Hannu tasa tana share hawayen da ya zubo mata, wani irin zafi zuciyarta takeyi da ta manta lokacin da taji irin shi, filin da Bukar yabari na kara yi mata girma kamar babu kowa a duniyarta sai shi kadai
“Dan Allah kiyi hakuri Dije, addu’a zaki bishi da ita, Allah ya tsare shi duk inda zai shiga.”
Idan wutace take ci a cikin kirjinta, maganganun Abu sai suka zama kamar ta kara zuba mata itace ne a ciki.
“Me yasa Adda? Me yasa tunda na haifi Bukar babu abinda ya ke so sai nisanta da ni?”
Numfashi Abu ta sauke cike da neman kalaman daya kamata tayi amfani dasu wajen tausar Dijen ko zata samu sauki.
“Ji nakeyi kamar tunda na haifeshi ban huta ba, tunda na haife shi nake kokawa da ya zauna kusa dani, saboda ina ganin kamar hakanne kawai gatan da zan iya bashi…”
Kafin yayi wannan girman sai take jin bashi da zabi a duk wani abu daya danganci rayuwar shi, shisa take kokarin ganin ta zabar masa. Shisa tun farko bata son yana rabar gidan Baabuga.
“Ina so inje wajen su Madu.”
Da wannan ya fara, da wannan kalaman ya fara, ta so ta hana, har a kasan zuciyarta ta so ta rabashi da ‘yan uwan da jini ya hadasu.
“Um um Dije, karki fara, karkice zaki rabashi da su, yaron nan yana da hankalin daya girmi shekarun shi, duk yanda ba kyaso Baabuga ne baban shi, yanda duk zanyi kokarin maye masa wannan gurbin ba zai goge hakan ba, Bukar yasan Baabuga ne baban shi, hana shi rabar gidan zai jefa masa wasu tambayoyi a zuciyar shi da zasu rikita tunanin shi.”
Haka Hammadi ya ce mata, shisa tabari, shisa tabar Bukar yana zuwa gidan Baabuga, tunanin Bukar da Hammadi ya hango zai rikice idan ta hanashi rabar gidan Baabuga shine ya faru, kuma zata dora laifin a kanta ne kawai. Saboda duk zuwan da zaiyi ya dawo yakan zo mata da labarai mabanbanta, a bakin shi tasan kaf sunayen yaran Baabuga har wani lokacin tana kokarin dora fuskoki akan irin labaran su da Bukar yake bata. Tana so taga ko zata gane su adan zaman da tayi a gidan, amman sai ta kasa.
“Hamma ya dawo Daada.”
Hamma, Hamman shi da ko yazo ko baizo ba, baka raba bakin shi da ambaton shi
“Baka da wani Hamma daya wuce ni, idan zaka kira wani da Hammanka, nine Bukar”
Julde ya taba fada da yaji yana bata labarin Hamman shi kamar bashida wani mudubi na dubawa daya wuce wannan Hamman. Dan Julden ya bata dariya, ta dauka Saratu kawai take da kishi irin na Datti, don ko kaya bata so ayi mata iri daya da kowa, cikin wannan kowan harda Yelwa kuwa. Komai nata tafi son shi ita kadai. Julde bai damu ba, ba zakaga kishin shi ya nuna ba sai idan kaso ka nuna kamar kafi son wani akan shi, baya so sam, shisa take kokarin danne yanda take kaunar Bukar dan batason wannan kishin na Julde ya gifta tsakanin su. Bukar dinma a gaban Julde saiya daina bata labarin Hamman shi.
“Daada baki ji karatun da Hamma yake yi ba, kamar ya sammun wani sashi na kwakwalwar shi.”
A yanayin yanda yake yawan maganar Hamman shi ne tasan irin girman kaunar dake tsakanin su. Duk da Bukar ne, kowama so yake, kowa ma nunawa kauna yake. Amman kaunar da yakeyi wa Hamman nan nashi daban take, kuma da alama yana daga cikin manyan ‘yaran Baabuga da yakan tura neman karatu gari-gari, cikin wanda zamanta bai tsawaita a gidan shi ba balle ta san su.
“Hamma am fa ya haddace sittin, rubutawa yake yi yanzun.”
Bukar ya karasa maganar da yanayin nan mai cike da alfahari. Duk wannan kaunar bata dameta ba, a hankalima sai ta bude ido taji tana taya Bukar son ‘yan uwan shi, son Hamman nan nashi.
Da ta sani, in da tasan cewa wannan kaunar zata kawo su inda suke yanzun da tayi komai a karkashin ikonta ta yanke wannan kaunar
“Ina so zan bi Hamma Maiduguri inda yake karatu wannan karin Daada, ina burin yin karatu mai zurfi kamar na shi.”
Maganganun Bukar suka daketa, irin duka na ruwan saman da baka ga haduwar hadarin shi ba, bakaji yayyafi ba, karfin ruwan daya dirar maka kawai kaji.
“Ke na fara gayawa.”
Bukar ya dora kamar hakan ya isa ya dai-dai jirkitar da yayi ma duniyarta gabaki daya.
“Idan shawarata kake nema bana so kaje, idan ra’ayina kake son ji babu inda nake so kaje. Idan kuma gayamun kakeyi saboda ban isa ba Bukar kayi abinda kake so.”
Tace tana mikewa tabar masa wajen. Ta dauka zai hakura, har kasan zuciyarta ta dauka zai hakura saboda Bukar na da gudun bacin rai, nata fiye da na kowa. Amman kaddarar da take fisgar shi saita rinjayi komai. Da yaga daga Hammadi har Abu sun kasa shawo masa kanta saiya nufi Baba, Baba da yayi bata umarni a maimakon ya tausheta.
“Me yasa zaki hana shi tafiya tunda yana so? Namiji ne, idan karatu baisa yayi nisa da gida ba, wata rana neman na kan shi zai iya nisanta shi da gida. Ki godema Allah daya baki yaro mai hankali irin Bukar, ke in ba rashin hankali ba ai abin murna ne ace ya dawo da sittin akan shi.”
Hawaye takeyi da tun daga ranar har zuwa yau take jin sun kasa tsagaita mata. Banda nisan Maiduguri da Marake babu abinda take hangowa, yanda duk suke labarta mata kaurin sunan da yankin yayi a wajen ilimin addini mai inganci kunnuwanta basa karasawa da zancen zuwa zuciyarta. Shima Bukar din da ya ce,
“Ida na tafi ba saina gama zan dawo ba Daada, irin yanda Hamma yake yi zan dingayi nima. Duk bayan wasu watanni zanzo gida inyi sati kamar yanda yake yi.”
Jin shi kawai tayi, nisan da take ji yayi da zuciyarta na kara tsayi yana barin wani fili da batasan me zatayi da shi ba.
“Dan Allah Daada, bana so in tafi zuciyarki bata aminta da zuwan ba.”
Nan ma babu abinda tace masa, saboda karya bata taba shiga tsakaninsu ba, bata so ta fara. Ba zatace masa ta aminta ba, ba zata ce masa zatayi komai don yabar wannan tafiyar ba. Hankalinta bai kara tashi ba sai da tagan shi da kullin kayan shi, da tarkacen da Abu ta hada mishi, duk abinda take tunanin zai bukata, ita babu wani abu data tanada, tunanin ma baizo mata ba saboda tanata addu’ar Allah ya canza mata zuciyar shi, da kanshi ya ce ya fasa.
“Daada me yasa zai tafi? Dole sai can? Nan babu makaranta?”
Yelwa ta karasa maganar idanuwanta cike taf da hawaye.
“Shi ka zaba ko Bukar? Bayan nace maka ni kadai ne Hamman ka.”
Murmushi Bukar din ya yi yana girgiza ma Julde kai.
“Bashi na zaba ba Hamma, karatu na zaba.”
Su duka basa so, zuciyoyin su basu aminta da tafiyar ba. Babu yanda zasuyi da Bukar ne tunda ya kafe, suna ji suna gani ya tafi yabar su da kewar shi da suka fara tun kafin a kwana. Yelwa ma Saratu ce ta jata suka shige gidan Abu saboda kukan da takeyi. Julde ko raka Bukar kinyi yayi daga baya, sai da yaga ya bace mishi, ya sha kwana sannan ya bishi da gudu, ko ya dawo ba gidanta ya shigo ba, sai dai in ya shiga gidan Abu ne.
“Ki yi hakuri Dije, ki taushi zuciyarki tunda ya ce duk bayan wasu watanni zai dawo.”
Yanda Abu ta karasa maganar da wani nisantaccen yanayi a muryarta yasa Dije dagowa ta kalleta. Akwai kyallin hawaye a idanuwan Abu da taketa kokarin dannewa. Bukar ba daga jikinta ya fito ba, daga farko ma tana son yaronne saboda ya fito daga jikin Dije, saboda kaunar da takeyi wa Dije mai girma ce. Amman daya dawo hannunta sai ya tabbatar mata ko da Dije, ko babu Dije idan hanya ta hadasu zata kaunace shi, zata so shi wata irin soyayya da ba zata kwatantu ba. Rabon da tayi baccin kirki tun ranar da Bukar yazo mata da maganar yana so ya bi Hamman shi. Amman sai ta danne nata ciwon, ta danne nata zafin zuciyar saboda ta tausashi Dije.
“Adda”
Dije ta kira muryarta a karye, kunyar Abu na kamata, tunda aka soma maganar tafiyar Bukar ta manta cewa a hannun Abu yake, tama manta cewa itama Abu zata iya jin ciwon tafiyar Bukar din ko da bai kai nata ba.
“Muyi masa addu’a kawai… Allah ya tsare shi ya taimake shi.”
Kai Dije ta daga mata, tana sake share hawayen da suka zubo mata.
“Bari inje gida, yamma na yi in dora tuwo.”
Kan dai Dije ta sake dagawa, duk da taga hawayen da Abu tayi saurin daukewa da yatsa. Gara taje gida tayi nata kukan ko zata samu sauki itama.
*****
Rigar da Datti ya cire bayan ta dawo ta dauke daga kan gadon tana kokarin ninketa, sai taji kamar goro a cikin aljihun, hannu tasa ta ciro, harda dabino ma
“Ina ka samo goro da dabino?”
Ta tambaye shi, tana kallon inda yake zaune yana kokarin saka zariya a jikin wandon sakin dake hannun shi. Lokaci ya koya mata gujema duk wata magana ta Bukar a tsakaninsu. Saboda hakan baya jan komai sai fadan da suke shafe kwanaki bai kare ba, koma tace Datti yake shafe kwanaki bai daina ba. Bata da karfin biye masa, ta kowacce fuska sai da ya tabbatar ta gane fada ko jayayya dashi babu wata riba. Ko na rana daya bai nuna mata yasan Bukar ya tafi Maiduguri ba, baima nuna ya kula da baya nan ba, abin yayi mata ciwo na ban mamaki.
Amman a zaman su yana abubuwa da yawa da suke mata ciwo, abubuwan da ta koyi shanyewa tunda ko tayi magana a kai ba zai sauya komai ba. Hammadi da kan shi ya saka su Julde a makarantar allo, amman Julde sai ya yi sati biyu baije ba, randa Datti yaga sawun Bulala kwance a damtsen hannun Yelwa ya yi tashin hankalin da har saida Hammadi ya biye masa.
“Saratu ce kake son nuna mun ban isa da ita ba, sai kasa taje makarantar ita, amman ni dai nawa yaran dana isa dasu sun gama zuwa. Babu katon banzar da zai kamamun yara yana duka saboda karatu.”
Hammadi kyale shi ya yi, sai dai Saratu ta nuna ma Hammadi cewa abinda Datti ya ke so itama shi take so, abinda baya so itama bata so. Ko Abu ta tirsasa mata tafiya makarantar sai tayi rashin kunyarta da babu wanda ta cirewa hula banda Datti, sannan zata tafi, idan ta tafin ma ba makarantar take zuwa ba, waje take samu tayi zamanta har sai lokacin tashi tukunna
“Mtswww”
Tsakin da Datti yaja ya maida hankalin Dije kan shi.
“Hamma ne fa ya jani auren nan na wajen yar Dammud’o….lalataccen aure ma irin wannan.”
Kallon rashin fahimta Dije ta yi masa.
“Kad’o fa ya dauka yaba, yana bafullatanin usul ya dauki yarinya ya hadata da bahaushe, Allah tsine wannan hadin. Kinga son da nakewa Yelwa ko? Gara in binneta da in hadata aure da bahaushe, inyi kuka in hakura.”
Wannan karin a tsorace Dije ta kalle shi, maganganun shi na taba zuciyarta. Tasan baya son hausawa, wata irin kiyayya yake musu da batasan tushenta ba. Tunda a iya saninta babu abinda bahaushe yayi masa banda bambancin yare, bai kuma taba bata labari ko akwai wani abu daya taba faruwa tsakanin shi, ko wani nashi da bahaushe da yasa yayi musu wannan tsanar ba. Itama zuwa yanzun ta tabbata da bata biyo Innarta ba, da batayi kama da fulani ba, da bai yara mata yaji ta fahimta ba, yaji ta amsa shi, tun ranar farko daya ganta ba zai taba amincewa da aurenta ba.
Yaron da yake magana Dije ta tabbata in dai haihuwa da kuma girman Marake ne zai wahala ace bayajin fulatanci. Saboda cudanya da juna tasa har hausawan cikin ma suna yarawa, duk da kanayi Datti yake gane kai ba bafullatani bane, yakan ce suna bata wasu kalaman wajen furtawa.
“Bafa yare ake dubawa ba a wajen aure Datti, kyawun hali ake dubawa.”
Daga kai yayi yana dubanta.
“Yare zan fara dubawa, ko Julde ba zai auri bahaushiya ba.”
Murmushin takaici ta yi.
“To ai kai ka auri bahaushiyar, kuma jinin hausawa na yawo a jikin su Julde.”
Shima murmushin ya yi.
“Allah ya tsare su, bangarenki na fulani ne kawai tare da ‘ya’ya na Dije, bangarenki na fulani na aura, da kuma shi kadai nake cudanya.”
Sai taji ya bata dariya. Dariyar da shigowar Julde ta katse mata.
“Daada hannuna zai kone, ki fito ki karba.”
Yake fadi, don sallama bata cikin abinda yake yawaita yi don zai shiga waje, musamman idan yayi daga farko, to a wajen shi ta dauke ta yini guda ko zai shiga ya fita gidan sau goma.
“Ya za’ayi ka rungumo kunu a langa?”
Dije ta fadi tana karbar kwanon daya dauki mugun zafi daga hannun shi tana ajiyewa a kasa, baiko saurareta ba ya fice yana komawa inda ya fito. Harya shiga gidan murza hannuwan shi yakeyi a jikin rigar shi cikin yanayin da yasa Saratu fadin.
“Me ya sami hannun?”
Tana daukar kosai ta kai bakinta.
“Konewa nayi.”
Ya amsa a takaice, radadin da tafukan shi sukeyi na shiga har kwanyar shi. Tashi tayi daga inda take zaune tana karasawa inda yake tsaya, batare da tace masa komai ba ta kamo hannun shi guda daya tana ware tafin hadi da saka nata a ciki ta murza masa. Nata hannun yake bi da kallo da kuma yatsunta, yatsunta da suke dauke da farata farare qal, yanayin taushin su a cikin nashi kamar bata taba aikin wahala ba tunda take.
“Sannu… Muga dayan.”
Ta fadi tana sakin wannan, tsintar kanshi yayi da mika mata dayan hannun nashi, ta murza masa kamar dayan, tana cikin yine Yelwa da taje kai ma su Dije kosai ta dawo.
“Me ya same ka?”
Ta fadi tana karasawa ta janye hannun shi daga cikin na Saratu tana dubawa, sai dai bata ga komai ba.
“Konewa ya yi.”
Saratu ta amsata, sosai Yelwa take duba hannun nashi, ko da bai kone ba jar fatar shi tasa bata ga wani bambanci ba ita. Daga ido tayi tana kallon fuskar shi, amman ba ita yake kallo ba, hannunta yake kallo, a zahirance yafi na Saratu kyau, yafi shi komai. Amman baiji abinda yaji da nata yake cikin nashi ba. Shisa ya zare hannun nashi, so yake ya kara rike na Saratun, yaji ko yanayin zai kara dawo masa, yaga ko zai gane dalilin da zaisa yaji abinda yaji a karo na farko bayan ya tuna lokutta masu yawa da ya rike hannunta, amman a rijistar kwakwalar shi babu wannan yanayin.
Babu dumin nan da yaji ya ratsa ta cikin hannun nashi yakai ko ina na jikin shi. Ya taba hannun Yelwa yanzun baiji dumin ba. Hakan na nufin a na Saratu kawai yake kenan? Ji yayi yana so ya gwada, yana so ya sake jin dumin nan, yana kuma so yasan idan a hannun Saratu hakan ya tsaya ko kuma akwai wasu mata da hannuwan su ke da dumi kamar nata. Jin idan ya tsaya zai koma inda Saratu take ya riko hannunta yasa shi juyawa ya fice daga gidan.
Sai dai fitar shi ba zata sake kaddara ba
Fitar shi ba zata sake komai ba.
Komai da yanzun ne zai fara.