In da wani yace kafafuwan shi zasu sake daukar shi zuwa kofar gidan su Dije zai karyata. Ya hakura da ita, shine abinda ya gayama zuciyar shi daga lokacin da Allah ya nuna musu cewar basu isa su cire cikin da yake jikinta ba. Tun tana mishi aiken yara a boye har itama ta hakura. A wajen Hammadi yaji maganar haihuwar ta."Dije ta sauka lafiya, ta samu da namiji."Kalaman suka bi ta cikin kunnen shi suna sokar wani abu a kirjin shi da yaji zafin shi ya gauraye ko ina na jikin shi, yawun daya hadiya mai daci. . .
Mahakurci mawadaci