suyiwa juna ba, kowa ya juya kwanciya, zuciyoyinsu cunkushe da tunanin da yayi kamanceceniya a lokaci daya kuma yasha bamban.

******

Da safe har wajen karfe goma suna daki, Nawfal yaji Khalid yayi waya wajen aiki yace musu ba zaije ba bashida lafiya. Shikuma yayi waya da Murjanatu tace masa ta gama shiryawa, za’a sauketa filin jirgi, yasan duk inda take tana gab da sauka, shisa yayi wanka ya shirya ya koma ya zauna. Khalid yake so yaga ya tashi sai su shiga bangaren Saratu tare, amman saiya koma ya kwanta, yana so yace masa ya tashi suje amman bayason fama masa ciwon da duka suke ta lallabawa. Dakyar ya tattaro karfin gwiwa ya mike yana fita, ya kai wasu mintina a bakin kofar dakin kafin ya shiga da sallama, a kitchen ya samu Saratu

“Ina kwana Nanna”

Ya fadi muryarshi na rawa, juyowa tayi, sai yaga fuskarta kamar a kumbure.

“Bajjo…kun tashi lafiya.”

Mamaki yasa shi ya bude bakin shi, amman sauti ko daya yaki fitowa, ya rufe yayi gyaran murya kadan kafin ya iya amsawa da.

“Alhamdulillah, ya jikin Daddy?”

Dan juyawa ta yi kafin ta amsa,

“Da sauki, bacci yake yi.”

Kai ya jinjina yana kokarin juyawa saboda baisan me zai sake fada ba.

“Ka tsaya ka wuce muku da abin kari.”

Wani mamakin ya sake dukanshi tare da maganganunta, tunani yakeyi, idan akwai ranar da ta taba yi masa tayin abinci, koma ta damu da yaci ko baici ba, asalima rashin cin nashi yafi muhimmanci a wajenta tunda yanda duk zata dafa saita tabbatar ya haramta a wajen shi.

“Sai dai in kaiwa Hamma, zan fita ne ni.”

Juyowa Saratu ta yi.

“Haka zaka fita baka ci wani abu ba? Ka tsaya ka tafar muku dashi ku duka, kaima karka fita bakaci wani abu ba.”

Ko yaso yayi magana ba zai iya ba, wani abu ya tokare masa makoshi, iya wannan maganar, iya wannan kulawar ya tuna masa dararen da ya shafe cikin kewar kulawar uwa, tasa zuciyarshi ta motsa da wani irin yanayi, har yanajin kamar idanuwan shi na neman tara hawaye, doyace da kwai. Sai ruwan zafi, karba yayi ya tafi, har ranshi baiyi niyyar cin komai ba, ko yunwa ma bayaji, amman da ya kai musu saiya tsinci kanshi da zuba shayin ya saka sugar, suna da kayan tea dinsu. Ganin ya kurba ya ajiye da sauri yasa Khalid dagowa sosai yana kallon shi.

“Ruwan zafi ne Bajjo.”

Ya fadi kamar yana son tunawa Nawfal din.

“Nanna ce ta bamu.”

Cewar Nawfal yana dago kofin hadi da hura iska a ciki, kallon shi Khalid yakeyi, ya sha ya kai rabin kofi kafin ya ajiye ya bude kular yaci doya yanka hudu, ya karasa shanye ruwan shayin ya mike saboda kiran daya shigo wayarshi, a bakin kofa ya daga da fadin.

“Jaan yanzun zan fito daga gida, na tsayawa karyawa ne, Nanna ce ta bamu doya da shayi.”

Yanda ya karasa maganar zaka rantse babu wanda ya taba bashi doya da kwai da shayi a rayuwar shi. Ya samu cunkoson abun hawa sosai a hanya kafin ya karasa filin jirgin, shisa tana ganin shi ta shagwabe fuska, ya mika mata hannun shi da ta kama cikin nata, ya dan dumtsa cikin ban hakuri, mutanen da suke wajen na hanashi hade jikinshi da nata, karasawa yayi yana karbar dan akwatin da take rike dashi a dayan hannunta ya jata dan su karasa inda ya ajiye motar Khalid din daya fito da ita

“Cunkoso yayi yawa a hanya shisa…”

Dan tana daya daga cikin mutanen daya sani da basa son jira, ko kadan batason jira, da bashi bane da yasha mitarta da bata karewa, batace masa komai ba, shiya bude mata mota ta shiga, ya saka akwatinta sannan ya zagaya ya shiga shima

“Me yake damunka?”

Ta tambaye shi a sanyaye, numfashi yaja yana tayar da motar, ya manta yanda take iya karantarshi kamar littafi.

“I can’t talk about it.”

Ya fadi da dukkan gaskiyar shi, kai ta jinjina tana mika hannu ta shafi fuskar shi, lokutta irin haka yana godewa Allah da girman da tayi a cikin turawa, da kuma dabi’unsu irin wannan data dauka, in dai gaskiyar shi zai fada mata ta wadace ta, yanzun zata tabbatar da ta nuna masa in har yana son maganar ta hadasu to a shirye take da ta saurara, amman ba zata sake tambayar shi ba. Juya motar yayi yana nufar gidan Daada kai tsaye, suna shiga da sallama Murjanatu ta karasa tana rungume Daada da take zaune.

“Na yi kewarki.”

Ta fadi da fulatanci, dariya Daada tayi, babu yanda za’ayi ba zakaso Murjanatu ba

“Ina Madina?”

Ta tambaya saboda ita kawai take son gani, ko hotonta bata dashi, data tambayi Nawfal shima da mamaki a fuskarshi ya ce,

“Kinsan sai yanzun nake tunanin anya na taba ganin hoton Madina kuwa?”

Dariya sukayi sosai, yanda take jin Madinar, yanda komai nata yasha bamban dana sauran mutane yasa take son ganinta fiye da kowa a danginshi, daga ita sai kuma Salim, Khalid abinda ya rage kadan ne, tunda suna video call sosai da Nawfal din, kuma zasi gaisa, har ayi hirar da ita wasu ranakun. Amman Madina dan video call din da zasuyi da Nawfal lokacin da suke india duk ta fita, sai ta dawo ya gaya mata

“Kaman Madina bata so in ganta.”

Ta fadi rannan tana saka shi dariya.

“Madina!”

Nawfal ya kira yana samun waje ya zauna.

“Daada ina kwana… Ya jikinki?”

Murmushi ta yi masa.

“Jikina ai ya yi sauki sai abinda ba’a rasa ba.”

Kai ya jinjina yana shirin sake kwalawa Madina kira ta fito daga dakinta, bata ga Murjanatu ba sai da ta zagayo, ta kuwa bude baki cike da mamaki kafin tayi dariya

“Jaan, ga Madina, Madina ga Murjanatu.”

Nawfal ya fadi, karasawa Madina tayi ta zauna a kusa da ita tana rasa asalin abinda take ji, sai dai kallonta Murjanatu takeyi, har suka gaisa, ta tashi tana nufar kitchen tare da tsegumin Nawfal bai fada mata zata zo yau ba, yau ta fara ganin Madina, amman tasanta, koma a ina ne ta santa, sai da tayi dariya take ganin tabbas akwai inda ta santa. Duk hirar da suke wannan sanayyar take nema a zuciyarta, har suka karya da dankali da kwan da tayi musu da shayi, ta shiga ta kara gyara dayan dakin da Nawfal kan kwana idan yazo gidan Daadar, ta dauki akwatin Murjanatun ta kai mata can, ta mike da fadin zata dan watsa ruwa ta kwanta dan ji takeyi sam bata huta ba tunda suka baro India.

Nawfal ya bi bayanta, a tsakiyar dakin ya kamata yana juyo da ita ta fuskance shi, hannuwanshi ya dora kan kafadunta yana kallon fuskarta.

“Gidado ji nakeyi kamar nasan Madina, da tayi dariya sai inga akwai inda nasan yanayin da yake kan fuskarta da idanuwanta, inata tunani na rasa…”

Murmushi yayi yana sumbatar goshinta.

“Madina irinta ita kadaice, sai dai ko in a film kika ga mai kama da ita.”

Dakuna fuska tayi tana zame jikinta daga nashi, don da gaske wanka take so tayi, idan ta biye masa zancen ne zai sauya. Akwatinta ta bude ta dauki kayan wankanta ta shiga bandaki, saida ta murje jikinta da sabulu sannan kamar an kwada mata guduma akai ta tuna ina taga mai kama da Madina, a gidan kawunta ne, ba mace bace ba namiji ne, ko gashin da yake fuskarshi bai hana kamannin shi fitowa da Madina ba, da sauri ta zubama jikinta ruwa ta dauro tawul ta fito.

“Gidado a Abuja naga me kama da Madina…wallahi kamarsu daya, da tayi dariya irin fuskarshi nake gani.”

Wani abu Nawfal yaji ya doka a zuciyar shi

“Namiji? Ba mace ba?”

Ya tambaya yana son tabbatarwa, kai ta daga masa tana dorawa da

“Kuna da ‘yan uwa a Abuja?”

Da kai zai girgiza mata, saiya fasa, saboda ba zaice ga inda suke da ‘yan uwa ko inda basu da yan uwa ba, daga Daada sai Julde ya sani, ba kuma zai yiwu ace basu da wasu dangin ba.

“Wallahi ban taba ganin kamanni irin haka ba tunda nake, ana cewa ina kama da Umma, amman ba irin na Madina da mutumin nan ba, kamar babanta.”

Haka kawai Nawfal yake jin zuciyar shi na dokawa, ana kamanni a duniya, ya sani, ga Salim nan da Julde, daya gifta ko ba’a fada maka ba kasan ya hada jini da Julde.

“Ina zuwa.”

Yace yana ficewa daga dakin, baiga kowa a falon ba saiya nufi dakin Daada, ya kuwa sameta a zaune.

“Daada…”

Ya kira, ta dago ta kalle shi amman ya rasa ta inda zai fara tambayarta

“Kar wani abu ya rikeka Bajjo, lokaci yayi da dole zan amsa duk tambayoyin da nake ganin a idanuwan ku kaida Madina, amman kuna kasa tambayata, menene?”

Wani abu Nawfal ya hadiye kafin ya iya cewa

“Murjanatu tace mun tasan Madina, ko a ina ne ta santa, tun dazun take tunani, shine tace mai kama da itane ta gani, a Abuja…tace idan tayi dariya kamar fuskar mutumin, in wani zai gani zai iya cewa Babanta ne, zuciyata na dokawa Daada, jikina yana mun wani iri, bansan me nazo in tambayeki ba, mutum nawa ne suke kama da juna a duniya…”

Kallon da Daada tayi masa nasa sauran maganganun makale mishi

“Ya sunan shi?”

Ta tambaya da wani yanayi a muryarta, juyawa yayi yana komawa ya samu Murjanatu da take shafa mai

“Ya sunan shi? Mutumin?”

Kallon Nawfal tayi tana tunani, sau biyu yazo gidan tana nan, bata cika mantuwa ba, tana fada masa kamar karamin yaro ya fita da sauri yana shiga dakin Daada

“Kabiru tace sunan shi Kabiru…”

Kamar an saki kofin gilashi a kasa haka Daada taji wani abu ya fashe a cikin kirjinta, kafin burinta ya hau benen da take fatan karya ruso dasu gabaki daya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 47Rai Da Kaddara 49 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×