Skip to content

Rai Da Kaddara 2 | Babi Na Ashirin Da Uku

3.3
(3)

<< Previous

Ba don wani ya fada mata cewar don an haifeta a marake, ta girma, tayi aure anan zata kare sauran ranakun ta a cikin kauyen ba. Kawai a jikinta take jin cewa anan din za’a binneta wata rana, ko da zata bar Marake sai dai tayi tafiyar da sunan ziyara, ba wai bari na gabaki daya ba. Duk wani abu da yake da muhimmanci a wajenta a ganinta ya fara ne daga Marake, ya fara daga tsatsonta. Ta gilashin motar take kallon titi, take ganin bishiyoyin da suketa wucewa suna kara tazarar da take tsakaninta da Marake.

Shikenan? Da gaske tabar tsatson ta? Dalilai fiye da daya sun hade waje daya, a cikin wannan dalilan harda jinjirar da take rike a hannunta tana bacci kamar a duniya kaf bata da wata matsala. Sai take jin tsakanin juma’a da asabar kamar wata rayuwar ce zuwa wata saboda nisan da tazo mata dashi. Amman jiya ne, jiya ne komai ya faru, a daren shekaranjiya daya kasance na juma’a ne baccin da zata kira dana asara yayi nasarar dauketa. Saboda ji tayi kamar bata jima da rufe idanuwanta ba ta budesu da saukar kalaman Yelwa.

“Na kashe shi Daada… Na kashe Baba… Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Na kashe Baba Na!”

Tabbas ta mike zaune, ta kuma kama Yelwa da take wani irin fitar da numfashi kamar tana tsakanin rayuwa da wata duniya ta daban, akwai hasken fitilar da ta fara dishewa alamun batirinta yayi sanyi a cikin dakin, wani numfashin da Yelwa ta sake fitarwa da damkar da tayiwa Dije na tabbatar da ciwon nakuda ne ya kama Yelwar.

“Babaa… Na kashe shi Daada… Na kashe Baaba”

Yelwa take fadi a tsakanin ciwon nakudar da take yi, sai Dije ta saketa tana mikewa tsaye gabaki daya zuwa kan gadon Datti, tun kafin ta tabashi tasan babu rai a tare dashi. Abinda ya saukar mata wannan karin yayi dai-dai da ruwan daya sauko. Ya kuma yi dai-dai da wani irin nishi da Yelwa tayi tare da dirowar ‘yar da bata dauki lokaci wajen sanar da dirowarta duniya ba ta hanyar karade dakin da kuka. Idan Dije tace ga inda ta samu karfin halin raba idonta da gawar Datti ta dawo kan Yelwa da bata taimakon da take bukata tayi karya. Kafin ta gama gyara wajen bayan ta samu ta yanke cibi, ta kuma ajiye yarinyar kan shimfidar da ta tashi. Ruwan ya fara tsagaitawa, cikin nuna alamun asuba tayi. Dije kuma ta sami tabbacin hakan da rangada kiran sallar farko da akayi.

Saita fita daga dakin zuwa dakin girkinsu, jinta takeyi kamar ba ita ba, da yayyafin da akeyi ya sauka jikinta ma sai ta dago hannayenta karkashin duhun asuba, bata gane komai, bata gane abinda yake faruwa da ita. Komai dai ya kara canzawa, ciki harda bugun zuciyarta da bata juyo alamar shi. Dakin girki ta shiga ta hada wuta ta dora ruwa a tukunya ta dawo. Saitayi tsaye, kuka jinjirar takeyi har lokacin, amman Yelwa bata motsa daga inda ta haihu ba, kamar ma bata motsi itama. Saita rasa wa zata fara nufa. Yelwar dai ta sake tsintar kanta da tunkara. Ta kamata ta dago da ita tana jijjigata.

“Yelwa…. Yelwa”

Ta kira cikin wata irin murya, amman bata motsa ba, sakinta tayi tana fita ta dibo ruwa ta dawo tana sake dagota hadi da shafa mata ruwan a fuska, sai da tayi hakan wajen sau hudu, tukunna Yelwar taja wani dogon numfashi ta bude idanuwanta, ta kalli Dije, saita mayar ta rufe tana mirginawa ta sauka daga jikin Daada taja jikinta ta dunkule waje daya hadi da sakin wani kuka da alamu suka nuna daga wani sashi na zuciyarta yake fitowa, kamar bataso farkawa ba, kuka takeyi kamar babu abinda ya rage mata a duniya.

“Ki tashi Yelwa, ki karbeta ki shayar da ita ko zatayi shiru.”

Dije ta fadi, muryarta na komawa cikin kunnuwanta da wani sauti da ta kasa fahimta. Amman Yelwa bata ko nuna alamun motsawa ba, sai da ta sake kamota, ko ina na jikinta bari yake yi.

“Na kashe shi Daada… Na kashe shi…. Na kashe shi.”

Take fadi tana kara maimaitawa kamar karatu. Kai kawai Dije ta iya dagawa tana taimaka mata ta tashi zaune, ta saka mata yarinyar a hannunta, sai tayi shiru, kamar ta gane inda aka sakata, kamar tasan a jikin wadda ta kwanta cikintane tsayin watanni. Sai dai daga yanda ta riketa take bin muryar Dije akan ta shayar da ita zaka gane duk tanayin hakan ne cikin fitar hayyaci. Kamar rabi da rabi take cikin duniyar. Sake fita Daada tayi tana zama dakin girkin, kamar zazzabi takeji da kuma sanyi da ma wani abu da bashi da suna duk a waje daya.

Ta kwashe ruwan ta dauka takai bayi ta dawo ta kara zuba wani. Har taje ta karbi yarinyar daga hannun Yelwa ta goyata ta kama Yelwar ta fito da ita bata daina kuka tana maimaita.

“Na kashe shi.”

Ba, sai dai wannan karin kamar kanta take fadawa maganar ba Daada ba. Tunda babu itace da zani Daada tayi amfani taiwa Yelwa wanka, tana tuna mata lokacin da tayi mata hakan fiye da yanda za’a iya kirgawa a kuruciyarta, a jinyar da tayi. Sai dai na yau ya sha bamban da sauran. Kayanta ne ta daukowa Yelwa ta bata ta saka, ganin kamar hankalinta yayi nisa da ita yasa Dijen saka mata kayan da kanta. Jaririyar ta yiwa wanka itama, tana tunanin abinda zata saka mata a jikinta. Saita tuna ragowar kayan Haidar da suke gidanta. Ta bayar da wasu da yawa, amman akwai sababbi wajen kala hudu da tun na lokacin yana jariri ne da basuyi amfani dasu ba. Watakila Mero ta adana ne, sai kuma kaddara bata barta da zabin tsayawa daukar su ba.

Su ta lalubo ta saka mata. Ta mika ma Yelwa da take zaune ita tana daukar mayafinta ta lulluba taje ta bude gidan tana fita tayi tsaye a bakin kofar gidan tana rasa inda zata nufa kowa zata fadawa, sai Abu ta fado mata a rai, safiyar data shigo musu bayan rasuwar Hammadi. Mutuwar ta kadata, sai dai yau ta gane babu abinda taji, ba kuma ta fahimci komai ba, maraicin da take ciki na sake danneta. Hakama rashin Abu a kusa da ita, tana nan tsaye, yayyafin da akeyi na rage karfi har maza suka fara dawowa daga masallaci.

“Dije?”

Makocinsu ya kira cikin son tabbatar da ita din ce.

“Dije lafiya kuwa? Me yake faruwa ne? Ba dai jikin Dattin bane ba ko?”

Da yake yasan bashi da lafiya, bai ganshi ba kwana biyu yayi sallama, ya kuma shigo bayan Datti ya bada izinin hakan. Sai taji harshenta yayi nauyi, dakyar ta iya furta.

“Ya rasu… Ya rasu ne.”

Inalillahi wa ina ilaihi raji’un din daya furta na dira kunnuwan ta, wani gashi da batasan da zaman shi ba a wajaje mabanbanta a jikinta yana mikewa.

“Bari in fadama Audi sai aje a sanar da liman mu taho tare.”

Kai ta iya daga masa. Tana nan tsaye har suka dawo suka sameta, sannan ta iya motsa kafafuwanta tana binsu cikin gidan, ta kuma nuna musu dakin da Datti yake a ciki. Tana kallo suka shiga don su tabbatar da cewa ya rasun. Ita ta mika musu ruwan da zasuyu amfani dashi wajen yiwa Datti wankan shi na karshe. Tana tsaye bakin kofar, sai dai kafin a gama hadashi har mata na nan makota sun fara shigowa, su suka kama Dije da batayi musu ba suka shiga daki da ita. Idan da mamaki a fuskokin su ganin jaririya sabuwar haihuwa da take ta tsallara kuka basu nuna ba.

Ba kuma suyi yunkurin hana Dije da ta dauketa ta goya ba, tana samun waje ta zauna. Tun yarinyar na kuka har tayi luf alamar tayi shiru ko kuma bacci ya dauketa.

“Ki fito kiyi masa addu’a…”

Za’a taimaka mata taji ta mike da kanta, har dakin ta shiga, ta ganshi shimfide an hada shi. Tsayin shi na kara fitowa kamar an jashi. Tana tsinkayo muryar mutane, harda wanda zata iya kira da abokan Datti na fadin.

“A’a matar shi zatayi sallama da shi sai a fito da gawar.”

Tana kuma sake jin wasu sunata kiran “Gawa”. Sunan shi harya bace, wani abu da ya girmi tsoro ya tsirga mata. Tsugunnawa tayi, kirjinta kamar zai fado.

“Kace zakayi son kai idan ka rokeni gafara Datti. A iya zaman mu idan ka batamun na yafe maka, Allah nake roko daya shafe kuskurenka ya yafe maka…nagode nima… Nagode da tarin kaunar ka…”

Sauran kalaman sai suka makale mata, kallon shi takeyi kamar takai hannu ta yaye likkafanin ta sake ganin fuskar shi, sai dai ko da bata yaye ba, zata rantse da Allah idanuwanta sun yaye mata farin mayafin, fuskar shi take ganin tarau kamar yana bacci. Sai ta mike, tana jin zaren dake rike da sauran hankalinta na tare da yanda zata ja numfashi ta fitar da sanin kowanne a ciki yana kusantata da tarar da Datti. Basu kawo yau da sauki ba, sun fuskanci kalubale mai tarin yawa, akan auren su, a yaran da sukaita binnewa, a yaran da suka rayu kaddararsu tazo da nauyi. Sai dai zata zabi Datti, idan aka bata dama zata sake zabar shi a matsayin mijinta. Ko da kowa zai mata tambari da mahaukaciya, zata sake zabar Datti iya adadin da dama zata bata.

Saida ta fito ta kalli liman da yake tsaya yana ce mata.

“Sai hakuri, kowanne mai rai mamaci ne, muma duk lokaci muke jira… Allah ya jikan shi ya yafe masa”

Tana amsa shi da.

“Julde na hanya, inda duk yake yana hanya. Don Allah ku jira shi, da sassafe yake isowa. Yana hanya duk inda yake.”

Abinda duk suke fada baya karasawa kunnuwanta, rokon su tayi da su jira Julde. Kamar kuwa ta san yana hanyar. Duka alhamis din tazo masa da wani irin yanayi, haka ya koma gida daga kasuwa. Shisa ya biyewa Saratu sukai tashin hankalin da ta kwana biyu tana nema akan Nawfal. Yaran da baiga me ya tsare mata ta dauki karan tsana ta dora masa ba. Sai dai daya kwanta wasu mafarkai ya dingayi da suka kara hargitsa shi. Yelwa ya gani a tsugunne tana kallon filin wajen kamar tana jiran wani abu, ya bude bakin shi ya kirata amman babu sautin da yake fitowa. Bai san ya akayi yaga Datti ba, a tsaye yake shi, idanuwan shi na kan Julden, a maimakon Yelwa da yaga kamar tana jiran wani abu, Datti na kallon shine kamar yana jiran shi.

Farkawar da yayi bai iya komawa bacci ba, zuciyar shi bugawa takeyi kamar wani abu na shirin faruwa dashi. Shisa tuki ne abu na farko daya koya bayan sun koma Kano, sannan mallakar mota tashi ta kanshi. Ya godewa Allah ya sake gode masa da wannan ni’imar lokacin da bai saurari Saratu ba, ko wanka baiyi ba karfe hudu na safe ya fita daga gida yana kamo hanyar Marake. Ana ta yayyafi a wasu kauyukan. Baiyi karfin da zai kasa ganin hanya ba, ji yake tamkar Maraken ta kara masa wani irin nisa. Da ya shiga cikin garin sai yaji bugun zuciyar shi ya karu. Sai ma daya doshi gidansu yaga mutane a kofar gidan, daga nesa ya ajiye motar ya kasheta ya fito yana takowa da kafafuwan shi cikin hanzari.

“Sannu Julde… Sannu kaji.”

Wani a cikin taron mutanen ya fadi.

“Datti lokaci yayi.”

Kalamai uku, kalaman da ba zai taba mantawa dasu ba, lokacin da zuciyar shi tayo kundunbala daga cikin kirjin shi tana gangarawa cikin gidan, ya kuwa bita, bata tsaya ko ina ba sai a bakin gawar Datti da aka fito da ita tsakar gidan. Ya ji gwiwoyin shi a kasa, bai dai fahimci ko rarrafe yayi ya karasa ba. Ya kuma dora kanshi a jikin gawar Datti yana jin wani abu na rushewa a tare dashi.

“Yanda ka kunyata ni Julde… Allah ya kunyata ka a idanuwan mutanen da suka fi komai muhimmanci a wajenka…”

Kalaman Datti da sune na karshe a tsakanin su suka dawo masa, suna jijjiga zuciyar shi daga inda take tana komawa kirjin shi ta zauna da wani irin karfi. Mikewa yayi yana ratsa duk matan nan harya tarar da Dije ya kamota yana fito da ita daga dakin.

“Daada bai yafe mun ba, Baba bai janye kalaman shi a kaina ba… Ya tafi bai yafe mun ba.”

Kallon shi Dije takeyi, sai take jin wani abu na bude mata, kamar ganin Julden na fisgota daga duniyar fitar hayyacin da ta shiga ne, kamar yanzun zata dawo ta fuskanci komai.

“Ka taho a kama, gawa bata jira fa.”

Wani ya fadi, da sabon firgici a fuskar Julde yake kallon Dije.

“Kaje… Kaje ka dawo.”

Ta iya fadi, idanuwanta sun kankance duk da babu digon hawaye ko daya a cikinsu. Juyawar kuwa yayi, tana kallo suka daga munkarar da Datti yake ciki suka fita dashi daga gidan, suna tafiya tare da wani sashi mai girma na zuciyarta. Ta lumshe idanuwanta, kirjinta kamar an hura wuta a ciki. Bata sake saka Julde a idanuwanta ba sai dare, bayan mutane duk sun tafi, sai yan uwanta da suke uba daya, saboda wanda suke uwa daya matan ba’a cikin marake suke aure ba, da alama kuma labarin rasuwar bai karasa musu ba.

“Daada…”

Taji muryar shi, sai ta fita ta same shi yana tsaye. Kallon shi take yi.

“Daada da gaske Yelwa ta dawo?”

Kai ta daga masa, kiran Yelwa da yayi na bude wani sashi daya toshe a cikin kanta.

“Banganta ba, tun da dafe banganta ba, sai yarinyar.”

Numfashi Julde yaja ya fitar, abinda yaji ana fada a waje da gaske ne kenan. Anga Yelwa ta shigo garin da tsohon ciki, ance ma ta haihu, jinjirar ko jinjirin ne goye a bayan Dije. A wajen zaman makokin da Julde baiga amfanin shi ba, saboda ana dawowa aka fara fito da kokon da baisan wake da karfin halin sheka shi a yanayin da suke ciki ba. Hawayen dake ta masa barazana yake dannewa, saboda yanajin shi da Daada kawai ya kamata su ga raunin juna, ita kadai ta rage masa kamar yanda a halin yanzun shi kadai ya rage mata. Kafin azahar an fara fitowa da wake da shinkafa faranti faranti kamar ana biki ba zaman mutuwa ba.

Lokacin hira ta barke, ana kwasa ana labarai iri-iri, yana gefe yana jin kamar ya tarwatsa taron kowa ya kama gabanshi. Kasa-kasa ya fara jin zancen Yelwa, basuyi tunanin yanda suke maganar zai karasa kunnen shi ba, sai dai Allah ya hore masa ji, irin yanda yake zaton ya zarta na mutane da yawa, kamar iska na kara taimaka masa wajen kwaso masa maganganu zuwa kunnen shi.

“Da gaske da ciki ta dawo?”

Ya jefi Daada da tambayar, saita dan juya masa goyon dake bayanta. Don kukan da yarinyar take tayine ma yasa wata a cikin yar uwarsu ta bada madarar shanu a bulunbotin tace a bata tunda taki kama maman duk wata mai shayarwa a cikin, don ita bata da wadatar ruwan mama, sai dashi take hadawa yaron da take goyo da basuyi sati biyu da rufe arba’in ba. Sai gashi ta sha kuwa.

“Daada…”

Julde ya kira da wani yanayi a muryar shi.
“Daada a waje naji ana maganar Yelwa ta dawo da ciki.”

Wani abu ya hautsina a cikin Daada, zufa na karyo mata.

“Ki hada kayanki da safe mu tafi tare.”

Yanda take kallon shi yasa shi fadin.

“Baki da wani dalilin zama… Baki ga Yelwa ba idan ta sake tafiya fa?”

Kallon nashi takeyi tana juya kalaman shi, ma’anarsu da girmansu a wajenta. Bata amsa duk abinda yake fada ba ta juya ta koma daki, lokacin ne kuma ‘yan uwanta da suka rage a cikin gidan suka zagayeta da tambayoyin inda ta samo jaririya da kuma abinda sukaji mutane na fada.

“Da gaske Yelwa cikin shege tayo tazo ta haife shi anan ta sake shiga duniya? Wanne irin bala’i ne wannan Dije?”

Kallon su takeyi.

“Shege a zuri’ar Baba? Kamar abin kunyar da Julde yayi bai ishemu magana a garin nan ba? Ya zakiyi da wannan Dije?”

Maganganu sukeyi tana jinsu, tana kuma fahimtar su, su da suka hada uba kenan, a kalamansu take tsinkayo yanda duk da basu fada kai tsaye ba suke dana sanin jinin da suka hada da ita, saboda ita da ‘ya’yanta sun zame musu abin kunya, har a tsakanin maganganun taji kamar suna bada shawarar a shake jaririyar da babu wanda ya bata zabi ta inda zata fito, saboda komai zai fi zuwa da sauki idan bata numfashi. Wannan kalaman ne yasa Dije kallon su, zuciyarta tayi wani irin shiru a kirjinta lokacin da ta ce,

“Ku fitar mun daga gida.”
Ta sake maimaitawa, tana karawa a tsakanin zagin da suke mata, ta kafe akan basu amsa daya har saida sukai zuciya suka dauki mayafansu. Kamar fitarsu take jira ta dauki jaka tana fara harhada duk wani abu da hannunta zai iya kaiwa sama. Ta kuma shiga dakin Datti, nan ne ta ga ledar da ta gani a hannun Yelwa, ta dauko ta ta fito, sai ga Julde ya shigo.

“Ka tayani mu hada kayanmu Julde, da gaske ne babu abinda ya ragemun a garin Marake.”

Da sabuwar jaririya, da iya abinda zata iya hadawa wanda motar Julde zata dauka, bayan kuma yayi mata alkawarin zai dawo ya kwaso mata sauran kayayyakinta, zai biya yabar sako a gidan Baabuga ko da Bukar ya dawo, zai bar sako inda zai riski Yelwa ko da ta dawo itama. Sannan ta kulle gidan ta bishi. Bata san me ta gane a hanya daya nuna mata alamun sun fita daga Marake ba, iska dai taji tayi mata kadan har bata iya numfashi yanda ya kamata

“Ka tsayar da motar nan Julde…”

Ta fadi a wahalce, bai musa ba ya gangara gefen titin yana tsayawa. Saita bude murfin ta fita tana tsugunnawa cikin neman iskar data rasa, tana jin Julde ya dafa kafadunta yana kiran sunanta. Komai ne yake danneta yana hanata numfashi, dakyar taja wani tana fito dashi hadi da wani gunjin kuka. Ta zauna a kasa a gefen titi, a gefen dajin da batasan na wanne kauye bane tana kukan abubuwan da ta rasa, kuka irin wanda bata tabayi ba, kuka a jikin Julde da hawayenta suka bude masa nashi.

Kuka sukeyi da dukkan zuciyoyin su.
Kuka ne na kadaici
Kuka ne na firgicin rashin sanin mai gobe tayi musu tanadi idan har yau ta kasance musu a haka

Zuciyarta cike take da abubuwan da ta binne a wannan ranar, abubuwan da suka hadu suka kawo su inda suke yau, tabar Marake rike da hannun Julde, rike da hannun tilon dan da take jin shi kadai ya rage mata a wancen lokacin, yau kuma kasar ce gabaki daya zata bari, rike da hannun Nawfal

Amanarta
Amanar da Bukar yabar mata.

*****

ALHAMDULILLAH!
Finally…
Yau munga karshen dogon waiwayen da Daada tayi
Any guesses? Me zai faru?

Next >>How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Rai Da Kaddara 2 | Babi Na Ashirin Da Uku”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×