2003
"Adee..."
Ya kira ta da sunan da Khalid ya saka mata tun lokacin baya iya kiran sunan ta, maimakon Fadila din sai ya gajarce shi zuwa Adee da kowa yake kiranta da shi yanzun.
"Ke bakya jin rana?"
Kai ta girgiza mishi, duk rashin magana irin ta Nawfal bai kai Adee ba. Dan ta ita duniya bata tashi ba, komai da sanyi-sanyi takeyin shi. Kusan ita ta kwaso jikin fulanin. Yanzun haka idan kaganta ita da Nawfal din babu wanda zaice itace babba, kanta da wahala idan ya kai kafadar shi, bata da tsayi kuma bata. . .
B