Skip to content
Part 34 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Daga nesa suke jin labarin mutuwa, a wautar tunani irin nasa bata hango zumuncin mutuwa zai biyo takan wanda suka sani nan kusa ba. Sai dai kamar yanda ake fadine, rai bakon duniya. Musamman Yelwa da idan gari ya waye ta tashi, sai ta fito ta taka kafarta gidan sai taji wani abu a cikin kirjinta ya fadi, saita tuna shikenan, ba zata ga Hammadi ba, ba zai jata da hirar nan tashi mai cike da raha ba. Sai taji komai ya tsaya mata, a tare da kowa tana ganin yanda rashin Hammadi duk ya taba su, musamman Datti da yayi wata irin ramewa.

Tashin hankalin su duka ya karu lokacin da Abu ta gama takaba tace ba zata iya zama a gidan ba, duk kuwa Julde da Saratu da akasa suka dawo don kar kadaici ya dameta.

“Gidan yayi mun fili Dije, kinsan darare nawa na rufe idona da fadan kar in bude su? Ko zan tarar da Hammadi? Banda abinda zan cike ramin da Hammadi yabar mun. Idan ina cikin gidan nan babu ranar da mutuwar shi zatayi mun sauki. Ina bukatar shakar iska daban da wadda ta cudanyu da ta shi ko kirjina zai rage ciwon da yake mun.”

Watakila yanayin yanda tayi maganar ne, ko kasancewar ranar karo na farko da tayi wata magana data nuna halin da take ciki. Babu wanda ya iya hanata komawa gidan dan uwanta da suka karbeta suna kuma bata daki. Sai akabar Saratu da Julde a gidan kawai. Julde da yake jin kamar an dibi wasu shekaru an kara masa da rasuwar Hammadi saboda yanda abubuwa da yawa suka koma karkashin kulawar shi. Saiya zamana duk wani abu da Hammadi ke kula dashi na daga dukiyar su ya koma hannun shi, ciki harda gadon Saratu, tunda Abu an fitar da ita, komai ya koma karkashin kulawar dan uwanta da ta koma gidan shi.

Ya dauka girma a hankali yake zuwar ma mutum, tare da shekaru. Sai nashi ya dira batare da sallama ba, tare da auren Saratu da zuciyar shi ta karba a matsayin daya daga cikin kaddarorin shi duk da ya rasa yanda zaiji soyayyarta. Rasuwar Hammadi ta canza tsarin zamansu, batare da sanin dalili ba, ana fitowa da gawar sai ta fado mishi a rai, yanda ya kafafuwan shi suka dauke shi zuwa gidan ba zai tuna ba. Ya dai dauki mayafinta ya saka mata bayan ya kama hannunta ya mikar da ita.

“Lafiya? Me ya faru?”

Da duka sauran tambayoyin da take jera mishi muryarta cike da firgici na wucewa ta cikin kunnuwan shi da wani irin yanayi. Bai tuna ya rufe gidan ba, ya dai riko hannunta sun taho. Har yau idan ya kalleta sai yaga rashin tabbacin da ya bayyana akan fuskarta, kafin wani yanayi da ba zai taba mantawa ba ya maye mata gurbinshi hadi da gunjin kukan da zaka san ya fitone daga lungun zuciyarta. Bai sake sakata a idanuwanshi ba sai ranar bakwai din Hammadi.

“Kaje ka dauki matarka ku koma gida.”

Dije ta fada masa, bai musa ba, inda ya saka kafafuwan shi nan take mayar da nata a duhun daren da babu hasken komai saina farin wata da taurari. Sun koma gida, ya tuna hawayen da suke cike taf da idanuwanta lokacin daya kunna musu fitila.

“Hakuri zamuyi Saratu.”

Ya fada yana ba hawayenta damar zubowa, ya kama hannunta, ya jata zuwa jikinshi yana riketa cike da tausayin daya bude masa hanyar shigar wani yanayin da ya canza akalar daren nasu. Ta amsa masa tambayoyi da yawa, ta kuma sake tabbatar masa da abu daya, aurenta kuskure ne, kuskurene badan bata cika mace ba, sai dan ita kadai ta masa kadan kamar yanda ya hanga, irinta guda hudu sun masa kadan. Sai dai in duk bayan wani lokaci zai sake su ya sake auren wasu. Bai san ta inda zai fara kauda idanuwan shi da zuciyar shi daga kan wasu matan ba.

Kamar akwai wani abu a cikin jikinshi da yake saka shi jin son kasancewa da duk macen da zata gifta ta burgeshi. Ranar farko da ya labe a bayan ganin komai ya tafi dai-dai ya koma Kano, ya hada shimfida da wata ya tashi sai yaji kamar an dora masa wani dutse mai nauyi a saman kai, igiyoyin auren dake kanshi na masa wani irin dauri da harya dawo Marake bai sake shi ba. Musamman daya taka cikin gidan daya zama nasu yanzun, saiya ga kamar Hammadi na kallon shi, kamar bai rike amanar daya kamata ace yana rike da ita ba.

Sai dai akwai abinda yake fisgar shi da nauyin shi yafi na dutsen da yake ji ya danne shi, daurin shi ya girmi igiyar auren Saratu.

“Yan duniya na binni, kayi harkarka hankali a kwance baka da tunanin komai.”

Ya tuna zancen wani direban babbar mota a irin hirarrakin su. Shima haka ya dauka, sai da tura ta kai bango, matsi yayi matsi yanajin yanda Saratu tayi ma bukatar shi kadan. Lokacin ya fara abotar sirri da yaran da yake jin Datti na kwashewa albarka yana kira da ‘yan iska. Saiya fahimci ita lalacewa bata da wani layi a tsakanin binni da kauye, zabi kawai take bukata, na kaddarar da tafi karfin iko, ko na kaddarar da take zuwa da son zuciya. Saboda a cikin Marake da yake tunanin kowa ya san kowa, sababbin abokan shi suka tayashi binciko rayuwar da bai taba tunanin akwaita a kauye ba.

Kowacce rana a cikin tana kara busar masa da zuciya tana nisanta shi da tsoron kar wani ya binciko sirrikan da yake boyewa. Ya fara ninkayar da baya tsoron nutsewa sam, saboda a idanuwan Julde bashi kadai bane ba, mutane da yawa sunayi, wanda aka sani da wanda ma ba’a sani ba. A cikin wanda aka sani din surutun wani lokaci ne, musamman shi namiji. Maza nawane a kauyen aka kama da haura gidaje kuma maganar ta shude a cikin tarihi? Wasu sababbin labaran na binneta? Matan da sukayi cikine ake rabawa da kauyen ba mazan da sukayi musu cikin ba.

Daya daga cikin dokokin da al’ada ta shimfida da Julde yake ganin ba zai taba fahimta ba. Dokar tayi masa, saboda ta fifita zunubin da yake tunanin girma daya ne, a wani yanayin ma za’a iya kwashe kusan duka kason a mayar kacokan akan macen. Laifin da suka aikata da amincewar junan su zai juya ya koma kamar ita kadai tayi.

“Kudin shi ta gani ba komai ba.”

Wasu zasu ce.

“Julde fa dan gidan Datti, ko babu kudi tabi kyau.”

Ta kowacce fuska idan asirin shi ya tonu yana da yakinin mutane da yawa zasu nema mishi uzururrukan da zasu rage girman laifin shi. Lokaci kuma zai dishe musu hasken laifin har saiya zamana kamar bai faru ba. Kamar yanda lokaci ya fara saka shi daina jin nauyin laifukan shi. Shisa zuwa yanzun bai damu ba, lamurran shi yakeyi hankali a kwance, a gefe daya yana gudanar da harkar dukiyar su cikin basirar da ta dauke hankalin Datti daga sauran lamurran shi saboda ganin da yakeyi nutsuwar da yake masa hasashen samu tare da cikar kamalar da a ganin Dattin inuwar aure kan samar, ta tabbata.

*****

Yelwa zata kira sake haduwarta da Kabiru daya daga cikin abubuwan da suka fi karfinta, irin barin makauniyar da kaddara take yiwa mutane batare data duba ta ina takai dukan ba. Idan tace tunda ta hadu dashi daga farko bai dinga ziyartar tunaninta ba zatayi karya. Tana kwance, tana zaune, tana hidimar yau da kullum. Sai taji shi yana fitowa daga inda yake cikin dumbin tunaninta yana yo sama, yana sakata tunanin abinda yake dashi a fuskar shi da bata taba gani tare da kowa ba. Yanayin dake cikin kananun idanuwan shi da bata taba tunani ba. Sai mutuwar Hammadi ta binne mata shi har sai lokacin da ta sake ganin shi, ranar tana hanyar komawa gida daga aiken da Dije tayi mata.

“Yelwa”

Ya kira sunanta da murmushin shi, yana tuna mata da lobawar data kula bari daya na kuncin shine yakeyi duk idan yayi murmushi, kananan idanuwan shi na sake shigewa ciki. Bakine don baki, amman daga inda take tsaye zata iya kula da murjewar fatar shi da kyallin da yakeyi na alamar bai tashi cikin wahalar rayuwa ba ko da ba masu kudi bane, ba zasu rasa rufin asiri ba. A kasan yanda ya kira sunanta kamar ya santa, tare da murmushin shi kamar akwai wata alaka a tsakanin su.

“Daga ina haka?”

Ya jefeta da tambayar da tasata ganin karfin halin shi, har lokacin da murmushi a fuskarshi.

“Aikena akayi.”

Ta amsa tana tsintar kanta da dorawa da,

“Zan koma gida…”

Kai ya jinjina.

“Zan iya rakaki?”

Kafin ya gama rufe bakin shi ta girgiza masa kai, kirjinta na wata irin dokawa. Murmushin shi cike yake da fahimta.

“Ki gaida gida. Na gode.”

Ya fadi yana juyawa, tabi shi da kallo, kamar haduwar zata tsaya iya nan. Kamar ba zai samu wajen zama a zuciyarta ba. Kamar ba zata dinga neman duk wani uzuri da zaisa ta fita don kawai ta ganshi ba. Kwanakine suka dinga hadewa cikin satika har ta bude ido da soyayyar Kabiru da sanyin halin shi ya dasa mata. Mazan da suke cikin rayuwarta basu da yawa tun tasowarta. Datti ta fara dubawa a matsayin mudubi, sai dai tun kafin tayi hankali Hammadi yasa ta fara dora ayar tambaya akan halaye da yawa na mahaifinta, a cikinsu harda rashin hakurin shi.

Sai Julde da ya dauki taurin kai irin na Datti, amman idan ba ka kure hakurin shi ba, zaka dade baka ga bacin ran shi ba, sannan abinda duk yaso yi hanashi kan zama rikicin da rayuka da yawa sai sun baci. Sai Bukar, Bukar bawan Allah, Bukar da nisa bai sauya komai daga halayen shi ba. Ziyarar duk da yake kawo musu sai taga kamar yana kara yin sanyi ne, ko ta dan tsukun bayan rasuwar Hammadi sai da yanayin shi ya dawowa da kowa mutuwar sabuwa, saboda kuka yayi, kuka irin na maraici, kukan da zakayi zaton daga jikin Hammadi ya fito.

Harya koma duk idan ta ganshi sai taji kwalla ta cika mata idanuwa, saboda yanda yakeyin komai da sanyi-sanyi, yanda harya tafi mutuwar Hammadi bata gama sakin shi ba. Amman a cikinsu bata ga mai kama da Kabiru ba, bata san ta inda zata fara ba idan akace ta zayyana halayen shi. Watakila haka So yake, baka jin komai, baka ganin komai sai shaukin da kake ciki. A yanzun idan laifi Kabiru yayi zai wahala ta gani. A fuskar shi da mutane da yawa zasu kalla ba adadi kafin su ga abu daya me kyau taga tarin abubuwan da suka burgeta. Soyayyar da take masa ta kara haska mata abubuwa da yawa tare da shi.

“So banzan abu ne Yelwa.”

Saratu ta taba ce mata, kalaman sun bata dariya a lokacin, bata jin ta fahimce su, a cikin kanta basu da wata ma’ana. Amman yanzun sai ta kirga su, banda sunanta, kalmomi hudune suka tashi jimlar, kalmomi hudun da zata fassara a cikin shafuka masu yawan gaske.

“Nagaji da haduwa dake a wajajen da nake raba hankalin ki da duban hanya ko wanda kika sani zai ganmu. Nagaji da boyewa kamar abinda muke bashi da kyau Yelwa…ina son taka kofar gidanku.”

Ya fadi yana hargitsa zaman lafiyar da suke ciki, yana kusanto mata tshin hankalin da take hangowa daga nesa.

“Baba na…Baba na ba zai baka aure na ba.”

Ta fadi, kalaman na komawa cikin kunnuwanta suna sake hargitsa duk wani lissafi da yake tare da ita. Sai numfashinta ya soma yi mata barazana, idan ta shaki iskar sai taji bata kaiwa har cikinta balle ta karasa ta rarrabu a jikinta. Duk yanda tasan cewa Datti ba zai bar auren su da Kabiru ba, bata bar kanta ta hango meye makomar hakan ba.

“Kibar ni in gwada, ya zaka karaya da yaki tun bakasan su waye abokan karawarka ba?”

Ya karasa da nufin bata dariya. Sai dai ita da nishadi sunyi hannun riga a wannan lokacin. Jininta akan farce yake har juma’ar da Kabiru yace zai shigo Marake da dan uwan mahaifin shi kasancewar shi maraya, sai suyi masa jagorar tambayar aurenta a wajen Datti. Daren juma’ar na zama na farko data kwatanta sallar daren da taji ana yawan fadar anayi don neman biyan bukata, bata san raka’a nawa ya kamata tayi ba, goma ta fara, sai taga kamar tayi kadan, da ta fara jerowa saida gwiwoyinta sukayi sanyi. Akan dardumar ta kwanta, a karo na farko hawaye na silalo mata. Tana son Kabiru, wani irin so da bata da kalaman misalta shi.

Da safiyar ranar komai ta kasa ci.

“Kinyi zururu, baki da lafiya ne?”

Dije ta tambayeta, sai ta matsa jikinta tana kwanciya akan cinyarta.

“Kirjina ciwo yake Daada, kuma kamar zazzabi na son kamani.”

Da yawa zasu iya kiran shakuwar da tayi da yaranta a matsayin sangarta su, wasu ma suna ganin bata da kunya. Musamman yanda bata boye soyayyar da take musu ko a gaban waye. Har Julde da auren shi zai iya shigowa ya zauna a tabarma ya zame jikinshi ya dora kanshi a cinyarta.

“Daada na gaji.”

Yakan fadi, wasu ranakun zaiyi har bacci. A cikin su ukun, Bukar ne mai kunya, ko da kunyar shi bata hana masa kwanciya a jikinta ba, raunin zuciyar shi zai hana, zaiga kamar yayi mata nauyi. Tunda tsintsiyar shara bata dagawa idan har yana cikin gidan. Bukar dinta da kewar shi take cika zuciyarta lokutta mabanbanta, tafiyar shi bata taba tsaya mata irin wannan karin ba, ba don yanda mutuwar Hammadi ta tabashi ba, wannan yanayine da suma sun shige shi, ta kuma son a hankali ciwon zai ragu. Sai dai kewar tana nan daram, tunda kaunar da take tsakanin su mai girma ce. Kuma Hammadin ba irin mutanen da zasu dishe maka a zuciya bane ba.

Kalaman shine suke dawo mata suna nukurkusar ta.

“Me yasa son zuciya yayiwa mutane yawa Daada? Ashe dan uwa zai iya neman rayuwar dan uwan shi akan dukiya?”

Dan murmushi ta yi.

“Dukiya kace Bukar, mai hada iyaye da ‘ya’yan su…balle kuma ‘yan uwa.”

Numfasawa ya yi.

“Da irin dukiyar nan gwanda ace baka samu ba, in dai zata taba zumunci bata da wata rana.”

Sai dai Bukar bamai yawan magana bane ta wannan fannin, da wuya kaji cikakken labari a bakin shi, zai tattauna ne kan abinda yake tunanin ya shafe shi. Wanda bai shafe shi ba zai barshi.

“Wasu labaran bayar dasu bashi da amfani… Kai da ka bayar da wanda ya saurara inka duba duka ba zai amfane ku ba balle ku amfani madaukin labarin… To ina amfani bata lokacin da akayi?”

Shine kalaman shi inka nemi jin wani abu da akayi akan idon shi, ko aka fada yana zaune. Shisa bata tambaye shi dalilin da yasa yayi mata maganar ba. Watakila wani abinne daya ga ya faru acan Borno da yake karatu. Amman sati dayan da yayi maganganun shi duk akan cin amana ne da yake faruwa tsakanin ‘yan uwa. Sai da ya tafi take ta juyayin maganganun, tana neman tushen su. Hannunta da ya taba wuyan Yelwa na fisgota daga nisan da tunaninta ya yi.

“Ba zazzabi ke son kamaki ba, zazzabin kikeyi Yelwa…bari Julde ya shigo in fada masa. A dibo magunguna in dafa miki.”

Sake shigewa jikinta Yelwa tayi, yanda ta hade fuska tana turo baki na nuna rashin son maganinta. Shisa in ba lura akayi da bata cin abinci ba, tana kuma ramewa, sosai take kokarin ganin ba’a san bata da lafiya ba dan kar asa ta sha magani. Yau dinma dan rashin lafiyar ta wuce wajen jikinta, har a tsakanin hakarkarinta ciwo yakeyi, musamman kirjinta da yayi wani irin nauyi, shisa bata sake cewa komai ba. Wuni tayi a kwance, sallah ce kawai take fito da ita har bayan la’asar. Julde saida ya sake dawowa, amman tayi luf kamar bacci takeyi, kallo daya zai mata ya gane akwai abinda yake damunta daya girmi ciwon da ta fada.

“Wai bata tashi ba har yanzun?”

Ya tambayi Daada data girgiza masa kai.

“Tayi sallah, zazzabin ma ya sauka fa… Baccin dai ta sake komawa.”

Duka tana jinsu, kan tabarmar da ta saka pillow ta kwanta ya ajiye ledar kifin daya siyo mata tunda yasan tana so

“Allah ya kara sauki, kifi na dawo in kawo mata daman.”

Wani dan lokaci ta bashi da fita sannan ta mirgina ta tashi tana murza ido.

“Ga kifi nan Hammanki ya kawo miki.”
Dije tace mata, saida taje ta wanke fuskarta sannan ta dawo ta bude ledar kifin. Ta fara ci kenan duk da yau tashin hankalin da take ciki ko dandanon kifin bata ji. Ta zare kaya daga jikin wata tsoka da tayi nufin kaiwa bakinta Datti ya shigo babu ko sallama, ta daga ido ta sauke akan shi, kallon da yake mata na tabbatar mata da karshen duniyarta na gab da zuwa.

“Waye Kabiru? Ke kika turamun shi?”

Dan kifin da taci ya hargitse a cikinta yana barazanar dawowa.

“Kabiru kuma?”

Dije da take kwashin tuwo tayi tambayar cike da rashin fahimta, amman Datti bai amsata ba, Yelwa yake kallo da duka alamunta ya tabbatar da zargin shi. Ya dauka ya fara dawowa dai-dai, bayan mutuwar Hammadi nan kusa babu wani abu da zai hargitsa shi. Yana zaune karkashin bishiyar da sukan zauna da Hammadi lokutta da dama, aka zo masa da maganar yayi bakin da suke neman shi. Mu’amala ta kasuwanci ma sai an tona za’a kirga sanda ta hada shi da wani kabila, saboda yanda yaki jininsu, musamman hausawa da duk wanda yaci karo dasu basu san ya kamata ba a idanuwan shi.

“Daman dan wajena ne yaga yarka, muka zo neman izini.”

Mutumin ya fadi bayan sun gaisa ya zayyana masa daga shiyyar Kano suke, kauyen Bebeji, ya kira kanshi da Malam Lawalli.

“Ban mata miji ba, amman bahaushe baya cikin tsarin kalar wanda nake so.”

Ya tuna amsar daya basu a zafafe duk kuwa yanda yaso ya tausasa kalaman shi, yanda yake ta kokarin danne zuciyarshi a lokuttan da yasan Hammadi zaiso yayi hakan. Sai Malam Lawalli ya tsaya neman yi masa bayani harda kawo masa wasu zantuka da larabcin da bayaji yana kokarin fassarawa da hada masa da fulatanci cikin yanayin daya kara harzuka shi. Ba zai tuna duka abinda ya faru ba, amman yana sane da karshen, karshen daya ja kunnen Malam Lawalli akan kar hanya ta sake hada Kabiru da ‘yar shi.

“Ina son shi Baba…Kabirun, ina son shi.”

Yelwa ta fadi cikin wata murya da take jin ta fito daga kowacce kusurwa ta zuciyarta, kafin ta sadda kanta kasa hawayen ta na samun zubowa.

“Wani a cikin ku yaimun bayanin da zan fahimta, waye Kabiru?”

Dije ta fadi tanajin wani tashin hankali na dirar mata, yaranta suna da tasu rayuwar da bata san da ita ba, ta jima da yarda da haka, tun lokacin da Julde da Yelwa suka fara tasawa suka koyi shawara da junan su, suka koyi adana sirrikan juna suna wareta a ciki. Hakan bawai yana mata dadi bane, a matsayinta na uwa tana son sanin duk wani abu daya shafe su, mai muhimmanci ko akasin haka. Amman ya zatayi idan suna ganin sun ishi juna a wasu lamurran? Suna ganin kamar ba sai taji ba? Sai dai in ta fahimta wannan ba karamin abu bane, ba lamari bane da ya kamata ace ya tsallake saninta.

“Bahaushe ne.”

Cewar Datti da duk wata tsana da zai iya. Kamar yaren Kabiru ya isa ya zama dalilin da zata fahimta.

“Na sani.”

Ta amsa tana saka idanuwanta da suke cike da hawaye ana Datti.

“Ki fita idona Yelwa, ki kiyaye ni wallahi…ki zabi ko dan waye kaf Marake da tsallakenta, daga kabilarki, yarenki, ki zabi kowa indai bafullatani ne zan bashi. Banda wannan.”

Ya karasa maganar a tausashe, cike da son ta fahimce shi, hawaye wani na koro wani haka suke saukar mata. Ji takeyi rabuwa da Kabiru dai-dai yake da fitar numfashinta.

“Dan Allah Baba, shi din dai.”

Takawa Datti yayi yana zama gefen tabarmar da Yelwa take, su duka sunayin kamar basa jin me Dije take cewa, shisa ta dauki ido ta saka musu tana ganin Ikon Allah, zuciyarta na cigaba da lugude a cikin kirjinta.

“Yelwa bahaushe ne, bahaushene.”

Datti ya sake fadi kamar zai kamata ya jijjigata ko zata fahimce shi.

“Yana da halaye masu kyau…”

Itama tace tana so ya fahimceta.

“Yanajin fulatanci.”

Kai yake girgizawa, ba zai iya ba, hada jini da hausawa, ya tsane su, tsanar da ba kowa bane zai fahimta.

“Bana sonki dashi, umarni ne…”

Ya karasa maganar yana mikewa, kanshi sarawa yake saboda tashin hankali, tilon ‘yar tashi zai dauka ya mikawa bahaushe? Abinda ya guda kenan shisa ya hada Julde da Saratu, sai Yelwa ta kwaso masa? Duk samarin dake Marake sai bahaushe? Saboda ta hargitsa masa lissafi? Ba zata barshi yaji da kewar Hammadi ba, saita kara masa da wannan maganar da tashin hankali ce a wajen shi, ganin yanda take kuka na kara saka kirjin shi daukar dumi, akan bahaushe? Shisa ya zabi ya tsoratata.

“Allah ya isa tsakanina dake idan kika kara kula shi Yelwa…”
Kalaman suka fito masa suna tsayar da duk wani sauti da ke cikin gidan, suka dirar ma Yelwa da wani yanayi marar dadi.

Ya zatayi da kaddarar da ta kullu a tsakaninta da Kabiru tun kafin samuwar su?
Ta ina zata fara da abinda baya karkashin ikon ta?

<< Rai Da Kaddara 33Rai Da Kaddara 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×