Skip to content
Part 21 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

LITTAFI NA BIYU

Abubuwan da zai tuna kafin rasuwar mahaifin shi ba su da yawa. Ya dai san basu taba hada shekara biyu cikakku a waje daya ba kafin zuwan su Marake, kauyen da kaso tamanin cikin dari na mazaunan shi fulani ne, sai dai su suna cikin fulanin da ake ma lakabi da “fulanin tashi.” Bai samu ya tambayi mahaifiyar shi ko rasuwar mahaifin shi ce ta sasu yanke hukuncin zama a Marake da ke karkashin hukumar Dutsi ta jahar Katsina ba, itama nata ajalin ya risketa bayan ciwon cikin kwanaki biyu rak. Rasuwar ta dake shi fiye da ta mahaifin shi, saboda dalilai biyu, yafi shakuwa da ita, kuma yana da hankali fiye da waccen rasuwar.

Datti shine sunan da ya taso yaji kowa na kiran shi, saboda ance ya gaji sunan baban mahaifin shine Auwal. Su biyu ne kawai a wajen mahaifin su da mahaifiyar su, daga shi sai Hammadi, bayan rasuwar su dukan kulawar shi sai ta koma wajen Hammadin da bai sha wahala ba wajen samun matar aure, ko basu duba sanyin halaye irin na Hammadi sun bashi mata ba, zasu duba tarin dukiyar da aka bar musu. Dan ko lokacin da suka zo kauyen Marake ance babu masu yawan dabbobi irin su, tun daga shanu zuwa tumakai da awaki.

Ya na kula da yanda dukiyar da aka bar musu take kara habbaka saboda kulawa da tattali irin na Hammadi, ga gonaki da yake ta siye a hankali da ma’aikatan da yake tarawa a karkashin shi don ya fara zuwa kudu cinikayyar dabbobi, da yake mutum ne shi da baya son tafiye-tafiye, tunda ya samu mutum biyu masu amana saiya bar musu wannan ragamar shi ya zauna yana kula da komai daga nan kauyen. Sai da ya zamana da wahala kayi zaman awa daya a waje batare da kaji wani ya ambaci Hammadi ba, ya kawo ma matasan kauyen cigaba ta hanyar sama musu sana’ar da zasu dogara da kan su, ga alkhairi da yake da shi da son kyauta. Banda kamanni halayen Datti da Hammadi sunyi hannun riga ta yanda zakayi mamaki idan akace maka daga tsatso daya suka fito.

Hammadi na da sanyin hali, Datti na da fadan da wata irin zuciya da Hammadi kan ce.

“Ina tsoron wannan saurin fushin naka Datti, ka dinga sanyaya zuciyar ka. Ba kowanne al’amari bane yake bukatar tashin hankali…”

Sai dai ta kunnen da maganganun Hammadi suka shiga ta dayan suke fita batare da sun samu wajen zama ba. Bayan wannan yana ji da tarin dukiyar da suke da ita, Datti najin duka Marake da kewayenta babu kamar su, saboda haka babu wani wanda ya isa a idanuwan shi, yafi karfin kowa kamar yanda yafi karfin komai. Sunayen ‘yan uwan biyu ya zagaya kauyen Marake da kewayen ta, kowa a cikin su ya shahara da halaye mabanbanta,

“Baka ganin ya kamata Datti yayi aure?”

Matar Hammadi, Abu ta shawarce shi wani dare bayan ya gama cin abinci, murmushi yayi cikin sanyi.

“Ba auren ba Abu, kina tunanin Datti zai iya hakurin zama da mace?”

Yar dariya tayi.

“Waya sani, kila auren ma yasa ya rage zafin kai. Mai hankali za’a duba a hada su.”

Kai Hammadi ya jinjina, ba zancen bane bai zauna mishi ba, tun kafin ta furta yake tunanin a cikin ran shi. Sai dai halayen Datti suna damun shi, matuka, kusan rashin samun rabon su shi da Abu a shekara ta bakwai da auren su yanzun kadai ne abinda yake damun shi fiye da halayen Datti. Bashi da dangin da zasu tsangwame ta kan rashin haihuwa ko su matsa mishi da ya karo aure yagani ko Allah zai bashi rabo ba, sai abokan arziki da suma kai tsaye basu fito mishi sun ce ya kamata ya kara aure ba. Dangin Abu dai suna yi, har yanzun basu gaji da ce mata ta rabu da shi ba ko Allah zai sa itama taga kwanta a duniya, a cewar su ita din ta fito gidan da ake haihuwa, dan su talatin da biyu ne a wajen mahaifin su, su tara a gurin mahaifiyar su, biyu sun rasu.

Tana son mijin ta kamar yanda shima yake son ta, rabuwa da junan sune karshen abinda zasuyi, musamman akan matsala ta haihuwa da suka san Allah ne yake bayarwa, sannan duk tarin mutanen da suke musu surutu a ciki babu wanda zai taimaka da komai wajen kula da abinda zasu haifan. Amman Hammadi baya son ya tauye Abu ko na rana daya.

“Abu idan nine bana haihuwa fa?”

Murmushi tayi,

“Idan kuma nice fa?”

Numfashi mai nauyin gaske Hammadi ya sauke.

“Bana so in tauye ki, idan nine bana haihuwa, na san kina son ki rike yaro ko yarinyar ki.”

Gyara kwanciya tayi yanda zata fuskance shi sosai duk da babu wadataccen haske cikin dakin kasancewar dare ne, kuma sunyi kasa da fitilar kwan da take ci a hankali.

“Kai ma kana so ka rike naka yaron ko yarinyar, idan kaine baka haihuwa zamu raba kaddarar a tare, zan zauna da kai har randa mutuwa zata raba mu, ba zan taba gudun ka akan rashin haihuwa ba, kai nake so, yaran da zamu samu kari ne cikin kyautar samun ka. Amman zan so ka kara aure ko Allah zai baka rabon da zamu dinga kallo, ba sai yaran sun fito daga cikina ba, in dai nakane zan kaunace su Hammadi.”

Rabon da yaji hawaye sun cika idanuwan shi tun da ya kama gawar mahaifiyar shi aka zirata makwancin ta, sai kuma yau da kalaman Abu suka taba wani abu a kasan zuciyar shi, numfashi yake ja yana fitarwa a hankali har sai da ya tabbatar da idan yayi magana muryar shi ba zata fito da raunin da yake jiba tukunna ya iya cewa.

“Abu…”

Yana jira ta amsa sannan ya dora da.

“Ke kadai kin isheni, idan Allah ya bamu rabo zamuyi murna, idan bai bamu ba har abada kin isheni.”

Daga ranar ne kuma suka toshe kunnuwan su daga dukkan wani surutu da akeyi akan rashin haihuwar su, kamar yanda suka fadane, sun ishi junan su, samun yara cikon farin cikine a wajen Abu da Hammadi ba wai farin cikin gabaki dayan shi ba. A gefe daya kuma idanuwa da kunnuwa Hammadi ya bude yana neman yarinyar da zata dace da dan uwan shi, yarinyar da ta fito daga gidan mutunci da tarbiya. Cikin wannan neman ne akayi mishi zancen Dije yar gidan Malam Hamisu. Yaji nauyin samun Malam Hamisu da zancen daga farko saboda rashin tabbas din da yake da shi akan halayen Datti.

Abu ce ta karfafe shi akan zuwan.

“Kowa ka zo nemawa aure a wajena ba zan hanaka ba Hammadi, in dai Dije ce kace ya zo ya ganta, in ta mishi wallahi na baku.”

Malam Hamisu ya fada bayan yaji bukatar Hammadin, karamci ne da Hammadi yake jin har abada ba zai manta da shi ba, kamar yanda Malam Hamisu yake jin shima ba zai manta da karamcin da Hammadin yayi mishi ba, yaran shi hudune suke ci da sha a karkashin Hammadi, kuma hakan bai taba sa girmamawar da take tsakanin su ta raunana ba, mahaifi Hammadi ya dauki Malam Hamisu, yanzun kuma yana fatan zumuncin su ya kara karfi sanadin auren nan. Sai Datti ya sanyaya mishi gwiwa.

“Ko aure zanyi bana son yar gidan Malam Hamisu…ka sanni Hamma ni ba zan hada jiki da bahaushiya ba.”

Numfashi Hammadi ya sauke, ko a gonakibin har tare da Datti suka je zagayen ma’aikatan su, yafi tsangwamar hausawan, haka kawai ya dauki tsana ya dora musu kamar wani yaiwa rawa da yazo a bafullatani.

“Mahaifiyar ta bafullatana ce Datti, kaje ka ganta dan girman Allah karka sa inji kunya.”

Kai Datti ya kada.

“Ni dai da ka shawarce ni kafin kayi musu magana.”

Ya karasa yana kankance idanuwan shi.

“Kayi hakuri, laifina ne da ban fara maka zancen ba, na yarda. Ni dai ko sai daya kaje ka ganta, idan batayi maka ba sai in basu hakuri”

Har cikin ran Datti bai nufi hanyar gidan su Dije da niyyar auren ta ba, yaje ne saboda girman Hammadi da yake gani da kuma kasancewar shi mutum daya daya rage mishi a duniya da baya iya jan magana da shi. Sai dai kaddara ta riga fata, yana dora idanuwan shi akan Dije ya san kaf kauyen Marake bashi da matar aure banda ita, ba zaice ya yarda da wata soyayya ba kamar yanda yake gani a tare da Hammadi da Abu, amman a ranar ba zaman aure kawai ya hango a tsakanin shi da Dije ba, har da yaran da Hammadi bai samu ba. Yana ji a jikin shi sunan gidan su da tsatson su ba zai kare daga kan shi da Hammadi ba, zai samar musu dangin da suka rasa.

Ba Marake bane asalin su, amman kauyen zai zama asalin yaran da jikokin da zasu fito daga su. Ranar ta zame musu fari shi da Dije, ranar kuma ta share doguwar shimfidar da har ta kaisu da auren da labarin shagalin shi ya zagaya har kauyukan ketare, kudine Hammadi ya fitar kamar bai san ciwon su ba, haka dabbobin da ya fitar aka yanka don shagalin biki zakayi mamaki idan kaji cewa bafullatani ne na asali har hausar shi bata fita sosai, saboda kowa yasan fulani, yasan kaunar su ga dabbobin su.

*****

Katanga ce kadai ta raba gidan Hammadi da na Datti, daga farko zaman aure su Datti suka fara kamar babu wanda zaiji kan su, zamane suka fara irin wanda Hammadi da Abu sukeyi, sai shakuwa mai karfi da ta shiga tsakanin Dije da Abu, har tana saka Abu tunanin ashe a fadin garin Marake za’a samu mai sanyin hali irin na mijinta, mai hakuri da kawaici irin na shi. In dai dabi’a ake dubawa Dije bata dace da Datti ba, ko Abu ta dade bata jin maganar Dije saboda kunyar da take da ita, sai a hankali da yake Abu tana da shiga rai.

Suna cikin watanni na hudu da aure Dije ta fara wani irin zazzabi mai zafin gaske, kafin wani lokaci duk wata alama da zata nuna cewa ciki take dauke da shi ta nuna. Murna a wajen Datti ba’a magana, dan ya kasa boyewa ko a fuskar shi, dama can shi ba mai kunya bane ba, shisa inda duk ya zauna zancen cikin Dije da abinda zata haifa yake. Gabaki daya sai kulawar Dijen ta koma wajen Abu da har girki ta dauke mata, nan gidan su Abun take wuni, Datti na fita take shiga sai gabanin Magriba tukunna, abinda duk ta nuna tana son ci sai Abu ta samar mata shi. Karamci irin na Abu yafi karfin kwatance, addu’a kawai Dije takeyi mata itama ta samu nata rabon.

Kwanci tashi babu wahala, cikin Dije na shiga wata na tara gidan su suka nemi da ta koma dan ta haihu a kuma kula da ita tunda haihuwar fari ce, Abu ta so ta musa, ta so abar Dijen a wajenta don har zuciyarta tana jin babu abinda ba zata iyayi mata ba. Amman bata taba haihuwa ba, tana bukatar kulawa a karkashin wanda suka tabayi suka san komai, shisa ta bisu da fatan alkhairi. Sati daya bayan komawarta gida, da safiyar wata alhamis ta tashi da ciwon nakuda. Sanin shakuwar dake tsakanin Dije da Abu yasa aka tashi dan aike yaje ya sanar da Abu da mayafinta a hannu lokacin da ta karasa.

Kuka ta dingayi ganin irin azabar da Dijen take sha, wasa-wasa har azahar. Datti ma yana kofar gida yaron duk da zai shiga koya fito sai yayi zaton labarin haihuwar ne, amman shiru. Nan Hammadi ya same shi suka tsaya suna jiran ikon Allah, wajen la’asar ta haifo yaron da ya kwala kuka yana karade duka gidan, sanda aka fito aka sanar da su Hammadi, Datti baisan lokacin da yayi wani tsalle yana rungume dan uwan shi cike da wani farin ciki da bai taba sanin akwai irin shi a duniya ba.

Ruwan wanka aka dora, fuskar kowa ka kalla a cikin gidan zaka ga farin ciki shimfide, farin cikin da ba’a sauke ruwan wankan da aka dora ba ya sauya. Yaro ya koma, Allah ya karbi kyautar shi, sai gawa aka fito ma da Datti, bai rike dan shi da rai ba. Bai san hawaye sun kwace mishi ba sai da yaji zubowar su, ya kasa daina kallon yaron da babu rabon ya rike shi da rai. Ashe karyane baisan ciwon mutuwa ba sanda ya rasa Inna, yanzun ne yake jin zuciyar shi kamar ta rabu gida biyu a cikin kirjin shi. A ranar alhamis ya binne dan shi na farko a bisa tsari na shari’ar musulunci.

Sai dai ko kadan daga shi har Dije basu hango cewar bashi bane yaro na karshe da zai haska musu farin ciki ya koma da shi ba, ba shi bane karshen dan da zasu binne. A cikin shekaru biyar da auren su haihuwar ta hudu yaran suna komawa. Zuwa yanzun abin ya fara damunta, bata taba furtawa ba amman abin yana damunta fiye da yanda yake damun Datti, bashi yake kwana ya tashi na tsayin watanni tara ba, bakuma shi yake mata nakudar da mace yar uwarta ce kawai zata misalta tarin k’alubalen da yake cikin ta, amman sai yake ganin kamar ya fita damuwa.

Kananun halayen shi tun satin ta na farko a gidan ta fara kula da su, yana daga cikin mutanen da suke da wahalar burgewa, yana da fada, fadan da ta kasa sabawa da shi, da wahala a shafe ranaku biyu baiyi mata akan wani dan abu da bai taka kara ya karya ba har sai zuciyarta ta sosu ta kasa tsaida hawayenta. Sai dai banda kukan ko musayar yawu bata tabayi da shi ba. Fadan shi abune mai saukin dauka a wajen ta, haka saurin fushin shi bashi bane halayyar shi da tafi damun ta, sharrin da yake fita daga bakin shi yafi alkhairin shi yawa.

Labari in zai bata duk na wani mugun abune da ya sami wani, har tana rasa yanda yake samo irin wannan labaran, kamar inya fita baya neman yaji kowanne irin labari sai na wani abu marar dadi daya sami wani a kauyen. Ranakun da zai zo mata da labarin wani ya sami cigaba, ya siyi dabbobi ko ya siyi gona, ko dai wani abu na alkhairi, a muryar shi zaka fara jin rashin jin dadin shi, a idanuwan shi zakaga hassadar da take shimfide. Datti baya so wani ya kai shi, dukiyar da yake da ita bayaso yaji wani ya samu cigaba da kar ya kamo shi, karya ture sunan shi daga layin manyan attajiran kauyen marake.

Har yau basu raba gadon su shi da Hammadi ba, sai dai yanzun kowa akwai sashin dukiyar da yake kula da ita, tunda aka raba, bangaren Datti yanzun babu rabin ma’aikatan da, saboda ko riga kasa da tafi tashi haske zai kore ka, baya so, ko kadan baya son yaga wanda yake kasan shi yana neman fin shi. Har sun gane, kullum cikin boye wani cigaba da suka samu ko da ba’a karkashin Dattin ba suke. Wannan halin na shi shine abinda yafi komai damun Dije, yau ma kamar kullum, sun gama cin abincin dare suna zaune suna cin soyayyar gyadar da aka kawo mata daga gidan su ya kalle ta yana fadin,

“Ance dan gidan Musaji yayi ma wata ciki, tir da irin wannan mugun hali. Kinsan kakan shi ma fa haka naji labari yana haura gidaje lokacin kuruciya”

Kai Dije ta jinjina.

“Babu wanda yafi karfin kaddara…”

Gyadar da yake ci ya kara barawa ya murza yana afawa a bakin shi.

“Babu kaddara a cikin wannan abin Dije, mugun haline kawai, yanzun sai ace miki ina da kaddarar haura gidaje? Dan Allah ki rabani da wannan zancen, Allah dai ya tsine ma zuri’a irin ta Musaji, sun zama bala’i a gari.”

Shiru tayi, ita batayi wani ilimin addini mai zurfi ba, akwai makarantun allo a kauyen marake, duk da basu da yawa. Ta samu na sallah, ta dai san kaddara da girmanta, ta kuma fahimci kowa da irin tashi, ta su Hammadi da Abu rashin haihuwa ce, ta su ita da Dattin yaran ne basa zama, shisa tasan ta Musaji itace yara marassa jin magana, ta ma yan gidan farin sani tunda unguwar su daya. Sai dai shi Musajin mutumin kirki ne, haka iyalan shi, dan duk juma’a ya kan bada sadakar farar alawa, itama ta sha zuwa ta karba. Ko da taji ta girmi zuwan haka zai ba cikin yaran gidan su da kanje karba su kawo mata.

Idan kaji wani mugun abu ya samu wani nemar mishi sauki kakeyi kai kuma ka nemi tsari, haka taji mahaifiyar ta nayi. Amman Datti bai san wannan ba, ya daifi gane ya bisu da tsinuwa saboda shi yana jin har ran shi ya wuce irin wannan ta same shi. Suma din sun so ne shisa hakan ta faru da su. Karshe ma mikewa tayi saboda gyadar da taci taji tana daga mata hankali, ko bayan ta kwanta haka taita fama da tashin zuciya sai da tayi amai ta samu lafiya. Ta alakanta hakan da dattin ciki, ko kadan bata kawo yiwuwar tana da juna biyu ba, tunda wannan karin ta dade bata samu ba.

A zuciyarta sai da ta dinga jin tsoro ko iya rabonta ne ta binne. Har kuka tayi da ta gane tabbas tana dauke da wani cikin ne, cikin da kowa ya bude baki bayan anga fitowar shi zaice mata.

“Dije Allah ya rabaki da dakon gawa.”

Takan amsa da amin a cikin ranta, amman zuciyarta ta gama karaya, Abu ce take tausarta da kalamai masu sanyi. Ranar idi nakuda ta kamata, nakuda mai sauki ba kamar ta baya ba, cikin kasa da awa biyu ta haifo yaron ta namiji. Yaron da taki karbar shi saboda tana ganin kamar shima ba zai rayu ba, har akayi mishi wanka, itama Abu ta taimaka mata tayi ta fito sannan ta mika mata shi.

“Ki karbi danki Dije, ki rike danki a hannun ki yaji dumin ki.”

Karbar shi tayi zuciyarta cike da tsoro, tana kallon dogon hancin da zakaci karo da jarirai hamsin baka samu irin shi ba, gashi da wani irin hasken fata na ban mamaki.

“Anya wannan zai zauna kuwa?”

Zancen da taso yi a zuciyarta ya subuce mata, muryarta na fitowa a raunane. Dariyar da taji Abu tayi ta sata gane a fili tayi maganar.

“Zai zauna da yardar Allah.”

Kyawun shine ta ga har yayi yawa shisa take tunanin kamar ba mai zama bane ba. Ta kuma ga wannan tsoron a cikin idanuwan Datti kamar ta kalli mudubi, yanda batayi baccin kirkin ba haka Datti, gani yake sakon farko da zai riske shi da safe shine cewar yaron ya koma. Yini ya dinga wucewa yana hada dararen da suke wayewa cikin safiya har sati ya zagayo yaro yana nan. Shanuwa Datti yasa aka yanka saboda murna. Yaro yaci suna Isiya wanda shine asalin sunan Hammadi, har kuka sai da yayi saboda jin dadin karamcin da dan uwan na shi yayi mishi, suka kuma sakaya da kiran shi Julde kasancewar an haife shi ranar idi.

Sun rike shi da tunanin zai zama cikon farin cikin su
A cikin su babu wanda ya hango cewar Julde ne kaddarar su.

*****

Idan littafi na yayi muku dadi, ku taimakeni ta hanyar bude account da Bakandamiya don hakanne kadai zai baku damar yin like na shafin duk da zan saka da kuma yin comment ko da na fatan alkhairi ne. Hakan zaisa website din Bakandamiya su biyani.

<< Rai Da Kaddara 20Rai Da Kaddara 22 >>

6 thoughts on “Rai Da Kaddara 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.