Tsaye yake ba don babu wajen zama ba, idan ya juya a cikin gidan da zai iya kira da nashi yanzun sai yaji shi a cikin wata duniya ta daban. Duniyar da kamar idanuwa ya rufe ya bude ga ganta a ciki. Nisan daya hangone ya hade da shi kamar almara."Ba zabinka na tambaya a maganar auren nan ba Julde, umarni ne. Idan na isa kenan, idan kuma ban isa ba saika nuna mun iyakata."Ko da ya daga ido ya kalli Datti amsar daya bashi daga farko ita ya sake maimaitawa."Bana sonta Baba, bana son Saratu."Maganar. . .
Hmmm Allah Sarki Hammadi mutumin kirki
Allah sarki su julde, ai hammani babban shield ne a wajensu