Lokutta mabanbanta tana jin ana bada labarai akan soyayya, idan kafin aurenta da Datti ta dauka so wani nisantaccen abune da yafi karfin mutanen karkara, kamar so din nau'i ne najin dadi da bakowa yake da rabon samun shi ba, da yawan mutane, cikin su harda wasu a cikin 'yan uwanta mata, idan ana bada irin wannan labaran, ace an kalla a fina-finan hausa a binni, sai suyita dariya, suna daukar abin a matsayin shiririta."So ya wuce a baka ci, sha da suttura da wajen kwanciya?"Daya a cikin yayyanta ta taba fada, zantukan da suka zauna. . .
An interesting story please keep it up