Yelwa take kallo, idanuwanta a rufe, Saratu da take gabanta tana mata kwalliya, ta diga mata kwallin daya fara tun daga goshinta zuwa karan hancinta, da alama digon zai dire ne har habarta cikin kwalliyar su ta fulani, bakinta ma a zane yake da bakin kwallin daya zauna das yana kara fito da hasken fatarta da kamar tana girma yana kara fitowa ne, girman su harya daina bata mamaki. Ba son kai Dije zatayi ba idan tace kaf kauyen babu mai kyawun Yelwa, ko da bata fada ba, mutane da yawa sun fada, ita da kanta wasu lokuttan gani takeyi kamar ba daga jikinta Yelwa ta fito ba.
Yanda take yanzun, kyawunta kamar an cirota daga cikin zane. Kallon ta Saratu ta danyi.
“Yawwa an gama.”
Bude idanuwa Yelwa ta yi tana saka su cikin na Saratu.
“Na yi kyau?”
Ta tambaya tana duba gefenta in da ta ajiye dan mudubin da ta dauka ta haska fuskarta, tana danyin far da idanuwa cike da son ganin yanayin yanda kwallin ya zanu cikin idon nata. Kayan sakine a jikinta farare da suka sha ado, sai sarkar su ta fulani shake a wuyanta, ta daura dankwalin da harya fara soshewa amman son da take masa yaki bari ta iya bayar dashi, Abu ce ta bata shi, ta manta ko tun yaushe. Amman tana son dankwalin, zanen ganye ne a jiki da koren su ya fito sosai.
“Muje?”
Ta fadi tana duban Saratu, ba zaka kirata mummuna ba, amman idan har tana tare da Yelwa babu yanda za’ayi ka ga nata kyawun, bata da hasken fata kamar na su Julde, amman kuma ba baka bace ba. tana da madaidaicin tsayi, yanzun da alamun ‘yan matanci ya fara nunawa a jikinta zaka ga kalar cikar halittar da take da shi, batayi sirantaka irin wadda aka san akasarin fulani da ita ba. Sai dai kallo daya zakayi ma yanayin fuskarta da bakinta da bata cika sauke labban ba, a dage suke kusan ko da yaushe, alamar dake nuna saurin fushinta da yanda take a shirya da ta mayar maka da magana idan har bukatan hakan ta taso.
“Wai Daada babu abinda za’a siyo miki?”
Yelwa ta sake tambaya a karo na ba adadi tana mikewa.
“Babu fa, kuma yawo ne zai kaiku ba don akwai abinda zaku siya ba.”
Kafin Yelwa ta amsa Saratu data juya idanuwanta ta karbe zancen.
“Ita fa kasuwa baka sanin kana bukatar wani abin saika shiga.”
Numfasawa Daada tayi batace komai ba, lokutta da yawa bata cewa komai in dai har zancen ya zamana tsakaninta da Saratu ne, tana da hakuri, amman bata son raini, tun kafin Saratu tayi girman da za’a daina amfani da yarinta ana ma rashin kunyarta uzuri bata cika son yarinyar ba. Zuciyarta ta kasa natsuwa da ita, sai halayenta suka hadu suna kara sakawa ta fita harkarta in ba ta kama dole ba. Ko Abu ta yiwa rashin kunya kau da kai takeyi. Tunda idan ta shigama babu wani abu da hakan zai haifar, saima fadan da Datti zai rufeta dashi idan yaji.
Akan Saratu sai ya manta wacece Abu, saiya manta yanda a ko ina ya kamata ace ya kasance cikin mutanen da zasu iya bada shaidar halayen Abu, sai ya manta cewar ko Saratu bata fito daga ciki Abu ba, ko da ba ita take riketa ba ya kamata ace tafi karfin Saratu ta kalleta ta mayar mata da magana ko don dattako da cikar kamalar da suke shimfide a fuskar Abun. Rashin kunyar Saratu irin ta Datti ce, babu wanda ya wuce ta a wajen su muddin tunaninsu ya basu cewa anbi takan sune. da farko Dije ta dauka Abu kadai take yiwa, sai a hankali ta kula da har Hammadi ma bai wuce ta mayar masa da magana ba, baifi ta hade rai tana surutai kasa-kasa idan yayi mata fada akan wani abu ba.
“Allah ya shiryeki Saratu, Allah ya shiryeki.”
Ya kan fadi cike da wani yanayi a muryar shi, komai. Banda fatan shiriya babu wani abu da zaka iya bin Saratu da shi. Sai kuma ido, kamar yanda ta bisu da shi daga ita har Yelwa har suka fice daga cikin gidan hannuwan su cikin na juna, bambanci shekarun su bai rage shakuwar da take tsakanin su ba, duk da kowa yasan kauda kan Yelwa na daya daga cikin abinda yasa ba’a yawan jin kansu. Suna karya kwanar gidan suna hango Julde, zuciyar Saratu ta doka a cikin kirjinta, dokawar da ganin shi kawai kan sa hakan ta faru. Tun kafin ya karaso yake musu murmushi, ko tace yake yiwa Yelwa murmushi.
Farin wandone a jikin shi da rigar saki, ya tara suma a tsakiyar kan shi, yayi kitso dai-dai a kowanne gefe na kan shi da ya saka sauran sumar a tsakiya, sai sarka ta wuri da take daure a wuyan shi. Banda kwallin da yake idanuwan shi babu zanen komai.
“Kai ba bororo bane ba…”
Datti yace masa ranar farko da yayi kitso, kujera yaja ya zaunar da shi, yasa almakashi yana saita masa sumar da ya tara ta daga gaba tafi sauran cika, ba kamar sumar Bukar da take luf ba, tashi a cunkushe take, kuma yafi sonta a hakan. Idan ya kalli sa’annin shi a Marake, ya kalli fuskokinsu yaga tsagun fulani reras saiya kara godewa Datti da bai musu wannan zanen a fuska ba. Daya taba tambaya haka yace masa.
“Da muna da tsage na gado da na ganshi a fuskar Babana, ko ta Inna ta, da kuma anyi mana kagani a fuskata… Fulanin yankin da muka fito daga shi sukanyi adon sune da kaloli daban daban a fuska a maimakon tsagar… Idan kana so sai in koya maka.”
Dariya kawai yayi, bayason komai banda kwalli a fuskar shi, wani lokacin Yelwa da ita take masa kitson kan saka masa wuri guda biyu ko hudu a jikin kowanne kitso, bashi da zuciyar da zai hanata.
“Hamma am.”
Yelwa ta kira shi tana fadada murmushin ta, tana kallon shi kamar duka duniya bata da wanda yafi mata shi. Shima murmushin yake mata, tilon kanwar shi da zai iya komai dominta.
“Ina zaki je?”
Ya tambaya kamar baiga Saratu tare ita ba, abinda yayi mata ciwo har kasan ranta. Da zata iya da ta dinga share shi irin yanda yake shareta, da tayi watsi da lamurran shi kamar yanda yakeyi da nata. Da ta ganshi taki ganin shi, ta ji shi taki jin shi. Amman ta kasa, idan ta gan shi babu abinda take so irin ya kulata, idan bai kulata ba zata kula shi ko da ba zai amsa ba. Ta taso tana jin labarin soyayyar dake tsakanin Hammadi da Abu, da ta fara hankalin fahimtar wannan soyayyar da bata boyuwa ga kowa sai taji tana son kwatankwacinta tare da Julde. Tana hankali tana kara rage abubuwa da yawa da suke kawo musu rashin jituwa tsakanin su, sai dai yana nuna mata kamar lokaci ya kure.
Yanzun fiye da lokuttan baya, yana tsaye a gabanta kamar yau din sai ta dinga jin tamkae idan ta kai hannunta zata iya dangwalo nisan da yake tsakanin su, nisan da kan sata farkawa cikin dare ta kasa komawa bacci. Yanda duk zatayi tunanin aure, tunanin kwana da tashi a gida daya da wani namiji, hoton Julde ne a wannan tunanin. Hoton da girman shi ya hana mata ganin duk wani matashi dake kauyen, wadanda suke son samun dama a wajenta da wanda ma bata gabansu.
Wani zare ta hango a gefen wuyan Julde da batasan lokacin da ta mika hannunta da nufin cire masa ba, ta gefen idon shi ya ganta yayi saurin rike hannunta yana saukewa hadi da kallonta, wani irin kallo da yasa tsikar jikinta mikewa tanajin kamar an buge mata gwiwoyinta ta baya saboda sanyin da sukayi. Ya sha kallonta, ba zata iya kirga adadin lokuttan da idanuwansu suka sarke dana juna ba, amman bai tana mata kallon da yake mata ba yanzun. Numfashi yaja ya mayar a hankali yana sakin hannunta, yanajin yanda sakin hannun nata shine karshen abinda yake son yi. Me yasa zatayi kokarin taba shi? Ko dan bata san yanda yake kokawa da kan shi a duk rana ba yanzun na ganin bata shiga cikin jerin matan da yake tabawa ba?
Saboda ita ce, saboda tabata zaiyi dai-dai da tonuwar sirrin da yayi shekaru hudu yana binnewa yanzun. Sirrin da babu wanda ya sani.
“Ba fa zaka bi motar Ikko ba Julde, ba zakayi wannan nisan ba.”
Datti ya fadi cike da yanayin da yasan bashida wajen musu. Yanzun ana kai musu amfanin gona da dabbobi har garin Kano, nacin daya dinga yi sai da suka hadu shi da Hammadi sannan suka shawo kan Datti ya bar shi ya fara bin motar Kano din, amman ba ko da yaushe ba, saboda in sunje din anayin har sati daya ba’a dawo ba, su kuma duk bayan watanni biyune ake kai musu kayan Kano. A garin Kano, iyakacin su Miltara da Dawanau. Zuwan shi na biyune ya shiga gari yawo shi da wani yaron babbar mota da suka hadu anan Miltara da ake kira da Danjuma. Yace ma Julde shi dan asalin Zamfara ne wani kauye da Julde ba zai tuna sunan shi ba.
Almajiranci aka turo shi kauyen Badume, fadi tashi yasa shi fara neman na kanshi harya soma bin motocin dake zuwa kudu, a haka ya zama yaron mota, da suke daukar kayan masarufi daga nan Miltara zuwa Legas da sauran jihohin kudu. Cikin irin wannan hirarrakin da suketa ba Julde mamaki har ya fara bashi labarin kauyen Tafa da yanda sukan yada zango anan idan zasu je Lagos ko garin Lokoja. Anan yaji labaran da tunanin shi bai taba kai shi ba, tare da Danjuma suka soma shiga sabon gari, Danjuma ya rike hannun shi ya hada dana Ladi a cikin sabon gari. Ladi da yake tunanin zai wahala idan bata girmi Daadar shi ba.
Sai dai tarin shekarun nan ta ajiye a gefe ta bude masa ido da wata irin rayuwa da ta amsa masa tarin tambayoyin da suka dade suna masa yawo a kai, suna kuma bude masa wani shafin guda na sababbin tambayoyin da ya kosa da yasan amsar su a lokacin. Duka matane kamar Ladi? Ko suna da bambanci? Da duk komawar da zaiyi Kano da yanda yake samun amsar tambayoyin shi. Sai dai kalubalen na tare da yanda yake son Datti yabar shi yabi masu zuwa Ikko, saboda ya leka yaga ya rayuwa a can yake, idanuwan shi su gane masa labaran da Danjuma yake ta bashi.
A cikin Marake kawai akwai mutane mabanbanta, haka ma yanda suke gudanar da rayuwar su. Amman idan ka duba akwai kamanceceniya saboda duka kauyen nasu da mutanen ciki bayajin sun kai yawan al’ummar daya gani a sabon gari. Idan kana waje daya babu abinda zaka gani, tun randa ya shiga mota suka hau titi zuciyar shi take gaya masa an haife shi a Marake, ya girma a Marake, amman dawwama a cikin Marake ba nashi bane ba. Saboda idan duk yabar kauyen babu wani abu da yake kewa banda ‘yan uwan shi da iyayen shi. Idan zai dauke su subar Marake yana da yakinin ko na rana daya ba zai taba kewar komai daya danganci Marake ba.
Sai dai yanzun ba zuwa Ikko bane babban kalubalen shi, yanda zaiyi da sabuwar rayuwar da ya koya. Yanda yake tashi da safe yaji babu abinda yake so daya wuce ya rabi mace. Macen da tafi kusanci dashi itace Saratu. Duk idan ya ganta sai yaji kamar tana kara hura masa wutar da take cine a cikin jikin shi. Shisa ya rage shiga gidansu, amman idan shi bai shiga ba ita tana shigowa nasu gidan. Yana ganin giccinta, ko bai mata magana ba zatayi masa ita, muryarta na fitowa a hankali kamar a tsorace take saboda bata da tabbacin zai amsata ko ba zai amsata ba
“Julde”
Takan kira wasu lokuttan, dan tun lokacin yarinta yasha buge mata baki akan ta kira sunan shi gatsau kamar shidin sa’anta ne, rashin kunyarta da son ganin ta kular dashine yasa ta cigaba har ta fara sabawa, kafin tace masa Hamma ana daukar lokaci. Idan ta kira sunan shi da wannan muryar sai yaji yana so ta maimaita, yana so yaji ta kara maimaitawa kamar yanda yake jin mata da yawa sun maimaita a lokutta mabanbanta a yanayi iri daya amman cikin muryoyi daban-daban.
“Hamma…”
Muryar Yelwa ta kutsa cikin tunanin shi
“Kuje abinku… Karku dade amman.”
Kai ta daga masa tana riko hannun Saratu da ta daga ido ta kalli Julde, sai taga kamar launin idanuwan shi sun canza, kamar akwai wani abu a cikin su da ya girmi fahimtar ta. Yelwa da take janta tabi suna nufar hanyar kasuwar. Har lokacin tana jin jikinta a sanyaye, hirar da Yelwa take janta da itace tasa harta dan warware kafin su karasa kasuwar da aketa hada-hada. Da yake sanyi ya fara zuwa ga sabuwar goruba nan da magarya kamar ba’aso
“Yelwa kinga magarya”
Cewar Saratu don tana so, duk da tana da sauran wadda Datti ya kawo mata, wannan din sai taji ta shigar mata ido.
“Wai dan Allah dadin me kikeji a abin nan? Nifa na tsani ki shata cikin daki wallahi, duk saiya gume da wari kamar an bude daddawa.”
Dariya Saratu tayi.
“Magaryar ce take warin daddawa? Saboda bakya so? To sai na siya.”
Saratu ta karasa wajen mai magaryar daya bajeta a cikin buhu.
“Aifa sai kiyita siya. Da rake ma muka karasa mukai cinikin sanda aka yayyanka mana muka tafi gida da yafi wannan magaryar.”
Saida ta siyi magaryar tukunna ta dago tana duban Yelwa dake tsaye tana ta bata fuska.
“In dai rake ne mu zagaya a duba me kyau mu siya… Daga shigowar mu harkin fara mu tafi gida kamar bake kika damu da muzo ba.”
Sake bata fuska Yelwa tayi, ita duk yanda zataji tana son shigowa kasuwa, da ta tako kafarta taga mutane cunkushe sai taji hayaniyar na shigar mata har tsakiyar kai. Bata cika son shiga mutane da yawa haka ba. Baki ta bude da nufin yin magana, abinda bai taba faruwa da ita ba ya faru lokacin da idanuwanta suka gifta ta gefen kan Saratu suna sauka cikin nashi, kalaman ta fara ji sun koma mata cikin makoshi tare da wata irin iska da tasa makoshin nata bushewa tana jin kamar ta yini bata kurbi ruwa ba. Bata san ta rufe bakinta ba sai da taji har harshenta ya bushe. Ta kifta idanuwanta ta sake budewa a cikin nashi a karo na biyu, zuciyarta tayi yawo a wajajen da bata san zata iya kaiwa ba a cikin jikinta.
Kirjinta na budewa daga ciki kamar yana son sanar da ita zuciyarta tayi nisan kiwo na wucin gadi, lokacin da ta dawo mazauninta sai ta zauna mata da zanen fuskar shi tarau. Bakine, gidan su babu wanda za’a kira da mummuna, a iya danginsu na kusa ma bata taba ganin mummuna ba. Ko mai kalar fata irin tashi basu da shi.
“Bahaushe ne.”
Zuciyarta ta furta mata, tana kasa cire idanuwanta daga cikin nashi.
“Wai me kike kallo inata miki magana?”
Saratu ta fadi tana waigawa, maganar da tayi na karya wani abu da Yelwa bata san ya gifta a tsakaninta da matashin Saurayin ba.
“Muje”
Yelwa ta fadi muryarta na fitowa daga kasan makoshi, sake waigawa Saratu tayi tana son ganin abinda ya dauki hankalin Yelwar har haka. Amman bata gani ba, shisa ta bita tana riko mata hannu saboda saurin da taga tana ta zumbudawa, amman sai ta zame hannunta, bugun da zuciyarta takeyi na amsawa a duka gabban jikinta, sai take ganin kamar Saratu zataji yanda zuciyarta take bugawa ta cikin hannun nata data riko, tafiya take tana saka kafafuwanta amman bawai tana da nutsuwar fahimtar hanyar bane balle kuma inda ta dosa. Da Saratu ta tsayar da ita gaban wasu masu rake, tsayawa ta yi.
Yau Saratu ta bari da cinikin raken, ta nutsu tana fatan bugun zuciyarta ya koma dai-dai. Lokacin da ta fara jin alamun hakan lokacin ne kuma wata murya ta ratsa cikin kunnenta.
“Sannun ku, rake zaku siya?”
Ya fadi cikin harshen fulatanci shi da kamar yana tsoron hada jimlolin karsu kasance ba dai-dai ba.
“Kayi yarenka mana, banson me yasa hausawa ke saka kansu a wahalar dole sai sun koyi fulatanci ba, banda bata kalmomin wajen furtawa babu abinda sukeyi.”
Maganar Datti ta dawo mata, yakan shigo da mitar lokutta da dama, harma yace tayi masa shiru idan taso fahimtar dashi cewa koyon yaren da ba naka ba akwai aiki a cikin shi. Juyawa tayi a hankali, zuciyarta na tsayawa na dakika kafin ta cigaba da dokawa kamar tana son fitowa waje. Idanuwan shi take kallo, saida yake dab da ita taga kankantar su, da tashi shima don da kadan ya fita tsayi, idanuwan shi sunyi kankantar da za’ace suna da zurfin nan da yake fisgarta.
“Sannun ki.”
Ya sake furtawa.
“Yawwa sannu… Wannan zaiyi zaki kuwa?”
Saratu ta amsa shi, dudduba raken data nuna yayi, kafin ya mika hannu ya zaro wata sanda yana cema mai raken.
“Yanka musu wannan.”
Yelwa tayi tsaye, ta kasa daina bin duk wani motsin shi da kallo, ta kasa aiwatar da komai banda wannan, saboda bugun da zuciyarta yake ya gama cinye duk wani karfinta, jikinta yayi wani irin sanyi.
“Yar uwarki bata magana ne?”
Ya tambaya yana murmushi, gefen kuncin shi na dama yana lotsawa, idanuwan shi na kara shigewa ciki.
“Tanayi… Yelwa ana Magana.”
Saratu ta karasa tana zungurinta. Numfashi taja ta baki a hankali tana fitar dashi ta hancinta.
“Yelwa…”
Ya kira kamar ya saba kira, kamar bashi bane karon farko daya lankwasa harshen shi da sunanta.
“Sunana Kabiru.”
Ya fada mata yana sake saka idanuwan shi cikin nata, yanayin nan na sake fusgarta, yanayin nan da yasata jin kamar akwai zurfi a cikin idanuwan shi da zata iya ninkaya harma ta nutse a cikin su.
Nan ne mafari.
Nan zaren kaddarar zai fara jan su.