Skip to content
Part 27 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Dalilan da suka hanata yi ma maza kudin goro akan cewa basu da adalci, zuciyoyin da suke kirjin su bangaren tausayi na wasu da yawa a mace yake kadan ne, mahaifinta baya cikin wannan dalilan, saboda shima ya kalle ta ya ce.

“Ki dauki Bukar ki mayar da shi gidan mahaifin shi Dije, shine kwanciyar hankalin ki, shine kuma rufin asirin shi.”

Kasa cewa komai tayi, ta dai daga ido, ta kuma kalli Baba, ta kalle shi da idanuwan da bata taba kallon shi da su ba, ta kalle shi a ranar ba’a matsayin mahaifinta ba, zuciya ta uwa tasa ta kalle shi ta kuma saka shi a jerin mutane marassa tausayi, mutanen da suka kasa duba halin tagayyarar da rayuwar Bukar zata shiga idan ta dauke shi ta mayar gidan Baabuga. Kowa ya manta yanda da wahala ka fita baka ci karo da daya a cikin yaran Baabuga sun gantali akan hanya ba, yar makarantar allon da ake kokarin saka yara a kauyen ma su basa cikin wannan tsarin.

A cikin dalilan ta nakin yiwa maza kudin goro Hammadi yana cikin su, Hammadi daya fita daban da sauran mazan da rayuwa ta hada hanyarta da su. Saboda har cikin zuciyarta tana da yakinin Hammadi ba zaiki rikema Abu dan da ta samu batare da shi ba, ko da yafi daya kuwa.

“Ba zan rike dan Baabuga ba, ba zan rike ba wallahi. Karki fara kawo mun shi cikin gidana, idan ba zaki mayar masa da shi ba kisan inda zaki ajiye shi, amman ba cikin gidana ba…”

Sune kalaman Datti, kalaman da baiyi kokarin tausasawa ba, iya gaskiyar shi ce ya fada mata tasani, amman kai tsaye haka? Ba ana sakaya wata gaskiyar ba? Ana mata lullubi da bargo mai taushi yanda in aka jefa dukanta zai isa da sauki.

“Dan Allah… Kar ka duba Baabuga, karka duba Bukar din ma, ka dubani, ka duba halin da zuciyata take ciki…karkayi saurin yanke hukunci haka, Bukar ba mai rikici bane ba, zai zauna cikin gidan nan kamar baya nan.”

Tayi maganar cike da roko, zuciyarta a cunkushe, idanuwanta a cike da hawayen da tun ranar da aka fara mata magana kan ta mayar da Bukar gidan mahaifin shi suka soma zuba, ba su kuma yanke mata ba.

“Sai dai zan gan shi…idan na shigo gidana zan gan shi, zai tuna mun daren da kikace mun shi kadaine daren da kika rabamun kanki da Baabuga… Daren dana tsana, Baabuga dana tsana Dije, abinda daren ya haifar da bana son ko ji balle in tashi in gani a duk rana… Dan Allah… Dan Allah karki sake mun maganar nan…”

Yanda ya karasa maganar cikin roko yasa ta mike tabar masa wajen a wancen lokacin. Ta kuma turo kofar dakinta harta saka sakata abinda bata tabayi ba. Babu kalar abinda bata saka a cikin ranta ba, warwarewar dai ce ta gagara. Musamman da taga da gaske Datti yake ba zai rike mata Bukar din ta ba.

“Zanma Hamma magana in za’a kai masa dabbobi a hadamun da guda daya, ya bani kudin in rike yarona da su.”

Lomar tuwon da Datti yakai bakin shi ya tauna, yanajin ta wuce ta cikin makoshin shi, zafin na ratsawa ta duk lokon da tuwon ya wuce kafin ya saukar masa a ciki da wani irin nauyi, kallon ta yayi, babu alamar wasa a fuskarta, asalima yanda ta hade girar sama da ta kasa ya nuna cewa ba shawara tazo suyi ba, gaya masa takeyi, kawo mata wani zancen kuma zaiyi dai-dai da neman sabuwar rigimar da bai shirya ma ba. Bai taba sanin Dije ta iya rigima ba, ko zata iya kallen idanuwan shi ta mayar masa da magana haka sai akan Bukar din nan.

Bukar da ya tsana har kasan ran shi, Bukar da ko sama da kasa zata hade waje daya ba zai zauna masa a gida ba.

“Madalla…”

Ya amsa yana cigaba da cin tuwon shi, ta kasan idanuwa yaga ta mike sannan ya daga kai ya bita da kallo. Daki ta shige ta turo tana saka sakata. Murmushi ya tsinci kan shi dayi, in dai akan maganar Bukar ne ba zai taba biye mata ba, duk da fushin da ta dauka bashi kadai ya shafa ba, ya kula harda Julde, hanya daya da tasan tana da ita da zata iya bakanta masa rai, yanda duk taso ba zai bari hakan ya faru ba. Shisa idan ya dawo saiya biya ta gidan Hammadi ya ganshi ya dawo, can yake barin shi yanzun, saiya dauko shi ya dawo da shine zatayi abinda zaisa dole ya biye mata.

Da safe ma saida ya gama shiri zai fita, ya shiga dakinta don yayi mata sallamar da bata ko daga kai ta kalle shi ba, ya juya ya tsinkayo muryarta.

“Zanje gida.”

Labulen ya saki bai amsata ba, yasan me yaji lokacin daya rabu da ita, kuskure ne da yayi sau daya, kuskure ne da zai karasa sauran rayuwar shi yana kokarin ganin bai maimaita ba, shisa ya fice batare da yace mata komai ba kafin wata zuciyar tace masa ya nuna mata yana da iko a kanta, ya hanata yaga abinda zai faru.

“Sai mutane su dauka ni da Abu bama fada, babu wani zama da za’ace ba’a samun sabani Datti, yau da gobe tafi karfin wasa. A zaman aure sai ana kauda kai, sai kuma ana hakuri, idan kaga yayi karqo to dole akwai wanda akafi cutama, dole akwai wanda akafi tauyewa, dole daya na hakuri da daya fiye da yanda dayan yakeyi, bansan me yasa tsarin ya kasance haka ba, amman hakanne, kuma muma haka za mu cigaba da gudanar da zamantakewar…gata nan, zama ya sake hadaku a karo na biyu, a naku zaman ko ba’a fada ba ansan wa yafi hakuri da wani, kaima saika kai zuciyarka nesa a lokuttan da ka kure hakurin ta.”

Zantukan Hammadi ya dauka anan inda yayi masa su yabar su kamar ko da yaushe idan ya samu sabani da wani, Hammadi ya tsaya yana masa nasiha akan zamantakewa da mutane da kuma amfanin hakuri harma da yawan kauda kai. Saboda yasan baida wannan zuciyar, hakuri ba halin shi bane ba. Sai a yan kwanakin nan da Dije take saka kara tana zungurin duk wani abu da tasan zai hassala zuciyar shi amman ya kauda kai, duk da yana saukewa akan duk wanda ya gifta masa a waje. Hakan ne ma yasa Hammadi yi masa Magana.

“Da bacin ranka kake zuwa Datti, idan zaka dinga hucewa akan wanda basu san hawa ba basu san sauka ba, ka daina zuwa har saika warware matsalar ka da matar ka.”

Numfasawa ya yi.

“Saina rike mata yaro, akan naki rike mata yaro ne take ta tashin hankali.”

Ya fadama Hammadi din tunda boyewar bata da amfani.

“Bukar?”

Hammadi ya tambaya, kai ya daga masa.

“To mene ne dan ka rike shi? Taimaka mata zakayi, kuma shima yaron inka duba gidan Baabuga zaka taimaka masa.”

Kai yake girgizawa tunda Hammadi ya fara Magana.

“Wallahi ba zan rike wannan dan iskan yaron ba.”

Kallon shi Hammadi ya yi yana kada kai kawai hadi da fadin.

“Allah ya rufa asiri.”

Tunda yasan hali, abinda duk zai dora bayan wannan kamar zai kara tunzura Dattin ne. Akwai lokuttan da shiru shine mafi alkhairi, komin yanda kake ganin kusancin ka da mutum kuwa. Hidimar shi ta ranar Hammadi ya cigaba da gudanarwa, yana jin masifa da tijarar da Datti yake yiwa mutane. A gefe daya Dije shiryawa tayi, ko ta gidan Abu bata biya ba, saboda itama ta kara mata takaicin da take ciki da kafewar da. tayi akan Hammadi ya karo aure. Tana zaune da mijinta lafiya, bai daga hankalin shi akan halin rashin haihuwar su ba, ita ta daga nata.

Ko tsoron wata tazo ta haihu da Hammadi ta koreta daga gidan batayi. Idan akayi magana sai tayi murmushi, murmushin nan da Dije take jin zafin shi har ranta, kamar Abu tana son fada musu tasan wani abu da su basu sani ba, tana hangen abinda kome zasu taka ba zasu taba ganin shi ba. Har ta shiga gidan su zuciyarta a cunkushe take, ta daiji dadin ganin Baba bai fita ba, a cewar Innarta yayi ciwon ciki da dare, saiya tashi bayajin karfin jikin shi, shisa da ta same shi bayan sun gaisa ya jiki ta fara yi masa ya amsa sannan ta dora da,

“Akan Bukar ne daman Baba…ni ba zan mayar da shi gidan Baabuga ba, zanma Hamma magana yau akama dabbata a siyar sai in kawo kudin nan a ajiye a dinga masa hidima a cikin su kafin muga abinda Allah zaiyi.”

Numfashin da Baba ya sauke na korar shirun daya biyo bayan maganar da ta yi.

“Dije kina tunanin ba nida abinda zan rike Bukar da shi ne? Shisa nace ki mayar da shi gidan mahaifin shi?”

Kanta ta sake saddawa kasa saboda bata so yaga hawayen da suke cike da idanuwanta.

“Na ce ki mayar dashi ne badan ba zan iya rike shi ba, sai dan shine abinda ya kamata. Iya gatan da za’ayi ma rayuwar shi kenan.”

Mikewa tayi, hawayenta na zuba, Baba bai hanata ba, ko da ya hanata bata jin zata iya tsayawa saboda ko ganin hanya batayi sosai, hawaye sun mata duhu bayan wanda ya lullube zuciyarta. Bata bi takan Innar A’i dake mata magana ba ta sa kai tana ficewa daga gidan gabaki daya, bata ganin komai sai Bukar da ta baro kwance dakin Innarta yana bacci, yanzun sai taga kamar yana baccin ne a nutse sanin ba zata taba barin komai ya same shi ba.  Amman ina, duk wani kokari da takeyi na ganin ta kare shin nema yake ya subuce mata.

Gidan Hammadi ta shiga, kuka na kwace mata tana hada ido da Abu.

“Adda ba zan iya gani sun maida shi gidan nan ba, wallahi zuciyata ba zata dauka ba…baki ganshi yau yana kwance ba, kamar duka basu duba kankantar Bukar, mutuwa zaiyi a gidan Baabuga, mutuwa zaiyi a irin wannan rayuwar da sukeyi.”

Riketa Abu tayi tana jin zuciyarta na karyewa, maza akwai ikirarin soyayyar ‘ya’ya, a baki zaka dinga jin ikon su, a wajen jama’a zakaji alfaharin da sukeyi, musamman idan wannan yaron ya taka wani mataki ne na nasara.

“Dana”

Haka zaka ji su.

“Yata ce, yar waje na ce.”

Bata dandani zafi na haihuwa ba, amman a tsakanin laulayi, a cikin fitowar rana da faduwarta, tana tare da Dije, lokutta mabanbanta, hannunta yana rike dana Dije a yayin nakuda, yaran da basu ma zauna ba, a haihuwar Dije ta uku, a irin wannan wahalar da taga ta sha saida wani sashi na zuciyar ta ya numfasa cikin jin dadin yanda jikinta bai taba dandana irin wannan wahalar ba. Sai lokaci daya namiji ya kalli mace yace mata ba zai rike mata danta ba saboda ba nashi bane ba, ba zai rike ba saboda baiga wani dalili da zaisa ya rike ba. Tunda suka fara wannan maganar Abu take jin kamar ta kama Datti ta girgiza shi.

“Laulayin da ta sha kadai dalili ne, nakudar da tayi kadai dalili ce.”

Haka take so ta fada masa, idan bashida halin rikewa Bukar zata iya fahimta, duk da har abada ba zata fahimci kowanne irin dalili da zai raba uwa da yaranta ba, idan tace kowanne dalili tana nufin kowanne iri. Me yasa namiji zai auro mace kuma ta rike masa nashi yaran? Me yasa? Sai ace shi ba zai rike mata nata ba saboda basu fito daga jikin shi ba, amman shi ta rike nashi da basu fito daga nata jikin ba.

“Nayi magana da Inna, tace ko da za’a maida Bukar din ba yanzun ba, yayi kankanta tunda ko shekaru biyu bai cika ba, a barshi ya kara ko da shekara ce nan gaba… Kafin nan mun samu mafita da yardar Allah.”

Abu ta fadi a tausashe, amman kukan da Dije takeyi yaki tsayawa, saboda jikinta ya fara sanyi, zuciyarta ta fara karaya, ji takeyi kamar an dauki Bukar an mikawa Baabuga ne, abinda zaiyi dai-dai da tagayyararsu gabaki daya. Tayi kuka har zazzabi ya rufeta, da kyar Abu ta samu tayi shiru, anan gidan tayi azahar, sukaci abinci tare da Abun ta kuma kwanta ana. Abu tace mata Hammadi da Julde ya fita. Sai juyi takeyi zuciyar kamar an watsa mata ruwan kankara, amman kuma zafi take mata maimakon sanyi. A haka baccin wahala ya dauketa cike da mafarkin Bukar da rayuwar da zai tsinci kanshi a ciki a gidan Baabuga.

*****

Fada idan ka hango rashin nasara a cikin shi babu wani amfani, yanda ranta yake a bace haka take so na Datti ya kasance, amman yaki bata wannan damar, hanyar duk da zatabi don ganin ta bata masa rai ya toshe, daya biye mata, ko sau daya ne ya biye mata su fadama juna maganganu, ta fada mishi tarin abinda yake binne a cikin zuciyarta, ko sau daya ta fada masa bashi da tausayi, bashida adalci, ba kuma ya sonta tunda baya son nata, ko zata samu sassauci. Ganin yanda take wuni da kuncin zuciya, kuka ne abokin hirarta duk dare kafin bacci ya dauketa, yasa ta tsahirta ma kanta, ta dauki shawarar Abu na ta mayar da komai bakomai ba, tunda tana da sauran lokaci kafin a mayar da Bukar din.

Ita ta zabi raba shimfida da Datti, ita kuma ta zabi komawa da kanta, baice mata komai ba. Riketa yayi a jikin shi yana jin kukan daya kwace mata, kukan da yasan akan Bukar ne shisa zuciyar shi bata motsa ba, kamar yanda ya fadama Hammadi ne, ba zai rike Bukar ba, kome zai faru ba zai rike yaron da ko sunan shi baya so ya hau harshen shi ba. Abinda duk Dije take tunanin zatayi don ya sama mata saukin fahimtar hakan zai barta tayi, tsayin lokacin duk da zata dauka zai bata shi, zai koma gefe ya jirata har ta gama ta dawo wajen shi kamar yanda tayi yanzun.

Duk da har aka kwana biyu ya kasa sakin jikin shi, gani yake kamar zata koma Dijen nan da bai sani ba, Dijen nan da bata shakkar neman rigima da shi, Dijen da bai taba gani ba sai wannan karin. Amman shiru, hidima taci gaba dayi tana gudanar da rayuwarta kamar babu wani abu a ranta, har saida ya saki jikin shi. Rayuwa suka cigaba dayi yanda suka saba. A satin daya kama na bikin Hammadi da Pendo ne Dije ta tabbatar da cikine a jikinta, ciki me saukin laulayi. Da ta fadama Datti yayi murna ba kadan ba.

“Karka fadama Hamma dan Allah, saboda Adda…zatayi murna na sani, amman zai zama kamar muna tuna mata abinda ba zata samu bane, ga maganar bikin nan da dalilin shi.”

Kallon ta Datti ya yi.

“Idan ban fada yanzun ba, zai fito kowa ya gani. Meye amfanin kin fadin?”

Dan murmushi ta yi.

“Nasani, abari sai ya fito din sun gani ni dai.”

Numfashi yaja, numfashin nan daya kanyi idan magana bata gama zauna masa ba, a wajen shi maganar cikinta abin farin cikine da yake son fadama duk wani da zai saurara batare da kunya ba, baisan me yasa take son boyewa ba. Idan ya samu ai kamar Hammadi ne ya samu, haka Hammadin ya fada da bakin shi.

“Dan Allah”

Ta sake roko, ya dauki wasu dakika yana juya maganar kafin ya daga mata kai a hankali. Ashe kuwa gara ma da tace masa subar maganar a tsakanin su, dan cikin ba mai zama bane ba, a cikin watan shi na uku ta wayi gari da zazzabi mai zafi, zazzabin da bata kwana da cikin jikinta ba, amman ta sake kwana ta tashi da shi na tsayin kwanaki hudu, saboda barin ya jigatata. Batasan ko Abu ta gane ba, ta dai dafo mata zuma da kayan kanshi a ciki, ta bata a dan kwano tace tayi kokarin shanyewa da duminta. Sai da tayi mata hakan na kwana uku, cikin ikon Allah sai taji dadi, har karfin jikinta ta samu, kamar hadin zumar ya wanko duk wani sauran ciwo da take tare da shi.

Har kasan ranta tausayin Abu ne fal, yanda take kokarin ganin ta saukakama kowa komai duk da rayuwarta da take a hargitse, hargitsin da bata zubar da digon hawaye ko daya a gaban Dije ba, itace ma tayi kuka ranar da dangin Pendo suka tafi da ita saboda irin maganganun da suka dinga yi da habaici saboda ta samu rabo da Hammadi.

“Allah daya bata bai manta dani ba Dije…idan rashin haihuwar shine alkhairi na akan haihuwar fa? Naji dadi da kasa bata rufe mun ido ba sai da naga rabon Hammadi… Hakan ma ya isheni.”

Ta fadi da wani murmushi a fuskarta daya kara karyama Dije zuciya. Sai dai wauta ta tunani irin na dan Adam da kan shafe giftawar mutuwa a cikin tsarin al’amura na yau da kullum, duk kuwa da sanin cewa zata iya sada zumuncin ta da takanyi batare da sanarwa ba. Ko gudun da watannin sukayi baisa sun kawo komai a ransu ba, samu da rashin da ya samu Abu, ya same su dukkan su, saboda Dije tayi kuka fiye da Abun, mutuwar saita tuna mata da zafin da ta dandana itama, komai na dawo mata kamar ranar ne ya faru. Wannan ma baisa sun hango mutuwar Pendo ba.

Pendo da jinin Dije bai hadu da nata ba, Pendo da ko da mutuwarta ta daki Dijen fiye da yanda ta zata baisa taji ta sota ba, ta kasa goge laifukan dangin Pendo, kalar rashin darajar da suka yima Abu wani abune da ko ita kadai ta tuna sai wani daci ya mamaye zuciyarta. Da sun hango rayuwar Pendo ba mai tsayi bace kamar yanda suka dauka da sun sassauta burin su. Cikin da suke ta hauka akan shi, rabon da suke gani zai zama tsanin da zai mallakama Pendo duk wata ragama ta rayuwar Hammadi ga shi nan, ga ‘yar nan, amman babu Pendo. Abun da suke ki dole idan lokaci yayi Hammadi ya karbi ‘yar shi rikonta a hannun Abu zai dawo.

Tun kwana biyu da rasuwar Dije bata jin dadin jikinta, da kyar ta iya zuwa sadakar uku, har Datti na mata fada kan cewa kukan da tayi ne yasa mata rashin lafiya. Sai daga baya suka gane laulayi ne, wani irin laulayi da bata tabayin irin shi ba, ko ruwa tasha saiya dawo. Datti na gama shiryawa yake zuwa ya kira Abu, sai yaga ta dagata, ta kamata sun tafi gidanta sannan zai rufe gidan ya fita, anan take wuni kwance, saiya dawo da dare zai biya ya dauketa, ranaku dai-dai ne Julde yake kwana a wajensu tunda ta samu cikin, shima idan Datti ne ya dauko shi, saboda ita bata da karfin kula da kanta ma balle kuma Julden.

Kulawar su kacokan hannun Abu ta koma da takeyinta kamar bata san ciwon jikinta ba. Tasan hakan gidansu suka gani shisa suka kasa samun zuciyar cewa zasu dauketa a yanayin wahalar da take sha. Wannan damar kuma Baba ya samu ya dauki Bukar ya mayar gidan Baabuga, a cewar shi lokaci yayi, idan ma ba’a mayar da shi yanzun din ba gaba za’ayi. Haukane kawai Dije batayi ba, saboda Baba ya zabi lokacin daya dace, lokacin da ba zata iya tabukama kanta komai ba balle harta iya yin wani abu akan Bukar.

Damuwar ce ta kara mata ciwo na daban, ga rashin cin abinci, saiya zamana har cikin ya shiga wata na biyar bata da karfin kirki, yawan aman ya tsaya, amman kukanta bai tsaya ba, damuwar da take ciki banda karuwa babu abinda takeyi. Hankalinta da duk na wani makusancita ba’a kwance yake ba.

“Ka dubo mun yarona Datti, dan Allah ka dubomun halin da yake ciki.”

Ta roka wani dare da take jin numfashinta yana barazanar tsayawa, kukan da takeyi kamar zata shide yasa Datti cewa.

“Zan biya in dubashi da safe…zan duba shi Dije, ki daina kukan nan kinga baki da lafiyar kirki.”

Tunda yake bai taba ganin irin wannan lamarin ba, wacce irin kaunace take yiwa Bukar din haka? Wacce irin kaunace da ta danne wadda takeyiwa kanta, ta danne wadda take yi musu, akan Bukar shi kadai tana kokarin halaka kanta da abinda yake cikinta, shi da Julde ta jefa su cikin wani hali. Babu abinda hakan yayi banda kara masa tsanar Bukar, tsanar duk wani abu daya dangance shi. Ko kadan bai niyyar zuwa ya duba mata Bukar ba, amman saiya tsinci kanshi a kofar gidan Baabuga da safen daya fita, harma da aikawa akayi masa sallama da Baabuga da bayan sun gaisa ya rasa ta inda zai fara tambayar shi Bukar.

“Dije tace in duba mata ya Bukar?”

Ya fadi yanajin wani daci a ranshi, murmushi Baabuga ya yi, har ga Allah in zai fadi gaskiya bai san ya Bukar din yake ba, yara ne a gidan shi sun fi ashirin, wasu ma rabon daya saka su a idon shi anfi sati, sanda zai fita ba tsayawa yake ya duba su daya bayan daya ba, haka idan ya dawo. Da daddare Baban Dije ya same shi ya mika masa Bukar, bawai ya manta sun sami rabo da Dije bane ba, koba komai bai taba hada shimfida da matar da ta kasa gogewa a tunanin shi irinta ba. Bai dai kawo ma ranshi zasu mayar masa da Bukar ba sanin cewa suna da halin da zasu rike shi. Ya karba babu wani musu, yana mamakin kyawun yaron da irin sutturar da aka hado shi da ita, tun kuma da yaje ya mika ma uwargidan shi, bai sake bi takan shi ba.

“Yana lafiya”

Ya amsa yana kallon Datti daya daga kai, harya juya sai kuma ya dawo. Hannu yasa a aljihu yana zaro kudi, ya diba ya mika ma Baabuga

“A sai masa dan wani abu shida sauran yan uwan shi.”

Hannu Baabuga yasa ya karbi kudin dan yana da bukatar su. Yayi ma Datti godiya. Ko daya koma gida da dare, akan tabarma ya samu Dije zaune ta saka fitilar kwai a gaba tana kallo kamar ta samu majigi, tana jin sallamar shi bata ma amsa ba ta ce,

“Ya Bukar din? Ka gan shi?”

Karasawa ya yi ya zauna a gefenta, yana kallon yanda kasusuwa suka fito a fuskarta saboda ramar da tayi, da zai iya da yayi mata karya ko dan ta samu saukin da yaga tana nema.

“Bangan shi ba, amman Baabuga ya ce mun yana lafiya. Na kuma bashi kudi…”

Kai ta daga tana kai hannu ta share hawayen da ke shirin zubo mata.

“Ya ce yana lafiya.”

Ya sake jaddadawa, kan dai ta kara daga masa, zuciyarta na kuna, da bata zauna gidan Baabuga taga rayuwar da akeyi ba da kila sai hankalinta yafi kwanciya. Ko nama Datti ta siyo ta kai bakinta sai Bukar ya fado mata, tasan tunda aka kaishi gidan baiji dandanon nama a bakin shi ba, gidan Baabuga yayi kama da gidajen da ba’a ganin nama da wani abu mai galihu sai shekara-shekara, a lokacin bukukuwa na sallah. Iya abinci aka tsaya Bukar yana cikin garari, balle suttura da wajen kwanciya, ga rashin kulawar da tasan yana ciki.

Shisa babu wani horo da namiji zai yima mace daya wuce ya saketa ya kuma rabata da yaranta, saboda gabaki daya nutsuwarta ya rabata da ita, tunanin halin da suke ciki ba zai taba barinta bacci me kyau ba. Dije ta daina kokarin ganin wani ya fahimce ta akan maganar Bukar, tana dai jin kamar karshen duniyarta ne ya zo. Kamar tana samun karfin bude idonta ne da duk safiya don ta haifi abinda yake cikinta kafin ta rufe shi na har abada. Har Abu daina kokarin yi mata maganar Bukar tayi saboda,

“Hmmm…”

Kawai take iya cewa sai hawaye. A haka randa cikinta ya shiga wata tara da kwana biyu ta fara nakuda a tsai-tsaye, nakudar da bata taho mata gadan-gadan ba saida ta kwana hudu tana wahala. Ranar ma wuni tayi ta sake kwana, sai da kowa ya fara karaya da lamarin, Hammadi da yake da raunin zuciya sai da yayi kuka duk da bai ganta ba, Abu ya gani da yanda tayi zuru-zuru saboda tashin hankali, idanuwanta duk sun dashe alamar yawan kukan da ta sha, suna hada ido ta girgiza masa kai alamar har lokacin babu wani labari.

Kukan jinjiri ya fara sanar musu da ta sauka, saida Datti ya tsugunna yana wani irin mayar da numfashi, da gudun Abu ta fito take fada musu mace ce aka samu, an kuma fito musu da ita bayan an mata wanka, a karo na farko da Datti yayima Hammadi kara yana nuna ma Abu alamar da ta bashi ita ya fara dauka. Yaji dadi sosai, murnar shi bata boyu akan fuskar shi ba, daya mika ma Datti ita idanuwa ya kura mata yana kallo, Julde yayi kyau, har aka dinga maganar a cikin kauyen, amman baiyi kyau irin na yarinyar da take rike a hannun shi ba. Har saida Datti ya kalli Hammadi adan tsorace yana fadin,

“Kaganta Hamma.”

Saboda ya tabbatar bashi kadai yake ganinta ba, kai Hammadi ya daga masa,

“Ance ba’a gane kammanin jinjiri. Amman tana kama da Inna, fuskar Inna nake gani a tata.”

Saida ya fada Datti ya gani, yaga kamannin, yaga kyawun Innar shi da ba zai manta ba, kyawunta da yake zama abin magana akai duk inda zasu shiga.

“Shisa zata ci sunan Inna.”

Datti ya fadi, yana kuma cikawa, yarinya taci suna Karima.

“Muna da wani tsayayyen gari kuwa? To in dai za’a tambayeni zan iya cewa Yelwa.”

Inna ta taba bashi amsa, ba zai manta ba farko-farkon dawowar su Marake ne

“Ina ne Yelwa?”

Dariya Innar tayi

“Wani kauye ne a karkashin Shendam ta jihar Plateau, Innata da Babana anan suka zauna suka haifeni, shine gari na…”

Akwai sunaye da yawa da zasu iya yima Karima alkunya da shi, saiya zabi Yelwa.

*****
Idan labari na yana muku dadi, ku nuna mun ta hanyar yin like da kuma comment. Ta hakane kawai Bakandamiya zasu biyani.

Nagode.

<< Rai Da Kaddara 26Rai Da Kaddara 28 >>

2 thoughts on “Rai Da Kaddara 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.