Skip to content
Part 28 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

“Ki rage fita da yarinyar nan saboda bakin mutane da kuma miyagu, idan bikine ko suna ki barta wajen Abu, idan tare zaku je ki biyo ki kawota gida.”

Shine abinda Innar A’i tace mata lokacin da taje yawon arba’in ta kuma kwance goyon Yelwa tana mika ma Innar A’i da ta karbeta tana kura mata idanuwa. Ko ita haka take saka Yelwa a gaba tana kallo, tana jinjina ma ikon Allah da ya fitar da halitta kyakkyawa kamar Yelwa daga jikinta. Julde na da haske, Yelwa ma haka, amman farin yarinyar wani irin sirki gare shi da zakayi zaton ta hada jini da buzayen kasar Agadez.

“Mahaifiyar babana buzuwa ce.”

Datti yace mata randa tayi maganar, sai dai da alamar wasa a muryar shi da kuma dariyar da yayi bayan maganar, sai ta kasa tantance tsokanarta yakeyi ko kuma hakikanin gaskiya yake fada mata, ga kan Yelwa ya cika da gashi zaka rantse basuyi askin sunan da Abu ta ce.

“Wanzamin nan bashida tausayi ko kadan, jibi yanda ya sude kan yarinyar nan kamar sabuwar kwarya dan Allah.”

Har suka dinga mata dariya saboda tayita mitar dake nuna alamun da an biye mata ba za’ayi askin ba.

“Allah ya kare rayuwarki daga mugun baki.”

Innar A’i ta fadi tana sake juya Yelwa, watakila da a wani wajen Dije ta haihu ba gida ba, zatace ko sunyo musaya ne sun dauko yar data hada iri da larabawa, amman a gabansu Yelwa ta fado bayan doguwar nakudar da mahaifiyarta tasha.

“Kyauta, kyautar Allah ce kawai.”

Ta gasgata zantukan Abu, Abu da bata iya boye tsantsar soyayyar da take ma Dije da ahalinta a gaban kowa. Dije kuwa dariya takanyi idan suna irin maganganun nan, to saboda gudun bakin mutane kuma sai ace ba zata fita da Yelwa ba, miyagun da ake cewa har tsuntsaye suna zama su dira gidan da suke so, su lashe kurwar wanda tsautsayi ya giftawa, boyon Yelwa na me zatayi musu? Tunda dai zasu iya rikida su shigo gidan, ko ma ba’a tsuntsaye ba, sun kawo talla har cikin gida, kuma ba ganewa zatayi ba. Da zuciyarta daya take fita, abinda zai faru tasan ba zasu tsallake masa ba.

Tayi niyyar sai tayi isha’i zata wuce gida, shisa ta kara mike kafa, bata hango Baba zai rushe mata wannan shirin ba, sai da yammaci daya shigo gidan ya ganta, yayi tsaye saida yaga ta mike ta goya Yelwa, tayi ma su Innarta da Innar A’i da yake ma fadan suna kallon yammaci yayi har haka suka bar Dijen ta sake mike kafafuwa maimakon su korata gida. Harta kai soron gidan kafin ta karasa ficewa tana jiyo shi bai bar fadan ba, murmushi ta danyi tana kama hanyar da zata kaita gidanta. Kafin tunanin Bukar kamar ko da yaushe ya diro mata yana danne komai.

Idan tace komai harda kafafuwanta da tunanin ya jagoranta har kofar gidan Baabuga da bata farga ba sai da tasa kai ciki da sallamarta. Hararar da uwargidan shi Nana ta watsa mata nasa wani abu ya tsirga mata, saboda har ranta bata fito daga gida da tunanin kafafuwanta zasu daukota su kawo gidan Baabuga ba, zuciyarta ce, da kuma son ganin Bukar da take yi.

“Ina wuni.”

Ta gaishe da ita cikin harshen hausar da tasan tana ji, amman sai ta tsaya da kullin gyadar da takeyi tana kallonta kamar bata tabajin yaren da tayi magana da shi ba.

“Ya kuke? Ya yara? Daman nazo wucewa nace bari in shigo mu gaisa in kuma duba Bukar.”

Wannan karin Dije tayi maganar cikin harshen fulatanci tana yawo da idonta cikin gidan da yake kaca-kaca, kwantsin kayan wanke-wanke ko ina, harda wata miyar kuka mai munin gani da ta zube a kasa, bakuma a damu da ko kasa a zuba mata ba, an bar wajen harya bushe kudaje sunyi dandazo suna shagalinsu.

“Lafiya… Baya gidan to.”

Wani rugugi Dije taji cikin kirjinta.

“Baya gidan? Yana ina? Ina yaje?”

Ta jero tambayoyin cikin taradaddi.

“Ina zansan inda yake ko inda yaje? Sun fita wasa da yara.”

Nana ta amsa a zafafe, Dije bata bi takanta ba ta juya tana nufar inda ta fito, dogon tsaki da zagin da Nana ta rakata dashi na isa kunnenta, amman bai mata zafi ba, batajin akwai wani abu da za’a fada ko ayi mata a lokacin da zataji zafin shi kwatankwacin zafin da takeji a kirjinta a lokacin. Bukar take hangowa a yawon gantali, irin gantalin da yaran gidan Baabuga sukeyi, ta tuna ranar da aka zabga da zafinta bai gushe ba har yammacin da take gabannin faduwa, ta kuma tabbatar zaiyi wahala idan da takalma a kafar Bukar, ko yaci abincin rana ko baici ba, wannan duk wani abune da bata da tabbas akai.

Hannu takai tana share zafafan hawayen da suka zubo mata, idan tabi ta bayan gidan Baabuga zaifi mata saukin zuwa gida, a maimakon tabi ta hanyar da ta fito, kusan zai zamana kamar tayi zagaye. Hawayenta sun kasa daina zuba, zuciyarta ta cunkushe da tunani kala-kala, gefen mayafinta tasa ta share hawayenta da suke hana mata ganin hanya da kyau, kiris ta fada kwatar dake bayan gidan Baabuga, bayan da tayi tana kusan take wani dan yaro da yake kwance jikin katangar gidan, yanayin kayan jikin shi da daudar su na nuna alamun cewa almajiri ne. Kai ta girgiza kawai tana tsanar iyayen da suka turo karamin yaro kamar wannan almajiranci.

Har tayi gaba ta dawo, bambancin rayuwar gidan Baabuga da wannan shine kawai akwai tabbacin zasu ci abinci, ko basu koshi ba za’a dafa sau ukkun nan, ko babu dadi rana bata taba fitowa ta fadi ba’a dora tukunya ba. Dan rankwafawa tayi tana kamo dantsen hannun yaron, zafin zazzabin dake jikin shi na ratsa kayan shi yana shiga tafin hannunta.

“Kai baka da lafiya ne ha…”

Sauran maganar ta makale mata bayan ta dago shi gabaki daya ta kalli fuskar shi, taga fuskar Bukar ko abinda yayi saura a fuskar tashi saboda bakin dauda da yayi, sumar shi da yake da yalwarta ta cakude kamar sabon mahaukaci, kafafuwanta taji sunyi sanyi har suna barazanar kasa daukarta, bangon wajen ta dafa tana kokawa da numfashin da take ja tana fitarwa a wahale.

“Bu.. Bukar”

Ta furta tana rabo hannunta daga bangon ta hada duka biyun ta tallafi fuskar shi tana dubanshi, tana duban gudan jininta, tana jin wata tsana ta taso mata tana zama a kirjinta, amman bata da wanda zata jefa da wannan tsanar, sai dai ta rarrabata a cikin jikinta, saboda itace sanadi, ita tabar rayuwar Bukar haka, itace bata tsaya tayi fada yanda ya kamata da Datti akan rike Bukar din ba. Dagashi tayi tana sabar shi a kafadarta, bata taba ganin nisan gidanta irin yau ba, harta karasa kuka takeyi, duk da maimakon ta shiga gidanta, gidan Abu ta shiga.

“Adda kinga Bukar…. Kalli Bukar dina Adda…”

Dije ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, tasowa Abu tayi tana karbar Bukar daga hannunta, zuciyarta na wani irin dokawa ganin yanda yaron yabi jikinta kamar babu numfashi a jikin shi, karasawa tayi ta kwantar dashi kan tabarma, jikinta ko ina yana bari, ruwa ta dibo ta dawo ta zuba a hannunta tana shafa ma Bukar din, zuciyarta take ji a tafin hannunta saboda tashin hankali, sai da tayi hakan kusan sau hudu sannan yaja wani dogon numfashi yana bude idanuwan shi da sukayi fari qal kamar bashida wadataccen jini. Ita kanta Abu saida ta sauke numfashin sannan ta samu nutsuwar mikewa.

Dije ta kama ta zaunar a gefen shi, tana gama tuwo ta cika wata tukunya ta dora kan garwashin da sauran itacen tabarta, tasan komin zafi Hammadi saiya kashe ruwa yake iya yin wanka, duk tsokanar da zatayi masa ba zai kulata ba.

“Hammadi kana bada maza, dan ruwan sanyin nan ba zaka iya watsa ma jikin ka ba, yanzun da yaki ne kuma fa?”

Idan yana jin biye mata zaiyi dariya ya ce,

“Yaki daban, batun wanka da ruwan sanyi daban, azo yakin mana kigani, sai dai labari yazo miki ana ga Hammadin Abu can yana zubar da maza.”

Kuma wankan nan biyu a rana sai yayi, kafin ya fita, sai kuma kafin ya kwanta, idan ta cika tukunya ta rufe, sauran garwashin yana rike ruwan zafin har lokacin da zai tashi wankan, saita kwalfe, idan yayi zafi da yawa ta sirka masa, idan baiyi ba tabar masa haka. Cikin wannan ruwan ne ta dauko bokiti ta diba tana sirkawa, ta dawo ta dauki Bukar, sai da tayi masa sabi uku tana tunanin anya tunda aka mayar da shi gidan Baabuga yaron nan kuwa yaga ruwa? Ita kanta saida tayi kwalla ganin daudar da take wankowa cikin kan yaron kawai, daudar da yayi kanta cuta ce ta daban.

Cikin kayan Julde ta samu wasa ta saka masa, ta shafa masa mai, sai ga yaro ya fara dawowa hayyacin shi, sai dai duk yayi kasusuwa, ga kuma zazzabin har lokacin bai sauka ba. Duk abinda akeyi Dije na zaune tana sharar kwalla, da ido kawai take bin Abu, harta sake hada wuta ta dama masa kunun kanwa da yaji sikari, dan tasan da wahala ya iya cin wani abinci mai nauyi, da kanta ta dinga bashi, baifi ludayi biyar ya sha ba ya girgiza mata kai yana komawa ya kwanta. Bata matsa masa ba

“Ki tashi kiyi alwala…”

Ta ce ma Dije da bata musa ba ta mike, tana tuna Yelwa na goye a bayanta, da yake bata da rigima, in kaji kukanta yunwa ce ko kuma an tsomata a ruwa za’ayi mata wanka.

“Ba zan mayar dashi ba Adda, sai dai in hakura da auren Datti, amman wallahi ba zan mayar dashi gidan Baabuga ya mutu ba.”

Ta karasa maganar tana goge fuskarta da bayan hannunta, jin saita shiga bayi yasa ta kwance Yelwa tazo ta kwantar da ita. Ko da tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah, ji tayi ita kanta bata yadda da ingancin sallar da tayi ba, saboda rabinta tunanin yanda zata fuskancin Datti ne, shisa ta kara sakewa, zaune tayi a inda tayi sallar har aka kira isha’i, ta mike ta gabatar da ita. Ko da Abu tayi mata tayin abinci kai ta girgiza mata, rikicin da take ji ya gama cika mata ciki, bata da wajen saka wani abu. Balle da taji sallamar su Dattin, muryar shi na danne ta Hammadi, alamar yana cikin nishadi, sai taji ta kara harzuka.

Saboda Hammadi ne kawai tayi musu sannu da zuwa, ko Julde da yazo ya fada jikinta daga shi tayi, girman Hammadi a idanuwanta na hana ta wanka ma Julde mari saboda ta fara batama Datti rai, sai yafi biye mata ko zata fada masa maganganun da zaisa zuciyarta ta sauka.

“Dagani dalla…kai baka san ka girma ba.”

Ta fadi tana sake ture Julde, da yake yana da kulafaci baiyi zuciya ba ya sake binta.

“Waye wannan a kwance?”

Datti ya tambaya yana zama kan tabarmar da Abu ta shimfida musu.

“Kai dai kuci abincin tukunna.”

Ta fadi da sauri tana katse Dije da ta numfasa ta bashi amsa, bai musa ba, abincin ta zuba tana kawo musu. Suna ci suna hirar da Datti yake kokarin sako Dije ciki ganin yanda ta koma gefe kamar bata gidan, hakan da yayi baisa ta kula shi ba, zuwa yanzun sai dai yaba wani labarin halayenta, ranta a bace yake ba sai ta fada masa ba. Bai dai san dalilin bacin ran bane, yasan bashi bane tunda lafiya lau sukai sallama da safe. Har sai da ya wanko hannun shi ya dawo ya zauna, ya dauki kwanon ruwa ya kafa a bakin shi kenan ya tsinkayi muryarta.

“Bukar ne na dauko, bashi da lafiya, na dauko dana, ba kuma zan mayar da shi ba…”

Tayi maganar tanajin wani daci a makoshinta, saida yasha ruwan shi sannan ya sauke kwanon yana kallonta, fitalar kwan dake ci a tsakar gidan bata haska masa fuskarta yanda yake so, amman yana fatan ita tana ganin fuskar shi, saboda taga yanda maganarta ba mai yiwuwa bace ba, ta karanci fuskar shi, ta kuma gani a idanuwan shi ba zai zauna da Bukar ba.

“Mayar da shi kuwa zakiyi, bashi da lafiya ba matsalata bane ba, na rigada na gaya miki ba zan rike shi ba, wallahi babu wanda ya isa yasani rike dan Baabuga.”

Ya karasa maganar yana mikewa ganin Hammadi na shirin saka musu baki.

“Idan ba zaka rike dan Baabuga ba, dana fa? Datti dana fa? Ko ka manta ba dan Baabuga bane kawai, nima dana ne, Bukar dana ne kamar yanda yake dan Baabuga, idan ba zaka rike dan Baabuga ba, ka rike nawa tunda nima ga naka nan ina rike da su…”

Wata dariya Datti yayi, dariyar da bata da alaka da nishadi, asalima kirjinshi ya dauki wani irin zafi da maganganun da tayi.

“Dije ni zaki gayawa Bukar danki ne ke da Baabuga? Ni zaki kalla kina fadamun ke da Baabuga dan ku ne? Ni?”

Rigar shi Hammadi ya dan kamo.

“Ka zauna Datti, ka zauna muyi magana gabaki daya…”

Mikewa Dije tayi itama, idonta ya rufe, ta dauki kunyar Hammadi ta ajiye a gefe, idan Bukar din ya mutu ta kula ita kadai take da asara ba Datti ba.

“Sai me dan na fada maka? Karya nayi? Gani nayi kamar ka manta shisa nake tuna maka… Yarone na dauko shi ba zan mayar da shi ba kuma wallahi, sai dai ka sawwake mun ni da shi duka sai mubar maka gidanka, in dire maka naka yaran ka nemo wadda zata rike maka su…”

Sosai yake kallon Dije yana mamakin yanda ta saka idanuwanta cikin nashi tana fada masa maganganun nan, akan Bukar, akan dan Baabuga, ita dinma a wa take? Ko igiyar data kulle su tare take ganin harta isa ta dinga gaya masa magana haka, duk fadin Marake da kewayenta babu wanda ya isa, ko Hammadi ba zai dinga kallon shi yana datsa masa maganganu irin haka ba, ko dauka tayi kamar inya rabu da ita karshen duniyar shine zai zo? Numfashi yaja, yana sauke shi akan fuskar Hammadi daya mike yana shiga tsakanin shi da Dijen.

“Karka fadi wata magana, idan har na isa, ni Hammadi na isa ina da wata kima a idanuwanka karka furta komai, dan Allah karka ce komai.”

Hammadi ya karasa cike da roko, jikin shi har kyarma yake saboda baya son tashin hankali, ba kuma yason ya zama shaida akan danyen aikin da zai iya faruwa idan Datti ya furta abinda Hammadin yake gani kwance cikin idanuwan shi.

“Wallahi ba zan rike mata Bukar ba, ko ita zata rike danta ba zatayi shi cikin gidana ba, Hamma gara ka fada mata, bata isa ba, Baabuga bai isa ba, dan su ma bai isa ba…ka fada mata ba’a gidana ba.”

Kai Hammadi yake daga masa, so yake ya dan natsu daga dokin zuciyar da ya hau.

“To sai me idan baka rike shi ba? Ba sai in bar maka gidan ba?”

Dije ta fadi, muryarta na fitowa a raunane saboda kukan da ya kwace mata, magana Datti zai sakeyi Hammadi yai saurin katse shi da.

“Ban isa ba nima ko? Datti ni dinma ban isa ba kenan.”

Shiru yayi yana wani irin maida numfashi, tabbas yau da babu Hammadi, da su kadaine a cikin gidan su, ko zai kora Dije gidansu zaiyi hakan ne bayan ya nada mata dukan tsiya, dan makwancin shi da ta gani yasa raini ya shiga tsakanin su, gara ya nada mata duka ya fara cire wannan renin kafin ya korata gidan su ita da Bukar din, in yado taga yanda zaiyi rayuwa shi da Julde da Yelwa lafiya kalau batare da ita a ciki ba.

“Dije kema biye masa zakiyi? Idan shi ban isa yaga kimata ba, kema hakan ne ko?”

Kai ta girgiza tana share hawayenta da bayan hannu.

“Hamma ni ba zan mayar da shi ba, wallahi mutuwa zaiyi a gidan Baabuga.”

Kai Hammadi ya daga mata.

“Ni zan rike shi, zai zauna a gidan nan…ni da Abu zamu rike shi, shikenan?”

Kai Datti yake girgizawa tunda Hammadin ya fara magana.

“Saboda me? Akan me zaka rike shi?”

Juyawa Hammadi ya yi.

“Saboda gidana ne, akan na isa inyi abinda nake so tunda ban isa kai in saka kayi ba.”

Takalma Datti ya zira yana ficewa daga gidan, komawa Hammadi ya yi ya zauna yana kallon Dije.

“Idan kin amince ni da Abu bamu da matsala da rike Bukar, kibar shi anan wajen mu… Dan Allah karki biyewa Datti kuyi abinda ba zai mana dadi gabaki daya ba…in dai akan Bukar ne kar inji bakin ki ke da Datti… Dan Allah Dije ki zama me hakurin nan da muka sani.”

Kai ta daga mishi, ta kasa magana saboda kukan da take tayi, duk da wani bangare na zuciyarta ya nutsu da sanin ko ita ba zata rike Bukar yanda Abu da Hammadi zasu rike shi ba. In dai a hannun sune tana da tabbacin matsalarta ta kare.

“Na gode Hamma… Adda Na gode.”

Ta fadi can kasan makoshi tana daga kai ta kalli Abu data share kwallarta, tun baya ita taso ace sun rike Bukar din.

“Ko zamu rikema Dije yaron nan ne Hammadi Am?”

Shiru ya yi yana juya maganar.

“Rike mata shi ba matsala bane kinsani, amman bana son mu shiga maganar tunda yaron bana Dije bane ita kadai, karmu saka mata rai Baabuga yaki amincewa, kinga zamu kara dagula mata lissafi, mu dai cigaba da mata addu’a… Allah ya kawo mafitar da duka zata bulle mana.”

Bata sake daga ma Hammadi maganar ba, duk rikicin da ake tayi, shima kuma bai sake daga mata maganar ba, taji dadin hukuncin daya yanke yanzun. Ka samu kyautar yaro amman rike shi ya zama wahala, su suna nema ido rufe, wasu sun samu suna watsarwa. Ita tanata kirga ranakune da taqi ganin saurin su don su cike da dan lokacin daya rage Hammadi ya dauko Saratu ta dawo karkashin kulawar su. Ko da ta wanke fuskarta, ta goya Yelwa zata tafi sai da Hammadi ya sake ce mata.

“Kiyi ta hakuri Dije, kinji, wata rana sai labari.”

Kai ta daga masa, zantukan shi na zauna mata. Sai da ta kalli Bukar da yake bacci, taga Julde daya kwanta a gefen shi, shima yana baccin, wani sanyi ya ratsa zuciyarta. Shikenan, hankalinta ya kwanta, amman data fita daga gidan tana shiga nata da yake a bude sai taji nisan nan da take ji a tsakaninta da Bukar ya dawo, katanga ce kawai ta rabasu, amman jin shi take can nesa da ita, ko da kafin a maida auren su da Datti, ga Bukar din a jikinta sai ta dinga jin shi can nesa da zuciyar shi, wannan nisan ne yasa ta tunanin ko shidin ba zaiyi tsahon rayuwa ba, ko alamune na cewar ta rike shi a jikinta iya yawan yanda zata iya.

Ta so shi da dukkan zuciyarta saboda ba zata samu lokaci mai tsayi tare da shi ba, numfashi taja tana mayarwa hadi da kauda yanayin daga ranta, abu daya a lokaci daya, yau dai nasara tata ce, zata maida hankalinta kan wannan ne kawai, kan yau kawai, ba zata daga hankalinta akan goben da bata gani ba.

Sai dai goben cike take da hargitsin da Dije bata hango ba.
Nisan.
Nisan nan dai shi Bukar zai mata.


<< Rai Da Kaddara 27Rai Da Kaddara 29 >>

2 thoughts on “Rai Da Kaddara 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×